Showing 39001 words to 42000 words out of 132482 words

Chapter 14 - ZAZZAFAN SO COMPLETE

01 Sep 2026

68

'Solar' kasancewar babu wuta, sannan suka saka wani tsohon film d'in ',(Home alone') suna kalla cikin nishad'i, hakan yasa hafsah taji d'adi sosai ta mik'e, 'Abba ya bita da kallo, sai

ta kawo mishi uzurin cewa bacci take ji'

'Ya jinjina kai, sannan yace "Shikenan, kiyi addu,a," ya Kalli mama, ita ma ta kalleshi, itama ta karanta mishi nata mamakin', Na baccin da hafsah tace tanaji, a irin lokacin k'arfe takwas baifi da rabi ba'.. 'Abin

da yaran sai k'arfe tara da rabi ko goma suke bacci, shima sai Abban ya kora su, saboda makaranta.'

'Hafsa ta kwanta shiru, ta takurawa zuciyarta kan dole sai ta gano, abin da ke tsakanin Yusuf da Basma.. Da har ya sashi kafewa kan zuwa birthday d'in don

kada ran Basma ya b'aci.' Yadda zuciyarta ta karanta mata kenan..'

'Abubuwa da yawa zuciyarta tayi ta karanto mata wanda ita kuma gefe guda tayi ta k'okarin sai ta k'aryata hakan, don kada ta jawo wa kanta tarwatsewar farin ciki babu shiri'

'Da farko kaw

ai ta sa wa ranta, Basma tace wa Yusuf 'Tana Sonshi ne..

'Sai kuma ta tuna a irin class na basma tana fad'ar cewa ita babu namijin daya isa tace tana sonshi'.. Sai ta sauya tunanin da cewa ' kodai kawai son kula maza ne da iyayi irin na basma yake jan han

kalin Yusuf d'in zuwa ga kulata, ??

'Kishi ya baibayeta Wani b'angaren kuma na zuciyarta ya shiga rarrashinta, da nuna mata sam fa wannan tunanin ba haka bane, 'Idan ta lura da irin kallon da yusuf yayi wa basma ranar da suka fara had'uwa, sai kuma d'inbi

n soyyayyarta (ita Hafsan) da ke dank'are cikin zuciyarshi, wacce bata da kokontonta, idan ba lokacin da ta shiga rudu, irin wannan ba'..

'Da taga dai, ta rasa abin kamawa, sai kawai ta bari kalmomin Yusuf sukayi tasiri, itama zuciyar ta ta ta,allak'a abi

n da, 'Ganin kirkin basma da Yusuf d'in keyi, kamar yadda ya fad'a mata, wanda kuma hakan sanadinta ne ita Hafsan.'..

'Ta saki nannauyar ajiyar zuciya, sai lokacin taji dama-dama, sai kuma ta shiga nemawa zuciyarta hujjar da zata k'ara yarda da hakan.' sa

i tunaninta yakai kan ranar da yusuf d'in ya turowa Aysha katin 2000' wanda shima fa kawai albarkacinta taci don kawai, suna waya da wayarta.'

'Ahankali taji zuciyarta na hak'ura da lamarin har taji tausayin Yusuf d'in bisa mummunar fahimtar datayi mishi,

take taji zuciyarta ta k'ara kamuwa da sonshi, taji kawai babu abinda take son ji sai muryarshi. Amma ina babu dama, hakan yasa ta tsunduma tunanin yadda suka rabu d'azu tana k'ara halarto irin kyan da ga yayi yau d'in...

'Ahakan har tayi bacci'

'Washe

garin ranar Yusuf na kwance a d'akinshi da daddare, yaji kira ciki wayarshi, ya duba yaga basma ce, ya d'aga kiran tare da kai wayar kunnanshi. "Hello"

Takai k'arshe wajen kashe muryarta wacce ta yi tasiri sosai a kunnuwanshi tace, "Hi, ya kake"? Am fine

" "Ok gud, ya gajiyar birthday yai dariya, "Hah babu gajiya kuke cewa koh"?

'Itama tayi dariya "Oh Na manta fa you're Californian.!" suka k'ara yin dariya, sannan ta mayar da muryarta kalar ta tausayi, kamar mai yin kuka tace, "Yusuf,..

"Na,am." shima ya

amsa cikin taushin murya'

'Sai kawai ta saki kuka, hankalinshi ya tashi, ya rud'e ya hau rarrashinta, bai san ma me yake fad'a mata ba.'

