Showing 42001 words to 45000 words out of 132482 words
fito, ta tsaya gefen gidan, sannan ta d'akko wayarta, ta danna kiranshi, ringing d'aya ya d'auka. Yanzu, muryarshi ta fi d'azu yin sanyi.
"Hello,"
"Am gani a gate enku."
"Ok, ki shigo kinji"
'Ya kira mai gadi, a waya yace ya rakata har
k'ofar sashinshi.'
Tana shigowa, mai gadin ya mik'e da saurinshi, "Barka da zuwa Hajiya"
'Ta kalleshi kawai.' Ya shige gaba, tana binshi a baya, yana mamakin wacce irin bak'uwa ce wannan..??
'Asanin shi dai Yusuf, yana yawon daren shi, amma bai tab'a
ganin ya kawo wata, cikin gidan su ba.'
'Azuciyarshi yace 'Allah ya shirya'
Ba wai don yana zargin, Yusuf d'in da wani abu bane, amma, bai ga dalilin da idan zaku tattauna wani abu da mace ba, har sai ka kirata gida kun keb'e..
'Suna isa dai dai bakin
k'ofar wajen nashi, yai mata nuni da k'ofar, "Hajiya nan ne shashin oga Yusuf, d'in."
Ta yatsina fuska, sannan ta ce "Ok."
'Ta murd'a k'ofar a hankali, ta sanya k'afarta cikin wani madaidaicin, falo.
'A kwance ta hango shi, kan kujera 'Three seater', da
ga shi sai singlet da gajeren wando, ta d'an so razana, amma sai ta dake.'
'Ta k'arasa cike da yanga, ta nemi kujera mai kallon tashi ta zauna.'
'Shi kuma tunda ta bud'e k'ofar ya k'ura mata ido, har ta zauna, sannan ya mik'e zaune ya fuskanto ta sosai,
ita kuma ta wani lumshe ido ta bud'e.'
'Ya saki murmushin daya nuna mata yaji dad'in ganinta sosai, sannan ya bud'e baki ya fara magana cikin k'asa da murya.'
"You're welcome"!
Tayi murmushi mai sauti, "Hmm, thank you."
'Ya karkatar da kai, "Zaki, iya.
.
zuwa.. dama"?
Tayi fari da idonta, "Hmm why not"?.
"Yai murmushi thanks alot"
Ahankali ya mik'e ya ya isa fridge ya d'akko lemo da ruwa da d'an plate da cup, duk a ciki, sannan ya tako har kujerar da take zaune, ahankali ta dinga jin fad'uwar gaba, a
mma sai tayi k'arfin hali ta dake, a zuciyar ta tana kishin ka da yaga hakan ya rainata, sai ma ta dinga k'ak'alo murmushin kan leb'e tana yi.
🤔
_k'arfin hali_
😅
'Bayan ya ajye su akan d'an wani table, sannan ya zauna a wajen da yaji ya mishi, wato da
f da ita sosai, sannan yayi gyaran murya,
"Hmm Basma ma friends"
"Hmm, Yusuf, ya akayi ne"
'Cikin juyayyiyar hausarshi yace,
"Hmm mene ma ba,ayi bane, ke dai ki sha lemon nan kinji."
'Ya sunkuiya yana zuba mata a cup sannan ya mik'a mata, "Thank you.
"
'Tace dashi.'
Ta d'an sha yadda bazaice tayi k'auyancin kinsha ko kuma ta shanye ba."
'Ta dire kofin yayin da shi kuma ya ke kallonta cikin k'ura ido, tana k'ara k'awatuwa a idanunshi, wani b'angaren tana kore Hafsah, ta hanyar karanto mishi idan, ita
ce bazata iya ba, saboda gidadancin ta, (ita Hafsan)
'Ita dai Basma jiran, cewar shi takeyi wato taji, ('Dalilin gayyato ta)
'Hum, yai wata gauruwar ajiyar zuciya sanan ya ce cikin muryar da take bayyana mata irin halin da ya ke ciki.'
"Am basma,.. Nasa
n kinyi mamakin inviting enki dana yi, koh,? '
'So kada ki damu, ni ina so ne mu k'ulla friendship ni da ke, yafi na da, and then ina so ki bani shawara da kuma k'arin bayani akan Hafsah."
'Ya k'arasa yana zuba mata idanunshi, ita kuma sai da ta d'anyi k
okawa da tunaninta kafin ta k'arasa fahimtar inda dunkulellen zancen ya nufa.'
