Showing 33001 words to 36000 words out of 132482 words

Chapter 12 - ZAZZAFAN SO COMPLETE

01 Sep 2026

43

party ne "

"Ok, ya wuce'

"Yanzu yaushe zanzo ganinki?

'Tab'.. Ta fad'a a zuciyarta.

Shi ana ga-yak'i yana ga-k'ura'!!

😅😅

"Hmm,

sai bayan kazo kaga Abba."

"Hm okey", yace mata kawai, don ta rufe mishi baki'

"I love you" ya fad'a mata babu tsammani, taji dad'i sosai,

Me too dear"!

"Ok, sai anjima, koh, take care of yourself "

'Sai taji babu dad'i fiye da koyaushe idan suna w

aya yai mata sallama, da k'yar tace mishi,

"Bye bye,"

'Yai mata kiss, a wayar'

'Ta gaza cire wayar

daga kunnenta, har wata k'walla ce ta cika mata ido, sai yaushe abba zai yarda da Yusuf?

Tayi zumbur ta mik'e da ta tuna aika aikatar da Basma, tayi mat

a, ta mik'awa Aysha wayar, tare da cewa "Thank you sister," ta fita da sauri, tana huci, kishin Basma ya rufe ta...

'Tana zaune tana cin cake, Hafsah ta zauna gefenta tana d'an huci,

"Am Basma ina son magana dake".

Basma na ganin yanayinta itama ta d'a

n daure fuska, "Uhum go ahead"

'Ta fad'a batare da ta bawa zancen Hafsan muhimmanci ba.

"Me yasa kike kiran yusuf a waya? Sannan mene zaki wani gayyaceshi partynki"

Basma ta d'an gyara zama, "Am H. Hamid dama shine kike wani huci?"

"So maida wuk'ar" ta

fad'a tana kaucewa hafsan hanci. Hafsah ta m

do ke hannunta,

"Kinga ki fad'a min dalili".

'Basma tayi dariya, "Nothing fa I just take him as my brother, so kuma nasan idan na gayyaceki partyn bazaki je ba, shine na fad'amishi, becouse partynma na dare

ne"

"Hmm, waye ya ce miki bazani ba, kuma da kika fad'amishi shi zai sani naje,?..kinga please, kada ki k'ara kiranshi, kiyi ma delete contact enshi, Bana son irin haka ni"

Basma ta d'anji ta kaici, amma sai ta share, saboda har yanzu, ba,a zo inda take

so azoba."

"Haha H. Hamid' kenan"

"Yanzu dai please kuzo partynnan ke da shi"

"Bazan zo ba" shi tunda kin gayyaceshi sai yazo ai"

"Hmm, H. Hamid, kenan, ai nasan yusuf zai zo"

"Mts, Hafsah taja tsaki sannan ta bar mata gurin.'

Basma tayi murmushi "H

mm yarinya ai dama baso nake ki zo ba yarinya"

'Yau Hafsah cikin nishad'i ta yini a gida, har da taya mama aiki. Mama taji, dad'in hakan har tana mata nasiha'..

"_Hafsah dama babu, wanda ya sauya miki a cikin gidannan amma duk kinbi kin damu kanki kin da

ina shiga cikin 'yan uwanki,.. ??_ _Mufa iyayenki ne, idan bamu miki fad'a ba wane zai miki, Don Allah ki gyara rayuwarki, ki daina abinda kike yi kinji"._

Ta gyad'a kai, "In sha Allah mama na daina".

"Yauwa, Allah yai miki albarka"

"Amin"

Abba ma ya

u yaga d'an chanji a tattare da ita, ('Yaga tana walwala'.) ya ji d'adin hakan, yau har hira sukayi da ita..

Dama ba a son ranshi yake d'aure mata fuska ba, kawai dai yana son 'horontata' ne.

'Yanzu har sun gama exam, kuma, ayau ne sukayi papper ta k'ars

he yau kuwa yawanci duk sunzo da waya, bayan anfito daga exam akasha hotuna, da ('exchanging numbers,) ana farinciki ana kuma tunanin kewar juna.. _'Rayuwar makaranta kenan'_

'Gobe ne kuma za,ayi graduation party na makaranta, an gayyaci iyayen yara, sann

an kuma kowanne dalibi an bashi damar gayyatar mutum uku banda iyayenshi.

