Showing 114001 words to 117000 words out of 206525 words
saboda sunsa mutuwar aransu saide Dole suka fara hakura tunda sunsan bazai dawoba yan niger motoci biyu sukazo bayan sadakar uku suka koma amma minata da tuwasai sunce baz
asu ba sai bayan arba'in Sardauna saida akayi sadakar ukku daket ghaisha ta matsa masa, suka koma gidansu saide kullum idan sunzo sai dare suke komawa, yarame sai fari da ya kara ya tara k'asumba Nisha ma tarame dan mutuwar ta shigeta dadinta daya har yau
Sardauna bai kusancetaba bangaran zee baby har yau bata farkaba tsawon sati daya hankalinsu ba karamun tashi yayi ba ummi har tagaji da kuka tanaso tace abata ita sutafi saudiya amma ta kasa ganin yada suke nuna damuwarsu akan zainab gashi suna tatalin umm
in da kwantar mata hankali duk da suna cikin tashin hankalin mutuwa akullum Sardauna so uku yake zuwa dubo zee tanada rai lokacin farkowarta ne baiba
da misalin karfe biyar na yamma Sardauna na zaune cikin parlon yana kallon tashar Sunnah TV zauwarsu
Kenan daga gidansu"Nisha ki kawo mun mana" gani fah yi hakuri Rabia ce take aiki agurin na nuna mata wani abune zama tayi kusansa ta kafa masa cup glass d'in abaki ya kurba yana yamutsa fuska jikinsa ta kwanto" my Dr yi hakuri kasha please kaifa kace na ha
doma coffee mai dadi muyi hakuri babu yada zamuyi da hukuncin Allah amsa ya rikayi tana bashi abaki yanasha idanunta sun ciko da hawaye Sardauna ko tunda ta rumgumeshi yaji yana bukatar kusantarta dan satin da yayi tashin hankaline ya kauda masa sha'awarsa
amma yanzuma sam bazai wani iya tabuka komaiba bashida kwanciyar hankali mutikar baiga zee baby ta farka ba bayan ya shanye coffeen ya rumgumeta gam yana sabke ajiyar zuciya"Nisha kibar kukan mu amshi kaddara da hannu biyu kara shigewa jikinsa tayi tana b
uga bayansa itama
alamar lallashi wayar Sardauna ta dauki ringing idanunsa ya bude ya kalli screen d'in wayar yaga Dr Nabeel da sauri cikin rawar jiki ya dauki wayar gabansa na faduwa yayi picking ya kara, akunnensa" hello Dr meya faru? " Dr Sardauna k
ayi kokari kazo yanzu na'urorin jikin zainaba Faisal Hashim Almahadee sun dauki ruri alamar ta farka ai bai tsaya, sauraren karshen zancanba ya janye Nisha ya zaunar da ita"Nisha natafi hospital sai nadawo key din mota ya dauka, aguje ya fice Nisha hankali
nta atashe tana Addu'ar Allah yasa dear dinta ce ta tashi Sardauna yana shiga mota ya figeta da karfin gaske kafin ya ISO mai gadi ya bude masa get ya fice aguje wani irin gudu yakeyi Allah ne ya kawoshi hospital lafiya ko parking bai gama yiba ya bude ya
fice aguje ya yashige direct d'akin da zee take mai cike da na'urori ya nufa har likitoci sunyi tsaye kanta, yana zuwa suka matsa gefe kowa ya fice dubata ya fara ko minti uku baiba ta fara motsi tana fizge fizge cikin farin ciki Sardauna ya riketa gam yan
a kuka "Zainab ina mutikar farin ciki da farkawarki kanwata yau tsawon sati gudu banaci bana sha saboda rashin Abu biyu masu mahimmanci arayuwa sosai yake kukan farin ciki ya matseta jikinsa har ta daina fizge fizgen amma idanunta arufe hawaye yana kwarany
a saman fuskarsa ya zuba mata manyan idanunsa cike da tausayinta ya zauna ya cire mata na'ururin ya rumgumeta gam ya kirata"zainab tashi bude idanunki kinji ahankali ta bude idanunta ta sabkesu akan Sardauna tayi masa kuri da idanu murmushi ya sakar mata h
