Showing 48001 words to 51000 words out of 132482 words

Chapter 17 - ZAZZAFAN SO COMPLETE

01 Sep 2026

62

ta samu tace, um bansan.. Au na manta sunan shi"

"Haha, 'Abba

yayi 'yar dariya..' "Ya akayi kika manta"?

"Babu komai"

"Hmm, to meyasa ki ke ta kuka."?

'Tambayar ta razana ta.'

"Babu komai."

"Wani ya dakeki ne"?

'Ta girgiza kai.'

"Hmm tom yayi kyau "

'Ya tsare gida sosai ya kuma nuna ta da yatsa'

"Hafsah, Haf

sah,!! Ki kiyayeni cikin sha,anin fita daga gidan nan batare da kin fad'a min ko kin fad'awa mamanki ba, haka kika ga bashir nayi? Ace k'aninki yafi ki hankali'? Wallahi kinji na rantse idan kika kuma fita ko nan da k'ofar gida ne bada sanina ba sai na yi

mummunan sab'a miki.!!"

"Kin manta kwanaki koh? To zan hanaki fita gaba d'aya ma."

"Abba kayi hak'uri."

Kada in sake jin wata k'awa tazo kun fita ke da ita ko ina kuwa zakuje, kina jina"??

'Ta d'aga kanta.'

"Ki kiyaye kafin na sab'a miki fa"

"To Abba

"

"Ta shi ki fita saura inji labarin kink'i yin bacci."

'Ta wuce d'aki, ta kwanta' ko babu komai fad'an abba ya shige ta, da tana bin umarnin shi da bazata fita ba bare taga wannan abin bak'in cikin.'

'Ta d'akko Diary tana son ta rubuta wani abu a ciki

, amma kuma ta kasa saboda cinkushewar zuciya.' Da ta d'ora biron akai sai taji hawaye ya cika idanunta."

'Ta cillar da Diary gefe guda, afili ta furta "Yusuf wai you choose to BROKE MY HEART??

😭😭😭

'Ta kife kan pillow tana rizgar kuka har bacci ya d'au

keta.'

'Washe garin ranar tatashi babu yabo babu fallasa, sannan kuma taji kwata kwata bata k'aunar fita ko da falo.'

'Ta daure tayi wanka ta koma gado ta k'ara kwantawa zuciyarta ce keson yi mata 'Karatun baya'

'Ta dinga tuno farkon had'uwar ta da Yusu

f, halayenshi da ya dinga fito mata dasu, yadda Basma, ta fara chanja mata, da kuma zancen zuwanta birthday, sai kuma abinda ya faru ranar birthday d'in da kuma wanda idanunta suka gani jiya.'

'Ta rantse idonta, ta cije lebe, hadi da huro iska daga bakint

a, ta dad'e tanajin ana cewa NZAFIN SO,' ko kuma 'SO GUBA NE.'

'Amma ita da yake tun farko rayuwarta bata ginu akan Soyyayya ba bata gane zancen sam.'

Tana jin haushin Jamila idan ta dameta da zancen 'Salim' ko ta zauna kod'a mata shi.."Ai Salim ya had'u

, ina sonshi d'an beauty nah.."

'Wani lokacin har tsaki take yiwa Jamila, "Aikin banza shi mutum kamar kowa amma kita faman wani rawar kai kina kod'a shi kamar wata marok'iya sai kace da 'Gold' akayi shi.. Mtsw"

😠

'Idan ta tuna jamila murmushi takeyi ta

ce mata, "Hmm Hafsah bazaki gane ba ne."

'Akwai ranar da wata 'yar ajinsu a islamiyya tazo tana ta rizgar kuka, har da bubbuga benci, Hafsah har dariya taji ta bata. "Wai saurayinta ne ya zagaya yana son k'awarta.'

'Ko lokacin suna tare da Yusuf, amma ha

kan bai hana ta yin dariya ba, musammaman data ga bilhak'k'i kuka take yi."..