'Ta kuma jiyo muryarshi yana cewa, "kin dai son irin mu,amalan da Hafsah ke min, please kina ganin ya za,ayi na jure zama da ita haka,"
Basma tayi murmushi azuciyarta, amma sa
i ta gimtse da taji yace, "I don't mean zan rabu da ita ne, sai dai na fad'a mata zamanmu ba zai yiwu haka ba,.. saboda ita ne fa, for more than 1 year duba rabona da..".
'Sai ya katse zancen babu shiri, ita kuma ta hau ajiyar zuciya.'
"Dole ne kinga na
samar wa kaina, solution koh"
'Ya fad'i hakan cikin k'aramin sauti.'..
'A gidan su Hafsa kuwa, tana kwance, a falo kan kujera, taji sallama, ta amsa tare da tashi zaune don tabbatar wa da wacce take tunani.'
"A Taheer!!
'Ta fad'a cikin k'araji suka run
gume juna.
'Aisha dai ahankali take sakin murmushi kawai.'
'Hafsah ta shiga hidima da ita, ta kawo mata lemo, ruwa da snacks har abinci ma da yaji nama acikin shi.'
'Aisha ta shiga tab'awa tana jimanta yadda zata ruguzawa Hafsah d'an farin cikin da ta
ganta ciki yanzu, amma sai ta sami k'warin guiwa da ta tuna babu ishashshen lokacin b'atawa.
'Tayi goron numfashi cikin rashin sanin ta ina zata fara.'
"Oh dama zaki zo gidanmu Aysha."
"Hahh gani kuwa"
Kinyi k'okarin ganewa."
"Hmm Koh."
"Sosai
ma, don ma babu wuya gidan."
"Hakane kam."
"Ma manku bata nan ne"?
"Eh wllhi ba nisa tayi ba dai ta d'anje barka ne."
"Hmm, lallai kam shine ke kuma baki tafi islamiyya ba."
'Babu kowa ne a gidan, kuma kinsan munyi sauka mun ma juya bita ake tayi fa,
ni hadda ma nake."
"Allah, izufin ki nawa?
"Ai na dad'e a ajin hadda tun kafin muyi sauka izufina 35"
"Kai Masha Allah, hafizai Allah ya bamu yaku."
Hafsah tayi dariya "Hmm Kinjiki."
'Sukayi shiru kad'an kowa na son jin ta bakin d'an uwanshi.'
Hafsa
h dai jikinta na bata akwai magana fa, da akwai abinda Aysha ke son fad'a a yadda taga yanayin ta.'
'Sai kuma, Ayshan ta daure tace "Hafsah ina Yusuf kuwa."?
'Dam' gaban Hafsah ya fad'i tare da jin wani shauk'i, tayi ajiyar zuciya sanan tace, "Aysha na r
asa laifin da na mishi, ya daina nema na, ko zuwan nan na katsalandon da yake min, rabon da na ganshi yafi sati biyu tun fa ranar birthday d'in Basma.'
"Hmm, inji Aysha, lokacin da take ciro wayarta daga jaka, tayi saurin danna wajen videos ta kunna wa Ha
fsah ta mik'a mata. Cikin sha,awa da nishadi ta fara kallon, kafin daga bisani tayi nadamar d'ora idanunta kan wayar,
'Komai burgeta yake har zuwa lokacin da Yusuf ya bayyana cikin videon, sai kuma nishad'inta ya koma kishi, abin bai k'ara tsuma ta ba, sa
i da suka zo yanka cake, gashi ta kasa magana, har zuwa lokacin 'Gift, dake videon wani na k'arewa wani ke shigowa.' Aysha bata ankara ba sai k'arar
Hafsah taji, tare da yin cilli da wayar gefe guda ta kifa sai wani sautin kuka mai tsuma zuciya.'
'Aysha t
a san dole haka zai faru, amma yanayin sautin kukan ke tsoratata, kanaji kasan anayi ne cikin rashin sanin mafita kuma yana fitowa ne daga zuciyar data k'untata rauni ya baibaye ta matuk'a, kuma bata da mafitar hakan, kuka mai sa mai sauraro yaji kamar shi
ma yayi kukan..
'Cikin rauni itama Ayshan, ta d'an daure ta fara magana.'
'Kiyi ha'kuri Hafsah yanzu ba lokacin kuka bane, ki k'arfafa zuciyarki don Allah, kiyi yak'i domin samarwa kanki 'yanci, in yaso daga baya kya koka, ni nasan anci amanarki, amma ki
yi ha'kuri kuka mai zaiyi tasiri anan ba, don Allah ki tashi muje akwai sauran al,amarin da yafi wannan.'
