Showing 66001 words to 69000 words out of 132482 words
ta koma bacci ba, _"Zauna yau kema kiyi lazimi."_ haka ta fa
da mata. Sai da rana ta b'ullo lokacin kuma maman ta gama shirinta na fita office, "Tunda ba zaki karya yanzu ba, sai ki kwanta, maybe karfe 2:00pm, ma ni na dawo, sannan asabe ( _tana nufin me aikinta_ ) zata zo, sai kuyi aikin tare kiyi mana abincin rana
."
"To, mama me za,a dafa."? Inji Hafsah cikin ladabi.
Cikin murmushi tace, "Kin iya tuwo."?
Hafsa tayi murmushi itama tana d'aga kai.
"To kiyi mana shi, miyar agushi kuma saura naga bai tuk'u ba." Maman tayi maganar da sigar zolaya.
Sannan ta cigaba
da cewa, "ki duba akwai komai cikin kitchen d'in, da kwai nama a fridge."
"To mama."
Suka fito palour tare.. Lokacin duk yaran sun Ida shiryawa har da Fateema. "Yawwa kuyi sauri tare duk zamu fita tun da kunga Nazeer baya nan bare ya kaiku." _Mama ta fad
a musu haka._
Kamar kuma tayi mantuwa sai, tayi sauri, ta koma d'akinta tare da kwalowa Hafsah kira.
Tana shigowa ta durqusa "mama gani, maman na tsaye bata zauna ba, tayi mata nuni, "Tashi tashi sauri nake."
Tana ida mik'ewa ta nuna ta da yatsa.
"Kada
ki ga sai ke kad'ai a gida, kiyi tunanin, fita koda bakin gate ne, zan fad'awa mai gadi ma, kuma muddin kikayi attempting fita zaki gamu da fushi na.!!
Babu alamun wasa a fuskar maman tayi mata wannan maganar.
Daga kai kawai Hafsah, ke faman yi alamar,
"Toh."
Azuciyarta, tana cewa, ( _"wane Tsautsayin ne zai qara fitar dani.!!_)
Sai na dawo, maman ta fad`a da murmushi kamar ba ita tayi wannan maganar yanzu ba.
"Adawo lafiya."
"Allah yasa, Maza ayi bacci, bye."
Ta fita tana daga mata hannu. Hafsah ta
ji wata 'yar dariya tazo mata, ko ta mecece oho, ta fada kan gadon tayi shuru har bacci ya d`auke ta.
Sai wajen, sha d'aya, ta farka, ta nemi abu mai sauk'i tayi break dashi lokacin kuma, me aikin har, taci rabin wanke-wanke.
Hafsah tayi wanka sannan ta,
fara shirin dora girkin, suna yi suna hira ita da me aikin, wacce bazata wuce shekaru 35 ba, tana da 'ya'ya uku da mijinta ya rasu ya bar mata. Duk a hirar su ne take fad'awa Hafsah.
Hafsah ta k'ara godewa Allah, a zuciyarta tana cewa, _"Gaskiya akwai ma
su buqatar taimako a duniyar nan!_
Sanda mama ta dawo, fara,arta ta zarce ta safiya, musamman da taga an gama komai gidan tsaf, kamar babu abinda ya faru, sai zolayar Hafsah ta take, "Toh zubo min Tuwon naki mana, nayi testing, ice ko babu hannun asabe a
girkin."?
Suna dariya asabe tace, "Ita tayi abinta wallah, ai d'iyar taki ba daga nan ba, nima nace 'ko training d`in aure aka kawota ta d'auka.? Mama tayi murmushi kawai, Hafsah tabar gurin da sauri da alama taji kunya."!
Wasa wasa har kwana hud`u
, da alama ma mama ta manta Hafsah tayi wani laifi.( _A ganin Hafsan don ganin yadda maman ke janta a jiki fiye da koyaushe_)
Tunda, Nazeer ya tafi taji gidan ya k'ara yi mata dad'i, jiya ne ma daya kira Fateema, suna waya yace ta bawa Hafsan, babu yadda
zatayi haka ta karba suka gaisa.
Da yammacin ranar Juma,a tana taya mama gyaran drawer, sai ga ledar da Yusuf ya bata, dam, gabanta ya fadi tare dajin wani farin ciki ya mamaye zuciyarta, gaskiya tana cikin tsananin kewa, in ba don idon maman yakai kai ba
, da babu abinda zai hanata da fe abarta ta b'oye.
