Showing 99001 words to 102000 words out of 132482 words
yayi min magana akan wani d'an company da zasu bud'e shida abokan shi."
Khady ya bada hankalin yana sauraron shi.
Ukhasha ya cigaba.
"To yace idan ina so nima zan iya saka nawa kud'in."
Khady ya nunfasa sannan ya fara magana, "Eh nasan da
zancen, ya fad'a min zasu bud'e companyn sarrafa shinkafa ne koh."?
Ukhashatu ya gyad'a kai, "Eh shine."
"Yayi kyau hakan, nawa zaka saka aciki kai."? Cewar Khady yana kallon Ukhashatu.
Cikin ladabi Ukhasha yace, "Shine nake so a bani shawara Abba."
Khady yayi yar dariya, sannan yace, _malam_ kenan, "To ai shawara na wajenka, kai kasan nawa zaka iya sawa."
Ukhasha ya d'anyi murmushi, ya sosa kai.
Cikin Hikima Khady yace, "To komai dai za,ayi ayi daidai misali dai, yadda ba za,a takura ba, idan
Allah ya sawa abin albarka sai kuga yana ta hab'aka."
Ukhashatu ya jinjina kai.
"Shi nawa yace ka kawo."? Khady ya tambaya.
"Bai kayyade min ba, amma ya bani shawara.
Yace ka saka nawa.
"Million hud'u." Ukhasha ya fad'a yana sunkuyar dakai.
Khady y
ayi dariya me d'an tsaho.
"Kana da million hud'u Ukhashatu."?
Ukhashatu ya hau shafa kai.
Khady ya cigaba da magana.
"Amma baka fara ginin ka ba koh."?
Ukhasha yayi tsit, saboda anzo wajen.
Khady ya takaita zancen da cewa, "Ka saka million uku
kaga babu takura koh, tunda shima million shidda ya bada."
"Nagode, Abba Allah ya k'ara girma."
Ya shiga godiya kamar wanda akayi wa kyauta.
Sannan cikin nutsuwa Khady ya kira sunanshi. "Ukhashatu!!
Ya amsa a sanyaye.
"Na,am Abba."
Khady bai jir
a komai ba ya fara maganar da zaiyi.
"Basai an fad'amin ba, nasan kana da isassun kud'in da zaka fara gini, idan aure ya zo maka ma kuma kayi shi, hakane koh."?
_Yana sane ya maida zancen salon tambaya._
Cikin sanyi Ukhasha ya hau gyad'a kai.
"T
o ka samu ka fara gininka cikin watan nan. Abba ya fad'a yana d`auke murmushin fuskar shi don Ukhasha ya san bada wasa yake mishi ba.
Cikin ladabi ya shiga d'aga kai, zanyi Abba in sha Allah, a taya mu da addu,a."
"Addu,a ai kullum cikin yi muku ita
ake Ukhasha kuma in sha Allah, Allah yana amsawa."
Ukhasha, ya motsa kamar zai mik'e don yin sallama da Abba ya tafi, yaji Abban na wata magana.
"Kaji yau in sha Allah, masu kawo lefen maryam zasu zo koh, kuma za,ayi bikin cikin sati uku"
"Allah y
a sanya alkhairi Abba. Inji Ukhashatu.
Amiin ya allah, Khady ya fad'a yana k'ara kallon Ukhasha kamar zai mishi magana, sai kuma bai ce komai ba. Shi kanshi Ukhasha a tsarge yake, Allah-Allah kawai yake a sallame shi ya tafi.
Sai kuma ya tsinkayi abb
an nacewa, "Yau baka je daukar karatun ba ne."? ( _yana nufin makarantar manya da Ukhasha yake zuwa da asuba, a wani masallaci kusa da su_)
Yayi murmushin jin dad'i, don bai zaci haka abban zaice mishi ba.
Eh Abba, yau ana idar da sallah gida na yo, sabo
da inason zan fita da wuri.
"Khady ya gyada kai, amma gashi ka b'ata lokaci anan.
Ukhashatu yayi yar dariya, "Aa, Abba, dama inason ganawa da kai d`in.
To yayi kyau tashi maza kada a makara.
Ukhasha ya mik'e.
Nagode Abba a huta lafiya.
Khady yayi m
urmushi yana bin shi da kallo.
_____________
Fitowar ta daga wanka, kenan tana goge jikinta da towel, wayarta ta shiga yin d'an kida.
