Showing 78001 words to 81000 words out of 132482 words

Chapter 27 - ZAZZAFAN SO COMPLETE

01 Sep 2026

55

wandon shi ba baya, sai da komai yayi _settled_

sannan ya nemi hanyar dawowa gida, lokacin an kiran sallar isha'i.

Sai da ya shigo, gida, yayi alwala, zai fita ya laluba aljihunshi don yasa wayar a chaji, yaji babu komai.

Gun Hafsah ya nufa, tana palour tana cin abinci, _"Sister an sacen wayata fah._

"Ta zaro ido, a ina yaushe kuma."?

Gashi ban ganta ba, "Ina tunanin wajen snooker da naje ne."

Bata ce komai ba, tahau kiran wayar amma _is switched off_ ake ce mata itama.

_Basheer ya fice, kawai ya nufi masallaci ya barsu suna, jajantawa.._

📝



*HAJEEYAH KHAREEMERH*

















*ZAZZAFAN SO*

(masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so*

*(Guba ne)*

💔💔

*By:*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah khareemerh )*

*Dedicated to Unique in your love heart group members.*

📄

*47*

*Da* safe Ukhasha, da kiran number Basheer ya karya, amma _still is switched off._

Wata irin zufa ce ta hau tsatstsafo mishi, _ya Ilaahi_ anya kuwa number daidai ce, kada fa ace _yaga samu yaga rashi._

Ya tuna cewa yana da d'aurin auren _JB_ dole y

a tashi ya hau shiri. Yana toilet wayarshi nata ringing.

Har ya fito, kira na k'ara shigowa, ya duba, sunan _JB_ ne ya fito wato angon.

_UK me kuke nufi ne, ya zaku barni ni kadai gashi har na shirya banga ko dayan ku ba."_

"Kai Dallah can wanka nake, k

aga sarkin zumudi dududu, k'arfe tara da rabi fa yanzu, zaka dami mutane."

_"Iyehh, Lallai ma UK wato kaima kabi layin su Mubarak kenan koh, kada ka manta ni yayanka ne yanzu."_

Ya shek'e da wata dariya, "Haha, gaskiya ne, dan rainin wayo."

_Please UK

don Allah ka taho."_

_

"Okey ganinan Allah, k'arasa shiri zanyi kawai.

"Yawwa aboki, abokin gwauran taka."

"Hmm, Allah sai kasa na fasa, zuwa yanzu."

Ahh yi hak'uri, rufamin asiri.!!

Ukhasha yace,

"Kai da bikin naka ma, damuwa ya gadar min."?

_"Ah

aba UK kada dai wannan matar, ta k'ara kiranka neh."?_

"No no no, ba ita ba, wata yarinya ce fah ranar yinin nan."

"Oh wai wacce akace ta yarfa ku koh."?

Suka shek'e da dariya duka.

Hmm, au kace har kaji labari, gaskiya su _NZee_ (_Nazeef _)munafukai n

e.!!

"Ka bari kaidai ku nutsu don sai kun nemo min ita kaida amaryarka.."

_"Haha, UK ashe gaske ne, kenan ka zurma".._

Yai ajiyar zuciya. "Ya na iya.? Suka had'a baki _JB na cewa "Allah ne ya kamaka"_

Shima na cewa "Allah ne ya kamani ni."

Haha, kaim

a ka fad'a ko da kanka, amma babu komai aboki Allah ya sanya alkhairi.

To ya zakayi da 'yar kwailar can.

"Kai chab zaka b'atan rai wallah, kusan yadda zakuyi da ita dai."

_"Hmm, Allah ya kiyaye ka Aboki, amma akwai dan barwa.!_

Amin ango, bari na shir

ya kada mu b'ata lokaci.

An kammala komai anyi d'aurin aure, su Ukhasha ansha zirga zirga har zuwa lokacin kai amarya. Hidimar da suka shiga ne, yasa ya d'an manta da damuwar shi, don bai ma samu ya zauna ba. Allah-Allah yake washegari tayi, ya bujurowa d

a ango abinda yafi damunshi, wato inda zai sami

Hafsah..

___________________

Ta tsammaci kiran Jamila amma shuru, sai yau da daddare, sai ga kira, da wata number.

"Hello,

Hafsah ma tace Hello,

"Kina magana da Jamila ne."

Murna ta cika Hafs

ah, "Oh ya kike.?

"Lafiya lau, wannan ne number sai kiyi save."

Okey Hafsah ta fad'a.

"Bye bye."

Jamila tace, tare da katse wayar.