Maman ta fi ta hanzari wajen sunkuyawa ta dakko ledar, ta lura sosai da yanayin Hafsan."
"In ba don Laifin da kikayi min ba ai da tuni na baki abubuwan ki ai."
'Inji mama, tana so ne ta shigar da Hafsa
h hayyacin ta, ta dinga gane abubuwan da suke rufe mata ido suna kaita ne kawai suna baro ta babu wani riba.
_Don a kasan zuciyarta ko hafsah batayi mata wanna laifin ba, bata da niyyar bata wayar yanzu, don bata ga amfanin hakan ba._
Hafsah ta langab'ar
da kai kawai, tana bawa kanta laifi.
Hakan ya bawa mama damar cigaba da magana, tabar wancen zancen ta kamo wani, don ta samu ta aika sak'oninta ga Hafsah.
"Hafsah.!!
Ta kira sunan Hafsah a hankali,
Cikin sanyi ta amsa itama.
Kuna zuwa islamiyya koh,
Hafsah ta jinjina kai,
"Yawwa." inji mama.
Kinsan shikashikan musulinci koh"?
Hafsah ta k'ara jinjina kai, har yanzu da mamakin tambayoyin a fuskar ta.
"To fad'a min su."
Ta d`anyi shuru sai kuma ta tuna kada mama ta zaci ko bata sani bane, yasa ta s
huru. Don Allah a hankali ta fara zayyyano su.
Tana gamawa mama tace _"To saura na imami."_
Hafsah ta fad'o su guda shiddan nan, tanayi tana kallon mama, so take taji dalilin tambayoyin.
Yawwa, 'ya ta."
Ashe dai baki manta karatun islamiyyar ba.
( _zu
wa yanzu sun kammala gyaran, amma har yanzu ledar na hannun mama._ )
Mama ta zauna gefen gadon, Hafsah ta zauna kasa gefenta.
"To me ake nufi kaddarar da naji kin fad`a. aciki"?
Hafsah ta kulle baki da alama bata san yadda zata faro bada amsar ba.
"Uh
um."? Inji mama.
"Baki sani ba."
"Ta jinjina kai."
"Hmm.. To marin da na yi miki rannan shi ma ai kaddara sunan shi koh."
Kunya sosai ta lullub'e Hafsah ta sinne kai a cinyoyin ta tana dariya.
"Hmm, bada wasa nake miki ba Hafsah, tunda har an koya mik
i a makaranta, kuma kin iya kina fad'a to kuwa dole kiyi amfani dashi.
"Kinaji nah.."? Hafsah ta daga kai.
Cikin muryar nutsuwa mama ta fara mata jawabi.
_"Kin sani a makaranta, an koya muku, dole ne mutum ya nemi ilimi kuma dole yayi amfani da ilimin s
a Koh?._
Hafsah ta daga kai.
Ta tausasa muryar ta. "Ki fada min gaskiya kinji kada ki boye min ni maman kice. " _Kina son Yusuf_ "?
Hartar cikin Hafsah ta kad`a wani irin tsoro ya mamayeta. _Sunan Yusuf, kuma daga bakin mama."_?
_Kina son shi._"?
Mam
a ta k'ara maimaita mata tambayar. _"To ko kuma wannan wata dama ce ta samu, wajen dawo da yusuf bisa hanya, tunda har mama ta shigo cikin zancen."_ ?
Ganin maman bata buk'atar b'acin lokaci yasa Hafsah daga kai a hankali, sai kuma ga hawaye na d`iga.
Mama ta tallafo ta da hannunta ta jigina ta da gefen k'afarta, "To menene na kuka kuma."?
Ba tambayar ki kawai nayi ba.?
Aka danyi shuru, kafin mama ta cigaba, "Idan nace ki daina kulashi zaki daina."?
Wannan tambayar daidai take da zubar garwashi a zu
ciyar Hafsah, don yanayin data shiga da jin maganar bazai misaltuwa ba, wannan karon kuka
ta fara harda shashsheqa, _wanne irin zance ne wannan mara dad`in ji a kunnuwa."?_ Ita ta zauna ma ta kissima ('Imagine') rayuwar da babu Yusuf asara take gani saboda
tasan, abu ne da bazai tab'a yuwuwa ba a wajenta.