awaye fuskarsa suna zuba saman fuskarta " zainab sannu ya jikinki da idanu ta kafesa ko giftawa batayi "my kanwas bazaki mun maganaba ya fada yana langwabe kai yana sakar mata murmushi ga hawaye na kwaranya daga idanunsa duk dan ya saka mata kwarin gwiwa m
urmushi ta sakar masa ta dora hannuta saman fuskarsa ta shafo hawayen ta langwabar da kai ahankali kamar mai koyon magana tace" my kanwas bazaki mun maganaba ta fada tana sakin murmushi kara rumgumeta yayi hancinta yaja" banson raini ni sa'an kine murmushi
ta saki ta beka hannuta saman dogon hancinsa ta ja tace" banson raini ni sa'ankine idanu ya zaro" my kanwas ni ko itama tazaro manyan idanunta ta tsaresa da kallo tace "my kanwas niko gaban Sardauna ne yayi wani irin faduwa da Sauri ya janyeta daga jikins
a ya Mike tsaye ya kw
antar da ita ya jona mata wata na'ura akanta ya nufi gun wata na'ura da gudu dan ya kunnata ya binciki zee tashi tayi ta fashe da kuka tana kokarin cire na'urorin jikinta da ya jona mata dan tabishi arikice ya nufo gunta "zainab tsaya
ganinan..............
✍
🏻
💃🏻
Ladingo Yar ilu
*
💖💖👩🏻
🦱
ZEE BABY
👩🏻
🦱
💖💖
*
MALLAKAR UMMU FAREESA NE
*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*
*Allah Nagode maka da yan uwa musulmai da suka sanya bakunasu masu Albarka w
ajan yin Addu'a har Allah ya fitomun da fareesa lokacin da bamuda tsammani hakika Allah abin godiya yan grp dinan ina godiya sosai da gudun muwar da kuka bada wajan yin Addu'a*
*
👉🏻
42*
....cikin sassarfa ya karaso gareta ya riketa ya mannata jik
insa yana buga bayanta" zainab ki tsaya mana kukan me kike babu inda zani shiru tayi ta kwanta kirjinshi ta d'ago da kanta tana kallonsa murmushi ya sakar mata" my kanwas murmushi ta sakar masa hawaye nabin kumcinta cikin sanyin murya tace"my kanwas lumsas
sun idanunsa ya zuba mata zuciyarsa na wata irin bugawa ya tallabo kanta hawaye yacika masa idanu ya lakuto. hawayen fuskarta ya lasa" my zainab meyasa zakimun haka me haka yake nufi menene ya faru dake please idan wasane kike ki dainamun kinji murmushi ta
Saki ta zuba masa manyan idanunta ta beka hannuta ta shafo hawayen fuskarsa ta lashe ta rike fuskarsa ta maimaita abunda ya fada mata da sauri ya Mike ya cire mata na'uran da ya jona mata ya zaunar da ita ya juya ya nufi gun wata na'ura aikuwa ta fashe da
kuka da Sauri ya dawo ya ware mata hannunwasa tazo gareshi Sam batasan
hakanba Dole yazo ya Sanya hawansa ya dauketa kamar baby ya rungumeta " to yi shiru kallonsa take tana shashekar kuka tace"my Kanwas" Na'am my Kanwas please kimun rai kibar kukan
ahaka tana jikinsa ya nufi gun Na'uran ya kunna ya dawo bakin gadon ya kwantar da ita harzata fara kuka taga ya zauna tayi shiru jona mata Na'urorin wayarsa ya dauka ya kira Daddy bugo daya ya daga da sallama "assalamu alaikum Dr Allah yasa muji alkhairi"D
addy" please kuzo yanzu hospital harda momyna da ummi duk kuzo kuga hukuncin Allah ya sake sabka akanmu Allah yasake Dora mana wata jarabtar arikice daddy yace" Sardauna meke faruwane? " Daddy sai kunzo kitt ya tsinke kiran ya kwantar da zee da ta tsareshi
da idanu ya shiga duba lafiyarta, su Daddy sunzo suna waje saida ya kwashe awa daya cur ko ina na jikinsa rawa yakeyi sai sunayen Allah yake kira ya cire abun da ya jona akunnesa dabas ya zauna ya cire mata na'uran ya zuba mata idanu kukanma ya kasa Nabe
