Showing 18001 words to 21000 words out of 132482 words
ta mik'e ta bishi..
Suna fita taga ya wani had'e rai.
Tuni tana d'an sha jinin jikinta.Ta rakashi har waje, inda ya ajye motarshi.
Har yanzu ko k'ala
baice mata ba.
Suka tsaya a bakin motar, ta d'anyi murmushi sannan tace,
"Baby me ya faru ne?
Ya d'an kalleta ya watsar. Sannan yace.
"OK, ke biki san abinda kika min ba koh?.. Is good, ai nine nazo gidanku ai,..This gave you opportunity to disgrace m
e!".. Ok let's see if you will see me here again!"
Take tsoro ya kamata. Ta tausasa murya.
"Haba Baby, me kake fad'amin ne ? Me aka maka kuma koh Hajiyah c..
Bata k'arasa ba ya shige motar shi ya figa da gudu ya bar ta da k'ura.
Ta d'aura Hannu aka tar
e da cewa "Oh my God, me ke shirin faruwa da ni ne?
Tana tsayen uncle Abdallah ya fito daga gida, dole ta bar wajen.
Ta shiga gida zuciyarta a jagule.. Wannan wacce irin al,mara ce?
Yanzun idan Yusuf ya rabu da ita ai ta kad'e.. Take kwallah ta ciko mat
a ido.
Har yanzu bata gano me yasa ya chanja mata ba, a cikin abinda baifi mintuna biyu ba.
To koh don ta kaishi wajen Hajiyah ne.? Ko kuma yanayin da Hajiyar ta karb'e shi ne bai mishi ba??
Yace wai tayi 'Disgracing' d'insa?
Bata lura ba ashe har ta
shigo falon Hajiyah, tayi saurin goge fuskarta, kawai sai ta nufi hanyar d'akin kwananta.
Muryar Hajiyah taji tana ce mata,
"Ke Hafsah zo nan"
Dam.. Gabanta ya fad'i, yanayin yadda Hajiyar ta kira ta ya nuna mata akwai wata a k'asa.
Ta tako ahankali ta
zauna a k'asa gefen Hajiyah.
"Gani.
Hajiya ta fara magana fad'a-fad'a.
"A ina kika samo wannan Yaron?.. bata jira cewarta ba ta d'ora.
"Yaro kamar ba d'an bahaushe ba, sai wani turancin k'arya yake yana wani b'ab'bata hausa?..
"Kuma don rashin d'a,a
ya wani gaisheni yana kan kujera koh..?
Wai ku 'yan boko har yana cemin wani 'Bebai' (bye bye) saboda raini
π
" wato don ina kakarki ba zai girmama ni ba. Ko ance mishi wasa nake da ku?..
"Kiyi ha'kuri Hajiyah"
Hafsah ta fad'a tana share kwallah.
"Ke
hak'uri ya kama."
Hajiya ta fad'a tana kauda kai gefe..
"Yo ni Allah na tuba meye abin yabawa a wannan yaro abu kamar 'Karan-bawul'
π€£
"Yaro sam babu hankali a tattare da shi.?
"Shi habibun har yana ina kike kula wannan d'an?"
Gaban Hafsah ya fad'i.
Ya zatayi idan Abba yasan da wannan magana?
Sai yanzu ta gane kasada tayi fa ta kawo Yusuf gidan hajiya, sam ta manta zancen zai iya zuwa kunnen Abba, idonta ya rufe buqatar ta kawai ganin Yusuf, nan fargaba da tsoro suka cika ranta.
"Don Allah kiyi hak'
uri Hajiyah."
"Hmm Ni me akayi min ki tashi kije ki kwanta.
Zumbur ta mik'e dama Zaman ya isheta, to da wanne zataji?
Ta fad'a kan katifa ta kife kanta, tana tuno maganganun Hajiyah..
"Wai Yusuf bai da d'a,a??
To me yayi wa Hajiyan?
Ita bata ga me y
ai mata ba? Meye abin kushewa a Yusuf?
Ahankali taji haushin Hajiyah na shigarta. Yanzu idan taja Abba ya rabasu ai an cuceta..
Sai yanzu take danasanin kawowa Hajiyar shi.
wallahi ba don dare yayi ba babu abinda zai hanata tafiya gida.. Haka kawai don
jininsu bai had'u ba sai ta hau aibata shi?
(A tak'aice dai idanun Hafsah sun rufe, so ya hanata ganin aibin Yusuf.
Ta manta abinda babba ya gani yaro baya iya hangoshi.