Sai kid'e kid'e da raye-raye ake a ajujuwan, uniform yasha zane, da rubuce rubuce, musamman d'an k'aramin farin hijabinsu' ita dai Hafsah batayi ba'

Aysha ta tawo da gudu tana ihu

'Yeee H. Hamid you're lucky gaskiya'.. Ajin yayi shiru ana son jin me zatace,.. 'Aisha ta cigaba da magana'

"She's the first person that received 'A Congrats Text' from her hubby" class ya rud'e, "heyy.. Can wata ma ta d'aga "Am the second'!!!

Suka rud'e

da ihu..

Basma tanajin, abinda akace kan Hafsah, ta cije lebenta, azuciyarta tace, "Hmm, yana son yarinyar anya kuwa.. Zanyi nasara?.. Wata zuciyar tace mata "You have everything he needs, and you can give him. So that _u are the winner"!!_

Tayi wani ih

u da yasa kowa ya juyo da kallonshi zuwa gareta'

"Heeyy,.. Celebration of new life"!! Ta buga hannunta akan desk wata ma ta d'ora nata, haka sukayi ta tawowa da gudu, suna d'orawa, sannan suka d'aga hannenyen suka watsar... Happy candyy!!

Azatonsu mur

nar candy Basma takeyi'

'Hafsah ta ja hannun Aysha suka bar cikin hayaniyar nan, suka zauna kan 'baranda'

'Kinga text en fa har uku Aysha ta fad'a tana mik'a mata wayar.

'Ta karb'a cikin zumud'i tafara karantawa'

_'Am very happy to witness this remar

kable day, am wishing you happy graduation.._

_Wishing you best result, babynah.._

_"Hmm,.. My dear struggle has now ended,.._

_'Congratulations to myself bcoz, now, I know_ _I will get more Caring from you.. Happy_

_graduation baybee nah'_

'Hafsa

h tayi murmushi taji d'adin hakan sosai.. Sai ta hau 'typing' reply:

'Thank you my dear'

"You made me feel special.. Much of love to you."

Bata dad'e da turowa ba sai ga text na transfer 2000 credit, ya turo..

Can kuma text ya kuma shigowa, ('For aysha

thank you')

Aysha har da tsalle, "Wow Hafsah kimin godiya naji dad'i wallahi..

Hafsah tayi murmushi kawai, tana son ta fad'awa yusuf taron da za,ayi gobe, tana kuma tsoron kada su had'u da Abba, don tasan Yusuf baizai tab'a yin yadda baza,a gane ba.

'W

ashe garin makaranta ta cik'a sosai, da mutane hall d'in taron yasha decoration, dalibai sunyi kyau cikin rigar graduation mai kalar dark blue da ratsin ja' suna kan kujerun da aka tanadar musu..

'Abba da Mama sun sami damar halarta.. Can idanun Hafsah su

ka hango mata wani kamar Yusuf, gabanta ya fad'i.. Tsoro da kishi suka had'ar mata. Kada Abba ya ganeshi ta shiga matsala, sai kuma kishin cewa basma ce ta gayyaceshi.. Haka dai tayi shiru cikin fargaba.

'Anyi jawabai masu muhimmanci da kuma nasiha ga d'a

libai, daga k'arshe aka fara raba kyautuka, ga d'alibai masu hazak'a.

'Daga ajin maza aka fara, sannan bangaren mata, a B'angaren 'Art class' Hafsah ce ta farko a mata, wacce aka fara bawa kyautar d'aliba mafi hazak'a (Best student), sai monitor ta ajinsu

, sai wata d'aliba sai Basma, d'alibai da yawa sun sami kyautukan.'

Ak'alla hafsah ta k'arbi kyautuka guda uku, sunyi hotuna da malamansu sannan aka nemi a fito waje domin iyaye su sami damar yin photona da 'ya'yansu.

' Hafsah tayi saurin zillewa, tayi b

ayan wasu ajujuwa, tace wa Aysha ta kira mata Yusuf don Allah, saboda ta nuna mata shi tun cikin 'Hall' don hafsah kusa da Aysha ta zauna.

Yana ta waige waige Aysha ta mishi magana "Am kaganta can". Ya biyota sukayi bayan class d'in.'

' Tun daga nesa yak

e mata murmushi, ita ma haka, yana k'arasowa tace your welcome dear"

Ya akayi kazo yayi murmushi, nasan za,ayi ne fa"

"Thank you alot.. I hope ba basma ce ta gayyaceka ba"

Yai 'yar dariya, no ba ita bane"

"Sure?

"Yes, I swear i just come for your sa

ke.."