el ne ya kirasa awaya su Daddy sun matsu suga zainab yace ya kawosu, kofar aka turo da sallama ya amsa ghaisha da ummi da gudu sukayi gun zee ai tana daga kwance taga mutane na nufota akidime ta Mike zaune ta fashe da kuka ta fada jikin Sardauna tana kark
arwa ta boye kanta acikin kirjinshi
tana kiransa" my kanwas rungumeta yayi yana buga bayanta ya Kara boyeta jikinsa sosai tamkar cinyeta zasuyi hankalinsa atashe yace" baby yi shiru bari kukan lafewa tayi jikinsa ta rikeshi gam tayi shiru ta lumshe idan
unta ya kalli su daddy " wlh Daddy akwai babbar Matsala batasan kowa ba fah ayanzu sai ni sabode tayi losing memory ta mance kowa da komai nata na baya sai Wanda za'a koya mata yanzu da ita da Wanda aka Haifa yau basuda banbanci Nima abinda yasa ta yarda d
ani saboda tana bude idanunta nita fara gani ita atunaninta babu kowa cikin duniya sai mu biyu daddy yace "innahlillahi wa'innailaihi Raji'un Allah mun gode maka kuma mun amshi jarabawar da kake bamu ummi Raiyan fashewa tayi da kuka ghaisha ta rungumeta"ki
yi hakuri Raiyan zata samu sauki da yarda Allah kinsan bawa baya wuce kaddarasa Daddy yace"Raiyan don Allah kiyi hakuri zata warke insha Allah daddy yazo bakin gadon ya zauna "Dr yanzu yaya za'ayi fitar da ita za'ayi k'asar waje ko yayane?" Daddy zata wark
e insha Allah akwai maganin da zan dorata akai da yarda Allah lokacin da yaso zata dawo haiyacinta koda yaushene babu yau babu gobe ghaisha taja hannun ummi Raiyan ta zaunar da ita saman kujera ta nufi gun Sardauna ta dafa kafadunsa"Dr Sardauna yanzu ya za
muyi momy ta saba damu ta yarda murika koya mata abubuwa? Daddy yace tashin hankalin kenan, ai
Sardauna ya furzar da iskar bakinsa ya kalli zainab da tayi luf ajikinsa idanunta arufe ta rikeshi gam kamar zai gudu murmushin karfin hali yayi"Daddy muje g
ida yanzu sai nasamu nayi Mata yan dabaru ta yarda da ummi saboda ta Rika koya Mata abubuwa idan yaso zan kasance ina bata abunci da magani mu dage dayi mata Addu'a zata warke Dr Nabeel yace" Dr ayanzu yarinyarnan bazata iya rayuwa da kowaba sai dakai sabo
da kaika dai take gani mutum Dan uwanta Sardauna ya kalli Dr Nabeel "Dr kaje ka dubo mun irin magugunan da ya dace mu dorata akai ka kawomun kai Nabeel ya d'aga ya fice ghaisha kukan tausayin zeey ne ya kufce mata Sardauna yace"momy kiyi hakuri Adfu'a zaku
mata ba kuka ba janyeta Sardauna yayi daga jikinsa ta bude idanunta ta saka masa kuka"baby tare zamu yi hakuri sabkota yayi daga saman gadon ya shidota k'asa ya rike hannuta boyewa tayi abayansa tana rike da rigarsa daddy yace"Allahu Akbar
Allah ya ba
ki lafiya Sardauna yace"Amin ya kwashe wayoyinsa ya kalli iyayan nasa" Daddy mutafi gida asamu tayi wanka taci abunci mik'ewa sukayi Sardauna yana rike da hannuta ya rigasu fita waje zainab na rike da rigarsa har suka fito yana jiran Nabeel kafarta ya kal
la ba takalmi ya cire na kafarsa " baby bari nasamiki nawa sakarmun Riga idanu ta zuba masa dan bata gane me yake fadiba ahankali ya cire hannunta daga rigarsa ya sunkuya gabanta ya kamo hannuta ya dora akafadarsa ta rike tana dariya ya kamo santaleliyar k
afarta fara tas tamkar ta jarirai dan taushi ya saka mata takalminsa sun mata yawa sosai murmushi yayi ya Mike tsaye ya dagota dariya tayi ta fada saman faffadan kirjinshi tace"my kanwas? rungumeta yayi"Na'am my kanwas kallonsa take tana murmushi shima ka