Zatonta k'iyayyar Hajiyah da 'Boko' ne yasa ta aibata Yusuf, wanda azahiri Hajiyah
bata k'in boko sai dai tana kyamatar dab'iun turawa da yaran yanzu ke ara yawanci, wanda ita sam 'ya'yanta da jikokinta Allah ya tsare su.
Kana ganinsu kaga wayayyu wad'anda Bokon ya ratsa sai dai kuma wayewa irinta addini da sanin rayuwa da kuma addu,ar
iyaye ya hanasu su kaucewa hanya.
Sab'anin irin Basma ko Yusuf wad'anda basu sami wannan gatan ba. Amma Hafsah sam ZAZZAFAN Son data ke yiwa Yusuf ya hanata ganin hakan.)
Tunaninta ya tsaya data tuna yadda suka rabu da shi Yusuf d'in..
Tayi saurin mik'e
wa ta dauki wayarshi ta danna kiranshi.
wajen sau biyar bai d'aga ba.. Sai a na shidan ya d'auka
"Mene ya faru?
Da haka ya amsa wayar..
Cikin kuka tace:
"Haba Yusuf yanzu na chanchanci haka a wajenka?..Please me na maka? Baka ganin irin son da nake ma
ka Koh?
"To me zan miki ne while kink'i ki min abinda nakeso, mene amfanin relations enmu, kina wulak'anta ni, So I think kawai mu rabu, am tired with this meaningless relation. Wanda babu wani abu da kike min and u always claiming kina so na!?.. A ina so
n yake?
*Nikam nace azuci yake Yusuf*
πππΌ
ββ
Ya cigaba u can't even allow me to kiss you?.. Wanne irin Soyaya ne kina min?..
Sai yanzu Hafsah ta gano zancen.. Tab' al,amra sun Chakud'e.
'Anan ya dace ta fahimtar dashi wani abu, amma kalmar 'su rab
un' daya fad'a shine ya rudata ga kuma tasirin soyayyarshi a zuciyarta bata son ta kuma bata mishi, don haka ta kwantar da murya ta shiga rarrashinshi.'
please kayi hak'uri ni ba ina nufin komai ba ne,..
please ka daina fad'amin cewa mu rabu, numfashi na
ba zai d'auka ba." please am sorry.
"I know I hurt u but
trust..
"Noo ya katseta, I need to rest, ki kyaleni kawai.
Ya katse wayar.
Tafi minti biyar bata motsa ba, bare ta cire wayar daga kunnenta..
Ya akayi Yusuf ya iya fushi haka shi baya lura da
cewa hakan bai dace ba?
Baya tausaya mata da irin son da take mishi har yake ik'irarin su rabu??
Wai Ita meye mafitarta a wannan al,amari, zata kwa iya yin abinda yakeso?.. Wata zuciyar tace
"Idan har shi kad'aine mafita ba!!
To ldan tayi haka kuwa lai
fi nawa tayiwa iyayenta, musammaman ma abbanta?
Ta mallaki waya bada saninshi ba.
(Duk da tana da yak'inin lokaci yake jira ya mallaka mata ko da iPhone ce idan tana so)
Tana tare da Yusuf bada saninshi ba.
Sannan ta zo taci amanar tarbiyyar daya mata?
?
Wata zuciyar tace,
"Hafsah idan fa kika rabu da yusuf kin rasashi fa har abada... Ki tuna gogewarshi da wayewarshi ga kud'i kuma, duk matan garinnan ke kad'ai ya zab'o kina da yaki'nin ('Assurance') baya kula kowa sai ke.
Secondary level kike , amma h
aka ya zab'o ki..
Yusuf ya fiki sanin rayuwa amma ahaka yake sonki. Shin ma ya zaki iya jurar rashinshi bayan shine daidai da burinki?
"Hafsah idan fa kika yi asarar Yusuf ba zaki sami wanda ya fishi ba..
*Ku biyo ni don jin ko Hafsah zata bi layin da j
amila tabi ne??*
*Taku HAJEEYAH KAREEMERH*
πππΌππΌ
*I need your comment to encourage me!*
[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): β₯β₯β₯β₯
*ZAZZAFAN SO*
(Guba ne)
*Abroken*
*heart story*
ππ
Story and writing by:
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Kareemerh)*
*Dedicated to:*
*Unique In Your Love Heart Members.*
π
Doctor Hauwa,u Ibrahim Umar (Gambosy)
π
Maman chappa
Aysha Naseer sheriff
And kawar rai da rai _AYSHA D'AHEER ADAM_
ππππππππππ
*And also My lovely siste
r Sadiya Lawan Abdullah*
*"I love you from the bottom of my heart."*β₯β₯β₯
π
*17*
*Tunani* ya hanata sakat, da k'yar ta samu bacci ya d'auketa.
