Showing 69001 words to 72000 words out of 132482 words
kuwa ba karfin hali H. Hamid tayi ba.. Ya zaayi, ma tace Yusuf ya zama _useless_ a wajenta, baya
n basma tafi kowa sanin irin son da Hafsah keyi wa yusuf d`in.
_"Kai k'arya kike kawai kinji ba zaki iya yakin bane saboda anfi karfinki. Dole ki rungumi sorry_
Abinda Basma ta aiko dashi kenan, zuciyar ta cike da zafin kalaman da aka aiko mata, _bansaki
a layin mutane ba."_
Wato ana nufin ita dabba ce kenan.
" _Haha..ni fa na fad`amiki yusuf bola ce wacce nayar kika d`auka banda hakanw bazaki tab`a iya winning d`in heart dinshi ba yanzu ma da kike kurin, koda ace tabbas kwatuwa yayi daga wajena, ki tun
a da yadda kika kwace shi mana, siya kikayi da mutuncin ki, kika maida kanki qaramar karuwa ko kin manta..."? Kuma n fad'a miki ki jira randa abinda kika tsinta zai tsere miki.!!_
Fateema ce tayi reply da haka. Kan Basma ya kulle, anya kuwa H. Hamid ce za
ta iya turo wad`annan kalaman, yarinyar da tasan ta da tsoro, wata zuciyar tace, zata iya fin haka ma, tunda kinfi kowa sanin me kikayi mata, kuma ai dama shiru-shuru ce, irinsu kuwa babu mai sanin zurfin cikinsu.
Kalmomin sun mata zafi ta rasa martanin m
ayarwa, sai kawai tahau turo da zage-zage Fateema ta ga asarar ta barta don haka ta tura mata reply d`in qarshe da nufin tayi block d`inta.
_Kanki ake ji..kuma nasan rashin abinyi ne yasa kike ta zagi haka, kedai kiji da asarar da kikayi, zagi kuma kanki
kika zaga, kar ki k'ara turo min da text don bani da wata alaqa dake if not kuma...Hmm._
Tana kokarin yin block kira na shigowa ta katse kiran tare da yin block na number.
Fateema ta lura da yawan kallonta da Hafsah keyi da alama akwai magana a bakinta.
"Meya faru ne Hafsah."
Tayi ajiyar zuciya sannan ta fara 'yan soshe-soshe.. "Um Fateema da.. dama don Allah waya zaki ara min in..kira."
Tayi ta rarraba zancen kamar me tsoron tambaya.
"Wa zaki kira."
Fateema ta tambayeta kai tsaye.
"Don Allah ki ar
a min so nake na tabbatar da wani abu."
Me zaki tabbatar."?
Nidai ki fad'amin wanda zaki kira."
Cikin matsuwa take, don haka ta muskuta.. "Don Allah kada ki fada wa mama na ari waya."
"A,a ni nace ki fadamin wanda zaki kira mana."?
"Nidai kiyi alk'awa
ri bazaki fada mata ba.
"Hmm, to meye idan ta sani, nidai ki fada kawai."
Hafsah ta k'ara cewa "Don Allah, kinji."
"To naji, ki fad`amin wanene."?
:Da gaske ba zaki fad'awa mama ba."
Hafsah ta tambaya tana murmushi so take ta k'ara tabbatar wa don gu
dun matsala.
"Kaii wai so kike na rantse neh, Allah bazan fada mata ba, Shikenan?."
Hafsah ta rungumeta "Thank you sister.!!
A kunyace tayi k'asa da murya tace, "Shi zan kira."
"Hmm", inji Fateema.
Don ta yarda Hafsah ta shiga koro jawabin kariya.
"
Kinga dai nice ban neme shi ba shiyasa, gashi bashi da hanyar nema na."
"Hmm, gaskiya.!!"
Cewar Fateema kuma da yake itama tana son a kira d`in don taga k'arshen _game_ d`in sai ta bada wayar.
"Ungo, amma with one condition."
Hafsah ta amsa cikin zumud
i tana zaro ido. Mene."?
"Zaki sa wayar a hands-free naji."
Ita dai Hafsah _buk'atar maje hajji sallah_ don haka tayi saurin jinjina kai alamar yarda.
Take ta danna kiran waya, tayi ringim mai tsaho, aka d'aga. "Hello, akace daga can.
Taji muryar cik
in ko ina na jikinta yaushe rabonta da jin muryar shi, har kwalla ta tarar mata a idonta, Basma tayi mata laifin da baya yafuwa.!
