Showing 60001 words to 63000 words out of 132482 words

Chapter 21 - ZAZZAFAN SO COMPLETE

01 Sep 2026

61

shuru.

"Ki d`ago me yasa kike jin kunya."?

Hafsah ta dago tana noqe-noqe.

Kinaji nah."?

Ta d`aga kai.

"Ki daina yin abinda zaki zo kiji kunya, ko kizo kiyi dana sani."

_"Kinga yanzu kin bata record d'

inki."_

"Kin ga da tuni, idan kina bawa Yaranki ('ya'yanki) labari, _you claim and proud that_ baki tab'a tsallake na biyu ba koh."? Amma yanzu kin bata abin."

Mama ta fada da muryar nuna damuwa.

Ran Hafsah ya cika da kishin abin, _Tabbas ta tafka asara

ba komai bane kuma sai don dalilin biye wa basma da son farin cikin ganin Yusuf._

A hankali idonta ya cika da kwalla ganin sam bata ribaci hakan ba illa bata record dinta da sukayi kamar yadda mama ta fad'a.

Mama ta lura da kwallar, duk da Hafsah taki b

arin ta ta zuba.

A hankali ta girgiza kai tace, "Me abbanku yace miki a time d`in daya ga result d`in.

A kunyace tace, "Yayi min fad'a yace kada na sake sakacin yin hakan."

"To Ke me yasa kikayi hakan Uhum."?

"Kina tunanin wani abu neh."?

Hafsah ta gi

rgiza kai.

"To menene.. fad`amin me yasa kakai failing a lokacin."

Ta qara yin shuru.

"Wasa kuke koh.? Kin chanja qawaye koh, kuna zaman hira."

Gaban Hafsah ya fad'i, ya akayi Maman ya Nazeer take neman baro jirginta."??

"Kinyi shuru Ko ba haka ba

ne."?

Bata da amsa, sai kawai maman ta bar zancen ta shiga wani.

Me yasa kike batawa mamanki rai."?

A hankali ta girgiza kai, "babu komai.

Babu komai amma kike yin abinda bata so."?

Idan mama ta lura fuskar Hafsah tayi rauni lokacin.

"Me yasa kike fi

ta bada saninta ba."?

Duk Cikin qasa da murya maman take magana.

"To rannan ina kukaje ke da qawarki."?

Gaban Hafsah ya fad'i, wannan fita ta zame mata jaraba. Sam ta tsani a tambaye ta ina taje."

Bayan inda taje d`in ba alkhairi ta ganowa kanta ba.

Ehe."? _Inji mama jin tayi shuru._

"Asibiti mukaje dubiya."

Wanne asibitin."?

Uhum.. A ina yake."?

_Hafsah bata iya qarya ba don haka ta kasa qirqiro amsa._

"Kin sami babu kyau sabawa iyayen koh."?

Tame daga kai.

To ki daina yin abinda zai b'atawa m

ama da Abba rai kinji.

"Tom."

_Ta fad'ad'a murmushi._

"Yawwa hafsy, gobe zaki raka ni wajen gyaran jiki na."

Ko Bakya son muje."?

Hafsah taji dad`in hakan sosai don haka cikin fara,a tace "Inaso mama."

"Yawwa jeki wajen su fateemah kuyi hira."

_Ta m

iqe ta fita mama ta bita da kallo._

Da daddare suna zaune suna kallo, Nazeer ya shigo ya zauna cikin su.

Abinda Mama ta lura dashi shine, kwana biyu Nazeer nason ya zauna cikin su ya dad'e musamman da daddare.

_Bata raya komai aranta ba._

A gurin Ha

fsah kuwa zaman nashi takura ce a wajenta. _Domin indai ya zauna sai ya tsokane ta, ko yayi ta janta da hira. Gashi tunda tazo gidan duk wata hidimar shi ita yake sakawa, Kama daga zuba mishi abincin, d`akkon kaza-da-kaza._

Amma banda haka tanajin dad`i

n zaman gidan sosai da sosai banda damuwar dake cikin ranta.

Yanzu ba yusuf ne kad'ai damuwarta ba, a,a harda damuwar Basma, so take ta d`auki fansar abinda tayi mata ko dan ta rage damuwar abin aranta.

_Da Wannan alwashin, ta kwana a ranta._

Gefe g

uda tana jin takaicin ledar kyautar ta da ke wajen maman Ya Nazeer, damuwar ta wayar dake ciki, da tana wajenta tabbas sai ta yi amfani da wayar ko mai zai faru kuwa, sai ta kira Basma ta huce fushinta akan ta.