Batayi mamaki ba don tayi zaton abokan aiki ke neman ta.
Tayi saurin k'arasawa inda wayar take don dubawa ta d
'aga.
Wata iriyar faduwa gaba taji, wacce sai da ta d'an had'a da da fe k'irjinta.
Cikin mamaki tayi saurin d'agawa zuciyarta tana cewa, lafiya kuma kiranshi da sassafe."?
Cikin sanyin murya tayi sallama, sai kuma taji shi muryarshi ras ya amsa mata.
Hakan yasa taji babu wata ragowar damuwa a tattare da ita.
Ranki ya dad'e Barka da safiya, Allah yasa dai bani na tasheki ba da safenan.
Ya fada da nutsuwar murya kamar ko yaushe, wanda tunda ya fara magana take murmushin boye, na jin dad`in muryarshi.
Uhum."?
Taji yace, ta kalli kanta, daga ita sai towel, sai taji tana jin kunya gani takeyi kamar zai gano ta.
Tayi murmushi mai sauti, dayaji shi sosai har cikin jininshi.
Ga mamakinshi sai yaji tace, ka tashi lafiya."?
Ta gano farinciki tsababa
cikin muryarshi sanda yake amsa mata.
"Lafiya lau _my queen,_ ai da tunaninki na tashi.
Tayi murmushi itama.
Jiya bamuyi waya ba, ji nake kamar mun shekara."
Itama a zuciyarta haka ne amma bata furta komai ba sai murmushi.
Cikin rage sauti yace mat
a, I miss you dear, you do miss me too."?
Ya fad'a kamar rad'a.
Babu wani tunani ko bata lokaci taji bakinta ya furta _"yeah!!."_
Ukhasha tsaye yake, amma babu shiri ya zauna, a gefen gado.
Really."? Yace mata cikin taushin murya.
Ta toshe bakinta,
tana yar dariya, tuno abinda bakinta ya fad'a.
"I have to go to work earlier today, ina son in shirya."
Ta fa ke da fadar haka.
"Dariya, yayi mata shima, yasan dalilinta na fad'ar haka, "me too."
Yace mata, kinga nima shiri nake, amma ina son inji ki
..
"bazan iya aiki ba idan banji muryarki ki da safen nan ba."
Tayi murmushin jin dad`in kalaman shi.
Lokaci d'aya kuma taji yace, kada na tsaida ke koh, bye."
Itama "OK bye" tace mishi.
Ya k'ara mata da "I love you."
To fa anzo wajen sai tayi ts
it kamar babu ita.
A hankali taji yace mata, "Kinji."?
"Um." tace mishi.
Cikin marairaice murya ya ce, to ni me zaki ce min."?
Tayi shuru tana tunanowa, wato yau dai k'ure ta zaiyi.
Uhum."?
Ya k'ara tambayar ta.
"Thank you!! tace mishi.
Yayi kamar
baiji ta ba, ya d'ora da.
"please Say you love me too, please Hafsah.!!
Ta nemi guri itama babu shiri ta zauna jin yanayin muryarshi.
"Please!! taji ya k'ara fad'a.
Nan ma shuru tayi,
please Hafsah ki taimake ni!! Ya fad'a murya can k'asa sosai.
(
Kiran sunanta da yake ba k'aramin tasiri yake ba.)
"Nan ta shiga tunani akan ta fad'a ko kada ta fad'a."?
Cikin sanyi ta juyo shi, yana cewa "Okey can't you."?
Bata son su kuma maimaita irin na rannan, don haka da sauri wanda shima babu zatonshi yaj
i tace, _"me too."!!_
a k'age yace, "You too what.."?
Hmm, tace.
"Ki daina min rowa don Allah wallah kina wahalar dani.!!
Tayi jim na wasu muntuna tana hasashe.
ta jiyo shi yana cewa, idan nine bazan kasa fad'a miki ina sonki ba, wallah I love
you with all my heart Hafsah.
Da alama zancen zuci yake, ta fahimci wasu abubuwan suna zuwa bikinshi ne batare da niyyar shi tayin hakan ba, haka kuwa na nuni da zallar soyayyarta ne cikin zuciyarshi.
murya na d'an karkarwa tace don ta huta itama, _i
love you too.!!_
Zo ki ga farin ciki gurin ukhasha, har sai da ya zame ya kwanta.