Hafsah bataji dad'in takaitacciyar wayar da sukayi ba, taso suyi 'yar hira, don ta gano wane mataki Jamilan ke kai."?

A

mma kuma taji dad`in samun number, tayi saving d'inta da nufin gaba ita zata kira..

Ukhasha, yayi juriya, har ya bari akayi Kwanaki uku, da bikin Jabeer ( _kafin ya fara mishi zancen Hafsah_ )

Duk kwatancen da yayi mishi kuma, sam Jabeer ya kasa gano wa

cece..

Kuma yaga alamun Ukhasha d`in ya damu sosai.

"Wai Aboki na baka san sunanta ba neh."?

Um kai dai bari JB wallah, na fada maka har ganinsu na karayi ranar dinner d'inka, ( _Ya bashi labarin yadda abin ya faru._) ka ga amma kullum sai nayi trying

number amma har yau _is switched off._

Kasan taimakon da zanyi maka."

JB ya fad'a.

"A,a"

Kaga nan da k'arshen sati zamu, d'aga (_zasu bar k'asar_) so kazo gobe kawai akwai photos da video na biki ko za,a dace.!!

Murna ta cika ukhasha, kuma fa JB ya ka

wo shawara.

"Wow thank you angon Aisha, gobe da asuba zaku ganni.

"Hah, kazo d`in kaga mana."

"Nagode kai dai."

"Okay UK ana tare fah."

Sukayi sallama, suka katse wayar.

Ya tashi ya nufi d'akin hajiyarshi.

Suna zaune ita da su maryam da Fadwa suna

kallo.

Ya nemi guri a k'asa ya zauna, Hajiya ta kalleshi a zubo maka abinci."?

Ya daga kai alamar "eh.

Maryam jeki zubo mishi abinci.

"To Hajiya."

Sannan ta mik'e ta mik'e, ta fita.

Sai lokacin kuma ya kalli Tv, d`in, wani shiri ake gabatarwa, dama

an hasko wata mata ne tana ta jawabi, sai yanzu aka hasko mai gabatar da shirin.

Gabanshi, ya fad'i, saboda bayyanar fuskar da yake ta bulahin nema.

Ya ware ido, yana kallonta, yanayinta, kamannin ta, Itace dai daya gani a zahiri.

Zata fara magana, ke

nan d'if TV ta d`auke da alama NEPA ne suka d`auke wuta.

Ranshi yayi bak'i ya mik`e zai fice, shi ko jira ma a kunna solar ko yaje ya kunna ma baiyi ba.

Hajiya ta kalleshi. Ina kuma zakaje."?

Ina zuwa Hajiya.

Ya fice ya nufi d'akinshi.

Number JB ya ki

ra.

_"Ya akayi kuma."?_

"Kaii yarinyar nan zata zautani fah."

_Meya faru."?_

Wallahi a TV na ganta yanzunnan tana gabatar da program.

"Hmm, kaii UK kodai zaucewar ce ta sa take maka gizo."?

"Ka manta, ai ban zama _majnoon_ d`in ba tukuna.

Jabeer yay

i dariya, "ah to naga abin naka yayi over ne, ni ka dameni ma fah.

Hmm, to ya zakayi dani, ni nace ku gayyatota bikin ku."?

"Hmm, haka kace koh."?

"Aa sorry Yayana tuba nake."

Abin ya bawa JB dariya, _"Lallai, su Mubarak su zo akwai labari._

A,a JB ka

da kamin haka plz ka san halinsu bazan iya dasu ba.

Shikenan toh, amma ko ban fad'a ba zasuji labari kaidai sai kazo.

Washe-gari daya je, Gidan JB, bai bata lokaci ba ya k'ara mishi jawabi, amarya na zaune na jinsu, sai da angon yayi tambayeta sann

an ta magantu, _"Aysha kin gane ta._?

"Ina tunanin ko H Hamid, ko kuma Ummi nuhu, sune suke service a gidan tv."

Please ki taimaka bari naga photos d`in.

Photo album, na bikin suka miko mishi, sai da yaje kusan tsakiya kowanne photo kallon k'urilla

yake mishi, ango nata zolayar shi shida amarya. Sannan da kyar yaga wani photo, ta gefe, fuskarta bata fito sosai ba, anyi, musu tana lik'i.

"Wannan ce.!!

Ya fad'a da sauri kuma da k'arfi.

ango ya karb'a ya mik'awa amaryar.

"Eh Itace.

Tare suka hada b

aki shida JB wajen cewa, "wacce daga ciki."?

