Showing 72001 words to 75000 words out of 132482 words

Chapter 25 - ZAZZAFAN SO COMPLETE

01 Sep 2026

46

Sai _Nura_ k'aninshi, shi kuma bangaren shari,a ya karanta, shine yayi aure, shekara d'aya data wuce, sai kuma _Fadwa,_ Itace autarsu, tana shekara ta uku a Jami,a.

D'akin mama kuma, _Nasir_ shine

babba, wanda shine sa,an _Nura_, ( _wato sa,an mai bin ukhasha a d'akinsu_) sai _Maryam_, zata bawa Fadwa kusan shekara d'aya, sai _Zainab_, _Abdullahi,_ _Najeeb,_ sai autarsu ( _Mahseen_) Itace auta, duka gidan, shekarunta bazasu wuce goma sha biyu ba.

Idan har ba zaman gidan kayi na wani lokaci ba, ko kuma dama ka sansu, toh babu yadda za,ayi ka iya banbance 'yan wannan d'akin da 'yan wancan. Rayuwa ake ta had'in kai babu banbanci.

~_Connect with page 36_ (Inda ukhasha ya dawo gida daga party)~

*UKHASHA*

_____________

Yana ta son ya kauda tunanin ta, amma ya kasa, Yarinyar ta tsaya mishi arai, duk wani motsi nashi sai ya tuno ta. Matsalar d'aya ce, bai san a ina zai k'ara ganinta ba, bai san ita dawa suka zo bikin ba, bai san a wanne dangin tak

e ba, na amarya ko na ango. _"Ya ilaahiy"_ Ya fad'a a hankali fargaba kawai yake, yana fatan kada Allah ya d'ora mishi son abinda bazai samu ba.

Wayarshi ke ta k'ara amma ko kalla baiyi ba, bare yayi tunanin d'agawa, don ya tabbatar idan ya d'aga komai

zai iya faruwa, zai iya fada mata maganar da sai tayi da na sanin kiranshi.

K'arar shigowar text yaji, kamar zai share sai kuma yaga gwara ya duba.

_Allah ya huci zuciyarka, don Allah kayi hak'uri in sha Allah this wouldn't be happened again, na ajye

wayar ne shine maman ta d'auka ta kiraka.. Plz am sorry, u know bazan iya jure abinda kake min ba plzx._

Ya sa, hak'oran sama ya cije leb'en shi na k'asa, daya tuno irin bak'ak'en zantukan daya sha a waya..

_"Mara mutunci,_

_mugu azzalumi wallahi

ka sakar min kur,war 'ya in ba haka ba zaka ga abinda zai biyo baya.._ _Don tsabar mugunta ka asirce min yarinya!! Wa yasan abinda kake mata kana son ka lalata min yarinya!!_

~_To ba alk'ali ba koma waye mahaifin naka bazai hana nayi shari,a da ku ba.!!_~

Babban abinda yafi b'ata mishi rai shine, mahaifinshi da aka ambata. Meye dalili..? Shi baice yarinyar dameshi ba da irin bak'in nacinta sai shi wai za,a ce ya asirce ta.? Allah ya sawwak'e, ai ko asiri yake bazai yiwa wannan 'yar ta ta ba, yarinyar d

a bai tab'a ji kalarta ko wani abu ya nata ya burge shi ba sam.

_Wai lalata.!_ shi ake cewa zaiyi lalata da wata yarinya..? Akan me zata yi masa wannan sharrin.. Ta taba ganinshi k'ofar gidanta."? Kawai tsabar sharri irin na mata, don 'yarta ta nace mish

i tana son ta rabata dashi sai ta fake dayi masa sharri, ai kuwa idan haka ne dole ya d`auki mataki akai, duk nacin yarinyar sai ta daina kulashi ko bata so, sai dai in ta mutu, tun da abin ya na neman yazo da sharri..

Gyangyad'i yake tayi saboda gajiy

a, sai ya mik'e kawai ya kwanta, bai bi takan wayar ba ma, ranshi a b'ace, _amma yarinyar akwai k'arfin hali da naci.._

Shi banda bazai iya ba, ai shine yake da abin cewa, badon ba halin shi bane cin fuska, da babu abinda zai hana shi mayar mata da munan

an kalamanta kan 'yarta.

_"Ai yarta ce mayya, ita ce ke bibiyarshi, ga mugun naci sam bata da zuciya._

Amma da ke bazai iya ba wayar kawai ya katse ya kyaleta.