llonta yake baima San iyayansu sun fito ba da kallo suka bisu daddy ya jinjina kansa yanajin dadin yada Sardauna yake kula da zeey Dr Nabeel ne ya ISO
da leda ya hado Wanda suka samu dafa kafadar Sardauna yai "Dr gasu kallon Nabeel yayi ya beka hannu y
a amshi maganin"OK zan duba idan mun isa gida thanks Dr murmushi Nabeel yayi" ai munatare uban gidanmu kai Sardauna ya girgiza ya kalli daddy" my dady mu tafi ya janye zainab ya kama hannunta ummi Raiyan hawaye ya cika mata idanu yau gata ga zainaba amma b
atasan taba Sardauna yace" dady kuje gamunan zansa takalmi a Office "to sai kunzo Dr hannuta yaja suka nufi Office d'insa ya ciro makullai ya
bude yana rike da hannunta suka shiga idanu take zarowa tana kallon ko ina na Office d'in sakin hannuta yayi y
aje yasa takalmi da gudu ta biyoshi ta rungumeshi ta baya tace "my kanwas" Ya Salam ya fada yana juyo da ita gabansa ya rike kafadunta ya zuba mata tsumammun idanunsa"baby babu inda zani takalmi zansa kai ta langwabe tana turo baki sakinta yayi ya kama han
nunta sukaje yasa, takalmin ya riko hannuta suka fito ya rufe Office d'in suka fito tana rike dashi gam har gurin mota ya bude ya zaunar da ita agaba ya rufe da ya zagaya ya shiga idanunta har sun tara kwalla yana zama ta kifa kanta saman cinyarsa ta fashe
da kuka tana kiransa"my kanwas"Ya
Allah gani gareka baby ya zanyi Dole fah zamu rabu tunda ba guri dayaba zamu rinka kwana dake ba please ki daure kisaba da rashina ah irin wannan lokacin jikinsa ya janyota yana bubbuga bayanta yakai bakinsa kunnenta"
yi shiru baby nine nataba Habibty shiru bazan sake barinki ba ina tare dake baccine zai rika rabamu lafewa tayi jikinsa tanajin dadin maganar da yake mata akunnenta ta lumshe idanunta ta kamo hannunsa ta rike cikin nata gam jin tayi shiru yayi murmushi ya
janye bakinsa ya gyara mata kwanciya jikinsa ya tashi motar ya nufo bakin get horn yai aka bude masa get ya fice ana ta daga masa hannu driving yake cikin nutsuwa zuciyarsa babu dadi damuwa tayi masa yawa ga zainab cikin halin da take ayanzu tana bukatar
kulawarsa hannusa da ta rike janye ya dora saman kanta ya shafi gashinta" my baby kanwas kara shigewa jikinsa ta d'ago da kanta tana lumshe masa idanu muryata can k'asa tace"my baby kanwas kallota yayi ya daga mata
gira ya maida hankalinsa kan driving ta
maida kanta kirjinshi ta lumshe idanunta Nisha ta kirasa,har sau biyu bai dagaba ahaka har suka ISO gida horn yayi aka bude masa get ya shige da motar nan tskiyar harabar gidan yai parking ya kashe motar,
ya dagota"My Baby Kanwas Oya mushiga ciki murm
ushi tayi ta dora hannunta saman dogon karan hancinsa tanaja kai ya girgiza ya janyeta jikinsa ya bude motar ya fito da ita shima ya fito ya zagayo ya kama hannuta da ido takebin gidan har suka shiga parlon da sallama hafeeza ta taresu da gudu zata riko ze
e tayi tsale ta makale Sardauna tana ihu. janyeta yayi ya nufi gun ummi ya zauna zee na daga gefe tana makale dashi sai wani irin kallo takema su Najib da su minata da Tuwusai Sardauna yace" ummi kuje ki gwada mata wanka da sallah da sauran abubuwa agyara
mata gashinta kufito ina jiranku na bata abunci da magani sai natafi mik'ewa ummi tayi Sardauna ya mikar da zeey tsaye"baby kuje agyaraki tsaresa tayi da idanu tsaye ya Mike ya kama hannunta yajata har kofar d'aki yaba ummi ita fur taki tafiya ta fara kuk