Yana rik'e da wayar amma yayi shuru.
Itama wani iri take ji, har wani zif-zif take ji a jikinta.
_Anya kuwa tayi wa kanta daidai.?_
Sai da ya gama saita kanshi san
nan ya sauke wata ajiyar zuciya a hankali yace, "Nagode, "Nagode Hafsah, in sha Allah by time zaki fahimci irin son da nake miki, kuma in sha Allah bazan taba baki kunya ba, zakiyi farin ciki dani.
Thank you.!!
Ita dai bata da bakin magana, ya san ba zat
ayi d`in ba, don haka yace..
"Hafsah.! A hankali.
Ta kasa amsawa don bata son ya k'ara jin muryarta a lokacin saboda kunyarshi.
"Ina sonki." taji yace mata, maganar da ta k'ara kashe mata jiki.
Ki shirya kinji, kada na saki kiyi late.. nagode, Alla
h ya tsare min ke."
Babu sauti amma ta motsa bakinta wajen cewa, "AMIIN."
Don taji dad`in kalaman shi.
Tanajin karar katse kiran shi amma bata motsa ba, ji take kamar ta sauke wani nauyi daga kanta, haka kawai ta yardarwa zuciyar ta, ukhashatu ba k'
aramin sonta yake ba, daga jin muryar shi zaka tabbatar da haka.
A hankali ta motsa ta d`auki mai da niyyar shafawa, gaba-d`aya ji take kamar an kwashe mata duk wani _energy_ da ke jikin ta.
A sanyaye ta dinga yin komai, gefe kuma na zuciyarta tana m
amakin kanta, da kuma tuhumar kanta kan kalmar da ta furta da sanyin safiyar nan.
Azuciyar ta take fata, _"Allah yasa takai Soyayyar ta inda zata sami kulawa, ba inda za,a cutar da ita ba."_
Bata sami nutsuwa ba, har sai da raunin da jiki da zuciyart
a yayi ya kaita da fitar da wata 'yar kwalla, sai da ta goge a hankali, sannan taji ta sami k'wari.
Tun bakwai take shiri, amma saida nawa ta kaita har k'arfe takwas, hakan yasa mama biyota.
Ta ganta zaune ta gama saka kaya, tana d'aura d'ankwali.
Yaya, me kikeyi hakane, keda kika ce da wuri zaki fita kinga takwas har tayi fa.
Ita kanta ba zatace ga abinda ya tsaida ta d`in ba.
"Na gama mama."
"Kiyi sauri kizo kiyi break dai."
Ta gyada kai.
Gani nan mama."
Maman ta juya itama ta fita.
Ukhashatu, tsahon ranar yinin farin ciki yayi, jiyake babu wanda ya kaishi farin ciki a yau. Godiya yake kawai ga Allah don shi ya mallaka mishi ita. Zuciyar shi cike take fal da tsare tsaren yadda rayuwar su zata kasance shida ita.
Bai iya jure
wa ba, har sai da kira wayarta da azahar amma Hafsah taki d'agawa, ji take bazata iya mishi magana a yau ba.
Yayi murmushi lokacin da kiran ya yanke.
Kawai sai ya zana mata _text messages_
_"Hmm, dole kik'i daga waya mana dama, kin rikita bawan Allah,
kin barshi a rikice kuma.!!_
Text d`in dariya ya bata, ta dinga yinta, har abokiyar aikinta na tambayarta "meke faruwa."?
Sai kuma ta dinga jin kamar da ita yake, domin itace a rikice ai, tun safiyar yau."
Don ta kare kanta ta aika mishi da, _lots
of work dear, let's phone to night.!!_
Sanda ya ida karantawa, sai da ya maimaita kalmar _Dear_ a fili.
Ya dinga murmushi shi kad'ai shima, yana fatan daren yayi da sauri.
Amma murnarshi ta koma ciki, daya tuna yana da meeting da daddaren..
📝
*HAJEEEYAH KHAREEMERH*
[17/03, 2:48 p.m.] UMAIMA BASHEER: ♥
️
♥
️
♥
️
♥
️
*ZAZZAFAN SO*
(Masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*
💔💔
*By*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Khareemerh)*
*Dedicated to unique in your love heart*
📄
*57*
____________________
Bai samu ya kuma kiranta ba a ranar, itama kuma sai taji tana da jiran kiranshi, amma bai kirata ba, haka ta hakura har zuwan lokacin baccinta.
