Showing 75001 words to 78000 words out of 132482 words
ita maiyi d`in tana ganin daidai ne._
_________________
UKhasha tuk'i yake sosai, yayi watsi da tsokanar da su fadwa ke mishi, shakiyan ci ne kala kala, _Wai gaskiya yaya tunda Yaya Jabeer yayi aure kaima ya dace,
kayi tunda dama ku biyu kuka rage._ Yayi burus dasu baice musu komai ba. Yanaji fadwa na bawa maryam labarin, _Bahijja_ da ke sune a baya. Sukayi shewa harda tafawa, ya juyo rai a had'e.
"Bana son shashanci, Allah zaku fita daga motar nan kuna min ihu a
mota."
Haha.. Dariya suka mishi, ya juya kawai ya cigaba da tuk'inshi..
Wani Uturn suka zo daidai, lokacin Basheer shima ya taho dake mik'ewa zasuyi street su, shi kuma ya riga ya taho, Allah, ya kiyaye aka d'an bigi bayan motar tasu kawai. Dukkans
u parking sukayi, kafin Bashir ya k'araso shi har yazo inda suke, _"Yi hakuri mai gida._ Abinda Basheer ya fara fad'a masa kenan, ya daga mishi hannu, _"Bakomai bakomai, muyi hakuri duka._ motar taku batayi komai ba."?
"Eh.. Inji Basheer "Hope kuma ha
ka." "Babu koma, ka dinga kula kawai k'anina"!!
Karaf idanunsu suka had'u dana Hafsah. Yaji wani shock, Tabbas Itace.
Itama fad'uwar gaba taji, _kamar ta sanshi fa._
Bashir na shirin juyawa zai koma mota, _Dan Allah k'anina kaji mana._
Basheer ya
dawo da mamaki.
"Me kace."?
"Um.. K'annen nan naka ka taimaka min da d'aya."
Bashir ya kalleshi da mamaki.
Me yake nufi kenan.?
Yayi k'asa da murya don yasan tambaya yake shirin yi mishi.
Kaga bamu da lokaci kana sauri ina sauri, taimaka min da num
ber.
Bashir yayi jim, kafin yace okay.
Ya sa mishi number, yayi saving.
Ya mik'a wa Bashir hannu sukayi musabiha, "Nagode sosai abokina."
Bashir ya shiga mota, shi kuma ya k'arasa inda yayi parking, ya buda motar, gaba-d'aya yanayinshi ya sauya zuwa
sanyi, akan idonshi suka wuce, da alama su ba wajen bikin zasu ba.
Yayi amanna Allah ne, ya dube shi ya k'ara had'a su. Su Fadwa sunyi mamakin sauyawar shi lokaci d'aya.
Basheer kuwa ya tafi yana mamaki, mutumin nada kyan mu,amala, shifa aka bugawa
amma shine ya fito...
Mufeeda ta ji bazata iya shuru ba tace, Yaya naga kamar kunyi exchange numbers da wancan."
"Eh.."
Kawai yace mata, don bai son fad'ar dalili don baisan wa ya gani cikinsu ba, aranshi yaji yana fatan _Allah yasa Hafsah ce._
Da
suka zo wucewa ma sai da ya d'aga wa Basheer hannu, sannan yaja tashi motar...
_Addu,a Kawai yake axuciyarshi Allah ya taimake shi akanta ta yarda dashi..._
📝
*HAJEEYA KHAREEMERH*
♥
️
♥
️
♥
️
♥
️
*ZAZZAFAN SO*
(masoyin k'warai )
*Cigaban litt
afin Zazzafan so*
*(Guba ne)*
💔💔
*By:*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah khareemerh)*
*Dedicated to Unique in your love heart group members.*
📄
*46*
*Allah-Allah* yake ya dawo gida, ya kira number da ya karb'a, number da ko sunan ma
i ita bai tambaya ba.
Biki yayi dad'i sosai. Ango da amarya kowa na cikin farin ciki, anci an sha, sannan an sha rawa, gobe shine kai amarya.
Ko a wajen bikin ma kiran bahijja wajen uku, amma bai ji bama saboda k'arar kida bare ya d'aga.
Sanda suka dawo
gida kuma, wajeny misalin tara na dare, shi kanshi shakkar shiga gidan yake saboda Abba bare kuma k'annen nashi. Babu yadda ya iya biki ne na aminin shi, ya kamashi ne sosai abin, banda haka shima ba son hayaniyar biki yake ba, kuma muddin baiga k'annen s
hi gurin bikin ba bazaiji dad'i ba, shiyasa yaje da su na yau.