"No baby I trust you, basai ma ka rantse ba, thank you"

Ta mik'a mishi gift d'in ya karb'a yana cewa

"Wow how lucky iam,? to have a Gifted and also the school over roller.. As my girlfriend"!..

Tayi 'yar dariya kana tsokanana ko?

Sai ta lura a

she Aysha video take musu, ta nuna ta da yatsa kin ganki koh,"

"Perfect match" inji Aysha, "Yusuf yace thank you"

'Aysha ta musu, photona sosai kuma sunyi kyau, Hafsah, ta tuno ta baro su Abba, gabanta ya fad'i, ta kalleshi suka had'a ido, duk sai suka k

asa d'auke idanuwasu kusan minti guda, Aysha kuwa na gefe tana faman musu video, sun burgeta sosai'

Atare suka saki murmushi,.. Ahankali tace baby na baro su Abba, so let me go to them, "

Yai mata murmushi "Okey' ahankali ya zaro wata leda ya mik'a mata.

"Ta girgiza kai" shima ya girgiza mata nashi kan'

Aysha ta mata alamar ta karb'a ta amsa ta mishi godiya'.

"Thank you dear".

"You deserve it"

Ta mik'awa aysha, ta rad'a mata

"Ki "ajyemin, ko yaushe ne zan karb'a.

"Ok"

Suka taho taga alamun Yusuf

ma biyo su zaiyi, ta juyo tace mishi, "Please dear, act like you were aysha's bros"

"Okay"

'Ya fad'a yana murmushi.

'Hafsah ta d'aga mishi hannu, ta k'ara sauri ta wuce ta barshi shida Aysha'

Tana isa ta saki fara,a Mama wai Ashe chanjen gift aka min

shine teacher d'inmu yace nazo achanja min"

'Ta k'arashe maganar tana mik'awa abba kyautar" ya karb'a yana murmushi Allah ya sanya albarka"

'Sunyi hotuna sosai, ita dasu Abba da bashir, da wasu k'awayen nata, Aysha ma wajen nata family ta tafi, akabar Yu

suf gefe yana kallon su Hafsah yana murmushi, can ya hango basma ya tafi wajenta'

'Sunyi pictures shida ita, tacewa mamanta yayan k'awarta ne.

Sai da aysha ta gama ta hango shi wajen basma aiko taje ta yafito hafsah, suka zo akayi pic en dasu, duk da Ha

fsah bata ji dad'in ganin shi, wajen basman ba, kuma dake basman 'yar duniya ce, sai ta dinga jan hafsan da hira, suna gamawa, suka wuce wajen su abba, aysha ta gaida mama da Abba, sannan yusuf ma ya gaidasu, gaban hafsah sai fad'uwa yake, mamakinta abba h

ar hannu ya mik'a mishi, suka gaisa, Hafsah tace wa mama Mama wannan k'awata ce aysha" "Ok, Aysha angama school Koh "? Tace "Eh mama,"

"To Allah ya bada result mai kyau." "amin"

Aysha ta mik'awa Yusuf Wayarta, "Please yaya yi mana pics,

Ya karb'a yana

murmushi, yai musu ita da su mama,

Sanan sukayi selfie a wayarshi shida Aysha da Hafsah"

'Shi dai Bashir baki ya saka don ya gane yusuf' lol

Abba yai wa Yusuf sallama to mu zamu wuce Allah ya sanya alkhairi.

"Amin dady"

Abba da Mama sun jera sunyi ga

ba yayin da ita da Aysha suna baya yusuf na tsakiyarsu ', cikin rad'a rad'a yake mata magana,

Please baby kizo partyn nan gobene"

No, bazan je ba?

"Why?

"Kawai.

"Ya Kalli Aysha "Please friend ki rok'e ta taje"

Aysha ta Kalli "Hafsah waike meye haka?

"Hmm, Aysha baki ji, me basma tamin bane, nan ta d'an rad'a mata"

Aysha ta jinjina kai "Ok, kinsan basma, kiyi ahankali dai" "Ok"

"Nima ta gayyaceni fa"

"Hafsah ta tab'e baki kawai"

Dai dai lokacin sunzo bakin gate, dake, a waje su Abba sukayi parki

ng, har sun fita daga cikin makarantar su'

Yusuf ya d'aga mata hannu bye dear, naji dad'i yau sosai, kuma, zanzo gobe muje party"

"Please kada kazo dear kasan da akwai matsala... And please kada kaje party nan"

Yai murmushi,

"No baby dole ne wani yaj

e, because basma bazataji dad'i ba ke bakiyi attending ba nima haka"

"Hmm, ni dai bance kaje ba"

Sunzo daf da fita, saboda haka, ya d'aga mata hannu,

Itama ta d'aga mishi "Bye bye dear "

Thank you aysha"..

