Showing 96001 words to 99000 words out of 132482 words

Chapter 33 - ZAZZAFAN SO COMPLETE

01 Sep 2026

49

na fara ganinki, bare jiya da na k'ara ganinki kinyi min sosai."

Jin zancen da yake yi, yasa ta bada hankalinta gabadaya kan abind

a yake cewa, tana bukatar nutsuwa, sannan bata saba da dinga yin waya gaban wani ba, bare shi da yanzu yake mata wani irin zance, tana bukatar ta saurare shi sosai. Don Allah tayi Zainab nuni data fita.

Zainab tayi mata dariya, sannan ta noke kafad'a.

Za

inab ta aika mata da harara, sannan ta mik'a hannu zata kai mata duka, Zainab ta tashi da gudu tana mata gwalo.

Baiji tace komai ba, don haka ya cigaba da magana..

_Ki yarda dani, ban taba jin ina da niyyar wasa da hankalinki ba, zan fada miki gask

iya, wallahi tunda na ganki naji kinyi min sosai, ina son kulla alak'a dake, ina son ki, kuma zan iya aurenki idan kin amince min..

Ya marairaice murya, "Don Allah idan har banyi miki ba, ki sanar dani, bana son in d'inga bata miki lokaci..

Thanks

for your time, gud night."

Ya kashe wayar take.

Wayar na kunnenta, ta kasa motsi bare ta cire ta, jikinta yayi sanyi da kalaman shi.

Kanta ya kulle tamau, ta rasa wanne irin tunani ma zatayi"? Me yasa yake mata haka. laifin waye a cikinsu n

ata ko nashi."? Ya zaiyi mata magana irin wannan sannan ya kashe mata waya ta ke."? Tunda amsa yake nema daga wajenta to meyasa bazai jira yaji ta bakin nata ba."

Sai kuma ta shiga kasa musu laifukan ita da shi.

Laifinta shine jan aji. Inji wani b'anga

ren na zuciyarta. _"Hafsah kina ja wa mutumin nan aji sosai, yanzu ak'alla kunyi fiye da wata ke da shi,

kuna waya, amma kin kasa sakin jiki da shi, magana ma doguwa bayi mishi kike ba, aganinki zai ta zama dake haka ne."?_

Tayi saurin kare kanta. _Tabb

as tana da dalili lokaci baiyi ba da zata fada mishi irin abinda yake bukatar ji. Tana da buk'atar sanin wasu abubuwa muhimmai ga me da shi."_

Me yasa zai k'i sanar da ita abubuwan da ya dace ta sani game dashi."? Wannan shine laifinsa.

Na nutsa tu

naninta cikin tunano shi, siffofin shi, da kuma wasu abubuwa da ta lura game dashi a had'uwar su.

_Mutumin ya hadu ba shi da makusa ta bangaren halitta. Yana da kyau matuk'a, ga kwarjini komai nashi zai iya burge ko wacce mace._

Yana da barkonc

i, kuma ta lura bai fiya daga kai ba ko nuna isa. Ya damu da ita matuk'a, sannan shi mai mata hidima ne ta gani a zuwanshi wajenta. _A yadda ya nuna kenan a zahiri, don bata san ainihin cikin zuciyar shi ba. Tunda sanin gaibu sai Allah.!!_

Wata zuciyar

ta tambaye ta. To me kike son ki sani banda wannan kuma."?

A zahiri ma sai da bakinta ya motsa, ta furta babu sauti. _Waye shi."?_

Tabbas akwai buqatar ta san waye shi, dan gidan waye, Matsayin karatun shi, sana,ar shi da sauran abubuwa.

Wani

gefe na zuciyarta ya k'alubalenceta da cewa. Yanzu Hafsah don zaki amshi Soyayyar mutum sai kinsan dan gidan waye."? Har da binciken aikin shi."? Anya kuwa son gaskiya kike mishi, ko ma kina son nashin kuwa."? Lokacin da kika amshi Yusuf AI baki kawo wad

annan tunanukan ba sam, ko dan shi bakya sonshi shiyasa kika tsaya tantance wadannan abubuwan, Yusuf kuwa idanunki sun rufe saboda Soyayyar shi koh."?

Sai dai idan ba son gaskiya kike shirin yi mishi ba, kina da abinda kike so kawai.

Gabanta ya fad'i

, bata so ace abin ya zama haka, bata son zargin ya fad'a akan cewa sonshi ne da batayi shiyasa haka. Don haka ta lalubo hujja.