Da asuba tatashi tayi sallah, amma ta kasa komawa bacci. Tana kwance kawai shiru har yanzu takas
a samun mafita akan al,amarin.
Hajiya dai bata kuma yi mata maganar Yusuf ba.
Da la,asar ta hau shiri. Hajiyah ta kalleta "To Yanzu Hafsah sai yaushe kenan?" k'ak'alo 'yar dariya.
"Hajiyah sai an kwana biyu dai"
"To shikenan, sai na ganki"
Bayan ta g
ama shiryawa ta d'auki jakar ta.
"To Hajiyah zan tafi. To shikenan ki gaida mutanen gidan"
Kyautar atamfa da turare Hajiyar tayi mata.
Bayan taje gida ma tunanin ne ya dameta, ta kira Basma amma wayar ta bata shiga ba.
Gashi yar yanzu Yusuf bai kirata
ba, ita kuma tsoron kiranshi take, bata san abinda zai ce mata ba. Ahankali hawaye yake bin kan kumatunta, wani zafi zuciyar ta ke mata.
Kwance take bisa filo akan gadonta.ta d'aga kanta sama..
Zancen Jamila ta tuna *"Hafsah baki so bane shiyasa*
Tabbas
lokacin hakane, shiyasa taji haushin Jamila alokacin don taga tana kuka akan _rashin-masoyi..._
Ta shafa kumatunta taji hawaye wato dai da gaske kuka take akan wani..?
Ahankali ta mik'a hannu ta d'akko wayarta, text ta rubuta mishi kamar haka:
*I have
committed a sin to make you sad,*
*and am realizing that am very bad,*
*so, plz forgive me* *to lessen the grief,*
*ur forgiveness will led to a relief,*
*So plz forgive me*
Ta tura mishi, sai lokacin tayi ajiyar zuciya.
Bashir ya shigo cikin d'aki n
ata.
"Yaya kizo Abba ya dawo yace ina kike."
Tilas ta mik'e ta nufi hanyar toilet d'inta,
Bashir gani nan"
Fuskantarta ta wanko sannan ta fito ta zari dankwalinta bayan ta b'oye wayar ta ta fita.
"Yaya. Abba ya kirata bayan ta zauna. Ta d'ago ta kalle
shi.
"Na,am ta amsa a k'asan mok'oshi.
Baki da lafiya ne? Ta girgiza kai "A,a"
"To ya kika baro min Hajiyata.
"Tana nan Lpia tace tana gaidaku"
"Gobe in sha Allah zanje in gaidata, kwana na uku kenan ban je ba"
Ya fad'a yana kallon mama.
"Ai shiyas
a na tura Hafsan saboda an dad'e ba,a je mata ba."
Inji mama.
"Ai kin kyauta"
Ya Kalli Hafsah cike da kulawa.
"Ko dai baki so baro gidan Hajiya ba ne?
Ta d'anyi murmushi "A,a Abba"
"Kinga yaya katin DSTV d'innmu ya k'are kinga babu kallo yau, ki ka
ranta mana wannan kinji.
Ya fad'a yana mik'a mata littafin 'Magana Jari ce' (Na Marigayi abubakar Imam)
Ta sa hannu biyu ta k'arbi littafin.
"Abba wanne za,a karanta?
"Ki Karanta mana mai dad'i,ko wanne ma."
Mufida tace "Abba ni ma zan karanta."
Bash
ir ya harareta "sai kace iyawa zatayi.
Abba yai murmushi "Wa yace maka mamana ba zata iya ba? "
Labarin 'HASSADA GA MAI RABO TAKI'
Shi ta fara karanta musu, tanayi abba nayi mata gyaran hausa saboda Hausar irin ta da ce me sarqaqiya.
Labarin nada tsaho
da kyar ta k'arasa.
Ko babu komai Hafsah ta d'an manta damuwarta zama cikin 'Familynta' ya d'ebe mata kewa da kuma damuwa.
Abba ya d'anyi musu sharhi akan labarin, Mufida ta dameshi da tambaya
"Abba Menene 'kusumbi'?
Abba yayi dariya kije ku kwanta da
safe zan fad'a miki.
Yasan idan ya fad'amata sai ta k'ara k'irk'iro mishi wata tambayar.
Suka mik'e suka nufi d'akinsu.
"Ayi addu,a dai, inji Abbah.
"To Abba" Mufida ta fad'a.