"Tana ambaton an cuceta."

'Ita dai dramar soyayya na burgeta.'

'Ashe marmari ce daga nesa.'

😳

'To yau gashi abu ita ma ya sameta kuma ta rasa mafita.'.

"A tunaninta ko dai

tayi wa Yusuf wani abu ne shiyasa ya rama.'?? 'Me yasa yanzu sai ka yarda da mutum, yake cin amanarka?..

W'ani Babban abin takaici shine gashi dai k'iri- k'iri tana jin zafin Yusuf, amma kuma gefe na zuciyarta na k'ara wassafo mata shi, da kuma karanta m

ata kada ta rabu dashi, tun da shima bai nuna mata ya rabu da ita ba.."

'Ita kanta tasan idan ta rabu da Yusuf, to tabbas tayi wa rayuwarta illa, tasan zuciyarta ma bata da jarumtar jure hakan.'.. Dole ne ta rungumi abinda yai mata, ta yi d'amarar kwato s

hi itama da k'arfinta, don idan ta barwa 'Basma' shi to tabbas ta tafka babbar asara, kuma Basma tayi nasara akanta kenan..'? Banda kuma dumb'in soyayyar shi dake dank'are cikin zuciyarshi, wacce bazata iya sadaukarwar da ita ba ga wata'..

'Ta sani aiki n

e a gabanta ja, amma bata san ta ina zata fara shi ba.'

Dole ne dai tabi umarnin Abba idan tana son zaman lafiyarta, to idan kuma babu fita ta ina zata dinga had'uwa da Yusuf'?

'Tasha alwashin idan taga basma sai ta yi mata abinda bazata manta ba, sai ta

d'and'ana mata b'akin ciki ita ma...'

Sallama ta jiyo a falo kamar ta Aysha, amma kuma kusan minti uku bata shigo d'akin ba kamar yadda ta saba.'

'Sai kuma taji an turo k'ofar. Mama ce tsaye kanta, "Sai ki fito ai." 'Abinda tace mata kenan, ta juya.'

'

Ta mik'e ta fito, taga Aisha zaune, ta d'an saki fara,a, tazo kusa da ita ta zauna.'

'Ta lura da hararar da mama ke aika mata da ita.'

'Tayi yake sannan tace "Aysha Sannu da zuwa"

"Yawwa"

"Ya mamanku"?

"Lafiya lau wllhi."

'Duka sukayi shiru saboda

ganin idon Mama.'

Ita Aysha nason tayiwa Hafsah zancen jiya kuma tana son kwantar mata da hankali, shi yasa tayo azamar tahowa lokacin baifi 11:00am, ba. Don tun jiya hankalinta ya kasa kwanta wa.'

'Hafsah ta lura da akwai magana don haka ta mik'e muje d

'aki, "To" inji Aysha, taji kuma d'adin hakan.'

'Dama tunda tazo bayan sun gaisa da Maman, zata wuce d'akin Hafsan, mama tace ta dakata Hafsan, tafito.'

'Aysha na mik'ewa hankalin Mama ya yo kansu' fuskarta a d'aure ta kalli Hafsah, "Ina kuma zaku je"?

"Um bed room zamu shiga."

"Ba inda Zakuje, ku zauna anan."

'Har yanzu bata saki fuskarta ba.'

'Hafsa taji kunyar hakan, tare da jin takaicin Mama, "Meyasa take mata hakane yanzu."?

"Mama mai fara,a ga k'awayenta"?

'Amma yanzu duk ta sauya'?

'Dole ta

dawo ta zauna ita da Aysha sukayi shiru.' sai can ne ma Ayshan k e sako mata hirar makaranta jefi jefi.'

'K'arar wayar Mama yasa ta shi da sauri ta nufi d'akinta, ta basu iska.'

'Tana zuwa tashi Aysha ta bud'e baki.'