"Hello."
Itama tace da rawar murya.
"Wanene.""?
Aka tambaya, ita kuma ta rasa abin cewa sam, tayi d'if kwakwalwarta ta kun
ne, baya kawai take tunowa.
"Nace wanene."?
Aka k'ara tambaya daga can.
Cikin raunin murya tace, "Nice Hafsah ce fah."
"Hmm.." akace daga can, sannan ba,a b'ata lokaci ba aka katse kiran.
Mamaki da tsoro suka saka Hafsah daskarewa ta kasa motsi.
Yau.
.? Ita.."? Kuma yusuf..? Haka ta faru."?
Fatanta kawai komai ma ya juye ya zama mafarki.
Fateema taji tausayinta matuk'a kuma fuskar ta ta nuna hakan, musamman lokacin da Hafsah take mishi bayanin _"Nice fah Hafsah ce.!_
Akan idonta taga Hafsah ta k'ara
danna kiran, amma ba,a d'aga ba.
Fateema tasan ko ta rarrashi Hafsah rarrashinta bazaiyi tasiri ba, zata b'ata bakinta ne kawai, kuma gwara ma ta kyaleta ta zubar da hawayen ko dan ta rage rad'adin zuciya.
Bata son sauraron kukan, don haka ta mik'e taba
r d`akin sai kuma taga kawai gwara taje ta fad'awa maman.
Maman a parlour take zaune da wani littafi a hannunta, Fateema tayi sallama, ta d'an rakab'e a gefe, tana kallon maman. Mama ta dago ta kalleta don taga alamun bata zauna ba. "Menene kike rab'e -ra
b'e"? Tana Sosa kai tace,
"Um, da dama Hafsah ce tayi kiran a waya.
"Matso nan ki fad`amin me ya faru."?
Ta ajye littafin a gefe ta bada dukkan hankalinta akan Fateema.
_"Kinga data kira, shine yace mata wa ye.. Tana cewa ita ce, yace hmm.. Sai ya kas
he."_
Mama ta jinjina kai.. "Okay okay, shikenan, ba suyi wata magana ba"?
"Eh." inji Fateema.
"Ok jeki nagode."
Har ta dan fara tafiya sai kuma ta juyo cikin k'asa da murya tace, "Um mama don Allah kada kice na fad`amiki."
"Hmm." Mama taji d'an murmu
shi, tayi mata alama da hannu irin, _jeki kawai."_
Tun daga ranar damuwar Hafsah ta k'ara nunkunwa, har Fateema ta saba da ganinta tana kuka haka siddan. Abin ya fara damunta har take k'ara fad`awa Mama, "Mama Allah kusan kullum sai tayi kuka fa take bacc
i."
Jinjina kai kawai maman tayi tace mata, "Toh naji."
Aranar ne kuma mama tayi niyyar d'aukar wani mataki akai.
Da dare ta kira Hafsah d'akinta, "Baki yanke shawarar ba koh."?
Hafsah taji jim, tana tunani, _wannan fa wata dama ce, gwara ta bawa mama
dama ta fad'i abinda ke ranta ko zai zama mafitar ta, don ita kanta ta sani ta damu da yawa, kuma ta gaji da zama cikin k'uncin zuciya.
"Na takura miki koh.."? To tashi ki tafi."
Tayi daurin girgiza kai. A hankali tace, _"Aa wallahi mama, na kirashi ma
bai yakashe."_
Sam Hafsah ta manta ma da mama take magana, abinda ke ranta kawai take son ta fitar.
"Hmm, kingani koh."? "Abinda nake fada miki kenan Hafsah kada ki damu kanki akan mutumin da bai damu dake ba, amma bakya ji."
Abinda mama ta hau fad`a ke
nan, wad`anda Hafsah taji mamakinsu, azaton ta fada mama zata rufeta dashi, akan kub'utar bakin da tayi.
Mama ta kamo ta, "Tashi ki dawo kusa dani kinji."?
Hafsah ta mik'e mama ta rik'e ta harda jingina ta da jikinta, cikin murya mai nuna alhini, take ma
gana.
_"Hafsah ba laifi bane don kinso yaron nan, tunda so baya zama laifin mutum, abu ne da yake faruwa haka kawai. Sau dayawa mutane suna tsintar kansu akan soyayyar wanda bai dace su so ba, amma babu yadda zasuyi._
"Kinga abubuwan da na fad'a miki s
un tabbata koh."?