Tana mamakin dalilin daya tare shi ga barin kiran nata.
Ranar data biyo baya, sukayi waya, dole ta saki jiki da shi, saboda salon shi, gareta. Duk wani abu da ukhasha zaiyi ya tabbatar mata da son da yake mata yayi shi, wani ta mayar mishi wani kuma ta bishi da murmushi ko tayi shuru, don yanzu ta gama fahimta
r dawa take tare. _Wato shi mutum ne daya k'ware a ko ina, yana matuk'ar son yaga ya sakata farinciki kuma._
Daga k'arshe yake rok'onta akan ta barshi ya k'ara zuwa ya ganta.
Da take tambayar shi, yaushe yake so ce mata yayi.
Ko yaushe kika ce nazo zak
i ganni."
Tayi dariya Kawai sannan tace, Aa dai mu bari sai k'arshen sati."
"Babu musu ya amince.
Allah ya kaimu lokacin."
Amiin tace mishi.
___________________
Shiri sosai Hafsah ta dinga yi ranar da ya kama zai zo d`in.
Har tunani ta sh
iga yi, me ya dace tayi mishi na tarbarshi."
Ta kasa tunana komai, k'arshe ta yanke shawarar bashi lemo da snacks kawai tunda suna da shi.
Shiri tayi alwashin yi sosai akan zuwan na shi. Ba su kara yin waya ba tun bayan wayar da sukayi, da rana.
Wani abu da ya da ya wargazawa Hafsah shiri, wanda badon zuwan Ukhasha ba babu abinda zatayi farinciki dashi kamar shi, amma sai zuciyarta ta kasu biyu gefe na jin dad`in hakan gefe kuma naga tunanin gudun samun matsala. Wato abin ba komai bane fa ce
zuwan _Jamila_ a ranar.
Misalin k'arfe uku da rabi daidai na yamma, lokacin Hafsah na cikin toilet, don tayi alwashin shiryawa da wuri, ba zata b'ata mishi lokaci ba, sannan tayi alwashin zata nuna mishi soyayya daidai gwargwado yadda zai fahimci tana
son shi itama.
Tana cikin band'akin taji sallama daga palourn mama kamar anyi bak'uwa. Bata damu ba take wankan ta a tsanake.
A falon kuma, mama ce zaune ita da mufida, tana mata tausa a k'afa, sukaji anyi sallama da wata iriyar muryar da ta saka
su juyawa duka, don basu gane wanene mai muryar ba.
Mama wata hamshak'iyar babbar mace ta gani, a cikin falonta, wacce ita a ganinta tafi mata kama da irin mata 'yan siyasa.
Mufida kuwa idonta ne yayi wani harr, sai da mai sallamar ta k'aras Shigo
wa sannan ta gane ta, don sun ganta Kwanaki ita da su yaya Hafsah.
Mama ce tace mata, "sannu da zuwa, zauna mana."
Ta tsuguna ta gaida maman kafin ta zauna a kujerar da aka bata.
Abun ya bawa mama mamaki matuk'a, kafin ta kai ga tambayarta wacece, ita
taji tanacewa.
Mama, Hafsah na nan."?
Eh tana nan inji mama, tana k'ara kallon Jamila.
Sannan ta kalli mufida, "Jeki ki kira Hafsan."
Maman taga alamun kamar mufida tasan bak'uwar, amma babu damar ta tambaye ta, sannan da taji wajen Hafsah tazo,
sai tafi alak'antata da abokan aikin Hafsah. Amma kuma taji kamar tasan muryar, amma ta manta a ina."?
Sanda mufida ta shigo d'akin hafsah na shirin fitowa daga toilet d`in, don haka ta d'an jirata ta fito.
"Yaya kinyi bak'uwa.
Hafsah na tsane ruwan j
ikinta da wani towel d`in banda wanda ta d'aura, ta kalli mufida. "Bak'uwa kuma."?
"Eh, Wannan da muka gani a park dinnan ce.!
Gaban Hafsah yayi wata iriyar bugawa.
"Toh, jamila!!
Ta fad'a a hankali.
Sannan ta goge fuskarta kafin ta kuma cewa, "Kice
ina zuwa bari na shirya."
Tunda aka, fad'a mata zuwan bak'uwar taji jikinta yayi sanyi.