Aysha ma ta mata bye bye"

'Ta tarar da su m

ama har sun shiga mota, itama ta shiga, tana fargarbar, 'Kada fa Yusuf yaje wannan partyn gashi babu, damar su tsaya suyi magana, sosai..'

Ta hango shi yana d'aga mata hannu, sanda motarsu ta hau kan kwalta'...

*HAJEEYAH KHAREEM

ERH*

*CE*

👌🏻

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken*

*heart story*

💔💔

Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to:* *Unique In Love*

*Heart Members*

📄

*27*

*Sun* isa gida cikin farin ciki, suna shigowa Mufida ta taso ta rungume Hafsah "Happy graduation yaya". 'Hafsah taji dad'i itama ta rungume ta "Thank you sisi na!"

'Mama ta shiga hidimar zuba musu abinci.. Yau girki na 'musamman'

(special) akayi. 'Dama tayi shi tun kafin su tafi makarantar.'

'Bayan sun kammala ne, suka yi sallah, sannan kowa ya shiga yin tashi hidimar.

'Hafsah dai wanka ta shiga, bayan ta fito tayi kwalliya cikin sabuwar Atamfar 'Super Holland' tayi kyau sosai k

o powder bata shafa ba.

Ta fito falo ta zauna shiru, shima d'in don kada Abba ya ganta babu walwala ne a cikin rana mai muhimmanci a wajenta irin wannan ya zargi wani abu.'

'Amma a b'adinin zuciyarta ('in side of her mind') abubuwane dank'are wad'anda su

ka sabbaba mata yin shiru.

'Na farko shine; Fargabar alak'ar dake tsakanin, basma da Yusuf, 'wacce irin mu,amalar girmama wa ce a tsakaninsu bayan, ta kasancewar basma k'awarta.. Da har zata sa Yusuf kasa k'in amsa gayyatar basma, bayan ita da take sanadi

n had'uwarsu tace bazata ba?

'Na biyu shine kewar 'yan ajinsu da kuma bak'in cikin rashin samun hanyar yin waya da Yusuf. '

Sai na uku tunanin makomarta a wajen Abba.. 'Yanzu dai tayi candy, tana zuba idon ganin ''Shin zai bata 'yancin rik'e waya da kum

a na tsayawa da saurayi''?

'Cikin wannan dogon tunanin ne taji kiran Abba d'aga d'akinshi.. Tayi saurin mik'ewa ta nufi d'akin.

'Da sallama ta shiga , yana zaune akan carpet ta tarar da shi, ta durk'usa sannan tace "Abba gani" ya sakar mata fuska, 'Fiye

da koyaushe a kwanakinnan.' "Yauwa yaya, yanzu anyi candy koh? An zama yaya sosai" tayi murmushi ya mik'e ya nufi, k'ofar bed room d'in cikin d'akin, mintuna kad'an ya dawo da leda ahannu, ya zauna a wajen da ya tashi, sannan ya mik'a mata ledar yana fad'i

n, "To ga gift d'in Abba shima" ta mik'a hannu biyu ta karb'a tana godiya, Abba an gode Allah ya saka da alkhairi"..

Ya amsa da "Amin yaya" sannan cikin nutsuwa yayi mata 'yar takaitacciyar nasiha.

("Hafsah yanzu kin girma fa, yanzu keya dace ki dinga t

ashin k'anne'nki su tafi makaranta ba ni ba ko mamanku." "Kuma kada ki ga kinyi candy ki sa wasa a ranki, yanzu lokacin da zaki fara karatu da kuma sanin rayuwa, saboda haka ki maida hankali don Allah, ki dinga addu,a kinji")

'Ta gyad'a kai "To Abba"

"Y

awwa Allah ya miki albarka ya bada result mekyau"

"Amin Abba"

'Ya d'an nisa sannan yace,

"Ki bar batun party sai bayan exam ta fito za,a had'a miki babban party, kin ga sannan kin san matsayin jarrabawarki koh"?

'Ta gyad'a kai kawai'

Cikin nutsuwa ya

sake ce mata,

"Yaya ayau naso in baki waya, amma na fasa, saboda dalilin da kema kin sanshi, amma zan duba na gani zuwa wani lokacin.