"Hafsah H. Hamid ce."

Azuciyar shi ya maimaita sunan _Hafsah_ sunan hajiyarshi kenan fah.!!

"Duba don Allah ki taimaka min da number ta."

"Ai kasan chanjin layin nan da nayi Allah yasa akwai contact d`in."

Ta fada tana duba cikin wayar, kaf babu number aciki.

Ta dube shi itama ya dan bata tausayi wallah kaga babu.

_Innalillahi."!!_

JB ya dafa shi, kada ka damu, ai bazamu bar k'asar nan ba, sai an samar maka solution, don bazan zuba ido a zautar min da

UK ba.!!

Ukhasha, yaso ya tambayi amaryar _"ko tasan gidansu ta kwatanta mishi.?_ Amma sai ya fasa, yaji nauyin hakan, kada suga kamar ya takura musu.

Abisa tilas ya hak'ura, ya dawo gida a sanyaye, don kafin ya taho ma, sai da aysha ta gwada number wata

k'awarsu, don ta turo musu number amma wayar tak'i shiga..

_Sun rabu akan, ana samu JB zai turo mishi. Yayi musu godiya sosai, sannan yabar gidan.._

A takaice dai sai ranar alhamis da dare, sannan number tazo, wajen ukhasha, shima da daddare wajen k'arf

e shad'aya, duk zumud'inshi, dole ya hak'ura zuwa da safe. Yayi godiya ga Allah ba adadi.

Washegari sakayau yake jin shi, cikin nishad`i da karsashi yayi shirin fita office.

Ya nufi d'akin hajiyarshi ya mata sallama, sannan ya fito. Har ya isa baki

n motar shi zai sa mata _Key_ yaji an kwalo mishi kira. _Yaya Ukhasha!!_

Mahseem ce autarsu cikin uniform.

Ta Kara'so da gudu ta d'ane shi.

"Muhaseem zaki karya ni fah.

Tayi dariya. Sannan ta sake shi.

"Yaya don Allah na bika ka sauke ni a school."?

"Eh muje." Ya zagaya ya bud'e mata k'ofar ta shiga. Sannan shima ya dawo ya shiga ya zauna. Ya tada motar aka bude musu gate, suka fita.

Suna tafiya tana damunshi da hira, "Yaya, wai yau Friday koh."?

Eh, ya akayi."?

"Zaka je dani Masjid d`in abba."?

"Waya ce miki mata na zuwa masjid."?

"Our islamiyya teacher, kuma su yaya Maryam suna zuwa wataran, amma sunki suje dani."

"To zanje dake, amma ni ba masallacin Abba nayi niyyar zanje ba, amma tunda kinaso to zamuje sai ki shirya da wuri, nima zan dawo d

a wuri."

"Thank you, Yaya."

Tayi shuru, sannan ta kuma samun abun cewa, "Yaya wai aunty Fadwa tace wai an kusa bikinka."?

Yayi murmushi me sauti, _"Kai fadwa ta raina shi, wato abin ma har ya kai a gaban Mahseem suna gulmar shi._?

Ta katse mishi tunani

"Eh Yaya."?

Ya d'aga mata kai, alamar Eh."

"To ya sunanta."?

Ahankali yace mata, "Sunan Hajiya ne da ita."

"Yehhh, yaya mu dinga ce mata hajiya itama."

"To, kiyi mana addu,a idan mukaje masallaci."

"Yaya me zance toh."

_Kice Ya Allah ka taimaki Ya

ya ukhasha!!._

"To yaya zanyi, dama "Abba kullum sai yace mu dinga yin addu,a."

"Yawwa, 'yar autar mama, nagode.

Yayi parking, sannan ta fito, don anzo k'ofar makarantar su.

"Yaya adawo lafiya, zan shirya da wuri.

Ya daga mata hannu. Yana gani ta han

go wasu k'awayenta ta tafi da gudu wajensu, sai ta bashi dariya ma.

Sanda ya dawo har Mahseem ta gama shiryawa, lokacin, shikuma, yana d'akinshi ya gama shafa mai, tazo bakin k'ofa ta tsaya.

Yana jiyo, hayaniyar su Zainab daga cikin gida, suna tsok

anarta, _"Inyeh yau za,a masallacin Abbah!!_

"Salamu alaikum. Tayi sallama daga waje, yayo mata magana daga ciki, don bazai bata izinin shigowa ba, "Mahseem ki jirani kinji, kije d'akin Hajiya."