Ta k'arashe maganar tana goge ragowar k'wallarta itama, sannan ta mik'a hannu tana tattaro wayarta data tarwatse, har 'Screen protector' d'inta ya fa
she.'
'Hafsa tayi wata irin d'agowa cikin zafin nema, ta figo hijabinta daga kan gado batayi magana ba ta mik'e, ganin hakan yasa Aysha itama saurin mik'ewa, ta na duban fuskar Hafsah da tayi wani jajir ga kamanninta da suka d'an sauya saboda b'acin ran d
a take ciki. Aysha ta saka ledar kyautar Yusuf, cikin drawer Hafsah, sannan suka jera babu wanda ya kalli ma d'an uwanshi bare suyi wani zance.'
'Ita Aysha tsoron Hafsah ma, ta d'an fara ji a yadda ta ganta duk ta sauya lokaci d'aya.'
'Yayin da ita Hafsa
h, take jinjina irin wannan cin amana na babu zato da aka yi mata. 'Gefe guda kuma tana tunanin yanzu ina zasu je, don ita dai kawai taji tana son tabi Aysha ne zuwa ko ma ina ne.'
'Tafiya suke a hankali har suka isa get d'in gidan, hafsah tasa key ta kul
le gidan, suka cigaba da tafiya, har yanzu zuciyarta na rad'adi, da tariyo mata lokacin da Basma ta rungume mata Yusuf d'inta, idanunta na zubar da zafafan, hawaye a hankali.'
Har suka tsare 'Napep' suka shiga ita dai tamkar kurma ko mutum- mutumi, zuciya
rta ko fal k'una da zafi cikinta..'
*HAJEEYARKU CE DAI*
👌🏼
[1/11, 1:38 PM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥
*ZAZZAFAN SO*
(Guba ne)
*A Broken*
*Heart Story*
💔💔
Story and writing by:
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Kareemerh)*
*
Dedicated to: Unique In Your Love Heart Members*
📄
*32*
*Kafin* su Hafsah, su isa gidan, yusuf da Basma, sun kai wani d'an mataki a shagala..'
( To dama abu ne da kowa ke buk'ata, sai kuma suka keb'e, sannan ga taimakon tattaunawar da s
ukayi ta tsawon wajen mintuna ashirin, wacce yawancinta Yusuf ne ya bayyana wa Basma cikinsa kaf, da duk wani sirri nashi, sanan ya b'ige da bata labarin rayuwarshi har da nuna mata photonan nan shi da yan matanshi na can wad'anda suka d'auka a yanayi daba
n daban.
Yusuf ya k'arasa hure mata kunnenta, sannan ya b'ige ga neman taimakonta bisa halin da yake ciki.')
Komai yayi tasiri a zuciyarta kuma sai yau ta k'ara yabawa dashi sosai, don haka, ta cire tsoron komai, bisa bin umarnin zuciyarta na ganin yanzu
ne ya dace itama taji dad'in rayuwarta.'..
🤔
Suna dira daga 'Napep' yar tafiya kad'an sukayi sai ga gidan da Aysha ta tabbatar shine, ta kuma duba address d'in dake cikin wayarta.'
'Suka tura gate suka shiga, mai gadin wanda bazaifi shekara 37 ba, cik
in shiga sosai kamar ba mai gadi ba, kana ganinshi kasan gidan 'yan boko yake aiki, yasa earpiece a kunne sai kad'a kai yake yi.'
Aysha ta mishi magana "Am kai yusuf na nan koh'?
Yace "Yes tare da kad'a kai.'
'Kaimu part enshi Kai tsaye tayi maganar'.
Dam gaban Hafsah yayi wata mummunar fad'uwar gaba banda wacce take ciki, tun d'azu.' ta ware idanunta ta kalli Aysha, kallon tuhuma dama gidan su Yusuf ta kawo ta.'??
Mai gadi, ya dakatar da tunaninta da cewa.' "Am sorry gaskiya oga baicemin zaku zo ba, s
o ku kirashi idan yace ku shiga sa..
Kai Malam bama son iskancin banza kasan matsayin mu kuwa..?
Wuce muje ka nuna mana idan yaso ka tsaya kaga mu su waye a wajen 'Yusuf"??
'Aysha ta fad'a cikin fad'a-fad'a, cikin son yi mishi baraza.'
Baiyi magana ba
ya wuce gaba suka bishi, yana tunanin wanne irin bak'in mata yau 'Oga Yusuf' yakeyi haka.'?
Har cikin part d'in ya kaisu sai da suka je dai dai k'ofar falonshi mai gadin ya tsaya, yana shirin yin 'Knocking' Aysha ta d'aga mishi hannu ta dakatar da shi.'