Bataji dad'in hakan ba, amma yanzu, sai taji tabbas cewa laifinta ne'.

'Ta kasa koda gyad'a mishi kai ne'.

Ya kira s

unanta "Hafsah!"

Sai da ta amsa sannan yace yana nuna ta da yatsa'

"kada ki d'auka gama makarantar da kikayi ya baki damar yin magana da wani saurayi..ban baki wannan damar ba,.. Kada ki sake ki saurari wani, har sai kin turo shi ya ganni na mishi izini

".. Kinji koh?

'Ta jinjina kai Eh" yauwa, to tashi kije'

'Sai taji duk jikinta ya d'anyi sanyi.

'Tana fita babban falo taji kiran mama,ta sameta a d'akinta, "Mama gani,"

Itama wani abu ta mik'a mata acikin wani d'an box akwati mai kyau, "Gashinan na ha

ppy graduation ne" taji dad'i sosai,

" Nagode mama" ta fad'a tana murmushi.

'Bed room d'in ta nufa, ta zauna kan gado, ta ajye kyaututan agefe, jinta take wata mai sa,ar iyaye, tabbas ta k'ara tabbatarwa kanta iyayenta na k'aunarta. Ta d'auki ledar Abba

tana shirin bud'ewa, 'Mufida ta shigo da gudun, cikin wata 'Red gown' tayi kyau sosai,

"Yaya ki fito falo,"

Hafsah ta zaro ido Menene?

Tayi murmushi tana d'an rawa da k'afarta alamar a k'age take, ('She eager')

"Surprise ne"

Hafsah ta mik'e.

Yaya

ki chanja dressing, ta fad'a tana shigowa cikin d'akin sosai, ta bud'e drawer ta dakko wa Hafsah, wata T. Shirts purple sai wani wando light pink Hafsa tasa da sauri, tana son taje taga Menene'?

Tayi sauri tayi d'auri me kama da turban, akanta da wani pu

rple d'in d'ankwali, ta nufi wajen dressing mirror ta fesa turare, sannan suka fito.

Bashir, duk k'annenta ta gani, sai abokin bashir na'eem, sai wata k'awar Zainab dake a mak'otansu Nusaiba',

Tsaye suke sun kewaye table d'in dinning, sun d'ora cake akai

.. Suna ganinta suka hau ihu happy graduation' suna tafi, ta shiga tsakiyarsu ta tsaya, suka yi photuna da wayar Mama, sannan aka fara irge "5..4..3..2..1.." Ita da Mufida suka rik'e wukar sannan suka yanka, sannan akashiga ci, ana b'ata fuska da cream, sa

i da suka gama sannan suka yi wasu photunan a wayar Abba, sai lokacin daf da magariba sannan suka gama, domin wak'a suka kunna a speaker na falo sukayi ta rawa isu-isu'

Hafsah yau farin cikinta babu misali, har ta manta da wani tunanin yusuf gaba-d'aya ba

yan sunyi sallah aka dora da kallo, ko bed room, d'inta bata shiga ba, sai wajen 11:00pm, kowa ya mik'e don yin bacci.

Hafsah ta shiga toilet tayi wanka, ta saka rigar bacci sannan ta kwanta. A gajiye take sosai don haka ko takan gift en abba da Mama bat

abi,ba bare kuma wani tunanin Yusuf, bacci yai gaba da ita'.

Da safe ta tashi fresh babu wani tension sai bayan, sun karya ne, sannan ta dakko kyautukan nata.

'Na Abba ta fara bud'ewa, 'wani agogone mai kyau na mata, sai takalmi akwalinshi goalding color

ya had'u, sai wani tsadadden turare.'

Taji d'adin kyautar sosai, tana murmushi ta bud'e box d'in Mama, wani zob'e ta gani mai kyau d'an k'arami.

"Thank you my parents!!

Ta furta a fili.

'Da yamma tayi wanka cikin b'akar after dress da d'an mayafi, ma

ma tace zata aikata wani gida cikin layinsu ta karb'o mata turaren wuta da Matar take siyarwa, ta fito ta nufi gate, aiko tana bud'ewa tayi gamo da Yusuf tsaye jikin motar shi, yayi kyau fiye da duk ranakun data tab'a ganinshi, ta dafe k'irjinta sanadiyyar

bugawar da yake, shi kuma sai wani murmushi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login