Har ya fara bacci ya tuna gwara ya kashe wayar, idan ba haka ba, zata iya cigaba da damuns

hi da kira don zata aikata. Gefe kad'an na zuciyashi, yana tausaya mata, bai tab'a ganin inda ake irin abinda yarinyar ke mishi ba, wani _"Makahon so"_ take mishi. Yayi imanin idan yace ta kyale mahaifiyarta tsaf zata barta!!

Ya nemi tsarin Allah daga f

ad'awa irin wannan son.

Yadda ya d'auka shine, su mutanen yanzu, ka so su tsa ka-tsaki shine maslaha, don yana da tarihi na soyayya kala-kala musamman a cikin abokansa, wad`anda suka _ZAFAFA_, k'arshe suka k'are a asibiti.

Yana mamakin kansa, bai t

ab'a jin ya kwana da wata arai ya tashi da ita, ya ku ma kwana ba, sai dai wani lokacin ya kan b'ata lokaci akan tunanin _Bahijja_ shima ba wai begenta ba, a,a kullum cikin tunanin yadda za,ayi su rabu salin alin yake, ba tare da ta zargeshi da b'ata mata

lokaci ko kuma k'inta ba. Amma duk wasu hanyoyi ya gwada basuyi amfani ba, ya sha fad'a mata, tayi hakuri tayi aure, shi a gida za,a bashi mata amma tak'i sai dai ta ji shi kawai, har fada' mishi take, _"Taji, ta amince ya auri uku ya cikashe ta hud'u da

ita wallahi zata yarda.!!_

*HAFSAH*

______________

Misalin k'arfe sha d'aya da rabi na, safe, sun gama karyawa, dake kuma _weekend_ ne babu makaranta, kowa ya kama abinda zai fishshe shi. Gidan tsaf yake an share babu datti, sai k'amshi kawai ke tashi

.

A parlour Hafsah ce zaune bisa kujera three seater, ta dora _Laptop computer_ akan hannun kujerar. Sanye take da riga da skirt na atampha, wanda suka d'an kamata, babu d'an kwali akanta. Gashinta wanda dama can

bai cika ci ka ba, sai dai tsaho ta tu

fke shi da ribbon, farar fatar ta sai shek'i take, babu alamun kwalliya a fuskar ta, idan ka kalleta zaka ga babu abinda ya sauya daga ita idan har ka santa ashekarun baya, komai cikin nutsuwa take yi kuma a hankali babu gaggawa. Kana kallonta zaga ga ala

mun hutu da wayewa atattare da ita, ba mamaki kuma ka k'i yarda cewa Bashir k'aninta ne, saboda yanayin jikinta bata da girma sam, sai dai matsakaicin tsaho.

Da Sallama Abba ya shigo palourn daga d'akin mam. Hafsah ta amsa tare da rankwafawa tana gaida

shi, _Abba Barka da safiya."_

Ya kalleta sosai, "Sannu Yaya, bakya son saka d'an kwali koh..?"

Ta danyi murmushi tana shafa gashinta da ke ta shek'i, ta kalli gefe da gefe kamar zata ga dankwalin a wajen.

Har yanzu yana kallonta. "Baki bi su zainab

d`in kitson ba ke."?

Cikin nutsuwa tace, "Eh abba ba ba sai nayi kitson ba, ai nayi _saloon."_

(Duk shirye shiryen bikin Fateema suke k'anwar Ya Nazeer )

Yayi kyau, "Ki saka d'an kwali toh."

Ta mik'e zata wuce d'akin.

"Nima zan fita wani meeting n

e."

"To Abba a dawo lafiya."

"Allah yasa Yaya."

Zai fita kenan Bashir ya shigo, ya zube har k'asa "Barka da asuba."

Abba yayi dariya "Asuba ko rana."?

"Ko dan ku baku son tashi da wuri koh."?

Ya fara tafiya Bashir na binshi a baya.

"Ya kuke fam

a da baccin nan a makarantar kuwa."?

Basheer ya sosa kai, "Ai Abba hakura ake."

"To da kyau ai."

Cikin ladabi yace "Abba fita zaa yi ne."?

"Eh zanje wani meeting ne, kasan an kusa yin _primary election_.

"To bari na raka ka Abba."