Ita da zata ganta ma babu abinda zai hana t

a illatata.

Ta rasa me ya hanata d'aukar mataki a lokacin. Ko kuma lokacin bata da kwarin guiwar yin hakan. Saboda taga abinda zuciyar ta bata tab`a wassafo mata faruwar abu mai kama da hakan ba.

Tayi kwafa, yayin da Fateema dake karatu, ta bi inda t

ake kwance da kallo, sam ta zaci Hafsah bacci take.

Washegari da safe tun wajen qarfe 11:00 na rana, Hafsah ta shirya ita da Mama suka fice zuwa wajen gyaran jikin Maman.

_Fateema`s touch_

Sunan wajen kenan, ya had`u sosai, ana gyaran jikin

amare, gyaran gashi, wankin qafa da sauransu.

Lokacin da suka je, ana ta yiwa wata amarya gyaran jiki, suna kwa shigowa ma,aikatan wajen suka hau gaida Mama, wacce suke kira da Mommy. Cikin fara,a ta dinga amsawa sannan ta wuce ciki.

Akwai wani d`an off

ice madaidaici wanda yafi kama da palour, nan suka shiga maman ta zauna a kujera, Hafsah ma ta nemi waje ta zauna. K`amshi ne kawai ke tashi, gefe ga _show Glass_ turaruka ne aciki da humra duk na siyarwa.

"Baki tab'a zuwa wajen nan ba koh."?

Mama ta tam

bayi Hafsah dake faman kalle-kalle. Ita dai wajen ya burgeta sosai.

Tayi murmushi, "Mun taba zuwa da Mamanmu sau biyu, cikin nan ne dai ni ban tab`a shigowa ba."

Suna hirar aka k'wank'wasa kofa, mama, ta bada izini a shigo.

Lemo tazo ta ajye musu, sanna

n ta fita.

"Kisha lemon kinji Hafsah na ko kina son ki fita kiyi kallo."?

Ta d`aga kanta.

"To kisha sai ki je ki kalla.

"Tom."

Anyiwa mutane biyu gyaran k'afa dana gashi, wato _Saloon_ za,ayi wa ta ukun kenan mama ta sa aka kira mata Hafsah.

Ta miqe

ta tafi kiran.

Tanajin dad`in zaman har suna ta hira da ma,aikatan wajen.

"Mama gani."

"Zauna kici abinci." Mama ta nuna mata abincin da ta musu order aka kawo.

Ta fara ci kenan, maman ta miqe ta fita, zagayawa don ganin meke gudana.'

Babu dad'ewa kum

a maman ta dawo Hafsah nacin abincin tana janta da hira so take tayi mata wasu tambayoyi masu muhimmanci.

" `Yan mata kinga Yenda ake gyaran jiki koh."?

Hafsah tayi murmushi,

"Ko kina so ayi miki."?

Hafsah na murmushi ta d`aga kai alamar Eh."

"To an

qi d`in sai dai anzo bikinki ayi miki yanzu sai dai ayi miki a fuska kawai."

Cewar mama cike da zolaya.

Hafsah ta sinne kai alamun jin kunya.

"Ai kina da saurayi koh."?

Hafsah tayi murmushi jin kunya tana girgiza kai alamar a,a.

"Gidanku!! kina da da

shi mana."

"Bani da shi.!!

"Au kikayi magana ko toh kina dashi."

"A,a mama" tayi maganar tana 'yar dariya.

"To wanda ya baki ledar nan fah."?

Ehe."? Inji Hafsah, ta ke yanayinta ya chanja, zuwa damuwa.

"Am um, ba saurayi na bane."

"Hmm, koh."?

Hafs

ah zaton ta mama ta yarda don haka qara d`aga kai alamar tabbatar wa.

Mamanki tasan da ledar."?

"Aa."

"To meyasa baki nuna mata ba..?

Bata da amsa don haka tayi shuru.

"Kiyi magana mana Hafsah."?

"Babu komai."

Kinga irin laifin da kike koh."?

"Daga

yau kada in qaraji kin qara yin laifi me kama da wannan."

"Ta d`aga kai alamar, Toh."

Mama ta d`ora, "Kin ce ba saurayin ki bane, amma meya kaiki amsar kyautar shi, kuma meya sa kika karb`a."?

Hafsah tayi shuru tana tuno amsar da zata bayar.

"Um, am w

allah.. hi, ba saurayi na bane."

To menene had`in ki dashi.

"Ni..ni bana kulashi yanzu." ta fad'a cikin in`inah..Fatanta kawai mama ta yarda da zancen ta."