"Don Allah Hafsah kada ki dinga saka

damuwa don Allah wallahi bansan abinda zamu tarar ba da bazan kaiki ba, badai je gidansu Basma ne na tarar zata fita, kuma dana karb'i wayar ta sai naga yusuf ya mata text d'in address d'inshi.' ta dakko wayar ta tana nuna mata.'

'Ta cigaba da cewa, "Don

Allah,ki cire Yusuf aranki don wallahi ba saurayin da za,a zauna da shi, bane."

'Hafsah ta zaro ido, zatayi magana kenan, Mama ta fito daga d'aki, tilas tayi shiru da bakinta.'

'Aysha bata jima ba ta mik'e, "To mama na tafi, hafsah sai anjima."

"Ki gai

da gida."

'Mama tace mata.'

'Aysha ta mik'e don raka ta.'

"Mama ta murtike fuska, Saura ki fita daga cikin gidan nan."

'Suna fita daga falon Hafsah ta fara bawa Aysha ha'kuri.'

"Don Allah Aysha kiyi ha'kuri da abinda mama tayi miki, wallahi tun jiya b

ayan dawo take fushi."

'Aysha tayi murmushi,'

"Babu komai wallahi."

'Amma don Allah ki rage damuwa wallahi har kin fad'a, daga jiya, ki daina saka abin aranki, kada mama tayi zargin wani abu."

"K'walla ta cika idanunta, Aysha dole na damu, Yusuf fa.."

Kuka ya hanata magana.'

"Kiyi ha'kuri dai.

"Ni dai shawarata ki cire shi daga ranki, don Allah, shine kawai maslaha."

"Hmm Aysha bazaki gane ba kawai."

"Allah ya kyauta, ki koma kada mama ta ga kin dad'e."

"To nagode Aysha ki gaida mamanku."

'Aysha

ta d'aga mata hannu sannan ta fice daga gate d'in gidan.'

'Hafsah ta tsaya ta goge fuskarta sannan ta dawo cikin gida, ta tarar maman na zaune inda ta barta.'

'Zata wuce d'akinta kenan, Mama ta kirata.'

"Ke zonan"

'Ta dawo ta zauna a kujera.'

"Mama

gani"

"Wannan Yarinyar daga ina take"?

'Hafsah taji banbarakwai.'

"Um, k'awata ce ita fa mukayi photo ranar graduation."

"Bana son jaye jaye"

'Hafsah ta gyad'a kai kawai, tana Mamakin Mama.'

'Kuma, bana son zaman cikin bed room d'in nan da kike, ko u

ban wani ne yake korar ki daga falon'?

'Ta girgiza kai.'

"To kada in sake ganin kin kwanta."

'Dole ta nemi guri a falon ta kwanta, saboda idan tana, 'Menstruation' ciwon jiki take fama, ga kuma kasalar son kwanciya.'

'Mama da ta ga ta kwanta taji sauri

n cewa, "Tashi maza kije ki gyara daki'n abban ku, kuma, ki wanke toilet d'inshi."

'Badon ranta yaso ba haka ta mik'e ta nufi d'akin Abban, tana murje ido, to da wanne zataji da fushin mama ko kuma abinda ya dami zuciyarta.'

'To haka ne yake ta faruwa ku

llum har wajen sati d'aya, Hafsah da son yawan yin tunani, mama kuma da son matsa mata, ga kuma tambayoyi da take damunta dasu, "Kya ma fad'i inda kika je"

'Ita dai, Mama batun fitar nan, ya tsaya mata aranta.'

'Hafsah ta kasa gano dalili.'

'Ko sanda t

a fita ita da yusuf daga gun party, bata d'auki zafi haka ba.'

'Hafsah ji take ita kad'aice mai matsala a duniya.'