Abba yayi murmushi

n jin dad'i "Yawwa, _amma dai ka sa hula koh."?_

Ya kalli jikinshi riga ce _long sleeves_ da dogon wandon _Jeans._

Yayi murmushi, sannan da sauri ya wuce cikin gida, duk da d'akinshi kafin a shiga ciki ne, yana shigowa palourn, Hafsah na fitowa daga

d'akinta, tana d`aura d'ankwali.

"Gud morning sister of mine.!

"Morning _Junior_ "

( _Haka ta dawo kiranshi._)

Tana tahowa shi kuma ya tsaya, bata gama k'arasowa ba yace, "Anjima da yamma zamuje park idan na dawo, yanzu zamu fita da Abbah ne."

"Okey

tace mishi."

"Ina mama, kice mata mun fita da Abba."

Ya fad'a cikin sauri, sannan ya juya. D'akinshi ya bud'e ya d'akko hular ya kifa akanshi, yana murmushi, yasan da Hafsah zata gani babu abinda zai hana tayi ta mishi dariya.

Murmushinshi ya k'ara fad'

ad'a yana son yayarshi yana son farin-cikinta.

"Haha, kufa yaran yanzu kwalliyar ku da ban ce!"

Cewar Abba sanda Bashir ya k'araso inda yake.

Ya bud'ewa Abba d'aya gefen, sannan shima ya shiga mazaunin _driver._

Don ance ka sako hula, sai ka sako ita

kad'ai..? "Ai ana nufin ka sako kayan da ake sawa hula."

Ya k'arashe maganar yana dariya.

Bashir ya sosa, k'eya, "Ai kada na bata lokaci ne shiyasa."

"Hakan ma yayi, ai naga haka kuke yi yanzu, _asa kayan bature, a d'ora hular bahaushe!!."_

"Kuna kwai

kwayon rappers kuke ce musu ne ko hip -pop"

"Bashir yayi dariya, kawai."

"To yayi, _bridged_ muka nufa, nan za,ayi taron.

Abba ya fad'a sanda Bashir ya tada mota.

Mai gad'i ya bude musu gate, suka fita, suna tafiya suna hira irin ta d'a da mahaifi.

__________________

Shiri suke, sosai duk sun baza kayan kwalliya a d'akin, mai yi musu kwalliyar fuskarta ko powder babu, Fadwa kenan, take wa su Maryam da Zainab kwalliya, kasancewar ta iya kwalliyar zamani. ( _makeup artist ce ita_)

Shirin zuwa par

tyn Abokin Yayansu Ukhasha suke wato Jabeer (JB). Shima Ukhasha yana d'akinshi yana shiryawa.

Zainab ce da ake shafawa powder tace, "Yaya Fadwa muyi sauri fa kinga, kada Yaya yayi ta jiranmu..Kinsan halinshi zai iya tafiya ya barmu."

Bata tsaya da abi

nda take yi ba tace, "Kedai ki tsaya kiyi kyau kawai, yanzu k'arfe nawa ne ma kwata-kwata"?

Sai da ta gama mata tsaf tayi mata d'auri, dama ta gamawa maryam. Ta d`auki mudubi kenan zata fara da fuskar ta, wayarta tayi k'ara, maryam tayi saurin kai hannu

ta d'auka, Fadwa ta miko hannu, maryam tayi gefe da wayar tana cewa, "Don Allah kiyi sauri Yaya ne fa bari na d'aga."

Hello..

"Ina ta jiranku fah."

"Mun kusa gamawa Yaya."

"Hmm, kada ku batan lokaci don Allah, me ita Dadwan keyi sarkin k'ak'ale-k'ak'a

le."

"Yaya ta gama, d'aura dan kwali take."

"Please Kice tayi sauri kunga sai kirana suke."

"Tom."

Ya katse wayar don jin kira ya shigo a zaton shi ango ne.

Sai kuma yaga Bahijja, kamar bazai d'aga ba sai kuma ya tuna wani abu.

Bai bata damar maga

na ba yace, "Kinga zan fita ne, idan na dawo zamuyi magana."

Ya katse kiran, sannan ya k'arasa d'aura takalmin shi, ya mik'e ya nufi mudubi dake manne jikin bango, k'asan shi anyi wata 'yar kanta mai kyau, kayan shafe shafe ne na maza, da sauransu akai.

Babu wasu tarkace dama a d'akin, drawer ce me biyu wacce ta cika da kaya, sai akwatuna, suma kayan ne dai aciki, sai abin d'ora takalma, sai madaidaicin gadonshi, gefe da gefen shi da _bed side drawer_ ya dora mata littafai aciki da wajenta.