Mama tasan za,ayi haka, don haka ba tare da nuna damuwa ba, akan Kukan da Hafsah keyi ta
cigaba da, zubo maganganunta, wad`anda baza,ace basa shiga kunnen Hafsah ba, tanajine, amma tunanin ta na wata du
niyar.
_"Hafsah ita rayuwar nan da kika gani, in bakayi-bani guri ake, nasan bazakiyi mamaki ba naji komai dake tsakanin ku da yaron nan, amma tambayar da zanyi miki shine, ya sunan matsayinki a wajenshi.?_
(zuciyar Hafsah ta raya mata _"wadda zai aura
mana"_)
Itama k'awar taki mene nata matsayin."? (gaban Hafsah ya fad`i, _wannan tambayar kam babu amsa, don daidai take da k'ure._ )
"Bazan zarge ki ba don ina miki kyakykyawan zato, amma tsakanin ki da Allah kin tab'a jin labarin soyayya irin taku."?
S
hin kin tabajin anyi haka..?
_Bari na fada miki gaskiya, _Duk ranar da kika sake kuka cigaba da alak'a ke da shi, to ki tabbatar kema ranar kin shirya zama irin Basma ne, ko kuma kin zama irin ta.!"_
Hafsah tayi saurin d`ago kanta kamar wacce aka tsikara
_ita kuma..??_ Mama ce take mata wannan magana, bata fatan ta zama irin Basma, azuciyar ta ma tana cewa _"Inaa.. sai dai idan ranar ba ni Hafsan bace._
"Hmm, a yanzu dole kiyi mamaki har ki kalleni, amma zan gaya miki wani abu, _Ba,a zama inuwa d'aya ida
n hali bai zo d'aya ba.!!_
_"Saboda haka, kodai ki rabu da shi, ko kuma ki zama irinshi."_
Kuma kada ki d'auka wak'ar da yake miki na zai aure ki gaske yake.. Duk k'arya ne!!.
"Ni Hafsah banda ma rufewar idanu, ki duba kiga tun sanda kika fara kulashi w
acce riba kika ci a rayuwar ki, banda koma baya da kakai ta samu."?
Iyayenki na d'aukar ki mai hankali, amma yanzu kin nuna musu ba haka bane.. Da an sanki da tsoro, da sanin yakamata amma yanzu komai randomly kikeyi, kawai gaban kanki kike, har kina iya
fita bada sanin kowa ba.!! Sannan kin san a baki abu ki b'oye k'iki nunawa, idan da gaske sonki yake babu abinda zai hana abbanki ya kirashi yazo, ke inya yi niyya ma, abbanki zai bawa abinda zai baki yace a baki.."
"Da yana son cigaba da kulaki ku cigaba
da mu,amala ai zai nemeki duk inda kike.. Amma duk baiyi haka ba, sai ke kike
k'untatawa ziciyarki."?
_Ita dai Hafsah tayi shuru ma da Kukan tana sauraron gaskiyar dake yi mata d'aci, azuciyarta tana ta kokawar dole sai ta kare Yusuf daga abinda ake ji
ngina masa."_
"Ke yanzu ba abin kunya bane, bayan sun kunyata ki agaban mutane an nuna baki da wani matsayi, sannan ki dawo kulashi."?
Wato kin nuna baki da class kenan, kuma babu wanda kike dashi sai shi koh."?
Abin da sukayi kin taba jin wani yaro mai
tarbiyya yayi.."?
"Nidai bazan matsa miki ba, amma ina fad'a miki ki fitar da yaron nan daga zuciyar ki, ki d`auki kaddara, ayadda kika yi sati biyun nan ba tare daya nemeki ba, to ki saba a hakan ki cigaba da rayuwarki harki manta dashi. Zaki sami wanda
ya fishi alkhairi in sha Allah."
Zuciyar Hafsah ta cika fal da kunci, so ya rufe mata ido, da da sa,arta take mata magana babu abinda zai hanata cewa, _"Ai Yusuf bani da wanda zaifi shi a wajena.!!_
Amma sai ta b'ige da cije leb'e kawai, mama fa tana fa
d'ar abinda bashi da ranar yuwuwa ne.
Ita ko Yusuf ya nemeta ko kada ya nemeta, ita zata nemoshi kuma tana da yak'inin bazai taba juya mata baya ba.!