'Abinda Yusuf yayi mata ya ki barin zuciyarta ga uwa uba kuma kewarshi data dameta, tun ranar bai nemi inda take ba gashi bata da wata hany

ar contacting d'in shi.'

'Tsoro ya cika zuciyarta.' shikenan basma ta k'wace mata yusuf d'inta da take so.'

'Matuk'ar zata tuno shi to tabbas sai

tayi hawaye.'

'Ta yi rama, kallon daya zaka yi mata kasan tana cikin damuwa, duk maganar da mama ke mata

kan zaman bed room taki ta daina.'

'Abin ya dami kowa cikin gidan, k'annenta sun lura ta rage walwala.' Bashir kullum sai ya tambayeta me yake damunta, amma amsar guda d'aya ce babu komai.'

'Abinda ya tashi, hankalinta shine, bashir yace mata, "Yaya Hafs

ah jiya antaso mu daga school naga wannan yusuf d'in shida k'awar nan taki a mota danja ya tsaida mu."

'Gabanta ya fad'i ta shiga damuwa sosai.'

'Kenan yusuf ya ajyeta.. Ya daina yayinta..? bazai rabu da basma ba,??.. 'Ta fita muhimmanci a wajanshi kenan

...'??

'Ta kasa hak'uri har sai da ta zubar da hawayen tausayin kanta bayan fitar bashir. Ita dai son Yusuf ya zame mata 'GUBA'

'Abba, a dole ya kira Yusuf, a waya.'

"Hello." inji Yusuf.'

"Assalamu alaykum."

'Inji Abba.'

"Wa alaykum salam"

"Ina mag

ana da yusuf ne"?

"Eh nine."

"Yawwa, ka gane mai magana."

"A,a." ('Don Yusuf sam baiyi serving number ba')

"Okay Abban Hafsah ne.'

Yusuf yaji fad'uwar gaba, kada dai yarinyar ta fad'a wa ubanta abinda ke faruwa."

'Ya daure dai yace.'

"Daddy ina wuni

"

"Lafiya lau.

'Abba ya fad'a cikin fara,a.'

"Am dama so nake in tambayeka ka."

'Yusuf ya d'auke wuta saboda fargaba'

"Hafsah ta fad'a mak a ina son ganin ka"?

'Yusuf yai wata wawuyar ajiyar zuciya'

"Huuam, No, bata fad'a min ba daddy."

Abba yai m

urmushi lallai ma shida aka fad'a mishi a gabanshi.'?

'A lokacin ya gane inda yusuf ya dosa.'

"Abba yace ok shikenan.'

"Idan babu damuwa gobe ko jibi kazo, ina son ganinka."

'Ya yi shiru, sai da abba yace "Kaji"?

Sannan yace okay Daddy."

"Abba yace n

agode sai anjima."

'Abba ya ajye wayar yayi shiru yana nazari, yasan da k'yar idan yaron zai zo.'

'Hakan ya tabbatar mishi irin yaran nan ne da ba aure suka shirya yi ba, sai dai su hure wa yarinya kunne.'

'Saboda haka ko yazo d'in ma zai san matakin da

zai d'auka kawai.'

'Mama ma a neman tata maslahar, da suna waya da yayarta take ce mata, "Wallahi yaya da akwai matsala ne"

"Lafiya dai ko"?

"Hafsa ce dai."

Yayar tayi dariya, "Hmm amina kenan, kin iya dagula al,amra kila ma ba wani babban abu bane."

"Hmm, Yaya Yarinyar so take tafi k'arfina wallahi."

Ke amina wannan wacce shashashar magana ce, ki haifi 'yar ki dinga kiran tafi k'arfinki."??

"Ki dinga saita bakinki don Allah."

"Hmm yaya.."

'Kada ki fad'a min komai ki bari gobe zan shigo.'

"To shi

kenan, yaya na gode."

'Yayar ta kashe wayar tana dariya.'