Ya kalli ka

nshi sosai a madubin, sannan yasa hannu ya gyara zaman hularshi yayi kyau matuk'a cikin _Brown shadda_ da sukayi ankonta, bai da kiba sam, sannan ba dogo ne irin sosai ba, yana layin tsakiya dai, fatar shi ba fara bace tas, amma tana da haske sosai, yana d

a saje a fuskar shi, haka dukkan jikinshi akwai gashi, amma basu cika cika ko tsayi sosai ba.

Akwai shi da kwarjini idan ka kalleshi, bashi da yawan magana barkatai musamman inda bai da sanayya ko sabo da mutanen gurin, amma yana

da hira harda zolaya i

ndai ka mishi farin sani. Bai bata lokaci sosai wajen tsayawa kallon kanshi ba, ya fesa turaruka masu sanyin k'amshi, sannan ya fito, daga d'akin kawai.

Lokacin suma k'annen nashi sun gama shiryawa, sunyi kyau sosai, cikin shigar _blue black lace_, maya

fansu mayalwata, baza,a ce sun fito da tsaraici ba. Sai kuma suka b'ige da zaman d'aukar photo.

_Wani abu game da Khady Abubakar shine, baya hana 'ya'yanshi mata zuwa biki, ko wani taro, indai har ya yarda da tsaftar mutanen, sai dai dole zasuyi shiga

ta mutunci, wacce dama kullum cikinta suke, sannan ba,za,a barsu su tafi su kad'ai ba, sai dole ke da 'yar uwarki ko yayanki ko k'aninki. Sannan basa sakewa su haura k'arfe takwas na dare.

_Aganishi ka hana yarinya mace zuwa taron biki, kamar shiga hak

'k'i ne da kuma bada k'ofar shigowar b'araka, don a yadda yaran yanzu suke muhimmanta biki, to idan ka hanasu dole su nemi hanya ko da bada saninka ba, har gwara ma a fita da saninka, kuma matuk'ar ka tarbiyyantar dasu yadda ya dace, babu abinda zasu yi n

a zubar da mutunci ko makamancin haka._

Yanzu haka ma sai da ukhasha ya nemi izini a wajenshi, sannan da k'yar ya yarda.

"Ku idan zakuyi biki kuyi iya ku mazaa, mana, amma kun hada har da mata."?

Ya sosa k'eya, "Akaramakallahu, ai na matan ne, gay

ytar mu sukayi.

"Ku bar angon ya je shi d'aya mana, tunda abin na mata ne."

Bashi da bakin magana sai yayi jim, kafin ya tuno abin fad'a, don baya son yawan tsawaita magana irin haka da Abban nasu, don ba,a nasara akanshi, sai dai idan yayi niyyar abu

kawai zaiyi.

"Shiyasa zan kaisu tunda an gayyace su."

" Zaka kai ku dai, ai har da kai kaima zaka ce zaka kaisu, kawai kun bata abu ne yanzu, mata na biki kuce sai kunje.. Shi ango ai da walima aka sanshi ita yake had'awa shi."

"Tuba muke, ranka ya d

ad'e."

"Yaushe ne kace."?

"Yaune da yamma.

"To Allah ya kaimu amma ba,za,a kai dare ba koh."?

"In sha Allah."

Ukhasha ya fad'a. Don yasan ba tambaya bace a wajen abba umarni ne kawai, yana nufin kada akai dare, don yasan partyn da aka fita, dayin ma

griba ai dole akai dare.

Cewar shi ta

👇



( _amma ba za,a kai dare ba koh."?_ ) Girma ne da kuma iya magana yasa yake umarni da sigar tambaya, Don babu mamaki idan sunyi daren kaji yana tuhumar su, ~_"Bance kada akai dare ba."_?~

K'ofar d'akin da

suke ya nufa. Ya tsaya a bakin k'ofa "Kuyi sauri fah, ni na fito." Da sauri suka fito, suna zolayar shi, "Yaya anyi kyau fah.!!

_______________

Suna zaune a kan kujeru, a wani wajen shak'atawa, Bashir Hafsah Zainab Ameera da Mufida.