_"Tabbas lokacin da ta amshi Yusuf batayi bincike ko tunani irin wannan ba, ta kalli Yusuf ne kawai a matsayin cikakke wanda

ya hada komai da take buk'ata. Amma yanzu ta mallaki hankali ya dace ta tantance kafin ta zaba ko dan gudun mamaita abinda ya faru._

Abinda kike son sani wannan bincikene na iyaye ba naki ba. Kawai in zaki amshi soyayya ki amsa, da wuri don shima ya nun

a ya gaji da baki lokacin shi.

To idan na shirya amsa ta yaya zan nuna mishi.? Yayi magana bai jira cewata ba ya kashe waya.!!

Ta tambayi kanta.

_Akwai sauran dama.!!_ Ai bacewa yayi ya daina kiranki daga yau ba, kuma dole ki nemo hanyar da zaki nu

na mishi kin amince da shi yadda zai fahimta.

Wayar da ke kunnenta ta shiga k'arar da tasa ta dawo daga tunanin ta take ta kullawa a zuciyar ta.

Tayi saurin zare wayar, sunan Jamila ta gani.

Ta saki ajiyar zuciya, ta daga kiran.

Hello.

"

Jamila tace.

Itama ta amsa da Hello

Jamila kina lafiya.

Cikin muryar ta da dama ta dad'e da chanjawa, tace, "I'm fine. "Ya mutanen gidan ya mum."?

Hafsah taji dad`in hakan..

Lafiya lau." tace tana dan murmushi tace, "Bayan kince zaki zo baki zo d`i

n ba."?

Wallah babu time ne, ina ta son inzo, but zaki ganni, savoda zanje Dubai nan da two weeks so zan shigo unguwar kafin na tafi."

Gaban Hafsah ya fad'i. "Dubai kuma."?

"Kada dai Jamila tayi shaharar zama _International."_

Don haka taga asarar

barin Jamila batare da ta nemi k'arin bayani ba. Da sauri tace.

Dubai me zaki je yi Dubai."?

"Zanyi rakiya ne."!! Jamila tayi magana tana wata 'yar siririyar dariya.

Kan Hafsah yayi wata iriyar sarawa.

Tana son ta k'ara tambayar Jamila, _Wa zata raka h

aka."?_

Amma kuma bata son Jamilar taga kamar tana binciken ta ne. Don haka tayi shuru kawai.

Sai ta juyo Jamila na cewa. "Thank you, ki gaida mama, bari na d'aga wani kira.

"Okay thank you bye bye.

Hafsah tace...



πŸ“



*HAJEEEYAH KHA

REEMERH*

[17/03, 2:46 p.m.] UMAIMA BASHEER: β™₯

️

β™₯

️

β™₯

️

β™₯

️

*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*

πŸ’”πŸ’”

*By*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Khareemerh)*

*Dedicated to unique in your love heart*

πŸ“„

*56*

_NAILA group 1 ina godia da Soyayyar ku... Espclly #ummita_

😊😊

_Sayyada_ kema Inayinki. (NAILA group 2)



*Team Ukhasha

*Team Hafsah.

Inajin dad`in comment d'inku.

πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ

*Ranar* da ta biyo baya, bai kirata ba sam tun daga safiya har wa

ta wayewar garin.

Hafsah ta sanya kanta cikin tsarguwa. Amma kuma tanajin ba zata iya kiranshi ba.

___________________

Yau gaba d'aya busy yake, abubuwa sun mishi yawa, bayan dawowar shi daga office, yayanshi Dr. Sunusi yace ya same shi a gida, za

su tattauna.

Yana dawowa abinci kawai yaci, yayi wanka sannan yayiwa Hajiya sallama ya wuce.

Bayan hira da sukayi ta zumunci, Dr. Sunusi ya bujurowa da Ukhasha maganar da yasa ya kirashi.

"Ukhasha."!!

Ukhashatu ya amsa.

"Naam Yaya.!!

Dama w

ata _share_ ce zan maka talla ko zaka sa kud'inka kaima aciki..

Ukhashatu ya bada gaba d'ayan hankalinshi ga yayan nashi.

Dr. Sunusi ya cigaba da magana.

Wani d'an k'aramin company ne, na had`in guiwa mukeso mu bude ni da abokai na mu shidda, to

kuma mun duba munga muna da buk'atar k'arin kud'i shine muke bukatar k'arin mutum d'aya.

Ukhasha ya gyara zama. Okey Yaya, kamar nawa ake buk'atar kowa ya saka."?