"Am sorry baby, kiyi ha'kuri please calm down, ki fad'a

min make faruwa waya tab'a ki ko Hafsah wani abu ya faru"

?

Sai da tayi kukan sosai sannan ta saita muryarta cikin shashshek'a ta fara magana, wanda shi yanayin muryar ya d'auki hankalin shi'

"Am na rasa wa zan fad'a wa, damuwata sai kai,.. Cikin nutsuwa yace "Mata ina jinki" tayi ajiyar zuciya sanan ta cigaba,

"

'Saurayina ne kawai don kazo birthday kuma yaga yadda kayi treating ena shine yace wai ya rabu dani!! Ta k'arashe maganar cikin kuka"..

Yusuf yayi shiru, yama rasa me zaice, tausayin basma ya rufe shi, cikin in, ina ya faro magana, " Um, d.. Do youu m

ean kun rabu kenan"??

"Of course".. Ta fad'a tare da k'ara rushewa da kuka..' "Oh my God"!

Yusuf ya fad'a, to Meyasa? A wanne dalilin, wato kishi yake da shi kenan,?? Yama rasa me zaice, sai kawai ya b'ige da rarrashinta "please kiyi ha'kuri, kada ki dam

u, I know it will hurt, but kiyi ha'kuri in sha Allah zaku sasanta kinji..'

'Zuciyarta ta dugun zuma, ita ba haka tasoji ba, amma sai ta kanne kawai, tace mishi, " I told you mun rabu kuma bana jin zamu k'ara yin wata soyayya ni da shi, so just pray for m

e 'Allah ya bani wanda ya fishi'

'Ya sauke ajiyar zuciya tare da cewa, "Amin."

Sai kuma ya shiga yi mata 'yar hira, yana kod'a kyan datayi a ranar birthday d'in

Duk a k'okarinshi,

na ganin ya kwantar mata da hankali, domin ji yake, shine sanadin tarwa

tsewar farincikin ta, ita kuma abin nema ne yasamu, taji dad'in hakan sosai.'

'Da k'yar sukayi sallama.'

'Wai ko anya zancen Basma gaskiya t

ne??

'A gaskiyar zancen dai, shine, basma bata gayyaci manyan samarinta, wad'anda tasan zasu ji haushin ganinta

da yusuf ba,..Amma da gaske ne tayi fad'a da wani saurayinta amma shima d'in kawai na rage zafi ne, baza,a kirashi da saurayinta na sosai ba, shine ta fa ke da hakan ta d'ora kukan makircinta akai, buk'atar ta kawai Yusuf ya tausaya mata, tana son tausayi

nshi yayi tasiri akanta, wanda shine zai zama mabud'in cimma dukkan manufarta, kuma gashi cikin sa,a ta sami hakan.'

'Domin ita tayarda da cewa, tausayi shike jawo soyayya..'!

'Basma ta kwanta har da burgima don murna, tabbas ta juyo k'amshin nasara.'

'

Ana cikin haka kira ya shigo cikin wayarta tana dubawa tayi tsaki sanan ta d'aga.

"Hello basma iam Aysha d'aheer"

"Ok, so ya kike"?

"Lafiya lau"

'Suka d'anyi shiru sannan Aysha tace,

"Basma Yunus Manyan gari,"

"Hmm, basman tace cikin rashin kulawa,

domin tun ranar birthday d'inta taji ta tsani Ayshan, saboda gani take kamar munafurci ne ya kawota.. Hafsah

ce ta turo ta donta kaimata munafurcin abinda ya faru kawai.'

'Amma dake ance bariki iyawa ne sai, ayshan ta chanja salonta, ta gyara muryarta t

ace,

'Gaskiya Basma, kin burgeni ranar nan fa, sai ranar na tabbatar H.Hamid jaka ce'

Basma ta shek'e da dariya,

'Aysha ta cigaba, wato in banda hauka irin nata, ko yaushe zaki bari number Saurayinki a wayar k'awayenki?? 'Sannan kuma Kalli yadda don k'

auyanci ta ki zuwa birthday d'in ta barshi shi kad'ai yazo, Basma tace "Hmm.'' So take ta gano inda Aysha ta nufa, Don tana tsoron kada dai bugar cikinta takeyi.'.. Amma hankalinta ya kwanta da taji Ayshan tace, "Ni wallahi ma sam gayen bai wani dace da it

a ba, bafa type enshi bace."