"No jeka thank you."
Batayi wani tunani ba ta tura k'ofar ta fad'a ciki Hafsah ma taga bata da zab'i illa ta bita, dukkansu wara idanu suke, kafin idanunsu su gama wayewa a cikin daki'n idon Hafsah ya hango mata su shi da wata da bata gama tantance wacec
e ba.'
'Zuciyarta ta buga da wani mugun k'arfi, ta yi saurin mutstsike idonta, ta k'ara dora shi kansu'
Nan ta hau waige waige kuma, idanunta yakai kan kofin Glass dake kan d'an table d'innan ta rarumo shi ta d'aga Kenan,..
Jikinsu ya basu akwai mai kal
lon su, babu shiri suka rabo, tare da juyowa sosai cikin muguwar fargaba.'
'Tsoro ne sosai ya shigi Yusuf yadda yaga Hafsa babu tsammani.'
'Ita kuma Basma ta hau soshe-soshen k'arya.'
'Zuciyar Hafsah ta tsaya cak cikin rashin sanin abin yi'
'Ko kwakwkw
aran motsi ta kasa.'
Sai wani jiri jiri ma da taji yana kwasarta.'
'Me idonta ke nuna mata shigen al,mara,? Basma k'awarta? da Yusuf mijin da take fata.'
Ta d'an rufe idonta ta bud'e don tabbatarwa.'
'Aysha ce tayi k'arfin halin tafa hannayenta tare da
cewa, dubunku ta cika munafukai, 'yan iska.. ' shed'anu.. Maciya amana, ta nuna Yusuf, lallai ka cika d'an iskan gaske..'
'Tana k'arasa fad'ar hakan Yusuf ya mik'e a zafafe ya wanke fuskar ta da mari.' tayi saurin rik'e kuncin, tana masa kallon k'askanci
, shikuma sai huci yake yi.'
'Sai lokacin bakin Hafsa ya bud'e daga kullewar da yayi, ta mik'e cikin zafin nama tayi kan Yusuf.'
'Taci kwalar shi cikin rashin hayyaci, ta fara magana cikin kuka, da huci,
"k'arya kake Yusuf, yaushe ka zama munafikin mata
..? Yaushe ka kware a yaudara..? Yaushe ka zama d'an iska??.. Yusuf ka cuceni.."
"Yanzu koh zaka aikata haka,.. karasa dawa zakuci amanata sai Basma..??
"Wayyo Allah, Yusuf ka cuceni wallahi, bazan yafe maka ba..'
'Tana k'arasa fad'in haka, ta sakeshi t
are da hankad'ashi da duk k'arfinta.'
'Tun da tayi masa rik'on ya gaza aiwatar da komai banda kallonta da yake, sai tunani da dama cikin zuciyarshi.'
'Yasan dai bai kyauta mata ba, amma to ya zaiyi da rayuwarshi.'?
'Tana hankad'a shin yai saurin zama a
kujera domin ya kusa fad'uwa, ya dafe kai cikin rashin sanin mafita.'
'Kamin yayi wani yunkuri yaji saukar wani bahagon mari a kuncinsa, asukwane ya d'ago don ganin wanne mai tsautsayin ne ya mare shi.'
'Aysha ya gani tsaye akansa tana huci, azuciye yaka
i hannu da nufin yi mata wani wawan duka, amma sai yaji an rik'e hannunshi, ya juyo rai a b'ace don ganin waye ya katse mishi hanzarin sa.'?
'Hafsah ya gani ta dakatar da shi cikin rawar murya mai rauni tace tana hawaye, "Yusuf dukanta zakayi, don ta rama
abinda ka mata."
"Yusuf ka koya min darasi kuma na koya..' me nayi maka da ka saka min da wannan mummunar sakayyar.? Yusuf ka yiwa rayuwata illah, sai da na gama yarda da kai sannan kaci amanata..'
'Ta durkushe a gurin tana kuka mai tsuma rai.'
Shima a
sanyaye ya durk'usa gabanta.'
"Hafsah believe me, banci amanarki ba, bakya tausayina koh, kiss and even hug baki rab'a yimin ba as my girlfriend, amma, Basma fa ita ta..''
"Ya isa! Ya isheka!! Ta fad'a cikin wani fad'a da wata murya mai k'ara gami da ku
ka, da haka basma ta fini a gurinka koh Yusuf, ta fad'a tana nuno, Basma data sab'a jakarta a kafad'a, tana gyara mayafi don shirin rantawa a na kare kafin hankalin Hafsa ya dawo ta juyo kanta.'