Ta koma ciki shi kuma, ya cigaba da shi shirin shi, cikin n

utsuwa, gefen zuciyarshi da tunanin Hafsah, so yake sai ya dawo daga masallacin sannan ya gwada kira. Yana so ne sai yayi addu,a sosai ya nemi d'aukin Allah da alkhairansa cikin abin.

Yayi kyau cikin farar shaddar shi, da bak'ar hula, bakin takalmi, da ku

ma agogo.

Ya nufi d'akin hajiyar, shi kanshi daya ga Mahseem sai da dariya tazo mishi, taci hijabi har k'asa, ga tasbaha a hanunta.

hajiyar bata nan ma. Tana ganinshi ta taso da gudu ta rik'e hannunshi.

Shima ya kama nata, idon Fadwa akansu, zatayi maga

na irin ta zolayar data saba ya kafe ta da ido. "

Zoki mana photo, sai kiji dad`in kallon mu sosai."

"Kai Yaya ni baku nake kallo ba.!

Ta matso ta amshi wayar, tayi musu, sannan ta mik'a mishi kayarshi.

_Ya karb'a sannan yaja hannun Mahseem, suka fita,

tana mishi hira.._

📝



*HAJEEYAH KHAREEMERH*

















*ZAZZAFAN SO*

(masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so*

*(Guba ne)*

💔💔

*By:*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah khareemerh )*

*Dedicated to Unique in your love heart grou

p members.*

📄

*48- 49*

*Yaune,* suke yinin, Fateemah, sun kacame, a wajen biki, ana ta rawa...

Bikin na matuk'ar dad'i a gurinsu, sun had'u duka 'yan matan, har da matar Nazeer ma, anata rawa, da yake, yinin iya mata ne babu mazaa, ko ango bai halarci

wajen ba.

Adaidai wannan lokacin kuma Ukhasha nata kiran number Hafsah tana ringing amma ba,a d'aga ba. Da ya kira karo na uku, sai ya hak'ura kawai.

Yayi shuru ya zuba wa _number_ ido, tunani yake kodai, ya hak'ura ne."? Sai kuma yayi wani tunani. _"A

yadda take, kuma tana irin wannan aiki a media, dole baza,a rasa, masu damunta da kiraye-kiraye haka ba. Saboda haka zai jinkirta zuwa wani lokaci kawai._

Zai cigaba da addu,a idan da alkhairi akan abin, Allah ya sauk'ak'a mishi samunta. Wani tunani mara

dad'i ya d'arsu aranshi. _Yanzu idan an riga an bada ita fah?_

_"a,uzubillah_

Ya fada a fili, bai ma san ya zai kwatanta halin damuwar da zai shiga ba idan haka ta faru..

Da Wannan tunanin kuma ya shiga wani tunani, na daban, wata zuciyar ta karanta mi

shi.

_To ita yarinyar mutane da kabar ta da damuwa akanka, ya zakayi da ita.. Ko kana ganin zaka samu yadda kake so, alhanin kana da alhakin wata akanka."?_

A hankali ya furta, _"Allah ya gani bana sonta, bazan iya zama da ita ba._

_To ka sama mata mafi

ta, tunda kana kokarin kulla taka soyayyar a wani waje._

Wata zuciyar ta fad'a mishi haka.

To wacce irin mafita, menene mafitar."?

Ya tambayi kanshi.

Kamar an tsikare shi ya jawo wayarshi, ya danna kiranta.

Cike da farin ciki ta d'auka.

Tayi mishi sa

llama, ya amsa cikin sakin fuska. Tana mamakin sauyawar shi, cikin kwanakin nan.

"Bahijja!!

Ya kira sunanta.

Na,am.

Ta amsa ad`an sanyaye don tana tsoron abinda zai fito daga bakin shi.

_Sau dayawa indai zaiyi mata magana mara dad'i yafi bata hankalin

shi, da kuma jawo hankalinta._

Yaushene ma kika ce min zaki cika _twenty years.?_

Farin-ciki ya mamaye ta. _Kodai party zai had'a mata ne."? Sai kuma ta tuna irin gidansu, sannan ta tuna data gayyace shi partyn graduation, yace mata baya zuwa party._

Tana son jin abinda zai fad'a mata don haka tace, "Nan da _three months._

"Okey.." yace mata kawai.

Tayi shuru tana son taji k'arin bayani.