Idon Hafsah ne

ya hango mata wata kamar idon sani a wajenta, ita da wani suke tahowa, cikin takun k'asaita, kayan jikinta kamar sa b'arke saboda kama tan da sukayi, babu ko mayafi a jikinta. Suna k'ara nufo su tana k'ara wayewa da wacece, nan ta hau tab'a Basheer tana nu

na masa ita da yatsa, "Basheer, ka ga wata, wallahi Jamila ce, ba bari dama na dad'e ina nementa."

Tayi zumbur zata mik'e Bashir ya rik'ota, "Haba sister ki bari mana, ki daina nuna su, me zaki mata idan kinje."?

"Ka barni Bashir, baka san na dad`e ban

ganta ba, nayi shekara biyu rabon da na ganta."

Zata kuma mik'ewa ya kara rik'eta

"Plz ki bari yanzu ba fa kamar da bane, ki kyaleta kawai, babu lallai ma ta kulaki."

Nan ta hau mishi magana fad'a-fad'a kamar zatayi kuka, "Don't you know for how lon

g nake nemanta amma kuma zaka hanani, kasan me nake ji araina.. I hate Wannan rayuwar da Jamila take, bazan iya dinga zuba ido ina gani ba..

Yasan halinta da saurin kuka, don haka, ya shiga rarrashinta, "I'm sorry aunty ba hanaki zuwa zanyi ba, amma ki

jira ita tazo kinga da alama ma ta ganki, kuma tunanin da kike akanta yana da wuyar yuwuwa yanzu fa, ba,a iya chanja mutum lokaci d'aya. Bata ce mishi komai ba ta mik'e ~_"Ai idan da alkawari ba zata ga Jamila ta share ba, ko a wanne hali take ciki kuwa._~

Shima dole ya tashi, yawa sauran k'annen nashi alamar su biyo su kawai, ya musu nuni da su dakkowa Hafsah jakarta.

Jamila na hango, Hafsah, ta rabu da wanda take tare dashi tazo da gudu ta rungume ta, sun nuna jin dad`in ganin juna kafin, Jamila tace

, Ai ina ganinki sometimes street haka ko wani waje, akwai distance tsakanin mu that's why bana miki magana.

Hafsah dai bata iya cewa komai ba, sai murmushi, kallon Jamila kawai, take, gaba-d`aya ta chanja, idan baka mata kyakykyawan sani ba ba zaka gan

e ta ba.

Jamila ta miko mata waya, lokacin su Ameera sun k'araso inda suke, ta daga musu hannu, ga mamakinsu duk sai da ta ambaci sunan su, "Ameera Zainab, Mufida, sannunku."

Ta kalli Bashir daya tsaya can gefe, bata mishi magana ba, shima kallon nat

a kawai yayi, ta mik'awa Hafsah wayarta samin phone dinki anan, munyi magana naga kina sauri nima ina sauri.

Hafsah tasa mata, ai kafin tau

k'ara kalma d'aya Jamila tabar wajen tana d'aga mata hannu.

Hafsah tayi ajiyar zuciya, zainab tace, "Yaya is s

he your friend Jamila."

Hafsah ta jinjina kai, ba zata iya magana ba.

"Chab." Ameera tace.

Mota suka shiga Basheer, yaja bai yiwa Hafsah maganar Jamila ba sam, Hafsah kam gaba d'aya yanayinta ya sauya ya koma damuwa, tsoron Allah ya k'ara shigarta, wa

i Jamila ce haka, babu ko mayafi, wacce a da bata iya yawo Inba da hijabi ba."? Kishin hakan ya cika zuciyarta, bai dace ta zuba ido tabar Jamila haka ba, ko ba komai ada ta amsa sunan k'awarta, ita gashi ta zama wani abu, amma Jamila fa, sam abinda take b

abu mai alfahri da ita.

Take ta sawa ranta zata yi iya kokarin ta wajen dawo da Jamila kan hanya, ita kanta tasan abin yana da matuk'ar wuya aiki ne ja, amma kamar jahadi ne, to kuma babban k'alubalen shine rashin sanin ta ina zata fara."?

Su Bashir na

ta hira ita kuwa tsit kake jinta, yana kallonta ta madubi, sai yaji ta bata mishi rai ma. _Duk wannan sauyawar da damuwar akan mutum d'aya, da babu alak'ar kusa ko ta nesa yanzu Tsakaninsu, matar da take yin abu bisa saninta, kuma da hankalin ta da ilimin

ta."? Mene zaisa ta damu kanta, tunda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login