'Washe garin wajen k'arfe goma sha biyu, Hafsa na zaune a falo, ta kasa samin nutuwar zuciyarta kiyasta wa take yau kome zai faru sai ta tura wa yusuf koda text ne.'

'Tana cikin tunanin ne 'Aunty

Nafisa.' ('Maman ya Nazeer') Tayi sallama hafsah ta amsa mata kuma ta d'an saki fuskarta. 'Tayi mata Sannu da zuwa.'

"Mama na jiyo sallamar ta ta fito da sauri, Aunty sannu da zuwa." "Yawwa Ameena."

"Ina wuni" inji mama "Lafiya lau."

"Yasu Naseer da Fa

tima"?

"Duk lafiya lau suke, nazeer shirin Service ('NYSC') ma yake"

"Allah sarki Allah ya taimaka to."

"Amin, ya yaran gidan."

"Suna nan k'alau sun tafi makaranta ne."

"To ya Abban su Hafsah"?

"Lafiyar shi lau wallahi."

"To Masha Allah."

'Hafsah m

a ta gaisheta'

"Bari in kawo miki lemo."

'Mama ta mik'e.'

"A,a ki zauna mana ga Hafsah."

"Ta Kalli Hafsah 'yan mata an yi candy koh."?

"Maza ki kawo min ruwa ne kinji, ki daina barin mama tana aiki ke kina zaune."

Hafsah tace, "To"

'Maman Naseer ta

kalli Mama, "Muje ciki koh"?

'Suka mik'e duka suka yi daki'n mama.'

'Hafsah ta d'oro ruwa da lemo da cup a plate ta bisu da su.'

'Ta ajye sannan ta fito, ta dawo falo.'

"To Sannu kinji"?

'Inji maman ya Nazeer.'

.'Ta tsiyaya ruwa tasha, sannan ta kall

i mama sosai cikin nutsuwa tace.'

"Me yake faruwa ne ke da 'yar taki."?

'Mama ta gyara zama cikin damuwa take karanto mata.'

"Kinga dai abinda tayi ranar bikin abdallah, to kafin nan sai da taje gidan Hajiya kakarsu... Nan ta zayya no mata duk irin abub

uwan da Hafsa tayi har tazo kan fitar da tayi bata sani ba.'

"Ta, k'arashe zancen da cewa ni tsoro na ma, kada inje yaron ya lalata mata rayuwa..."

'Auntie tayi saurin d'ago mata hannu.'

"Haba amina, wannan wacce irin magana ce mara ma,ana kike yi.?? in

a tunanin ki ya ke, da zaki yiwa 'yarki wannan mummunan zaton'?

"Allah dai yasa baki furta wa babanta wannan shirmen ba."

"Auntie kinga fa ranar data dawo har magariba tana aikin kuka, sannan kullum cikin tunani take, idan ba wani abu ba mezai kawo haka"

?

"Hmm, kin bani da dariya amina, shiyasa kike kyararta kika zuba mata ido koh,? Gaskiya tunaninki yayi Kama da na yara."

'Kawai kuma don yarinya ta fita ta dawo bada saninki ba, sai ki hau zarginta koh."?

"To dai ki chanja tunani, don me bazaki jata aj

iki ba kiji damuwarta, ai ko bata fad'a miki ba zaki fahimci me yake damunta koh."

'Ni kin b'ata min rai ma wallahi.'

"Yanzu dai, koma menene zan tafi da ita tayi koda sati biyu a wajena.'

"Shikenan aunty, nagode."

'Ita kuwa Hafsah ganin babu kowa a f

alon kuma ga wayar mama data bari yasa tayi saurin d'aukar wayar tayi d'akinta tana godiya ga Allah.'

'Cikin azama ta hau rubuta text,

'Ban tab'a zaton zaka yi min haka ba, koda a mafarki,..idan nayi maka wani laifine, sai ka rasa ta hanyar da zaka hukun

ta ni, sai kaci amana ta,??.. Yusuf cutar da kayi min ba,a tab'a yi min irinta ba'..