Ba wai bukata ake kowa sai yasaka daidai da na kowa ba. Zaka iya saka ko nawa kake dash

i kawai, tunda za,a dinga raba ribar ne, daidai da yadda kudin mutum yake aciki.

Ukhashatu ya jinjina kai, Okey na gane Yaya, amma kamar nawa kake ganin ni zansa."?

Um..To." Inji Doctor. Sannan ya kalli ukhashatu.

Zaka iya saka 4million, ko da rabi ma

.!!

Ukhasha yayi murmushin gefen kunci.

"Doctor, ansan nauyin aljihun fah.

Na sani.!

Inji Dr Sunusi yana murmushi shima.

"Ka saka 4million d`in dai."

Ukhasha yayi ajiyar zuciya a hankali, Dr. ya kalle shi da alamar tambaya. Ukhasha yace, "da in

ada wani lissafi da nakeyi ne."

Dr. Sunusi yayi murmushi, wanne tunani kuma."?

Ukhashatu ya sunkuyar da kai, yana shiga matsa k'afar shi, dama a kasa suke dukan su a zaune.

Dariya ya bawa, Dr. ma sai da ya gama dariyar sannan yayi magana.

Aure za

kayi."? Bai barshi ya bada amsa ba ya d'ora.

Ka gaji da zaman gwaurontakar kenan...

Ukhasha yayi wani dan murmushi. "A,a fa Yaya."

To mene tunanin naka idan ba shi ba.

Yayi shuru, don bashi da amsa.

Hmm, yanzu dai ka nemo, 4m. kawai kaidai, zamuji dad

`in abin fa idan ya kankama.

Okey in sha Allah."

Inji Ukhasha.

Zuwa Yaushe za,a karbi kud'in.

Nan da wata d'aya muke son mu fara shirya komai, amma muna yin meeting akan yadda abin zai kankama, gobe ma muna dashi, da daddare sai ka shigo muje.!!

O

key, in sha Allah.

Am naji Hajiya na cewa zatayi retire koh."?

"Eh haka tace, nan da wata d'aya ne."

Gud, ai gwara ta huta.!! Inji Dr. Sannan ya shiga wata maganar.

"Yaushe ma Abba yace zamuje gidan gonar nan don na manta.

Nan da sati d'aya ne." C

ewar ukhasha.

Ai abin ne da yawa abubuwan sunyi yawa.

"Ana kokari ai."

Inji ukhashatu, Naji yace yana so ne, ya k'ara fad'ad'a wajen."

"Yayi kyau hakan ai, kaga ya dad'e bai je duba gurin ba fah.

Ukhasha ya jinjina kai, "Eh amma

"yana tura ni akai-

akai ai, kuma naga babu laifi ma,aikatan suna kula da wajen yadda ya dace.!!

So ko zamu bude namu d'an k'aramine haka koda iya kaji ne, da kifi sai mu saka. Cewar Doctor yana dariya.

Ukhasha ya taya shi dariyar shima. "Hmm Doctor kenan.!!

Cikin nutsuwa

yake jawo hakalin Ukhashatu kan abin da cewa, "Ina da wani tunanine, kuma dana bujurowa da Abba shi naga ya nuna jin dad'inshi har ya sanyawa abin albarka ma."

Ukhashatu ya kalle shi irin kallon neman k'arin bayani.

Cikin nutsuwa doctor yace, inaso mu b

ude wani kasuwanci dukanmu har matan ma, kai hatta mahseem sai ansa mata nata kason aciki.!

Ukhashatu ya waro ido.

Doctor ya jinjina kai, Yes, wannan zai kara kawo had`inkai, sannan kuma gaba ake ji ba baya ba."

Ukhashatu ya jinjina kai. "Hakane..abun y

ayi kyau.

Baka ga yadda Abba ya d`auki abin ba, daga yi mishi zancen ni na zaci ma yayi maka zancen.

Ukhashatu ya girgiza kai.

"A,a" Amma waye zai sawa su yaran tunda kace har Mahseem."?

Doctor yace yana dariya. "Abba ne.!! Kuma ai ba wani abu mai yaw

a zai maka musu ba, tunda kasuwanci ne irin na kayan amfani irin na kasuwa da kadan zamu fara, kuma za,a saka equal ne babu mace babu namiji kowa _one hundred thousand._ Yayi kyau Yaya Allah ya bar zumunci ya taimake mu, Allah ya taimaki Abban."

"Amiin

ya Allah. Inji Dr. Sannan ya kuma kallon Ukhashatu.