Hafsah ta jinjina kai. Don tabbas hakan ne.
"Zaki hakura dashi."?
Hafsah taji saurin d'aga kai, don ita kanta ta gaji, gwara maman ta fada mata ta gwada d`in idan zai curu.
Mama tayi murmushi, a zuciyarta tana hamdala.
_"Kiyi hak'ur
i Hafsah, ki d'auka hakan kaddara neh._
Kinji.
Ta d'aga kai kawai.
"Abubuwan da zaki guda biyu ne, na farko aiki ne da gangar jiki na biyun kuma aiki ne da zuciyarki.
Nafarkon shine:
Addu,a.
_"Addu,a ita ce ta farko kuma ita ce maganin komai.
Ki dinga tashi da dare kina fad'awa Allah damuwarki, ki rokeshi ya yaye miki dukkan damuwa._
_Sannan na biyu shine, ki ragewa zuciyar ki yawan tunani, kinajin tunanin shi yazo miki kiyi kokari ki kauda shi da wani abin."_
_"Sannan ki daina
bari zuciyarki na k'awata miki shi, ki mishi kallo da idon da kowa yake kallonshi, kada ki sawa ranki yafi kowa, zaki ji kin rage wani kaso daga sonshi."_
_"Kada ki d'auka idan kin rabu dashi bazaki taba samun wanda ya fishi ba, ki tuna mutane, daban
daban ne, kuma kowa nada tashi baiwar, zaki iya haduwa da wanda ba kiyi tsammani ba a lokacin kuma zaki gane, ashe wancan ba komai bane kawai son zuciyarki ke kawata miki shi."_
_"Kisa aranki zaki iya rabuwa dashi kuma, ba zaki iya sab'awa Allah sabod
a shi ba."_
_"Ki bawa, kanki da rayuwarki, maimahimmanci fiye da shi, yadda zaki yardarwa kanki akwai masu buqatar ki aduniya banda shi, akwai masu son farin cikinki, ko shi baya so, akwai wad`anda suka damu dake kuma sun fishi yawa, saboda haka ba z
aki wulak'anta rayuwarki akan mutum guda d'aya ba."_
_"Ki kalli alkhairan da ke tattare da sauran mutane, masu nuna suna sonki, kada Ki rufe ido akan mutum d'aya."_
_"Ki d'auka cewa, da zaki bawa wani dama, zai miki son da shi baya miki rabinsa,
Hafsah meye amfanin damuwa da wanda ya nuna baya buk'atar ka."?_
_"Ki d'auki lokacinki da muhimmanci kada_
_ki k'arar dashi akan abinda bazai miki amfani ba, ko neman abinda bazai samu ba, kada Ki wayi gari lokacin kuruciyar ki ya shud'e amma baki amf
ani kanki, da sauran mutane da komai ba."_..
Mama tayi murmushi, _"Idan kika saka haka aranki, ina mai tabbatar miki, by time, zaki nemeshi a ziciyarki ki rasa, a hankali Soyayyar shi zata dusashe.!"_
Bance miki lokaci d'aya ba, don komai yana buk'at
ar lokaci, amma ki tsananta addu,a... Sannan kisa a ranki cewa zaki iya kinji.
Hafsah ta daga kai zantukan sun shige ta, sosai, indai har zasuyi mata amfani yadda mama ke nuna mata tabbas zata gwad'a.
A lokacin taji zuciyar ta ta cunkushe, da tunani daba
n-daban ta rasa na d'auka kawai sai ta mik'e a wajen ta kwanta sai kuma bacci.
Bayan ta farka ma hakane, taji zuciyarta tayi mata nauyi, maganganun mama sun tsaya mata a rai, a hankali ta fara hango gaskiya a cikin su.
Yusuf? Shine ya kashe mata wa
ya.."? Jin cewa ita ta kira shi..? To wanne irin mantawa yayi da ita haka.. Lallai tabbas ya nuna mata baya buk'atar ta. Nan take kishin kai ya shiga zuciyar ta, taji aranta tabbas ita ma abu ce mai muhimmanci ba _Banza ba._ don haka ta sawa ranta cewa ba
zata k'ara neman sa ba, matuk'ar bashi ne ya neme ta ba. Basma kuwa zata barta da Allah, don tasan komai lokacine, kuma alhakin ta bazai barta ba.