'Nagode sosai, bisa sakayyar da kayi min.'.."

'Hafsah H. Hamid'

'Ai kuwa minti kad'an sai ga reply,

"Hmm Hafasah kenan, shine yasa kika sa Abbanku ya kira ni koh..'So

ya kirani kuma yace min yana son ganina." Hm kin fad'a mishi ne koh.."?

"Tana cikin karantawa sai ga su Mama ad'akin, nan tayi tsuru-tsuru, mama ta rufeta da duka da hannu, tana fad'in kinganta koh.. Kinga dai abinda takeyi.'

'Maman ya Naseer, ta rik'e h

annun Mama, tana fad'in haba ki bari mana Amina, don Allah kibi komai a sannu.'

'Suka zauna, sannan Auntie ta d'auki wayar, text d'in Yusuf, ta fara karantawa, ita ma kanta ya kulle gaskiya ne akwai abinda ke faruwa.'

'Sai kuma ta kuma duba na Hafsah, sa

nnan hankalinta ya d'an kwanta.'

'Ta ajye wayar sannan ta kalli Hafsah.'

"Me yasa kika d'aukar mata waya"?

"Cikin kuka take cewa babu komai."

"To me kika yi da ita."?

"Ta, kuma, cewa babu komai."

"Hm, babu komai fa kika ce, amma kika d'auki wayar."?

'Cewar Auntie.'

"Um, game nakeyi"

'Auntie tayi murmushi.'

To kada ki k'ara d'aukar mata waya.'

"To"

"Ta dafa kafad'arta.'

Tashi maza ki deb'o kayanki kinji, gida na zaki je, tun da yanzu bakya zuwa makaranta.'

'Hafsah bataji dad'in hakan ba, ta mi

k'e babu k'wari ta fara debo kayan daga cikin drawer.'

'Shaf ta manta da ledar nan ta Yusuf, aiko tana dakko wasu kaya, ledar ta fad'o.'

'Mama tayi saurin d'aukar ledar cikin rud'ewa ta ke cewa Auntie kin gani koh, ai mai hali baya fasa halinshi."

'Aunt

ie ta karb'i ledar ta bud'e, sai taci karo da kwalin wayar mai tsadar gaske wato, 'IPhone' a ciki, sai wani tsadadden agogo, sai turare mai tsadar gaske, sai kuma, 'Greeting card'

'Auntie ta mayar da kulle ledar dama rubi biyu ce.'

'Hafsa ta gama shirya

kayan sannan ta kulle akwatin, tasa hijabi, suka fito dukansu.'

'Auntie tace maza ki kai kayan cikin mota.'

'Ta ja akwatin tayi waje inda drivern auntie take.'

'Auntie ta kalli Mama bayan fitar Hafsah, "Ki bar komai a hannuna, ba wani abin tashin hankal

i bane ina zatan kyauta aka kuma bata, in sha Allah komai zai yi daidai.'

'Mama tace "Toh"

Ina wayarki kira Abbanta zanyi mishi bayani da kaina.'

'Mama ta danna kiran, bayan ya d'aga "Hello, barka da rana, ya aiki."

"Alhamdulillah, aiki yasani gaba."

"Allah sarki to "Sannu da k'okari."

"Yawwa."

"Dama, Auntie Nafisa ce tazo tana son kuyi magana ne."

"Okay to bata wayar."

"Sun gaisa sannan ta ce, nazo ne kuma sai Amina keyi min k'orafi akan Hafsa, to shine ina so abani ita don Allah in tafi da ita ta

yi koda sati ne a wajena."

'Abba bashi da matsala da ita, kuma yasan ta macece jajirtacciya,kuma

babba ce, don haka yace, "babu komai ai, yayi kyau wallahi, na gode sosai."

"Sai dai Don Allah kada a barta ta kula duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login