'Sukayi dariya sosai ita da Basman, har Basman ta samu damar cewa, "Kema dai kya fad'a Aysha'.. "Hmm ai wallahi sam babu colour, yarinyar da babu inda take zuwa!!"

'Anan basma ta saki jiki sukayi hira, sosai da zata fad'awa A

yshan wayar da sukayi da Yusuf d'azu, amma sai ta fasa, suka kashe waya, Basma na farin ciki ta samu wata mai bata shawara akan al,amarin...

πŸ€₯

*Sabon salo*

.

*Khareemerh tijjani Mansur (Hajeeyah Kareemerh*

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writ

er): β™₯β™₯β™₯β™₯

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken*

*heart story*



πŸ’”πŸ’”

Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to: Unique In Love Heart Members*

πŸ“„

*30*

*Kimamin* sati d'aya kenan dayin

birthday d'in, Basma, kullum Hafash zuba idon ganin Yusuf take yi, amma shiru.'

'Duk da tasan ita take hana shi zuwa, amma sai zuciyarta ta fara raya mata 'kodai ya manta da ita ne'? ('Zuciya kenan')

'Ita a yadda tayi kewarshi batak'i yazo d'in ba, idan

yaso sai, tace wa Abba, 'Zuwa yayi ya amsa kiran da yayi mishi'...

πŸ˜…πŸ˜…

'B'angaren su Basma kuwa, abu yayi nisa ita da Yusuf, kullum sai sunyi waya, kuma Basman ce ke kiranshi, shi kuma baya k'in d'aga wa

'Yau da sukayi waya ne, take tambayar shi, 'Wai sh

in yau zaije club ne? Yace mata bashi da niyya, amma idan zataje shima zaije, taji dad'in hakan da yace, 'wato idan hakane tana iya samun alfarma kenan a wajenshi?..

'To kwa tabbas zata gwada sa,arta.'

'Aranar da suka had'u a club d'in bayan sunsha rawa

sosai, basma ta nemi dasu k'ebe tana so su tattauna, ya rik'o hannunta, ('Wanda zuwa lokacin k'aramin abune a wajen su su rik'e hannun juna') suka fito daga cikin hayaniyar zuwa harabar wajen inda aka ajye kujeru domin zama.'

'Kafin ta fara magana ya riga

ta, don shima d'in yana da abin cewar da yake ganin bazai iya hak'uri har ta fad'i nata ba.'

"Please basma help me" ta kalleshi da mamaki, "With what?

'Ya marairaice please ki daure kije gidansu Hafsah, ki bata wayanki ina so muyi magana ne please"!

'Take yanayinta ya chanja wanda shima sai da yaga hakan, har ya karanta mata alamun tambaya a fuskarshi, sai tayi saurin wayancewa ta k'irkiro murmushin dole ta d'ora akan fuskarta.'

'Hmm, banyi maka promise ba, but zanje cikin satin nan. 'Yai ajiyar zuci

ya tare da ce mata "please basma help me, kinji,' na kuma bata waya ne, so i think Abbansu ya kuma k'wace wa.'" ta d'an cije lebe sannan ta daure tace mishi, "Ok don't worry"

Yai murmushi sannan yace, "Thank you"

'Ya kuma tattaro hankalinshi gurinta, san

nan yace, "What about yours?

'Tayi wani murmushi sannan ta gyara zamanta tace cikin wata marainiyar murya,

"Nawa yana da wahala, bana jin zaka yarda."

'Ya girgiza mata kai had'i da cewa, "No, please tell me, zanyi miki kinji"

'Sai lokacin ta sami k'war

in guiwar fad'amishi abinda ke ranta.'

"Um, tun lokacin da muka rabu da ex ena, yake min abubuwan da banjin d'ad'i, yana min maganganu a status, sannan yace wai ban isa na sami saurayi wanda ya kaishi ba, so ina son in nuna mishi k'arya yakeyi..' Tayi shi

ru data zo nan a zancen, yayin da shikuma ya bata duk hankalinshi, da yaji tayi shiru, yai mata alamar, 'Yana sauraronta ta, ta cigaba.'

"So please ina so ne ka dinga acting like you're my boyfriend.."

"What? Ya fad'a yana girgiza mata kai,

"No, I can't

, am not like that, please am sorry to say 'bazan iya ba!"

'Basma ta d'ora mishi ido ta kasa d'aukewa, daman tasan hakan zai iya faruwa.'