_Wato ma ko 20yrs yarinyar bata cika ba. Ya fada a zuciyarshi. Baya son ta shiga damuwa a k'ananun shekarunta. Ta

bbas ma yaga tsaurin ido da k'ok'arin yarinyar, da har ta iya furta mishi tana sonshi, ashekarun haihuwa fa zai iya bata goma sha uku fa. Sai kuma ya tuna _shekaru ba sune abun dubawa ba indai da so._

"Meya faru neh Dear."?

Tambayeshi, jin yayi shuru ba

bu k'arin bayani.

Babu komai, kawai na tambayeki ne.

Ta danyi jim, kafin tace, _"Okey"_

"Yaushe zaku fara lecture, a makaranta."?

Ya tambayeta.

Nan da _2weeks_ fah. Tana jin dad`i a ranta, yana janta da hira.

"Ina mamanki."?

"Tana nata room."

Ta f

ada da mamakin tambayar kodai wani abu ya k'ara faruwa neh. Kafin ta samu damar magana,

ya saita muryar shi, cikin nutsuwa ya fara magana yace.

"In tambayeki Bahijja ."?

Ta danyi shuru kafin tace, "Um."

"Please ki fahimci tambayata kada ki _getting d

ina wrong."_

Cikin sanyin jiki tace, "Toh inaji."

Kasan zuciyarta na tsoron abinda zai fito daga bakinshi.

Meyasa, da maman ki ta nuna bata son mu,amularki dani baki d`auki mataki ba.??

Tayi d'if don bata da amsa.

"Uhum."? Ya sake ce da ita.

"Me ta k

'ara yi maka ne,?_was something wrong happened again.?_

Ta tambayeshi da damuwa.

"No, no no, kawai naga ta damu akan abin ne, kuma nima nayi tunani to this time ya dace ace muyi mata biyayya, mamanki ce tana da hak'k'i akanki, kuma zata fiki sanin what's

right for you."

Ya fad'o maganar kai tsaye.

Ai kawai sai ya fara jiyo shashshek'ar kukanta. "Why all this dear, kawai kace abinda mama ta maka ne, ba zaka iya d'auka ba, but since when muke tare da kai and you knew that mama bata so kuma bakayimin wanna

n tuhumar ba sai yanzu."

Ahankali yace, _"Calm down plz, ki daina kuka mana._

Sukayi shuru kafin yace, _ Bahijja Kinsan girman iyaye kuwa.."?_ _Kinsan girman da Allah ya basu.? Mamanki nada hak'k'i akanki, duk abinda bata sa mishi albarka ba cikin rayuwa

rki bazai yi miki amfani ba yadda kike so. Ina son muyi magana da ke, amma ki cire aranki don cewa abinda tayi min ne yake damuna, wallah is not, kawai naga time yayi da za,ace kin mata biyayya, ke ba yarinya bace, please mu hak'ura da wannan alak'ar, mu c

hanja mata suna, ki dawo k'anwata zaifi mana dad'i kuma mamanki zata fi amsar hakan pleasse!!_

Kamar ya bata sakon mutuwa, haka kalaman nashi suka shige ta fiye da koyaushe da yake fad'a mata irinsu, a muryarshi ta fahimci da gaske yake ya gama shirin tsi

nke zaren alak'arsu. Sai ta fashe mishi da kuka mai tsuma rai, shi kanshi sai da ya cire wayar daga kunnenshi sannan ya mayar.

Zuciyar shi ce ta karanta mishi, _"Ukhashatu idan fa tausayinta zaka tsaya, sam ba zaku je inda kake son aje ba._

_Cikin dakewa

yace, "Ki daina kuka, ke banda abinki mene abin kuka cikin wannan maganar, ni da ke fa bamu muke da ikon kanmu ba, kiyi tunani, akan abinda nake hango mana, alak'ar yaya da k'anwa ita tafi dacewa damu fiye da wacce muke yanzu."_

Ta saki ajiyar zuciya, "M

e nayi maka laifin me nayi maka."?

"Ya salam, Bahijja, me kwa kika min, me zaki yi min, me yasa kike tunanin kinyi min wani abu."?

Cikin bacin rai ta tace,

" Eh mana, saboda naga gaba-d`aya ka nuna ka gaji dani, baka son cigaba da kulani koh, wai baka g

anin irin son.."

Sai ta k'ara saka kuka, tana tausayin kanta, _wai mene haka ne, wane irin soyayya aka jarabce ta dashi."?_

Kiyi hak'uri kinji, ina sama mana maslaha ne ni da ke, bama son gaba ki zargeni."

A fusace ta cafe zancen, _Idan kayi aure ba."?

Saboda ni baka buk'atata cikin rayuwarka, baka sona._

Yayi shuru,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login