Yana parking suka fito, shima ya fito, bai wuce ko ina ba sai d'akin abban dake gefe.
Da sallama ya shiga, amma ba,a amsa ba, sai akayi gyaran murya alamar ya shigo.
Ya sami guri ya zauna, y
ana jiran abban ya gama jan charbin da yake. Carbin k'ato ne irin mai dubun nan, Allah ya so ya kusa gamawa, yana kammalawa ya kalleshi.
Ai kafin Abban yayi magana Ukhasha yayi. "Afwan akaramakallah, bamu dawo da wuri ba, abinne ba,a fara da wuri ba.."
Y
a d'aga mishi hannu kawai.
"Mun gode, Allah ya k'ara girma." Zai mik`e Abban ya dakatar dashi da hannu. Ya dawo ya zauna.
Yayi gyaran murya kafin yace, "Kaje kiran da Baffan yayi maka koh."?
"Wata fad'uwar gaba ta ziyarce shi, _Abba yasan da maganar ken
an, indai haka ne toh dole ya k'ara k'aimi don idan har Abba ya fara sa baki a maganar abin bazai mishi kyau ba._
"Eh naje Abba."
"To madallah, sai ayi k'ok'ari tunda ansan aje na wasu.
Ukhasha ya sunkuyar da kanshi kawai, a zuciyarshi yana cewa, _Ai ni
na riga na samu.!!_
"Za,a iya tafiya, Allah ya bamu alkhairi."
"Amin, Abba sai da safe."
Ya fita, shima kanshi sauri yake yaje ya gwada number nan.
Yana ta k'okarin kira amma kiran Bahijja dake ta shigowa ya hana sau biyu yana _rejecting_ ya gaji ya d
'aga rai a b'ace yace, "Wai ke meye hakane, ki kyale ni da-Allah, haba.!!
Ya katse kiran, sannan ya hau kiran number, _is switched off ake ta ce mishi_ amma ya k'i yarda sai kira yake yana kumawa,
har ya gaji ya daina, gaba-d`aya yaji ranshi babu dad'i t
o ko dai alhakin yarinyar can ne da yayi wa tsawa, tunda yasan irin son da take mishi bai dace ya mata haka ba. Nan take ya yanke shawarar ya kirata ya bata hak'uri ko shima Allah zai taimake shi, don ya tabbatar indai bai samu number ba ayau to tabbas ba
zai iya barci ba, yarinyar ta rikita shi lokaci d'aya, musamman yau daya k'ara ganinta, ai ji yayi jininshi na tafasa, gaskiya ba k'aramin al amari ne ya same shi ba.
Ya lalubi, number Bahijja, ya kira, ringin kad'an tayi ta d'aga tare da sakin ajiyar z
uciya. Shuru yayi itama tayi shuru, shi har ga Allah tausayinta ke tsarga mishi a zuciya. "Me yasa bakiyi bacci ba.?
Kawai ya fara da haka. Cikin shashshek'ar kuka ta fara magana, ba kaine kace kada na k'ara kiraka ba."?
"Ya isa toh, kiyi hak'uri kece ki
ka batamin rai, ina gaban abbana kina ta kira.
Murna ta cika zuciyarta, yau ita ce, ukhasha ke bata hak'uri."? Wacce irin rana ce yau data zo mata da sa,a haka."?
Yana ji a kunnenshi tana sauke ajiyar zuciya, ta ma rasa me zata ce.. "I'm sorry.." Yaji ta
ce, kana jin muryarta kasan tana cikin farin-ciki, shi kuma zuwa yanzu ya k'agu ya kashe wayar.
"Ok, kiyi bacci kinji."
Yace mata haka, amma ita sam bata son su katse wayar, yadda take jin farinciki yau, sai ta b'ige da mishi shagwab'a. _Um..um._
"King
a koh, meyasa haka toh ina miki magana sai ki k'iji, ni inason nayi bacci ne toh."
Sai kuma ta shiga hankalinta. OKey Dear ka hak'ura da abinda mamana ta maka."?
Cikin k'osawa yace mata yes."
"Thank you."
"Okay gud night."
Yace mata, tare da kashe way
ar.