_An kusa zuwa inda mama take son azo don haka tace:_ "To me yasa kika daina kulashi meya had'a ku

."?

Ai k'iris ne hafsah bata sa kuka ba.

Take muryata tayi rauni, har rawa take yi.

"Babu abinda ya had`a mu."

"Hmm, kina wasa dani koh."?

"Aa Mama."

"To ki fada min gaskiya."

Shuru babu magana har wajen wucewar muntuna wajen biyu. Sai Hafsah dake f

aman kokawa da qwallar dake son zubo mata."

"Kawai na daina kula shi ne saboda mama bata so."

"Mama bata so, to meyasa."?

Mama ta tambayeta da sigar irin tayi mamakin maman ne."

Tasan ba zata sami amsa ba, don haka tayi amfani da damar wajen cewa, "Shi

ne kuka fita dashi ranar bikin abdallah koh."?

Gaban Hafsah yayi wata mummunar fad`uwa, ta k'osa wannan lokacin ( _Moment_) d`in ya shud`e, ta gaji da tambayoyin, don ana neman qureta.

Mama bata jira amsarta ba ta d'ora.

"Kinga dalilin d`aya sa mamanki

ba ta so koh.. Meyasa zaki bishi wani waje."? Ke aganinki ya dace kiyi haka."?

Cikin nadama Hafsah ta girgiza kai.

"Duk mutumin da bazai taya ki yiwa iyayenki biyayya ba, ki rabu da shi kinji."

Hafsah ta d'aga kai alamar Toh."

Sai wajen la,asar suka t

afi gida wanda a hanya tunanin Hafsah ya kasu kashi-kashi, wanda yafi tsaya mata a rai shine, nasihar mama, sai kuma jin asarar barin Basma, haka taci bulus. Dole ta bata mata rai ita ma kamar yadda tasa ranta dana iyayenta b'aci.

Sunje gida da daddare, m

ama ta kira fateema d'akinta, so take ta sa Fateeman wani aiki akan Hafsah.

"Fatee, kun tab'a wata hira ne da Hafsah, wacce tayi kama data samari."?

Fatima ta tsorata da tambayar don haka ta bud'e baki, gwara ta fad'awa Maman gaskiya kada taje tayi laifi

don da alama akwai babban case wanda yake faruwa.

"A,a mama, saidai ta ari wayata tasa wata number, ta duba a Whatsapp amma bata kira ba kuma batayi magana ba."

"Me yasa baki fad`amin jiya ba."?

Mama ta tambaya da fad`a-fad`a.

"Kiyi hak`uri mama, baya

n ta sa number sai ta tsaya kallon profile d`in kuma sai ta fashe da kuka."?

"Kuka kuma."

"Eh Mama."

"Amma duk kika k`i fad`amin koh."?

"Mama kiyi hak'uri."

Kada ki sake boye min abu makamancin wannan, tashi ki d`akko wayarki ki nuna min photon yaron.

.

Kafin na fad`a miki abinda zaki min..."

Nan Fateema ta miqe ta nufi d`akinsu don d`akko wayar.

Acan D`akin kuma, Hafsah ganin ita kad`ai ce a d'akin sai tayi alwashin kawai aiwatar da abinda zuciyarta ke raya mata, don ta sami dama, tana gudun k

ada ta wuce ta.

Cikin zafin nama ta d'akko wayar dake gefenta, ta danna wasu numbobi, ringin d`in har ya katse ba,a d`aga ba, ta qara dannawa karo na biyu.

Wannan karon an d`aga.

"Hello."

Aka fad'a daga can b'angaren.

Cikin kaushin murya, Hafsah

ta fara magana.

"Hi Master of snatching H. Habeeb Hamid ke magana.!!

"Hmm, I already know it's you _good for nothing.!!_

Kada ki d'auka abinda kika yi kinci bulus, karuwar gida kawai.".. Bata bari ta sami kalmar mayarwa ba ta d`ora.. _"Ashe ke b'araun

iya ce ban sani ba, b`arauniya, mai sace samarin mutane, yar iska mara tarbiyya._

"Haha Haha, dariyar basma ta cika kunnen Hafsan,

_"I already know zaki fadi irin haka tun ba yau ba loser.!!_

"Kiji kawai da rashin Yusuf da bazai kara dawo miki ba, idan

kuma kina son ki tabbatar gobe k'arfe shida mu had'u _Garden_ idan kin isah.

"Qarya kike mayaudariya...