Babu laifi Hafsah ta sami nutsuwar zuciya, damuwarta ta d'an ragu game da
Yusuf. Yanzu ta juya akalar tunaninta izuwa nema musu 'Mafita'
akan al,amarin.
Meyasa Yusuf yake haka ne?? wai dama haka halinshi yake ko kuwa jiya ne kawai yai mata haka?..
Ko dai dama bata fahimci halayyarshi bane?
Duk wani saurayi na k'warai mai yi
n so tsakani da Allah ba zai tab'a yunk'urin zubar da kimar wacce yake so ba, zai iya jure komai saboda ita. Amma shi kodai manufar soyayyarshi ita ce 'Neman wani abu daga gareta'??
Tayi saurin korar wannan tunanin daga cikin zuciyarta.
*'So hana ganin l
aifi'*
π
Wani b'angare na zuciyarta ya k'alubalanci zarginta akan Yusuf.
Hafsah biki yiwa Yusuf adalci ba. Shekara d'aya yana jiranki, da haka yake nema daga gareki ke kad'ai ce mace a duniya? Amma haka ya zauna jiranki... Kuma kirasa shaidar da zaki ma
sa sai wannan? Saboda ansami 'Akasi' na lokaci d'aya??
Hafsah ki tuna waye Yusuf, murmushinshi, kalamanshi, soyayyarshi gareki.. Bakya tunanin idan kin rasashi kin tafka 'asara'?
Zuciyarta ta cigaba da karanto mata,hakan ya tilasta mata d'akko laifukan k
acokan ta d'ora su akanta...
Meyasa take yi mishi kwalliya?
Meyasa ma jiyan tasashi kallon cikin idanuwanta, tabbas itace ta jawo koma menene. Ai kowanene ma dole ya sami rauni, balle kuma da tasiri soyayarta.
Dole ne ta chanja tsarin mu,amalarsu...
W
annan ne matakin farko da Hafsah ta d'auka duk don tsoron kada Yusuf ya tsere wa samunta.
Bata samu bacci da wuri ba.
Da asuba Abba ya shigo tashinta, bayan ta yi sallah ta koma ta kwanta, cikin sa,a ta samu bacci mai nauyi.
Bashir ne ya shigo d'akin ya
na dukan filon (pillow) da take kwance.
"Yaya wai mama tace, ki tashi munyi late wai ko baki da lafiya ne?
"A,a yanxu zan shirya."
"Ok Yaufa har 7:00am tayi."
"Ok Kujira ni."
Agurguje ta shirya ta fito.
Amakarantar babu laifi ta d'an saki jiki, tunda
a ganinta ta samo maganin matsalar, sai dai damuwarta d'aya ce 'bai kirata ba' sai kuma tunanin, ya zatayi ta dawo da mu,amalar su kamar da, don tasan Yusuf da tsawaita fushi..
Tana cikin Aji bata fita break ba. Tayi shiru taji an daki bayanta.
"Shegiya
H. Hamid wa ya had'a miki tension? Ta fad'a lokacin da take zagayowa kujerar kusa da Hafsah ta zauna.
Hafsah, ta d'ago da sauri jin muryar Basma yunus.
"Au dama kinzo yau najiki shiru a class"
Tai dariya cikin muryarta mai karad'i tace,
"Wallahi nazo.
Kin san in dai 'Gajere' na class ba,a jin kaina."
Hafsah tayi 'yar dariya.
"Hah Basma Yunus baki bar kowa ba"
"Wallahi kuwa har Daddy"
Hafsah ta bud'e baki zatayi magana sai kuma ta fasa, abin ya fi k'arfinta.
Basma ta d'ana mata duka a cinya.
"Ke
wai me ya dameki ne?.. Jiya fa naga mutuminki a wajen wani party har mun gaisa"
Gaban Hafsah yai wani irin bugawa tace
"Yusuf d'in.?
"Yes"
"Hmm i'm telling you, ai yaro ne tsadadde biki ga 'yan mata First Class ba, yadda suke rububinshi.
Hafash dai j
inta kawai ta ke amma tunaninta na can wani waje.
'Wanne irin party ne haka?
Ta daure tace
"Ke me ya kaiki partyn meye?
Basma tayi dariya.
"You know, ina da wani friend Ahmad. So shine yai inviting ena na graduation en wani abokinshi, so ashe abokin Y
usuf ne ke graduation en"
"Wallahi Yusuf ya iya rawa biki ga ba, kinyi dace k'awata. Ina ma kaina 'wishing' in samu kamar Yusuf."
Ran Hafsah ya d'an sosu taji kishi ya d'arsu a zuciyarta.