a daurewa yayi ya had'e fuska ya daka mata tsawa wuce maza ku tafi nace cikin rawar jiki ta labe bayan ummi tana kiransa"my baby kanwas kai ya kauda"ummi kuje ki nuna mata ya fada yana juyawa ya
dawo kan kujera ya zauna kusan ghaisha ya kwantar da kans
a kafadarta ya lumshe idanunsa zee ko Dole tabi ummi suka shiga da ta rike mata hannu fizgewa tayi suna shiga ta shiga bathroom ta hada ruwan zafi tazo tajata tana tirjewa harda kuka tana Kiran my kanwas haka tajata ummin kanta hawaye take daket ta cire ma
ta kayan jikinta ta nasata cikin ruwan gumin tana zuba mata ruwan har kanta da kanta tayi mata wanka har dukanta take amma saida ta wanke tas har gashinta bayan ta gama mata ummi ta tube ta kunna shower ta dauki soso da sabulu tana wanka zee ta fito itama
ta tsaya gaban shower ta amshi soson tayi duk yada ummi tayi tana murmushi towel ummi ta d'aura itama ta d'aura ummi tayi Alwalla zee ma tayi suka fito tana karda gashinta tana dariya gaban dressing mirror ta janyota ta tsane mata gashinta ta shafa mata ma
n gashi ta dauré mata da Ribbon yada ummin tayi abaya mai kyau ummi ta dauko mata ta bata ummi ta dauko tasaka itama ta saka tayane mata kanta da mayafin abayar
Darduma ta shimfida itama zee tazo ta tsaya gaban ummin tana kallon tana turo baki tace"my k
anwas ta fada tana nuna kofar daki janyota tayi suka kalli alkiblah ummin ta tayar da kabarar sallah duk abinda ummin tayi cikin hukuncin Allah shi zee takeyi sukayi sallah isha'i bangaran Sardauna ghaisha ta shafi kansa"Auta kayi hakuri kafara cin abunci
ansan mutuwa da ciwo amma babu yada muka iya daddy yace"Faisal ka dauré muyi ta wakali mu amshi kaddara kaga yada Allah ya sake jarabamu ta fannin zainab minata ta share hawaye tace"wlh ina tausayinta sosai baiwar Allah sai abinda aka koya mata Sardauna ji
nsu kawai yake dan basu fishi shiga damuwaba dauriya yake ga rashin d'an uwansa na ragargazar zuciyarsa ghaisha ya kalla"momyna kanshi ta kuma shafawa"Na'am Autana me kakeso? " babu komai ya fada yana murmushin karfin hali" zakasha coffee? su ummi ne suka
fito zee tasha abaya mai kyau da mayafi da gudu tayi kan Sardauna fuska ya had'e ganin yada yayi yasa ta karasa anutse ta zauna kusansa tana kallonsa ta matsa ta kwantar da kanta kafadarsa"my baby kanwas daddy kallonsu kawai yakeyi janyeta yayi ya Mike ya
kama hannuta ya dauki ledar maganin
ya nufi kan dining.kujera yaja ya zaunar da ita ya dauki plate ya zuba mata abunci jalof d'in shinkaface taji busashen kifi shi ba ciba yake amma Dole ya zuba ya zauna ya dauki spoon ya ya tsakuro yakai bakinsa murmu
shi tayi ta dauki spoon d'in ta tsakuri abuncin takai bakinta tana kallonsa kai ya daga mata" Oya baby ci sake daukowa tayi tanaci ganin tanaci ya ajiye spoon din hannusa itama ta ajiyewa tai" baby kici mana kafada ta makale tana kallonsa dauka yayi ya tsa
kuro yana bata da kansa tako amsa tanaci ta matsa ta kwanta jikinsa ahaka ya bata abuncin har ta koshi ya bude robar ruwa ya dago kanta ya kafa mata robar ta rika sha saida yaga ta dan sha mai yawa ya barta ledar maganin ya bude ya duduba ya b'aballosu ya
tallabo kanta ya zuba mata cikin baki ya dauki robar ruwan ya kafa mata abaki tasha saida ya