Nibance ta fiki wajena ba, idan ta bani abinda kika hanani k
inga kowa matsayinshi daban',..
"Kai wanne iri ne Yusuf mai yasa baka ji ne, ehe, Meyasa ba zaka d'auka hakan laifi bane ko a addini.."
'Maganganun datake yi mishi kenan.'..
"Ta juya ga Basma, kin bani mamaki,kin ci amanata in sha Allah Allah sai saka m
in.."
'Ta finciko Aysha suka fita, inda Yusuf da Basma suka tsaya kallon kallo a junansu.'..
*Yours*
*Khareemerh T Mansur*
👌🏼
[1/12, 1:56 PM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥
️
♥
️
♥
️
♥
️
*ZAZZAFAN SO*
(Guba ne)
*A broken heart story*
💔💔
Story and
writing by:
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Kareemerh)*
*Dedicated to: Unique In Your Love Heart Members*
📄
*33-35*
*Basma* ta saki ajiyar zuciya tana wa yusuf kallon tuhuma, shikuma ya had'e hannayenshi biyu alamar Afwan sannan ya fice da hanzar
i, yafi su Hafsah.'
"Hafsah, hafsah baby.. Please ki tsaya mana".
'Kiranta yake amma Aysha sai faman janta take, tana d'aga mata kafada, alamar kada ta tsaya.'
'Abin mamaki sai ganin Hafsah, tayi ta fizge hannunta, ta d'an yi baya, ta tsaya cak.'
'Ya s
aki ajiyar zuciya, sannan ya k'araso cikin sassarfa.'
Am sorry Baby, wllhi banci amanarki ba, kuma, ki believing me, bazan tab'a rabuwa da ke ba, even if i got everything from Basma.."
"Ya isa,!! Ta fad'a cikin tsawa.'
Kana nufin hakan ba cin amana ne b
a koh?"
'Ya dafa kai, ke kika janyo koma menene, i have tell you for multiple times, idan baki yarda dani ba, komai ya faru kada ki zargeni."
"And I swear to God, ko yanzu kika daina guduna, zan rabu da Basma."
"Ki yarda ban miki cin amanar rabuwa da ke
ba'!
'Ji tayi hankalin ta na neman barin jikinta.
'Wanne irin soyayya kenan sukeyi, Zai rabu da basma idan ta aminta da buk'atar sa,.. Idan kuma ba haka ba zata zauna da kishiyarta kenan wato Basma??
"A hankalce ma abin babu tsari. 'Ta rasa wanne marta
ni zata mayar mishi, iya bak'in ciki dai ta shak'a acikin kalamanshi, har wani abu ne ya tare, mata mak'oshi.'
'Ta girgiza kai cike da k'uncin rai tace cikin sanyin murya.'
'Yusuf na gode da sakayyar da kayi min.'
Kuma nagode, da matsayina da ka nuna mi
n.' ta nuna kanta, "Yusuf wai ni kayi wa haka koh? "Na gode, wasu hawaye masu zafi, suka sakko zuwa, kan kuncinta.'
'Cikin gudu gudu, tayi saurin bar mishi wajen.'
'Kiranta yake amma ina tuni Aysha ta janye ta sukayi gaba.'
'Mai gadi ya yana musu a sauk
a lafiya,Hajiya.'
'Cikin sa,a suka sami Napep, cikin layin duk da GRA ne,
'Tunda suka shiga Hafsa keta faman aikin kuka, Aisha na faman rarrashinta, amma ina, abu yaci- tura, babu abinda take fad'a sai "Aysha yusuf yaci amanata, ya cuceni."
'Ita dai Ays
ha hak'uri kawai take bata.'
Sun kusa isa gidansu Hafsah, aka kira Aisha a waya, ta d'aga.'
"Hello mama,.. Ok, tom ina hanya yanxu zan dawo.'
'Ta Kalli Hafsah.' Kinga mama ce ke kirana, idan aka sauke ki sai ya wuce dani da nayi niyyar in raka ki gida.'
'Hafsah ta gyad'a kai kawai.'
"Amma don Allah Hafsah ki saita kanki kada mama ta gane, halin da ake ciki."
'Hafsah ta gyad'a mata kai.' ta d'akko 'Handkerchief' daga cikin Jakarta, ta mik'a mata.'
"Please ki goge hawayenki."
'Ta karb'a tana gogewa wa
ni na k'ara fitowa.'
'Har k'ofar gida, aka kaisu.' Kuma, tun sanda suka shigo layin, ta cikin madubi, Hafsah ta