Showing 12001 words to 15000 words out of 132482 words
yana kad'a kai.
Suna fita Basma ta Shek'e da wata shashashar dariya..
Tana wani abu da fuskarta kamar ta ga wani a
bin tsoro, look at your reaction H. Hamid, when Teacher catched us,...
π±π¨π€₯
uhum kamar kinga zaki" hahh
ππ
A gida kuma mama tunani takeyi akan, Kodai ta bawa Hafsah wayarta ne, a tunaninta, hafsah 'ya macece wacce Yanzu shekarunta sun kai 17, bai dace
a matsa mata ba, don takai munzalin tsayawa da saurayi. Don ma abin ya zo da zamani da dane ai da tuni tana d'akin mijinta..
"Ai kuma ya dace ki nuna mata kuskurenta"
Wata zuciyar ta fad'a mata...
'Zan bari zuwa suyi hutu'
Haka mama ta kudurce a ranta.
.
To kusan kullum a makaranta sai Hafsah sunyi waya da Yusuf, kuma kullum zancen shi d'aya yaushe zai zo?
"Ka bari dear, ka bani two weeks"
Haka ta fad'a mishi wata rana, lokacin sun fara jarabawa.
"What? Mene kina cewa??
"Ok bakya sona ne I realize
d, ok I will leave you kawai"
Ya fad'a, kawai ya kashe wayar.
"Na shiga uku Basma kinji wani abu kuma"??
"To ya zan miki an baki shawara kink'i karb'a, ba saiki bari ya kub'ce miki ba."
Ta fad'a cikin rashin nuna damuwa da zancen.
"To aini basma tsoro
nakeji..
"To ai shikenan"
Ta kuma kiran number ba,a d'aga ba.
"Oh my God! dama haka yake da fushi?.
So bata kuma samu sunyi waya ba sai ana gobe hutu (Bayan malaminsu ya kirata ya mata fad'a akan karatu )
Da k'yer ta samu ya hak'ura, amma yace mata d
ole ne su had'u cikin wani satin.
Aranar da aka musu hutu, ranar ne kuma bayan ta dawo, mama ta kira ta suka zauna a falon maman..
"Hafsah kinga kin girma, ki nutsu kisan abinda kike yi, zan baki wayarki..
Ta d'ago cike da murmushi,
"Nagode, Mama.
Ba
wannan ba, kada ki bari abbanku ya ga wayar nan, sannan kiyi taka tsan -tsan da samari, bance ki kula kowa ba, tunda abbanki baya so,.. Kuma kada ki k'ara karb'ar abu makamancin wannan a hannun wani."
"Nagode Mama, in sha Allah zan kiyaye."
Ta mik'a mata
wayar,
"ungo ki b'oye, k'awayenki kawai na yarda ki kira"
Cikin zumud'i ta karb'a..
Baki 'nunamin result d'in naki ba."
Tsoro ya cikata, babu yadda zatayi haka ta dakko ta bata.
"Kaii, ya akayi haka Hafsah??
Bari abbannaki ya dawo, wato don an hanak
i kula samari shine zaki k'i maida hankali kan karatunki koh?
(A tunanin Mama kenan)
"Kiyi ha'kuri Mama wallahi ba haka bane."
"Yayi kyau"
Tashi kije kya had'u dashi ai"
Tana zuwa daki'n ta tura mishi text zuciyarta cike da farin ciki.
"My phone is w
ith me.. But don't call me now, let's have phone by night..
I love you!!
*To shine fa wayar da tayi yau, bayan ta dawo daga wajen abban ya mata fad'an karatu, shine kuma wayar da mama ta kamata tanayi a darenna..(Page 1 to 3 )*
ππΌππΌ
*Muje zuwa muji
wannan soyyaya ya zata kaya..*
π
*Hajeeyah Kareemerh ce dai*
ππΌ
[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): β₯β₯β₯β₯
*ZAZZAFAN SO*
(Guba ne)
*A broken*
*heart story*
ππ
Story and writing by:
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Kareemer
h)*
*Dedicated to:*
*Unique In Your Love Heart Members.*
πππππ»ππ»ππ»
*Jinjina gareku ZAZZAFAN SO NOVEL GROUP*
π
*Farida (Farisam*)
π
*Gimbiya Bilkisu*
π
*Basma A adam*
*ΩΨ§ Ψ·Ω
*
π
*Ummi M shehu*
π
*Amina Yusha,u*
π
*Umman Aryan*
π
*Maman husna*
π
*Mufy expensive*
π
*Mummy khali*
ππΌ
*Ina yinku
π―
kamar yadda kuke yin novel d'ina*
π
π
*13*
*Nunkuwar* shak'uwarsu da yusuf, nunkuwar soyayyarshi azuciyarta..don a kullum soyayyar yusuf k'aruwa take a zuciyar Hafsah.