A ina ka sami yarinyar ne."?

Ukhasha yayi saurin bude baki, "Am ai bamu gama daidaitawa da ita bama."

"Hmm, koh.."? Baka sanarwa da su Abba ba kenan."?

Ukhashatu ya daga kai alamar, "Eh."

C

ikin nutsuwa doctor yake nusar dashi. "Kayi kokari dai, kayi abinda zai farantawa su Abba."

Ukhashatu ya gyada kai, In sha Allah, bamu dad'e da sanin juna bane shiyasa."

Okey, nagane Allah ya tabbatar da alkhairi.!

"Amin Yaya. Sannan ya duba agogon han

nunshi, "Bari na tafi dare yayi yaya.

Okey, ba zaka shiga cikin ku gaisa ba."?

To bari na shiga naga 'yar rigima.

Sukayi dariya sannan suka mik'e a tare.

Suka shiga da sallama. Fadeel na jin muryar auncle ya taho da gudu yana murna "uncle!! u

ncle!! Ukhashatu ya d`auke shi, ya daga shi sama suna dariya.

"Kaii Kaii Kaii." kai fa ka girma yanzu, kayi nauyi "Ya Fadeel zan daina d'aukarka kai da "Γƒrif. Na'eemah kawai zan dinga d'auka.!! Ukhashatu ya fad'a sanda yake sauke shi.

Suka zauna a Kujera

yaron ya zauna kusa da shi."

"Uncle su sunyi bacci."

"Kai meyasa bakayi bacci ba toh."?

"Assignment nake yi, nima yanzu zanyi bacci, aunty dinmu tace ina da k'ok'ari!!

Allah, ai na sani dama _my boy is a gifted.!!_

Suka tafa shida Fadeel d`in suna da

riya.

"Au uncle ina yini."?

Inji Fadeel harda d'an rank'wafawa. Doctor da Ukhashatu suka sheke da dariya, doctor yace, "Au sai yanzu aka tuna da gaisuwar."?

"Mantawa nayi Abba.!! Inji Fadeel.

To Lafiya lau, Fadeel d`ina kana lafiya."? Inji ukhashatu.



Lafiya lau uncle.

Suna cikin haka, maman yaran ta fito daga d'aki.

Au Engr. Sai yanzu kenan ka shigo koh."?

Afwan auntie ina yini."?

Lafiya lau, yasu Hajiya da Abba."?

Lafiya lau suke."?

Ta dan sami guri ta zauna.

"To yasu Fadwa M aryam, kwana

biyu basu lek'oni ba."

"Suna nan kalau, bari na wuce ma kada dare yayi min."

Daga shigowa kuma."? Inji aunty Jamila.

"Dare ne zaiyi min shiyasa"

Eh, kuma kazo kawar taka na bacci koh."?

Eh fa, ai gobe ma zan dawo in sha Allah."

"Tom sai kazo d`in.

Ya mik'e Fadeel ma ya mik'e ya rik'e hannunshi.

Ya kalli, yayanshi. Sai da safe yaya."

Tom ka gaida gida ukhashatu sai goben, ka gaida su Abba da hajiya.

Zasuji, yace, sannan ya juya ga aunty Jamila, Tom aunty sai da safe, Allah ya tashe mu lafiya, agai

da Hajiya da mama."

"Zasuji sosai, yace.

Ta kamo hannun Fadeel, oh baby zo kaje ka kwanta kaji.

Ya noke k'afada "A,a ni uncle zan bi."

Ukhashatu yayi dariya, Aa aboki ka bari gobe zan dawo sai muje gidan Abba amma yanzu kaga dare yayi koh."

Ya daga k

ai, a sanyaye da alama bai so ba."

Ukhashatu ya sake shi, sannan ya laluba aljihun shi babu, ya zaro 500. "Ungo Aboki."

Ya damk'awa yaron.

Asai chocolate yau na manta ban taho dashi ba.

Yaron yasa hannu biyu ya k'arba yana murna.

Thank you auncle, ka

gaida gida.

Aunty Jamila tace, Allah dama ukhasha shiyasa yaran nan suke makale maka, ka daina basu kudi don Allah idan babu alawa a hak'ura.

Yayi murmushi kawai, yana dagawa yaron hannu "Bye bye.

Shima yaron ya daga mishi "Bye bye uncle gud night.!!

U

khasha ya fita yana murmushi.