Kamar mama ta karanta abinda ke cikin zuciyar Hafsah tace, "Nid'ai ina fad`a miki ne, duk da nasan magan
ata ba zata taba shiga kunnenki yanzun nan ba, amma kiyi tunani, sannan kuma daga nan zuwa duk ranar da kika sa aranki zaki rabu dashi, to kizo ni kuma zan fad`a miki hanyoyi da matakan da zaki bi in sha Allah, ko wanne irin so kike masa sai kin manta dash
i."
Da a halin farin ciki, Hafsah take to da babu abinda zai hanata yin dariya, ji wasu kalmamomi wai _"wai na manta da Yusuf.!!_
Ashe kuwa ranar, zuciyata bata jiki nah.!! Abinda Hafsah ta sawa ranta kenan..
"Zaki iya tafiya, kuma daga yau zaki iya kom
awa dakin fateema da kwana har zuwa sanda kika ga ya dace ki tuntubeni idan zancen da na fad'a miki ya samu karb'uwa.
Da Wannan mama ta katse mata tunanin ta, wanda akwai hikima a cewar mama, _"Hafsah ta koma dakin fateema da kwana."_
Hikimar kuwa Itac
e, Hafsah da Fateema shekarunsu kusan d'aya ba kamar ita maman ba, sau dayawa yara sunfi yarda da shawarar sa,anninsu fiye da ta iyayensu ko kuma wanda ya girme su. Tasan Hafsah zata iya nemar shawarar Fateema akan zancenta.
"Nagode.!!
Haka Hafsah ta iya
cewa kawai, shima don gudun kada aga rashin kunyarta ne, mama ta d'auka cewa zancenta bai sami shigaba."
Ki dinga addu,a, dai ki nemi zab'in Allah, shine kawai.
Sai yanzu taji sanyi, kuma taji mama ta fad'i maganar da inda addua ce zata iya cewa "am
iin."
"Ki turo min fateema.!!
Mama ta rufe da wannan kalmar.
Ita dai Hafsah gaba tayi kawai, don bakinta yayi mata nauyi, mamaki ma take mama da girmanta amma take son sanya kanta cikin al,amran soyayyar yanzu, Hafsah gani take ma anya mama tasan so ku
wa da take ambata mata kalmar _rabuwa,_ _rabuwa._!!?
😅
Fateema na zuwa mama ta fara fad'ar sakonta babu b'ata lokaci, "Idan yarinya can ta nemi ki ara mata waya, ki bata, matuk'ar kin tabbatar yaron nan zata kira."
Fateema ta waro idanuwa da mamaki, ya
mama da ake zaton zata gyara, kuma da b'atawa."?
"Eh..!! 'Inji mama ganin kallon da fateema ke zubo mata.
_"Ai ko ni bazan goyi bayan Hafsah ta cigaba da mu,amala da wannan mutumin ba.!!_
Fateema ta fada a zuciyarta.
Mama ta katse tunaninta.
"Tashi k
ije idan hakan ta faru, sai ki zo ki labarta min, dalili ne ma zaisa na hanata wayarta, da tatan zan bata."
Babu fuskar yin tambaya ko nuna rashin gamsuwa, don haka fateema tayi azamar mik'ewa tana fad`in, "To mama Shikenan.!!
Mama ta bi bayanta da kallo
, hikimar ta shine "Don Hafsah ta sami damar yin shawara da Fateema, tunda Itace sa,arta zatafi yadda da zancenta fiye dana maman.
Gefe kuma, tana tunanin idan suka jone da yaron, menene mataki na
gaba kuma..."?
Tabbas yarinyar na buk'atar addu,a,
tuna cewa babu addu,ar da tafi ta uwa amsuwa yasa, taja waya don kiran Amina, cikin nutsuwa take kwantar mata da hankali, tana nuna mata komai ya kusa zuwa k'arshen addu,ar ta kawai ake da buk'ata."
_"Ki riqa yin addu,a nan da nan zaki ga komai yazo da sa
uk'i wannan ba wani babban abu bane can.._
Hakan maman ta fad'a mata...
📝
*HAJEEYAH*
*KHAREEMERH*
♥
️
♥
️
♥
️
♥
️
*ZAZZAFAN SO*
(masoyin k'warai )
*Cigaban littafin Zazzafan so*
*(Guba ne)*
💔💔
*By:*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Ha
jeeyah khareemerh)*
*Dedicated to Unique in your love heart group members.*
📄
*44*
*Tun* bayan da Fateema ta koma d'akin babu wanda yace wa wani komai tsakanin ta da Hafsah, kowa na sak'awa yana kwancewa Hafsah zantukan mama da ta d`auk
e su marasa yuwuwa ke mata yawo, Fateema ma, su d'inne dai. _"Mene zai sa ace Hafsah ta cigaba da kulashi."?_
Shirun ya d`auke su lokaci mai tsaho, kafin Hafsah ta nemi guri ta kwanta don gani takeyi gwara ta k'irk'iro bacci, da zaman juya kalaman mama ar
ai, masu tada hankali.