Aha
kan kuma waya, kawai suke shima ab'oye, amma kullum cikin lallab'ashi take akan lokaci ya kusa da zai zo wajanta..
Wata hira da sukayi, wata rana da daddare suna waya. Ya saisaita murya, dai dai yadda yafi jawo hankalinta gareshi.
"Baby"
Tace "Na,am dea
r"
"Ina son yi miki wani question ne"
"Ina jinka"
"Wai kina sona kuwa?
Ta d'anyi shiru sannan tace
"Haba dear me yasa kamin wannan tambayar?
Yai k'asa da murya "Am sorry bana nufin b'ata miki rai, ina tunanin, ni kad'ai ke wahalar son ki ne"
Ta mar
airaice.
"To Ba haka bane wallahi, u know my friend Basma koh, har cewa take wai
'Me yasa nake sonka da yawa ne?
Ya gyara kwanciyar shi, "To wane answer kika bata? "
Haka nace mata, "kanada abubuwan da nake so ne,..an then ka iya soyayya"!!
sai taji
yayi dariya ahankali.
"Hahh da gaske ina da abubuwan da kike so kuma na iya soyayya??
Ta gyad'a kai kamar a gabanshi.
"Exactly yadda nake son mijina ya kasance, to haka kake."
Yai ajiyar xuciya "Thank you my hafsat!
Ya fad'a da wata kasalalliyar murya
.
"Meya faru?" Ta tambayeshi.
Ya kuma ajiyar xuciya sannan yace "Am bacci nakeji, and abinda kika fad'a yasa naji wani 'Laziness' ya saukar min.
'Kasala kuma'??
Ta tambaya da mamaki.
"Oh, no kada ki damu, ki gaidamin da k'awar taki.. Gud night"Ya kas
he wayar.
Sai kawai ta yi kissing d'in wayar, abinda bata tab'a yi ba a tarihin soyayyar su..
Wata ranar juma,a hafsah ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa fiffted. Tayi kyau sosai ta yafa d'an k'aramin mayafi. Batayi kwalliya ba sosai.
Ta fito fal
o, tace wa mama "Mama zan tafi, "
Maman har da bata kud'in mota.
"don Allah Hafsah kada ki dad'e har abbanku ya dawo"
"In sha Allah"
"Ki duba ta.
"Tom"
Ta rayata jakarta ta fito."
Cewa maman nata tayi wai ' Mamansu basma ce bata da Lpia zataje dubo
ta, wai har asibiti ta kwanta.. 'Wannan shawarar basma ce, da Hafsah ta dame ta ya zatayi da yusuf?'
Tana zuwa unguwar ta kira basman a waya. Don bata san gidan nasu ba, layin ta kwatanta mata, da number gidan. Tana zuwa ta tarar Basman ce kad'ai a gidan
sai 'yan aikinsu, maman tata bata nan.
Gidan nasu ya tsaru babu laifi..
Basma ta ruk'unk'ume ta,
" H, Hamid a gidanmu lallai ina da Manyan bak'i.
A falo suka zauna wanda ya had'u da gujeru da adon fulawoyi..
Basma ta sa aka kawo mata kayan ciye ciye.
.
Kad'an taci. Ta Kalli agogon dake falon.
"Kinga bai Kira ni ba har yanzu, gashi mama tace kada na dad'e."
"Hum, kema ai baki shirya ba"?
Hafsah ta kalleta cikin rashin fahimta.
"Kinga ni tashi muje ki shirya dallah, ahaka zai ganki"?
Taja hannunta,
babu musu ta bita.
Wani dak'i suka shiga daya tsaru sosai basma ta nuna mata toilet.
"Ki shiga ki wanke fuskanki"
Ta shiga tayi yadda tace d'in.
Tana fitowa taga rashin ajye mata wasu riga da wando (pencil) iyakacinshi guiwa rigar kuma T. Shirt ce amm
a bata da hannu.
Ta nuna mata kayan "kisa wannan"
No, basma sunyi k'anana gaskiya"
Ta d'an b'ata fuska
"Kinjiki ai"
Ta mik'a mata wata powder shafa wannan"
Ta karb'a, Hodar ta amsheta sosai.