Kwanaki suka shud'e mama ta daina yi wa Hafsah magana mai kama data Yusuf ko makamancin haka. Gashi ita kuma
Hafsah a kullum maganganun mama suna mata yawo a zuciyarta, ta rik'i wasu daga ciki, misali addu,a, da kuma daukar kai da muhimmanci, sai kuma muhimmanta lokaci, ahankali kuma da taimakon Allah, da amfani shawarwarin hazik'ar mace, wato _Haj. Nafeesah_ a
hankali taji komai yana raguwa daga cikin zuciyar ta, har zuwa yau da zata iya claiming cewa babu d`igon son Yusuf ko ragowar damuwar shi aranta, ya zama tarihi, abin ya na bata dariya idan ta tuno lukutan, babu kamar ma irin musayar kalaman da Basma sukay
i a text ita da Fateema a
zuwan Hafsah ce, sai bayan ta fara dawowa hayyaci, Fateemah ke bata labari.
Zaman wata 3, tayi gidan mama wanda har Abba ya gaji dashi, tana zuwa gida, amma babu kwana, ita kanta tayi kewar komai, tana ganin tarairaya a wajen mam
anta.
Sanda ta cika wata biyu, a iya cewa komai ya saitu, nutsuwar ta ta dawo, to lokacin kuma mama ta nemi da a barta tayi azumi anan, tunda yan kwanaki kawai suka rage.
Daga baya kuma, mama ta dawo da ita gida, godiya kuwa sara wacce, Alhaji Habib Hami
d, zaiyi wa mama, yayi sai dai fatan alkhairi, don kud'i ko wani abin duniya, sunyi kad`an.
Duk wani labarin zaman gidan da Hafsah tayi da yar gwagwarmayarta mama ta bawa mamanta labari. Sannan ta mik'a ledar kyautar graduation d`in Hafsah wacce Yusuf ya
bayar ga maman tare da cewa, "Ki bata sauran ta amfana kawai ita kuma wayar ki mikata ga Abbanta duk ranar da yayi niyya saiya bata a sanda yaga ya dace ta mallaki waya. _"Ikon Allah wai yaran yanzu sun fi bawa soyayya muhimmanci fiye da komai a rayuwa.!!_
Allah ya shirya mana su." Inji aunty Nafeesa, mama tace "Amin.
Ta karbi ledar duka, da niyyar bada kayan duka
abban da hannunsa ya bawa Hafsah, bayan sun gama hirar _yaushe gamo_ a d'akin sa, ya cire wayar, ya bata sauran. Bata ga amfanin su wajenta ba
, tana baro d'akin ta bawa zainab agogon, ta bawa Ameera kuma turaren, tayi cilli da greeting card d`in mufida ta d`auke. Akan idon mama, tana murmushi zuciyarta tana godewa Allah.
Hafsah ita kanta tasan rayuwarta ta chanja, ta girma, kuma yanzu shine lok
acin da ya dace ta maida hankali Don gina gabanta. ( _feature_) Tana gode wa mama, da ta tsamo ta daga garari acikin wad'annan shekarun nata, da lokacin ta kassara rayuwarta to da babu, wani zancen ta yanzu, don da bata tsinana komai ba a rayuwar, da tuni
ta zama abar nunawa. Yanzu kuwa ita ce da digiri, guda aka, tana shirin karbar _certificate_ dinta na NYSC, kuma idan Allah ya taimake ta, zata fara aikinta.? Wai don ma ta bata shekara d'aya, wajen gyaran jarabawa, ( _da ke akwai Matsala a result d'inta n
a farko._) Lokacin Abba yayi amfani dashi wajen kaita makarantar koyon _computer,_ don rage zaman banza.
A irin haka ne wata ran a hanya takan hadu da Yusuf ko Basma ko kuma dukansu, sai dai a kalli juna kawai, Yusuf ne ma ke kokarin boye kanshi baya son
su had'a ido, ita tausayi ma rayuwarsu take bata, daga baya kuma lokacin ta fara makaranta take jin labari yusuf d`in ma yabar k'asar ya tafi k'aro karatu.
Alhamdulillah Allah shine abin godiya. Haka Hafsah ke fad'a bayan ta dawo daga wannan doguwar tafiy
ar tunanin.
Zancen daya tsaya mata arai kuma shine zancen Bashir, Tabbas gaskiya ne, amma zata sanya tunani da hankali sannan da addu,a wajen samun abokin rayuwa na gari. Ta duba agogo k'arfe d'aya har da kwata, mamaki ya cikata, gashi idanunta sun yi nau
yi, ta fara jin bacci sosai, amma tana son ta tashi ta roki Allah alkhairi a rayuwarta, don haka sai da tayi sallah raka,a biyu sannan ta kwanta.....