Ita kuwa farincikin daya sa mata Allah ne kad'ai yasan yawanshi. Tayi wani juyi akan gado cike da murna. Sai murmushi take, _Yau Itace ya nuna damuwa da ita haka.. Duk da ba yau kad'ai yake cewa ta daina kiranshi ba, amma tasan duk ranar da yayi mata
irin haka, baya k'ara saurarar ta. amma yau shine har da biyo kiranta..? Gaskiya taji dad`i da alamun nasara sosai a tattare da ita.
Mamanta ce ta shigo, ta tsaya akanta, bayan ta k'are mata kallo, ta lura da wayar dake hannun ta tace, waya kike da wa
nnan mara mutuncin yaron koh."?
Ta ke ta had'e rai, "mama please ki bari, stop abusing him, ni banga me ya miki ba fah!!
Uwar Tayi kwafa, "Hmm, idan an zage shi sai me, banzar yarinya kawai, idan bakiyi wasa ba, sai na k'wace wayar taki ma.
Yar ta juya
mata baya tana k'un-k'u ni.
_Bahijja, yarinya ce wacce bazata wuce shekaru 19, ba, asalin yaren mahaifiyar ta Ibra ce, mahaifinta kuma, bahaushe ne, mahaifiyar ta basa tare da mahaifinta, sun rabu tun tana yarinya, kuma ta hana shi ita. yarinyar na da kir
ki sab'anin mahaifiyarta, bata dad'e da kammala karatun ta na secondary ba.
A tsarin Ukhasha da ra,ayinshi, sam babu irin yarinyar a rayuwarshi, yanayinta, shekarunta, yanayin tarbiyyar gidansu duk baimishi ba sam, abinda yasa ma mu,amular su tayi tsaho
haka, saboda yana tausayin yarinyar, gashi shekarunta sunyi k'ank'anta ace tana fuskantar abu irin haka, ban da wannan da tuni ya yanke mu,amalarsu ko ta Yaya ne..
Kawai shi ya yarda kaddara ce ta had'a su.
_Wato wata rana ne, garin anyi ruwa irin na
asubahin_ _nan, shi kanshi badon dole ba, da bazai fito ba a lokacin, amma haka ya fito aiki. Kuma ranar sai ya chanja hanya akan hanyar da yake bi, saboda yayi sauri yaje inda zashi don ya so ya makara. Akan hanyar ne ya gamu da yarinyar cikin uniform, ta
na tsaye bakin titi, ta rasa mota. Da kanta ta tsaida shi, ganinta da uniform yasa ya tsaya._
_Sai da ta shiga, sannan tayi mishi magana "Ina kwana.."? Don Allah can gaba zaka ajye ni, na rasa mota ne."_
"Okay, yace, mata bayan ya amsa gaisuwarta.
Hanka
linshi nakan tuk'i, ya manta wayar shi akan kujerar da zata zauna ya bari, sai dai ya lura kamar ta d`auke wani abu sanda zata zauna.
Lokacin da aka k'araso makarantar su, tace masa ya tsaya anan zata sauka.
Ta mik'a mishi wayar, kawai yasa hannu ya karb
'a.
Tana ta godiya.
Shine ma ya tambayeta sunanta,
"Babu komai, ya sunanki ne, tace _Bahijja_ "kaifa.? Yace "Ukhashatu."
Tayi murmushi ta juya tafi.
To tun a washegarin ranar, shi dai bai san ya akayi ba, kira yake ta shigowa wayar shi, da w
ata number, tun bai d'agawa har ya d'aga take ce mishi, Bahijja ce."
Tambayar farko daya mata shine, "Ina kika samu number ta."?
Tayi dariya kawai, tak`i bashi amsa, sai cewa tayi, "Godiya na kira nayi maka."
"Kada ki damu."
Yace mata.
"Zamu iya ding
a gaisawa a waya."?
Shi kuma ganin ta yarinya, kawai sai yace, "Eh k'anwata amma sai kin fad'amin inda kika samo number.
A wayarka na gani.
"Hmm.."ki daina d'aukar wa mutum waya."
Tace "Toh.
"Kayi saving number."
Zanyi, sa anjimanki."
Tun daga rana
r take kiranshi, watarana ya d'aga watarana ya share, shi bai kawo komai a ranshi ba, ganinshi yarinta ce , kawai. Bai ankara ba har sun shafe wata uku.
Lokacin tace mishi ta gama makaranta.
Yayi mata murna. Sannan tace, "Ko zai zo partynta."?