Ta mik'o mata sauran kayan kwalliyar
"Gasunan bari nayi
wanka."
Ta shige toilet.
Hafsah ta yi kyau sosai.
Tana gamawa Basma ta fito d'aure da towel ajikinta da kuma wani d'an k'arami hannunta tana goge jikinta dashi.
"Wow kinyi kyau"
Yanzu dai ga wani humra ki shafa saiki sa kayan."
Ta dakko mata wani to
wel a drawer ki d'aura wannan sai ki cire gown d'in.
"Hafsah ta kalleta Nifa gaskiya Basma bazan iya fita gurinshi da wannan kayanba"
"So wai meyasa?
Kawai,ki barni da wannan gown d'in yayi ai"
"Nooo, bazaki fara zuwa wurinshi da dressing na wani atamf
a ba gaskiya, dole ne ki chanja malama."
"To gaskiya sai dai a chanja wani."
"OK ai ga drawer d'innan duba wanda ya miki.'
Ta fad'a tana nuna mata wardrobe d'inta.
Suna cikin haka wayar Hafsah tayi k'ara, da d'auka da sauri.
"Hello"
Am baby nazo ung
uwar wane link ne?
"Om..
Ta mik'awa basma ta kwatanta mishi.
"Sai kiyi sauri ki nema wanda zaki sa."
Ta fad'a tana mik'a mata wayar.
* * * * *
* * * * *
Wani kyakywan had'ad'd'en saurayi (First Class) Basma ta yi tozali da shi..
A zatonta da yadd
a Hafsah ke kwarzanta mata yusuf bata ta'ba zaton yakai Kwatar hakan ba.
(Colour of my dream)
Ta fad'a a zuciyarta.
murmushi kawai yake sakarwa Hafsah, tare da wani irin kallo wanda ya so rikitata.
suka isa wajenshi..
Hafsah ta nemi gefenshi shi ta ts
aya.
Ahankali tace mishi
"You're welcome my dear"
Ya zuba mata idanu "Thank you my baby"
"Am mu k'arasa ciki Koh?
Basma ta fad'a.
Sai lokacin ya kalleta. yace
"Sannunki fa"
Tayi wani murmushi cike da gogewa
"Am yawwa..
Basma na gaba suna bay
anta..
Wani d'aki ta bud'e musu dake farfajiyar gidan, sanyin AC ga kuma wani daddad'an k'amshi dake tashi..
A wata kujera ya zauna three seater,
Hafsah ta zauna a 'me kallonshi' suna fuskantar juna.
"Am ina zuwa.."
Basma ta fad'a, sannan ta fita, sa
i wani rangwad'a take.
Falon ya d'anyi shiru, kusan mintuna biyu, sai kawai kallonta da yusuf yake..
"Can taji yace " you look so cute my baby".. Kinyi min kyau."
"Thank you"
Kazo lpia?
"Lpia lau, but full of kewanki amma."
Ya fad'a yana wani d'age
gira.
Tayi 'yar dariya.
"Gani nan kam yanzu Koh??
"Ya mamanku"
"She's fine"
Ya d'an gyara zama sannan yace
"Baby baki son ganina koh,? duk na rame, kin hana in ganki..
"Am sorry ba haka bane, na fad'a maka abbanmu ba zai barni fitowa ba, sai nayi
candy."
"Hum long distance, u mean bazan dinga ganinki ba koh?
"A,a mana, yanzu ai mun had'u koh?"
"Yes, but this won't satisfy me.
ya zuba mata ido
"Ko dai zaki zo gidanmu ne kawai sai muna hira acan".
Ta d'an zaro ido.
Yayi wata siririyar dariya w
acce taji ta har cikin ranta.
"Ba zaki zo ba koh.."?
Ta rufe idonta d'aya da hannunta tana kallonshi da d'aya idon..
'Kallon yayi tasiri a zuciyarshi.'
"Bazaki zo bane Koh?
Tayi shiru
"Uhum..?
Ta kuma yin shiru
"Talk to me mana kinji..?
Basma
ce ta shigo da Tray a hannunta taja wani center table ta d'ora akai..
Ta Kalli Yusuf
"Ga drink koh?
"Ok thank you"
Leb'enshi kawai ta kalla ta gane me yake fad'a, saboda a hankali yayi maganar.
'Hafsah ta kalleshi.
"Dear ga Basma fa"
Ya jingina kan
shi jikin kujerar, sannan ya kallo Basma, yana jijjiga k'afa.