Iya zancen da kunnen Fateema yaji kenan anayi a wayar ta sanda ta shigo d'akin da azama ta warce wayar,

"Wacece..wacece mayaudariya.."??

Wa kik

a kira a wayata.. Me.. me yasa haka Hafsah."???

_Cikin in'ina fateema ke magana.._



📝



*HAJEEYA KHAREEMERH*

















*ZAZZAFAN SO*

(masoyin k'warai )

*Cigaban littafin Zazzafan so*

*(Guba ne)*

💔💔

*By:*

*Karima Tijjani Mansur*

*(H

ajeeyah khareemerh)*

*Dedicated to Unique in your love heart group members.*

I DEDICATED THIS PAGE TO YOU _(RUKKY NAILA GROUP 1)_ SURELY YOU ARE A TRUE FAN..

😊

📄

*41*

*Ki kyaleni..* Ni ki kyaleni.. Wallahi bazan rabu da ita ba,

bazan bar mata shi ba.!"

Abinda Hafsah ke fad'a kenan cikin kuka, yayin da Fateema ta riqe ta a tsorace.

"Kiyi hak'uri Hafsah don Allah ki fad`amin me ya faru, wa kika kira.?

Cikin kuka tace "Nidai, kiyi hak'uri na daukar miki waya, amma ki kyale k

awai.

Fateema taga bada da lokacin b'atawa don mama na jiranta don haka ta wuce zata fita. Ta kai bakin k`ofa kenan ta jiyo Hafsah na magana.

"Don Allah kada ki fad'awa mama, nayi kira a waya."

"To kawai fatima tace ta fita."

"Me Hafsan keyi."?

Mama t

a tambayeta tana zama.

Cikin son rufawa Hafsah asiri fatima har zuwa sanda zataji aikin da maman xata sata don haka tace, "Babu komai tana kwance ne."

"Tom, muga yaron."?

Fateema ta budo profile d`in yusuf ta miqawa mama.

Muntuna uku tana qare wa Yusuf

kallo, sannan ta miqo mata tare da jan siririn tsaki.

"Daga ganinshi bashi da cikakkiyar tarbiyya.!!"

Ita dai fateema kallo tabi mama dashi ta mayar da kai k'asa.

"Ki bani hakalinki nan.

Cewar mama, tana zubawa Fateema ido, yayin da ita kuma ta gyar

a zama ta bada hankalin nata ga Maman.

"Inaso ki dinga janta da hirar samari har ki gano min matsalar ta."

Fatima ta jinjina kai, mama ta d'ora.

"Akwai alamu yaron nan yana hure mata kunne, ada, don (Ameenah/maman su Hafsah) har qarar ta ta kawo min. Am

ma yanzu naga alamun tana da damuwa, kuma naga kamar yaron ya yaudare ta ne, shine nake son ki hilace ta da hira, ki gano min gaskiyar me ya faru."

"Kingane."?

Fateema ta jinjina kai "Eh, Mama."

Yawwa, ku dinga hirar samari da ita, da kuma hirar makara

nta.

"Toh mama."

"Yawwa nasan zaki iya koh."?

Fateema ta d'aga kai alamar Eh." Tana murmushi.

"Yawwa Allah ya taimaka yayi albarka."

Da Fateema taso ta fad'awa mama zancen wayar da ta tarar Hafsah nayi, sai kuma ta fasa, gwara ta kawo mata cikakken

bayani gaba-d'aya."

"Ta miqe ta zata fita mama ta kirata."

Kada fa ki matsa mata da tambayoyi ki bari a hankali, zaki bi abin, ba sauri nake ba."

"Okay mama.!

"Yawwa."

Wajen Hafsah ta koma, ta tarar da ita tayi tagumi, ga gumi da ta had`a.

Fateema ta

zo kusa da ita ta dafa kafad`unta.

"Am sorry my sister, kin sani cikin duhu, kiyi hak'uri ki fad`amin me yake faruwa."?

"Ni yar uwarki ce ko ba komai, zan taya ki da shawara da addu,a."

Hawaye suka qara zubowa, Hafsah, "Kada ki damu, wannan abin ni ta s

hafa kawai."

"A,a wallahi nima ya shafe ni, don Allah ki fad'a min."

Shuru babu alamun, Hafsah zata ce komai, sai ajiyar zuciya da take tayi tana cije leb`e.

"Hafsy..Hafsy,!!

Nazeer ya kwalo-mata kira.