"Bana zuw
a party.!!
Yace mata.
Tayi shuru bata yi magana ba. Sai bayan da ya manta, kawai sai gata a gidansu, abinda ya tada mishi hankali kenan, ya akayi tasan gidansu. Ta kirashi a waya, ka ganni k'ofar gidanku za,a barni na shigo."?
Yayi dariya sannan ya gimt
se, "Idan kika ce wajena kika zo za,a barki mana.
Shi duk cikin wasa yake maganar.
Minti kad'an ya jiyo ta window d`in d'akinshi suna magana da Fadwa a harabar gidan.
Tambayar ta take, "Don Allah ina zata ga ukhasha."
Ita kuwa Fadwa cikin mamaki take
ta jero mata tambayoyi, wanne ukhasha."? Anan gidan, ke wacece, bama gurin Zainab kika zo ba."? Dake taga ba zata wuce sa,ar zainab d`in ba.
Babu shiri yana jin muryarta yayi sauri ya fito, lallai yarinyar bata da hankali da gaske take kenan.
Ya rasa da
fuskar da zai tare ta, sai kawai ya had'e rai, "Ke dama da gaske kike."? Ita kuwa murmushi take na jindad'in ganinshi.
_"Eh, ai nasan gidan ku dama."_
Bashi da lokacin b'atawa wajen tambayarta ~_"Tayaya.?_~
Kawai sai yayiwa Fadwa nuni alamar _taje ind
a zata._
yana gani tana kunshe baki alamar dariya take mishi.
Yayi kwafa azuci,
"To kije gida, kada mamanki ta nemi ki, kuma ki daina fitowa irin haka, mata basa zuwa wajen maza."
Ya fad'a yana kakkauda kai.
_"To gashi_ ta mik'a mishi, ledar hannunta
. Bai karb'a ba ya tsaya yana mata kallon mamaki.
"Kayan party d'inne."
Nagode yace mata, rai a had'e zai juya ya barta gun, yaji tace, "Don Allah ka karb'a.
Baya son su tsawaita, Allah ne ma ya rufa mishi asiri abba baya nan.
"Ya mik'a mata hannu, ya
amsa.
Cikin k'osawa ya mata alama, _kije gida, kije gida._ yace da ita.
Yana k'ara kallon shigarta, riga da skirt na atamfa matsatstsu, sai siririn mayafi.
Tayi Jim tana kallon shi. Shima wani tunani yayi.
_Za,a iya zargin shi fa, musamman ma,aikatan g
idan._
Allah yaso a iya nan suka tsaya.
Wuce muje yace mata, don yaga kallon da take mishi yayi yawa.
Don gwara agansu tare d'in.
Sai da suka zo bakin gate d`in fita, yace mata, _"Maza kije gida na gode ki gaida mama kinji."_
Tana murmushi ta d'aga mi
shi hannu. Ya juya ya koma ciki da ledar a hannu.
Yana shiga yayi wurgi da kayan, a k'asa, suka zubo daga cikin ledar, memo ne, me photonta ajiki, sai tarkacen su snacks.
Lallai dole yasan abinyi, tun kafin abubuwa suyi nisa , ai baisan yarinyar haka tak
e ba.
Sai daya kintaci taje gida ya kirata.
"Ke ya akayi kika san gidanmu."
"Um da dama na sani fah."
"To ke a ina kike."
"Can gaba da layin ku."
"Kada ki k'ara min haka, kada ki sake zuwa gidan mu."
Ya fad'a cikin kaushin murya.
Sai ta fara kuka,
tana fadar wasu maganganu da bai bi takansu ba, wai ita sonshi take, ta gaji kwana biyu bata ganinshi, kuma don tazo gidan su shine yake mata fada haka."?
Shidai ya katse wayar yana, takaici. Ya zama wajibi ya yanke alak'arsu dama ya gaji.
Tun lokcin
duk wani block yayi amma, chanja layi take, kamar me aiki a companin _SIM card_ da yayi block zata chanja number ta kirashi, har ya gaji ya daina, idan ta kira ya share, amma haka zatayi ta kira kamar bata da aikin yi sai kiranshi, ala dole yake d`agawa k
o dan ta barshi yayi aikinshi sosai. Ya gaji da abubuwan, shine ya d`auki matakin tunda yarinya ce, bara ya bita ta yadda kwakwalwarta zata iya d'auka. "Ya kirata da kanshi wata rana yace, za,a bashi mata a gidansu.