"Am sannunki koh?
"How are you?
Kut..
π
(Basma ta fad'a azuciyarta) "Rainin sense" wato gayen nan wani nauyin kai ne dashi..
π
Ok bari na zo mishi ta yadda yazo min..
~'To Basma ya kike
so ya miki? Koh kece Hafsan ne'*~
π€
Tayi wani murmushi a d'an share tace "Am fine"..
yace "Gud"
"Am yau dai kaga hafsan naka koh??
Yai murmushi sosai wani b'oyayyen kyawunshi ya bayyana
"Of course, alot of thanks to you."
"No ai ana tare ne Koh,?
..
Ta Kalli Hafsah..
"Ai kamar sister na take."
"Gud!"
Ya Kalli Hafsah wanda dama Basma ta lura rabin hankalinshi na kanta dama.
"Baby friend enki nada kirki fa."
"Sosai ma, kuwa inji Hafsah"
Sannan ta mik'e ta zuba mishi lemon a cup.. Basma idonta
kir tana kallonsu..
K'okari take ta gano a ina ne Hafsah ke da rauni.?
Amma duk kwakwarta bata gano ba.
Sai ma wani sirri data gano a wajen Hafsan.
Wato yadda yanayin 'Movement' motsinta yake da banbanci da na sauran 'yan mata. Bata abu da gaggawa san
nan bata da sanya.. komai takeyi cikin nutsuwa take yinsa, sannan tana da shiga rai sosai.
Ta mik'a mishi lemon ya karba yana murmushi.
Ta zuba itama sannan ta dawo ta zauna tana sha..
Am bari na barku haka koh?
Ta Kalli
"Yusuf ka gaida gida"
Ok bye
bye"
Hafsah sai kin shigo.
Bayan fitar basma, Yusuf hira ya fara yi mata ta rayuwarshi a k'asashen waje, k'arara yake nuna mata 'banbancin' dake tsakanin can da nan.
Misali acikin labarin shi tsaf yake fad'a mata irin rayuwar shi da 'yan matan shi ace
warshi (School mate enshi ne) ko da cikin labarin yakan ce mata "She hugged me and then.." ita dai Hafsah sai dai tajishi da kunne ko tayi murmushi, itama bata son ta nuna mishi 'Gidadanci' kamar yadda yake d'aukar hakan, sai dai a hirar tasu ta fahimci wa
ni abu..
'wato, Yusuf sam bai san wani abu wai shi 'Babu ba' duk da itama ba wai wahalar tasani ba, amma shi batajin yasan da wata abu wai ita wahalar rayuwa..
Tsoron da take ji shine kada 'Banbancin' dake tsakaninsu ya kawo musu matsala acikin alak'ar
su.
"Baby meyafaru ne?
Babu komai.
"Sure?
"Yes"
"OK please close your eyes for me!
I have a surprise for you!
Ya fad'a yana kashe miki ido.
"Am ok"
Ta rufe idon..
Tsayawa yayi ya k'arewa fuskartata kallo tun daga saman goshinta har zuwa k'asan
hab'arta.. Ahankali yace
"My Baby is beautiful!
Hafsah ta gaji don haka ta bud'e idonta
suka had'a ido.. tare sukayi murmushi "plz baby ki rufe fa"?
"Ok"
Ta kuma rufe idon..
Ya taso ahankali ya iso gabanta.. sunkuyo dai dai saitin fuskarta.
Numfas
hinsa daya sauka kan fuskantarta yasata saurin bud'e idonta bata shirya ba.
Ta zaro ido.
Yai wata dariya me sauti..
Uhum.. "Calm down"
Ya fad'a cikin rad'a"
Ita dai shiru ta kasa magana.
Hannunta taga ya Kama wanda hakan yasa jikinta b'ari..
Zobe ya
ciro daga aljihinshi Gold ne mai kyau, ya fara sa mata ahankali.. tana son ta k'wace hannunta, amma kuma ta kasa, bata
son ta bada kanta da yawa.. Amma azuciyarta Allah Allah take yanayin ya shud'e, gabad'aya nutuwarta bata tare da ita..
Shiko fuskarta
kawai yake kallo yana mata murmushi..
Ya gama sa mata amma kuma yak'i sakin hannun na ta.
K'okarin kai hannun nata bakinshi yake.. Ta zaro ido
*"Kiss wai yake shirin min?*
π³
(ta fad'a a zuciyarta)
Tayi zumbur ta mik'e sai gata atsaye, ta k'wace hann
unta.
