Showing 57001 words to 60000 words out of 132482 words

Chapter 20 - ZAZZAFAN SO COMPLETE

01 Sep 2026

45

to be love, and you no longer have to fight for it.._

In ta tuna tana samun nutsuwar zuciya, da hakan, kuma tasan Tabbas wata rana zata iya samu, kasancewar tasha haduwa da wadanda kai tsayen zata iya

cewa basu dace da ita d`in ba ta fuskar mu,amala, suna mata kamanceceniya da irin ta Yusuf, ko kuma ta fuskar dabi,u da Yanayin fahimtar rayuwa.

A haka har ta tattara su ta watsar ta mayar da hankalinta gabadaya kan karatun ta wanda dashi take fatan gina

feature dinta.

To irin haka ce tayi ta gara rayuwarta da zamaninta, har kawo yanzu, da shekaru suka shud`a ba tare da ta ankare ba, amma yanzu bulaliyar da Basheer yayi mata ta farkar da ita, cewa Tabbas akwai buqatar ta matsa ta bawa 'yan baya waje, sum

a suci nasu zamanin.

Don da tuni ma Ameerah tayi mata tsallake, sai aka samun akasin tafiya k`aro course da mijin da ta samu yayi wanda zai kai shekara d`aya, zuwa da rabi, da tuni ansa rana, kuma abinka da itama karatu take sai duk ba,a damu ba.

Da ire

-iren qananun tunanin nan ta fada kogin tunanin tuno rayuwarta ta baya wato shekarun zaman ta gidan Mama, wanda ta kirasu da shekarun gwagwarmaya....

Muje zuwa.

👍🏼

















*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so

(Guba ne)*

💔💔

*By*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Khareemerh)*

*Dedicated to unique in your love heart*

📄

*38*

*Zaman* ta gidan Maman Ya Nazeer, zama ne da zata iya fassara shi da "Zaman qaruwa da qarin ilimi tare da samun experience akan ra

yuwa.

Zama ne wanda bata samu takura ba sam a yayinsa, sai ma tattalinta da aka dinga yi sam baa son kukanta.

Idan Hafsah zatayi lissafin mutane muhimmai wad`anda suka taka rawa a rayuwarta to tabbas daga abbanta, sai mamanta sai kuma yayar mahaifiyarta

wato maman Ya Nazeer, kamar yadda suke karanta..

Bawai don sun dauki tsahon lokaci tare ba, a,a sai dai taimakon da ta bata na tsahon wata uku kacal, amma shine zatace ya tallafi rayuwarta har kawo yanzu, wanda badon ita ba da tuni ta zama wata abu ta dab

an ba Hafsar da take ayanzu ba."

To dama hakane, wad`ansu mutanen suna da irin wannan baiwar, wad`anda zama kad`an zakayi amma ka qaru da abinda zai tallafe ka har qarshen rayuwa.

Maman ya Nazeer, ta jata a jiki, ta dawo da ita hayyacinta lokacin da ta f

ita daga cikin shi, ta nuna mata cewa tana da da ma lokacin da tayi losing duk wai hope nata, _she lost hope and she's completely broke._

Bata taba tunanin zata iya rayuwar da babu Yusuf cikinta ba, sai gashi maman ta nuna mata cewa zata iya kuma ta koyar

da ita yadda zata iya d`in, kuma gashi ta iya d`in.

Dole ne ta gode mata bisa wannan d`au ki data kawo mata cikin rayuwa wanda bata da abinda zata saka mata dashi banda addu,a.

Shiyasa wani lokacin Hafsan, ke tuhumar kanta da laifin _butulci_ na bujerew

a Soyayyar Gudan jinin matar da ta tallafi rayuwarta.

Amma takanji sassauci idan ta tuna cewar kai tsaye, Maman bata da masaniya bisa hakan sai dai hasashe, kuma baza,a iya cewa tak`i Nazeer kai tsaye bane, sai dai ace tak`i bada fuska gareshi yadda zai s

higar da buk`atar sa, har ya gaji ya haqurar wa zuciyarshi.