Tai ajiyar zuciya kawai.
Ta bud'e jakarta ta d'akko musu snacks
da lemo,
"Muci ni yunwa nakeji."
"Akwai abinda ke damunki fa"
Cewar Basma.
Hafsah tace
"Hmm ke dai bari. "Munsami misunderstanding ne da shi"..
"What, Meya had'aku.?
Hafsah sai taji ta kasa fad'a wa Basma.
"OK, tunda bazaki fad'a ba.
"Kinzo da w
aya.?
Hafash ta girgiza kai.
Basma ta ciro wayarta.
"Am bari mu kirashi saka number en. Banyi serving ba.
Hafsah tasa number tana cewa "Sai dai ki mishi magana idan yaji nice ba zai d'aga ba."
"Ok"
Yana d'agawa Basma ta kashe murya.
"Hallo,Basma ce
k'awar Hafsah."
"Ok how are you"
"Very fine"
"Am mene ya had'aku da Hafsah ne?
"Hmm, Basma your friend dont' care about me"
"Bata damu dani ba ne"
"No,ba haka bane meya faru?
"K'awanki bata sona, tana guduna ne she disgraced me! " she dn't allow m
e to touch even her hands, not talk about kissing.."
Ya fada bbu ko kunya.
""Hmm, I get an opportunity"
ππΌ
Basma ta fad'a aranta.
A fili kuma cewa tayi, "Am sorry, this is not a problem to worry about."
"What? Me kina nufi? "
"Calm down kasan yanayi
n ba da'ya ba, So I think my friend don't have interest about it"
"Hmm ok" Thank you"
"Kayi hak'uri fa"
No I know how to deal with her.
"Ok Gata to"
No ki rabu da ita.
"A,a dai"
"Ok"
Ta mik'a mata wayar.
"Hello,
"Hum, Hafsh me yasa kike min haka
ne?
"Am sorry please I don't mean to hurt you my dear"
"Hmm, ok zamu yi waya to night."
"Bye"
Hafsah ta rungume "Basma thank you my friend"
"Me ya ce miki ne? kinsan wayar ba a hands-free take ba."
"No, ki share tunda yace komai ya wuce.
"Ok"
Hafs
ah dai wasai take jinta,sun shirya da Yusuf d'inta.
ina sonka Yusuf d'ina Allah ya tsaremin kai!!
Basma ta bita da kallo..
To da yamma bayan abba ya dawo daga wajen aiki gidan Hajiya ya wuce, bayan sun gaisa tasa aka kawo mishi abinci.
Yana gamawa akay
i kiran sallar magariba yai al,wala,
"To Hajiyah daga can zan wuce."
A,a ka dawo dai"
"To Hajiyah.
Bayan ya dawo ya zauna a k'asa, yana fuskantarta, yasan da akwai maganar da zasuyi.
"Na dawo Hajiya"
"To madallah."
Dama cewa nayi shi wancan yaron d
a yake zuwa wajen Hafsah an daidaita ne?
Abba yaji abin banbarakwai,
"Wanne ake magana Hajiyah?
"Au to ,baku kirashi ba kenan."
"Wani yaro ne haka Mara k'iba. Shekaranjiya ya kirata a salularta (waya) ya zo ma nan sun gaisa."
Kan Abba ya kulle amma gu
dun kada Hajiya ta gane yace
" Oh to, eh saboda bata gama Makaranta, bane shi yasa"
"To yadai dace a tuntubeshi aji idan da gaske yazo."
"To za,ayi hakan Hajiya."
Yayi mamaki da Hajiya ta ambaci waya, amma don ya sake tabbatarwa sai yace.
"A wayarta k
enan ya kira, sannan yazo Koh?
Hajiyah tace,
"Eh mana, kasan zamani cigaba yazo, da ya iso ma kiranta yayi ta fita."
"To Hajiyah ni zan koma."
"To ka gaida mutanen gidan."
"Allah ya kiyayeku Allah ya tsareku, daga mugun ji da mugun gani. Allah yai muk
u albarka."
"Amin Hajiya, Amin".
"Sai da safe"
"Allah ya tashe mu lafiya"
"Amin"
Abbah tuk'i yake amma gabadaya ranshi ab'ace yake, ya kasa yarda da abinda Hajiya ta fad'a mishi, yama za,ayi ayi haka? 'yarsa?..Hafsah?.. Ta mallaki waya bai sani ba? Ta
dinga zance da saurayi wai duk bai sani ba?
Yasan tabbas da sanin mamanta.
Lallai zai nuna mata b'acin rai in dai haka