"Please stop it"
"Hmm ok"
"Am sorry I don't mean to hurt you"
Ta gyara tsayawarta ta Kalli zoben yai mata kyau sosai.
"Thank you"
Tace dashi.
"U deserve it"
"Baby kada dare ya min fa..
(Har yanzu a tsaye suke.)
Ya nuna kanshi
"ok kina ko
rana ne koh?
"No, you know, Wanan plan ne koh, kaga mama bata bani time da yawaba."
"OK you're right"
Tare suka fito ita da shi..
"Baby kije kuyi kuyi sallama ki mu tafi"
No, ka bari sai next haduwar mu.
"Bakya so Koh?
A,a ba haka bane.
"Ok"
"Muj
e na raka ka koh.. ?
Suka jera har wajen motar shi.
Ya shiga ya zauna.
Ta rik'e murfin motar..
"Baby sai yaushe?
"Zamuyi, waya.
"Ok bye bye, I love you"
"Cool story dear"
Ya mata wani murmushi ya d'aga mata Hannu
"Bye Bye.
Sai da taga tafiyar shi
sannan ta juyo.
A falo ta tarar da Basma tana danna waya.
Ta d'ago ta kalleta tayi dariya "woo Hafsah Hamid kina wuta.. Irin wannan azababben guy haka??
Wallahi wannan mai zafi ne, gaskiya fa kin faso gari.!!
Murmushi kawai Hafsah tayi, "Hmm, Basma
kenan akwai tsokana.
"Kinga"
Hannunta ta nuna mata.
"Kaii, wow.
Gaskiya yai kyau.
Am kinga bari nazo na wuce..
Ok kina shiga bed room ki chanja kayan.
Bayan ta fito ne tace
"To basma nagode, fa sosai, zan tafi ki gaida mamanku"
OK zataji.
Har wa
je ta rakota
Suna tafiya suna hira.
"Saura 2 weeks a koma school koh?"
"Inji Hafsah.
"Eh, yanzu sai yaushe to?"
"Inaga sai an koma schl gaskiya"
"Ok shikenan munyi waya."
Sai da tahau napep sannan ta dawo.
Hafsah na isa gida
ta tarar da dukka
k'annenta da mamanta a falo. A tsarge take da kanta.. don haka ta kasa sakin jiki.
Ta nemi waje ta zauna.
"Mama, na dawo.
Ok, ya jikin nata.
"Da sauk'i"
Make damunta ne
"Ulcer ne."
"Allah ya sawwaqe"
"Amin"
Dai dai lokacin idon mama yakai kan,
hannunta. Ahankali ta kirata cikin dakakkiyar murya.
"Hafsah?
A d'an razane ta d'ago wanda maman ma ta ga hakan.
"Zoben wane a hannunki"?
Tayi saurin d'ago hannun da zoben ke jiki,
"Am na Basma ne mantawa nayi ta taho da sh.
Hum Gold d'in kika taho m
ata dashi?
"Meya kawo shi hannunki."
"Um nunamin tayi wai mamansu ce ta taho mata dashi daga Dubai, shine muka manta na tawo da shi."
"Hmm to kawoshi kada ki b'atar mata "
Kamar ta rusa ihu haka taji,
jin wani son zoben take...
Tunda Yusuf d'in ya sa
ka mata taji babu abinda zata bari ya raba hannunta da shi.
Mama zan sa mata fa a drawer, wallahi bazan b'atar mata ba fa"
Ta fad'a da 'yar shagwaba.
Mama ta d'an tsare gida.
"Ki kawoshi nace"
Ahankali take ciro zoben, tana tuno lokacin da yusuf d'in
yake sa mata zoben, sai kawai ta yi murmushi.
"Mama ta kalleta da mamaki.
Ta mik'a mata.
Dai dai lokacin kuma wayarta tayi k'ara.
(Tunda ta je gidansu Basma ta cire wayar daga silent, don kada yusuf ya kira basu ji ba.)
Mama ta bita da kallon tuhuma.
Ita ma fargabar wayake kiranta take.
Bashir kuma tsorone ya kamashi, bai san maman tasan da zaman wayar ba.
Amira ce tace
"Laa Yaya waya sai miki waya.?..
Dai dai lokacin tana cikin yin maganar abbansu yayi sallama a falon ita ko wayar sai k'ara tak
e...
[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): β₯β₯β₯β₯
*ZAZZAFAN SO*
(Guba ne)
*A broken*
*heart story*