'Sai ta shiga kawo mishi hujjoji marasa tushe, yadda zata gamsar dashi har ya yarda.'

"Am sorry if I hurt you, but

ina cikin wani hali wallahi, nasan kuma Hafsah Kake tunani, to ka daina, I have an assurance that 'bazamu sami sab'ani da ita ba, ta fahimceni, kuma nima zanyi mata bayani, please help me"..

'Yai ajiyar zuciya, sannan ya fara magana cikin nutsuwa, "I can'

t gaskiya, kinga bani son in sami matsala ni da hafsah, 'sannan ex enki ina baki shawaran ki cancel duk wani abu da yake connecting enki dashi, kuma ki zuba shi a dustbin, ki daina damuwa da zancen shi, kawai, that's my advice"

'Tayi shiru, batason ta nun

a nacinta a wajen shi, sai ta share kawai tace "Ok thank you, my friend" yai murmushi sannan ya maimaita

"Your friend"?

Ta d'aga mishi gira, "Yes, as your girlfriend's friend so we are friends" isn't it?

Yai murmushi that's true"

'Sannan ya kuma mik'a

mata rok'on shi, da ya tabbatar mata cewa ya damu sosai "So please yaushe zaki je gidan"?

ita ko lokacin haushin shi, takeji ma, amma sai ta kanne tace " zan tambayi mum enmu, kuma yanzu yawanci bata gida ita Hafsan, so banso inje bata nan"

"Please kiyi

k'ok'ari kinji"

Ataik'aice tace "Ok"

Yai murmushi sosai "Thank you"

'To basma tana iya k'ok'arinta wajen yin, duk abinda tasan idan tayi zata ja ra,ayin Yusuf, misali 'Yanzu suna yawan had'uwa a gurare da yawa irin na shak'atawa, saboda haka duk inda t

a sami dama tana k'okarin ta nuna mishi tabbas, ita ba irin hafsah bace, a fannin wayewa.'

'Takan mik'a mishi hannu su gaisa aduk sanda suka had'u, sannan idan hira ta had'asu tana k'ok'arin nuna mishi cewa ita fa tana cikin 'kewa'..

'Shi kuma har yanzu

ya kasa fahimtar manufarta..

'Amma shima a nashi b'angaren akwai wani b'ahagon tunani a cikin zuciyarshi..

Amma da yake ance so sone, amma son Kai yafi, Yusuf, sai kawai ya yardarwa kanshi abinda zuciyarshi ta dad'e tana karanta mishi.'

A ganinshi sam b

aza,a kira hakan da yaudara ko cin amana ba.'

'Yanzu, 'kwance yake a d'akin shi, gaba d'aya yau babuy kowa acikin gidan nasu, shi kad'aine.'

'Ji yake komai yayi mishi zafi, har yake jin abin yau yafi na kullum.' ya tuno rabonshi da hakan tun yana makaran

ta, sai abinda ba,a rasa ba, kuma, ba wai rasa 'yan matan yayi ba, amma shi kawai yafi son 'yan matan can k'asar bawai na nan ba.'

'Hafsah ce kawai yaji yana so, kuma yaji zai ta dace da shi.' 'Shine ma dalilin da yasa, har ya d'auki wannan lokacin, wai y

ana jiran ta yarda dashi ne, to kuma yaga bata da niyyar hakan.. Gashi su 'yan matan nasa nacan, sunyi nisa dashi, sai dai a waya, kawai, shi kuma hakan sam baya wadatar dashi.'

'Yai shiru, yana tunanin abinyi, basma ce ta fad'o ranshi, yayi saurin d'auka

r wayarshi ya danna kiranta, tana ganin shine ta share don zatonta zancen Hafsah zai mata, har ta tsinke, sai a kira na uku ne ta d'auka, yanayin da taji muryarshi, tasan akwai magana, a d'an sama-sama suka gaisa, tana shirin tambayar shi, make damunshi' y

a riga ta,

"Please basma kina gida ne?"

Tace mishi, 'Eh"

"Please kizo gidanmu yanzu,"?.cikin mamaki tace gidanku, kuma"?

"Yes, please ina son muyi magana ne"

Ta d'anyi shiru, sai kuma wani tunani yazo mata na 'gwara ta dinga mishi alfarma ko shima

zai yarda da buk'atarta"

Tace "Ok"

Yace "Zan turomiki address"

'Nan da nan tayi shiri, cikin wasu, da wando da suka matseta sosai, itama Maman tata bata nan, tana gama shiryawa text d'in ya shigo na address d'in, ta mik'e ta d'auki jakarta, tana fitowa

harabar gidan ta gamu da Aysha tahir, taja tsaki a zuciyarta, wato zata b'ata mata shiri.' A d'an share suka gaisa,

"A,a basma ina zuwa haka?