Da safe, ta tashi sakayau, babu wani _tension._ don ta sama wa kanta mafita, kawai gwara tayi watsi da abubuwan da mama ta fad'a mata ta manta
kawai da ta fad'a mata su ta maida hankali akan dawo da Yusuf cikin rayuwarta, la-allah k
o mama ta gane, abinda take fad'an zai faru ba faruwar zaiyi ba.
"Hafsah ta sawa ranta yiwa yusuf uzuri cikin abinda ya faru, da tasirin tuno maganganun shi.. _"Dama na fada miki duk abinda ya faru ke kika jawo.!!_
_Banyi miki cin amanar rabuwa da ke ba.
!!_
To in dai kuwa hakane, ashe ita ce ta nisanta kanta dashi kenan,? Tana son dawo dashi cikin rayuwarta ba don ta biye mishi akan abinda yake so ba, sai dai da nufin, nusar dashi ya gane abinda yake nufin suyi, ba shine abinyi yanzu ba a wajenta. Abin m
amaki kuma sai take yiwa kanta fatan samin nasara mai kama da yak'ini. Ta manta da cewa wanda yayi nisa baya jin kira, kuma mutum baya sauyawa lokacin d'aya, sannan Yusuf kallon da yake yiwa rayuwa da banbanci da irin nata kallon.
_Akwai aiki a gabana."_
Ta fada a zuciyarta tuno cewa bata san ma ta yaya zata fara jawo yusuf d'inba su dawo ma kamar da. Kafin azo ga batun chanja mishi ra,ayi.
Duk wata hanya an toshe, bata da damar kulashi, an hanata fita, gashi bata da waya, sannan tana kunyar ta k'ara aro
n wayar Fateema. Amma kuma gefen zuciyarta na bata kwarin gwiwa.
_"Hafsah kunyar Fateema ne zata sa kiyi sakacin da zaki rasa farin ciki."? Baki da isashshen lokaci fah"_
Ta ke taji cewa a zuciyarta, zata iya tambayar Fateema waya, tunda tana da yak'inin
ba zata iya hanata ba, toh amma kuma idan ta sanarwa mama fah."?
_"Ki rok'eta akan ta rufa miki asiri.!_
wata zuciyar ta raya mata.
Wannan tunanin shine ya dinga yawo a zuciyarta har tsahon kwana biyu.
Abinda Hafsah bata sani ba shine, Basma har text
messages, ta turo a layin Fateema, da taji shuru Hafsah bata zo inda tace su had'u ba.
_"Hmm, dama nasan bazaki iya ba, hmm ke kin isa dama ki ja da Basma Yunus."?_
Sai da _text_ d`in yayi wajen kwana uku, sannan Fateema taga ya dace tayi mata _reply_ b
a tare da ta sanarwa da Hafsa zancen _sms_ d`in ba don gani take yin hakan ma kamar iza wuta ne, amma kuma yarinyar bata chanchanci ayi mata shuru ba, don kada ta zaci ana tsoron ta ne.
Saboda haka da zuciya cike da kishi irin na 'yan uwantaka, Fateema ta
rubuta _reply_ a zuwan Hafsah ce.
_"Ai idan kika ga mutum na tsintar abinda ke k`asa, to ya rasa mai zai ci ne, daga ke har shi kunyi min kad'an in zauna ina bibiyar k'azamar rayuwarku, ke dai da bakya ramin kanki sai kije kiji ta cusa kai da zubar da mu
tunci, ni nafi k'arfi d'aga murya akan abinda kika kula, don bansaki a layin mutane ba bare na zauna damuwa da abinda kika damu dashi, ai ke duk abinda zai burge ki to expired neh..masu hankali bazasu shinshina ba.. To kije ku qaraci k'azamar rayuwarku ni
na wuce ajin kulaku dukanku._
Kalaman sunyi matuk'ar zafi a zuciyar Basma, ita da taso suyi ta jan zaren, tayi ta k'onawa Hafsah rai, amma ta sakar mata, anya