Har aranta bataji dad`in kiran ba, bata son abi

nda yake mata bare yanzu cikin yanayin da take, da ita kad'ai ce babu abinda zai hanata yin _burus_ dashi, amma kuma ga k'anwarshi gefenta dole ta amsa, ko dan gudun kada ta ji haushin hakan, tunda ance _d`an-uwa rabin-jiki."_

"Hafsah Ya Nazeer fa yana ki

ranki."

Fateema ta qara qarfafa mata guiwa da haka. Ala dole ta miqe, ta fita, bata da qarfin muryar da zata amsa.

Yana tsaye a parlour ta motsa baki, zatace _"Gani."_ ya tare ta.

"Haba Sisi na, kiran ma baza,a amsa min ba."?

"Banji ba ne." ta fad'a mu

rya a dashe.

"Nidai ayi hakuri idan ni na b'ata miki rai, dama abinci za,a taimaka min dashi."

Ya fad'a yana qare mata kallo.

Abin ya bata kunya, taji kunyar kanta, ta dan saki rai sannan tace, "Ciwon kai nakeyi."

"Ayya sannu kinsha magani."?

Ta girg

iza kai.

'To kije kisha bari na zuba abincin da kaina."

Ta girgiza mishi kai, bata son ya dinga karantar k'osawar da tayi da shi don haka ta wuce kitchen.

Shi kuma ganin ya sami abinda yake so sai ya wuce d`akin shi.

Ranta ya qara b'aci bata son sh

iga d`akinshi sam, da yaran suna nan babu abinda zai hana ta basu su kai mishi. Amma babu yadda ta iya.

A bakin kofa ta tsaya. "Ga abincin."

Ta fad'a a qasan mak`oshi.

"Kiyi hakuri ki miqo min ciki."

"Shima yayo magana da ga cikin dakin.

Ta ajye abinc

in ko kallonshi bata yi ba, zata juya taji yace.

"Don Allah Hafsah, ki zo kiji."

Ta juyo ta tsaya tana kallon shi.

"Ki zauna mana please."

Ta dan d`osanu a Kujera.

Ya juyo gaba-d`aya Ya fuskanto ta.

Cikin marairaice murya ya fara magana.

"Jibi zamu

shiga _camp_ Hafsah, gobe zan tafi in barku."

Shuru tayi tana, nazarin zancen, mene alfanun fad'ar kalmar nan."?

Tana tsakiya da mamaki taji yace.

"Zanyi kewar ku Hafsah.!!

Binshi da kallo tayi kawai.

"Baki da waya koh."?

Ta gaji da irin salon nashi

me yake nufi, a irin wannan lokacin da take cikin halin k'ila wa k'ala, akan Yusuf, zai dinga zuwa mata da wani zance ?? don haka, ta had'e rai.

Ya lura da hakan, nan ya shiga tunani,

_"Ya dace, ya bar yarinya da wannan batun don da alama hankalinta ba

akanshi yake ba kuma, akwai sauran yarinta a tattare da ita."_

_Zai barta zuwa wasu lokuta yaga idan akwai rabon shi._

Ya saki ajiyar zuciya, "Okey thank you, kije ciki na gode."

Ta miqe kamar akan qaya take.

_Ya bi bayanta da kallo yana kissima abubuw

a da dama, ko dai ya hakura ne kawai.?_

To, babu yadda Fateema bata yi ba, don "Hafsah ta fada mata dawa tayi waya amma fir taki fad'a.

Don haka ta rabu da ita, sai kawai tayi saving number, da Hafsan ta kira.

Daren Hafsah, cike da mafarke-mafarken Yusu

f da Basma mara sa dad`in bada labari, haka ta wayi gari da alwashin sai taje inda Basma ta fad'a mata don a banbance tsaba da tsakuwa tsanin ita da ita.

Da sassafe, Nazeer ya gama shiri tsab, ya fito da jakarshi sab'e zai musu sallama, dakin Mamanshi y

a fara shiga ta dad'e tana yi mishi addu,ar samun nasara da tsarin ubangiji..

"Amin mama Nagode." haka yake ta fad'a.

Suka fito shida mama zuwa palour, yaran duk suna nan dake Lahdi ce, mama ta qare musu kallo babu Hafsah aciki, "Fateema jeki kira Hafsah

suyi sallama.

Yaji dad`in hakan sosai.

Tare suka dawo da Fateeman.

Ta saki fara,a kuma. "Har da cewa yaya tafiyar ce."?

Shiko abin nema ya samu, murmushi yayi mata. "Eh mun fito sai Allah ya dawo damu, kwana biyu kema ki huta da zubamini-zuba-mini."

Dariya, sukayi musu, mama nacewa, "Ah toh, ashe dai ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login