"Hmm kinji ki da k'wak'wafi, to some where"

"Aysha ta kalleta sosai sannan tace "Oh lallai kin fa had'u sosa

i," Basma, tayi murmushi,

"Thank you"

"Muje tare mana, inji Aysha, wacce ta zuba wa basma ido, tana karantar yanayinta sosai,"

'Basma ta d'an had'e rai kad'an, "No, am sorry gaskiya, bazaki bini ba"

'Aysha ta rik'e baki, tana mamakin alamun tsoron data

gani cikin idanun basma, da kuma sauyawar da tayi, 'sai ta jefa mata tambayar son gano, abinda take b'oye mata,

"Am lallai ma basma wa kika samu ne da har kike nuna min wariyar launin colour"

"Am um, kinga, am sorry ba haka bane, kawai dai, yau muka had

'u dashi ne, so kinga ba zamu fara zuwa mu biyu ba."

'Aysha tayi wani murmushi, "Ok, hakane, kice kinyi babban kamu."

'Suka shek'e da dariya duka har da tafawa.'

'Anan Aisha taga asarar ta bar basma ta wuce ba tare da ta tabbatar da zarginta ba, don hak

a tace cikin siyasa.'

"Please basma kada kice na tsayar da ke wani application, nekeson zan tura, a wayarki, saboda shi nazo ma."

Basma tace,

"Oh, sauri nake amma ungo ki tura."

'Aysha na karbar wayar taga text, akai sai kawai ta shiga ta duba, Address

ta gani, tayi saurin matse wayar zuwa silent, sannan tayi screenshots, ta shiga zendar ta tura, sannan ta zab'i application guda d'aya ta tura, ta goge history na photon 'screenshot' data tura, sannan ta dawo gallery ta goge shi, sanna ta duba logs taga w

ata number, wadda akayi kira baifi mintuna 25mins, ba da suka wuce, ta kalli number sosai sannan ta mik'awa Basma, wayarta, wacce ke ta faman gyara fuska da powder tun sanda ta bawa Aysha wayar.'

"Thank you"

'Inji Aysha basma ta karb'a suka jera suka fit

a, acikin layin basma ta sami 'Napep' ta hau tabar 'Aysha tsaye' tana d'aga mata hannu.'

'Aysha ce cikin daidaita' sahu' (Keke Napep) ta zaro wayarta ta kalli number da ta turo text a wayar basma, ta rik'e number, sannan ta saka a wayarta, number Yusuf, c

e ta fito, wacce ita rabon daya kirata tun ranar da sukayi final papper, da tana tunanin, goge number d'in ma, 'sau uku tana saka wa, amma abinda ke fitowa a wayar kenan, mamaki ya cikata, da gida zata,' tace aranta 'Dole ne fa ta sanar da Hafsah, abinda k

e faruwa, idan ba haka ba itama taci amanar Hafsan'

'Bata tab'a zuwa gidan su hafsar ba, amma, ta rik'e kwatancen da Hafsa ta tab'a yi mata.' 'Amma zata fara zuwa gida, ta d'akkowa Hafsa kyautar da yusuf d'in yai mata...

Ta isa gidan a gurguje ta ce wa M

amansu, zasu, je duba Hafsah ne ita da Basma, ta d'akko ledar sannan ta fito ta tarar mai adaidaitan yana jiranta, dama tsayar dashi tayi, ta fad'a mishi sunan unguwar da kuma, layin, ta shiga suka tafi, tana jinjina cin amana irin na Basma...

_

Muje zuwa.._

*Hajeeyah Kareemerh ce*

πŸ‘ŒπŸΌ

[1/11, 12:11 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): β™₯β™₯β™₯β™₯

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken*

*heart story*



πŸ’”πŸ’”

Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to: Uni

que In Your*

*Love Heart Members*

*'Masoya na kune silar yin murmushi nah'*

πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜

_Mom samhat, pretty, aysha Abdullahi (aysha sheka), Ayshaatou ('yan boarding book) ina yinku_

πŸ’―



πŸ“„

*31*

*A* k'ofar gidansu, aka

ajye Basma, ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login