📝
*HAJEEYAH KHAREEMERH*
Not edited might you face typing error!!
♥
️
♥
️
♥
️
♥
️
*ZAZZAFAN SO*
(
Masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*
💔💔
*By*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Khareemerh)*
*Dedicated to unique in your love heart*
📄
*45*
*UKHASHA*
_______________
*UKHASHA* ABUBUBAKAR (KHADI) shine cikakken suna
n shi, mahaifinshi kuma, ( _Khadi Abubakar_) Babban alk'ali mai rik'e da muk'amin _Grand Khadi_ a babbar kotun Shari,ar muslinci. Sannan kuma limamin masallacin Juma,a ne.
Abubakar Khady, d'a ne a wajen malam _Na,allah,_ shahararren malami, masanin addi
ni, wanda ya rasu shekaru ashirin da suka wuce. Ya bar mata hud'u da 'Ya'ya goma sha hud'u bakwai mata, bakwai Mazaa, mahaifiyar Khady Abubakar Itace uwar gida, kuma 'ya'yanta yawanci sune manya don babu wata tazarar shekaru tsanin aurenta dana abokiyar z
amanta, saboda haka yaran nasu suke tashi kamar ( _sakwanni_) babu tazarar shekaru mai yawa tsakanin su. Sauran matan sun zo daga baya, wad`anda su kuma Allah bai basu rabo a cikin gidan ba, sai dai suma sunzo da nasu yaran daga wani wajen, duk sai aka zam
a d'aya babu banbanci, saboda had`in kai da yake zaunanne a gidan har kawo yau ana zumuncin, har takai acikin 'ya'yansu idan ba manyan ciki ba, basa sanin cewa ba kakansu d'aya ba.
A D'akin su Khady Abubakar, malam _Ayyuba_ ne babba, kuma shine ya gado
mahaifinsu sosai, ma,ana ya gado _malintar._ Sai kuma _Khady Abubakar_ shine na biyu, sai alhaji _Auwal,_ wanda suke kira da (Baffa) Sauran duka mata ne, Haj. Zainab Haj,
Rukayya, Haj. Binta, sai Hajiya, Rabi, dukka suna da aure da albarkar 'ya'ya wasu
suna zaune a garin nan, wasu kuma a wasu garuruwan, kamar sokkoto, zamfara da sauran su. 'Ya'yan d'aya d'akin, su kuma mazan ne su biyar, mata kuma, su biyu, acikin mazan biyu sun rasu a shekarun baya-bayan nan, sumbar iyalai da yawa.
Wani abu daya k
'ara wa family d`in yawa shine duk cikin mazan babu mai mata d'aya banda _(Baffa_ na gadon k'aya,) kuma dukkansu daga matan har mazan, 'y
Ya'yansu zasu kai takwas zuwa goma sha, babu masu k'asa da haka.
Akwai arzik'i da yalwa, a yawanci gidajen wanda s
ai dai na wani yafi na wani, _wannan kuma falalar Allah ce da yake bawa wanda yaso._ Akwai tarbiyya ga yaran nasu, suna da ilimi na addini da na boko. Anyiwa familyn kyakykyawar sheda kuma an sansu sosai. wato _malam Na-Allah family._
*GIDANSU UKHASHA*
____________
Gida ne daya kunshi mata biyu, da yara goma sha d'aya. Hajiya Hafsah, wacce suke kira da _Haj._ Itace Babba, ta fito ne, daga tsatson sarauta,
gaba da baya, kuma ita k'anwa ce ga sarki mai mulki a yanzu. Sannan tana aiki a wata makarantar
'yan mata a Matsayin _principal._ Amma baifi 'yan watanni sukayi saura tayi _retire_ ba.
Sai kuma Haj.Kubra suna kiranta da _Mama._ Itace ta biyu, tana aiki a wani asibiti a matsayin _Nurse_
A 'ya'yan Haj. Hafsah, Ukhasha shine na uku, Babbar 'ya
a duka gidan mace ce, tana aiki da _Ministry of Women affairs, sunanta _Hajiya Na'ima_, a Abuja take da zama ita da yaranta da mijinta. Sai kuma _Dr. Sunusi_, Babban likita a asibitin Malam Aminu kano, yana da aure da yara uku, sai _Ukhashatu,_ kwararen
engineer, wanda ya kware a harkar 'Civil engineering'