__________________

Daya koma gida, 11 na dare ta wuce, kafin yayi wasu al,adu da ya saba kafin kwanciya bacci har sha biyu tayi. Dole ya hakura da kiranta da yayi niyya. Gashi ya gaji likis, yana kwanciya babu jima

wa bacci ya d`auke shi mai cike da mafarkanta..

_________________

Tana ta sak'awa da kwancewa akan neman dalilin rashin jin shi gaba-d`aya yau, amma tunanin ta yafi fad'awa kan cewa ya gaji ne, ya yanke hukunci. Hankalinta ya dugunzuma, meyasa bata

mishi koda SMS bane bayan wayar da sukayi. Ta shiga yiwa kanta fad'a, tabbatas da gaskiya r shi, su fa ba yara bane 'yan secondary da zata dinga yi mishi abubuwa irin haka.

Dole ne, ta sami hanyoyin fahimtar dashi abinda take ji game dashi.

Ta lalubi wa

yarta, akan wayar taga dare yayi har k'arfe 11:30pm, taji kamar ta mishi text da _I love you.!_ har ta shiga wajen yin typing message, sai kuma taja dan siririn tsaki, ta fasa.

Sai ta bige da kunna Data, kai tsaye ta shiga wajen sunanshi. Taga rabon da

suyi hira, tun randa ya roketa zaizo wajenta, asama taga _last seen_ dinshi k'arfe tun 9:30 na dare.

Nan ma zatayi mishi magana sai kuma ta fasa.

Ta duba profile d'inshi babu komai ma akai ya cire, takaici ya kamata dama bata taba ganin yasa photonshi

ba kamar yadda itama bata sawa kodan mutane.

Ganin tana bata lokutan ta, akan bibiyarshi da tunaninshi yasa ta matse wayar tata ta kashe ta, gaba-d`aya. Sannan ta nutse kanta cikin bargo wai ita dole sai tayi bacci. Dama kuma tana da fita gobe tana da

wani aiki da sassafe.

Data rufe idon sai taji tana son tunano kamannin shi, ji tayi ta kasa, amma abin mamaki sai ta shiga yiwa kanta dole, da haka tayi bacci.

______________

Kwance take ta nutsa kanta cikin pillow tana risgar kuka, ji take duk d

uniya babu wanda ya kaita bak'in ciki. Gashi a yau d`in dai gaba-d`aya wayoyinta abbanta ya karb'e, ta rasa wanne irin abun bakin ciki ya same ta haka, duk wani da zatayi _sharing_ damuwarta yau ita dashi babu hanya, banda takunkumin hana fita da abbanta y

a saka mata, sannan ya dad'a da kwace wayoyinta.?

Duk bayan minti sai ta tuno da wasu bakaken kalamai da sukafi komai muni a xuciyarta wato.

_"Basma yau dai Allah yayi ikonshi na bada ke, in sha Allah aurenki saura wata biyu, kiyi hak'uri kiyi min biyayy

a, ina kyautata zaton banyi miki zaben tumun dare ba.!!_

Ya had'e rai sannan ya mik'a mata hannu.

"Bani wayoyinki duka.!!

"Zan baki amma sai lokacin da aka d'aura miki aure.!!"

Tuno wad'annan kalamai da suke muna na, a kunnenta yasa ta bude baki

ta kwalla wata muguwar k'ara, wacce lokaci guda kuma tayi saurin toshe bakinta, tuno cewa abbanta na iya jiyo ta, kuma babu abinda zai hanashi hukuntata, koda kuwa da duka ne, don ta kaishi bango.

A hankali take zubar da hawaye tana wani marayan kuka, ta

na kiran mamanta. Har muryata ta dashe, amma bata daina ba, sai da ta raba dare, sannan dakyar bacci ya sace ta..

_______________

Yau da wuri, ya tashi, bayan ya dawo daga masallaci, ya wuce d'akin abbansu don ya gaida shi.

_Khaady_ Yana zaune y

ana jan doguwar tasbaharashi, gefe kuma ga wasu manyan litattafai kusa dashi, sai kuma al'Qurani mai girma. Yau shima yana da wata shari,a da yake saka ran yanke hukunci a yau.

Ukhasha yayi sallama, _khadi_ ya amsa.

Sannan ya shiga gaida shi.

"Abba ba

rka da asuba." Cikin sakin fuska ya amsa.

Barka dai malam, ( _kamar yadda yake kiranshi wani lokacin._) an tashi lafiya?

"Lafiya lau, Akaramakallahu."

"To Masha Allah.

Ukhasha ya k'ara duk'ar da kai sannan yayi magana cikin nutsuwa.

"Abba!!

yaya ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login