Amma ga mamakinshi bata nuna alamun dam
uwa ba tace, "Ta ji yayi ta biyu da ita zata jira shi.!!
Gaba-d`aya lamuran yarinyar sun dame shi, shi ba abin ya sauya number shi ba, yana da abubuwan da suke da matuk'ar muhimmanci akan number, Misali account d'inshi na banki, da sauransu.
Wasa-w
asa watansu shidda shida ita, ana fama, Allah yaso babu wanda yasan da ita idan ba Fadwa ba, itama saboda ta ganta rannan ne.!
_Sometimes yarinyar na bashi tausayi, wani lokacin ta bashi haushi, yau dai tausayinta ne yafi yawa saboda shima ya fara bin l
ayin da take bi yaji ya akeji.._
😂
____________
Abisa dole ya hak'ura da kiran number Basheer don tak`i shiga sam, haka ya kwanta jiki a sanyaye babu k'wari, fargabarshi shine _"Kada dai ace wrong number ya bashi.!!_
_________________
Baya
n su Hafsah sun koma, gida, d'aki tayi shigewar ta, tana ta tunani, so take ta samo hanyar da zata fara kudurinta akan Jamila. _Ki jawota ajiki._ wata zuciyar tace mata haka.
Kuma tabbas taga hakan don idan basu shak'u ba ko babu alak'a mai k'arfi a tsaka
ninsu irin ta da, babu yadda za,ayi ta iya aiwatar ta abinda ke ranta.
_Ya ilaahiy ka taimake ni._ Addu,ar da take tayi aranta kenan. Zuciyarta na k'ara hasko mata hoton Jamila a da da kuma yadda take a yanzu data ganta a yau.
_Dama can ana fad'a mata Ja
mila na zuwa unguwar, har gidansu tana zuwa, kawai dai wajenta ne bata zuwa._
Ta d`auki wayarta kamar zata yi wani abu da ita sai ta tuna cewa, ba ita ta amshi number Jamila ba, Jamilar ce kawai ta karb'i
tata Number.
Tana kwance, zainab ta shigo
d'akin, da waya a hannunta, cikin k'asa da murya tace "Yaya ga Na'eem zaku gaisa a waya yace na baki."
Hafsah ta girgiza kai, alamar ba zata karb'a ba. Zainab tayi saurin katse wayar don kada a bata mishi lokaci ko Hafsah ta fad'i wata magana mara dad'i,
ya jiyo.
Suka fuskanci juna Hafsah ta fara magana.
"Bana ce ki daina kula yaron nan ba."
Zainab tayi shuru ta sunkuyar da kai, haka kawai Hafsah bata son Na'eem ita kuma bata ga aibunshi ba.
"To zan fad'awa abbah tunda haka ne." Hafsah ta k'arasa fad
'a.
"Haba Yaya wai me Na'eem din yayi ne.."?
Zainab ta fad'a cikin shagwaba.
"Ban sani ba, nidai nace ki rabu dashi."
Zainab ta turo baki sannan ta tashi ta fita.
_Duk da Hafsah bata fiya takura ba, amma bata barin k'annenta su fad'a halin da zasu cut
u, haka kawai taji Na'eem bai mata ba, kuma don taga alama ba aure ne gabanshi ba kawai yana son ya b'ataw K'awarta lokaci ne._
_Shi kuma daya fuskanci cewa Hafsah bata yinshi, shine yake zuwa da siyasa, ko yaushe idan ya kira a waya sai yace a bawa Yaya
su gaisa._
_Hafsah bata son hakan tana ganin ba zata zuba ido, k'annenta su fada irin halin da ta tab'a shiga ba shiyasa take tsaye kam akansu, duk wani motsinsu akan samari ta sani._
BASHEER
________________ B'acin ran Hafsah bai barshi ya zaun
a a gida ba. bayan sun dawo gida, yayi alwala ya fice, don ya tabbatar idan ya sake suka zauna zaman hira da ita, hirar Jamila zatayi ta masa, shikuma ba zai zauna sauraro ba, don haka daga masallacin, ya nufi wajen wata _snooker_ can bayan layinsu. Bisa T
sautsayi kuma, sai wasu suka fara cha-char baki har takai sun fara kokawa, akan musun _snooker._ Basheer ya shiga tsakiya, har da shi a masu rabon fad'an gashi wajen an cika. Lokacin kuma wayarshi na aljihun