Da kyar ta tattaro nutsuwa, ta shafa mai sannan ta dakko kayan da tayi niyyar sakawa tasa.
Bata tsaya shafa ko da powder ba, shima kafin ta k'arasa sai da mama
ta leko ta.
"Hafsah kiyi sauri mana kin barta tana jiranki."?
"Mama gani nan, yanzu zan fito." Ta bada amsa da haka.
Maman ta k'ara kallonta sannan ta juya ta fita.
Leshin ya amshe ta sosai, tayi kyau duk da bata shafa komai ba, d'an kunne da ag
ogo kawai ta saka, sannan ta fito palourn bayan tayi amfani da turarukan ta.
A palourn sunyi shuru, duka, sai Jamila da jefi jefi take kallon wasu shashi na palourn.
Gidan ya chanja sosai ba kamar yadda tasan shi da ba, an sami cigaba a tsarin gidan da
komai ma.
Mama ce ta gaji da hasashen son gano wacece, don haka ta kalli Jamila tana murmushi tace, "Um kema wajen aikin naku d'aya da Hafasan ne."?
Jamila tayi yar dariya sannan tace, Aa, mama baki ganeni ba koh."?
Mama ta jinjina kai, naga kama
r na san fuskar koh kina zuwa gidan ne.
Babu jiran komai Jamila tace, "Mama Jamila ce fah."
Tana murmushi.
Mama kallonta ta tsayi sosai, kallon mamaki da tambayoyi, da k'yar ta d`auke ido, tace tana 'yar dariya.
Laa, ai ban ganeki ba sam, as
he kece."
Daga nan ta rufe bakinta.
A Kofar shigowa daga waje ta palourn, Basheer ne ya shigo da sallama.
Mama ta amsa mishi, ya k'araso ciki, daidai lokacin kuma Hafsah itama ta fito daga d'akinta tana takowa zuwa cikin palourn.
Sai da Basheer yaz
o Tsakiyar palourn sannan yaga fuskar bak'uwar don kujerar da take kai cikin falon take kallowa, sai kuma yaga Hafsah ta fito tana fara,a cikin shigar da tafi kama data fita, badon bata saka mayafi ba, sannan yaji cikin fara,a tana ambaton sunan Jamila.
"Ah, Jamila Sannu da zuwa ashe kece.!!
Maganar data saka Basheer, juyawa ya kalli Jamila sosai.
Ta ganshi itama. Amma basu yiwa juna magana ba, ya nemi guri a kujera 1 _seater_ ya zauna.
Yana bin Hafsah da wani kallo na tuhuma lokacin da take
cewaJamila, "shigo ciki mana."
Jamila ta mik'e ta bita. Mama bata ce musu komai ba sai kallo da tabi Jamila da shi, sannan ta k'ara sauke kallon akan Basheer.
Suna nesa dasu, bakin Basheer ya bude rai a b'ace yace, "Mama wai meyasa Yaya zata dinga yin
irin haka ne."
Mama ta gane akan me yake magana, amma sai ta cigaba da kallonshi don neman k'arin bayani.
Meyasa dole tace sai ta kula waccan, bata ganin yanzu ba da bace, kinga ta gayyato mana ita gida koh."?
Mama ta danyi murmushi sannan tace
, "Haba Basheer ai ba,a gudun mutum a duk halin da yake ciki, kuma ni yarinyar shekarunta nawa rabon da ka ganta a nan gidan, tun sanda akace _tabar gidansu fah._ Ba yawo sukayi da yayarka ba bare kace janta take suna fita."
Basheer ya sake bata rai, "N
idai mama bana son tana kulata bare har ta dinga zuwar mana gida, dama na sani tun ranar da muka ganta a park, Yaya ta wani rikice data ganta, saida taje sukayi magana sannan taji dad`i, shine fa sukayi exchange numbers"
Mama ta d'anyi shuru kafin tace,
"Ba fad'a ya dace kayi ba, bayani zakayi mata yadda zata fahimta, amma ka fara zuba ido kaga tunda ai yau ka fara ganin tazo gidan koh."? Kuma ko babu komai Hafsah fa yayarka ce dole ka bi ta a hankali."
Basheer yayi shuru yana had'e rai, _shidai sam b
ai gamsu da zuwan Jamila ba, kuma har su shige daki ita da yayarshi._
A cikin d'akin kuma, suna shiga Hafsah cikin farin