Ahankali take tuno abinda ya faru.

#TUNANIN #BAYA

Wato bayan isar su gidan ita da Mama a wancan lokacin sun isa gidan babu kowa cikin sa, kasancewar yaran sun tafi makaranta.

Driver ne ya shig

o mata da kayanta, inda Maman ta nuna mata wani dak`i mallakin yarta Fatima tace "Kai kayan naki wancan dakin."

Ta miqe a hankali, ta ja trolley din ta nufi d`akin.

Sun yini su biyu ita da maman cikin nishad`i har Maman ta sa ta tayi musu girki, sai waje

n qarfe biyu da rabi sannan yaran gidan suka fara dawowa.

Da farko Nazeer ne ya shigo wanda shine babban d`a a gidan, sai fateema mai binshi, sai Al,ameen, sai Nour, sai Siddiqa.

Hafsah ce kadai a palourn ta qurawa TV ido, Ahankali yayi sallama, da takar

da a hannunshi ta dago kai ta kalli mai shigowa, ta amsa sallamar, sannan ta kauda kan ta.

Murmushishi ya fad`ad`a, "Hafsy ce yau a gidan namu."?

Tayi murmushi, Nice "Ya Nazeer ina wuni."? Ta gaidashi tana mai dan duk`awa daga kujerar da take.

Ya sakar

mata murmushi sosai, yarinyar akwai tarbiyya ga Ladabi, lpia lau, Hafsah, ya mama Ina su zainab"?

"Suna lpia lau."

Ya qara kallon ta.

"Ina Mama nah"?

Ta kalleshi so take ya qara bayani ko zata fahimci zancen, wacce maman yake nufi.

Taji abinne banbar

akwai babba dashi yana cewa Mamanshi.

"Ina Mamy nah nace."?

"Uhum. Maman ku."?

Yayi `yar dariya.

"Yes, mamy nah, ai mamie tawa ce ni kad`ai k`wace min akayi aka min rubdugu."

Hafsah bata ankara ba sai jinta tayi tana k`yak`yata dariya, a zuciyarta ta

na cewa dama haka Ya Naseer din yake da hira.?

Ta sani dai yana zuwa gidansu, amma bai fiya jimawa haka ba, kuma ita bata cika zuwa gidansu ta kwana ba, idan ma tazo yawanci yana school.

Dariyar su Mama ta jiyo ta fito zuwa a palourn. "Oh dama nasani ai

sai kai."

Ta fad`a tana kallon Nazeer d`in.

Yayi kanshi mazauni a kujera kafin yace a shagwab`e Mama wai Taraba suka tura ni."

"Taraba"?

Mama ta maimaita,

Kuma kana so."?

Ya girgiza kai, gaskiya A,a Mama nafison koda jigawa neh."

Okay zanyi yiwa s

unusi magana, tana nufin qaninta wanda shi maman su Hafsah ke bi."

"Okay mamy na Nagode."

"Mamy yunwa nakeji." ya fada yana dan shafa ciki."

Sannan ya miqe ya nufi, Kofar fita daga palourn domin dakinshi yana daga waje ne.

Mama ta bishi da kallo, sanna

n ta kalli Hafsah.

"Ikon Allah kinga ya fice, tashi ki zuba mishi abincin kafin ya dawo kinji."?

Toh Mama ta miqe ta nufi kitchen din.

Plask ta samu guda biyu, ta zuba abinci a babban dayan kuma tasa miya, sannan ta shirya komai kan tray, lokacin data f

ito Maman bata palourn kawai sai ta ajye akan dinning, kusan minti uku bai dawo ba, sai ta jiyo muryar Mama nacewa, "Hafsah ki miqa mishi abincin kinji don da kyar idan zai dawo.

"To, kawai tace, ta kinkimi tray din tayi dakin shi.

Ad`an ka re taga k`ofa

r don haka tura wa kawai tayi ta shiga da sallama.

Daga cikin wani daki a dan palourn ta jiyo an amsa inda ya fito ya tarar da ita da kayan tray a hannu, aiko yace me zaiyi idan ba dariya ba.

Ya k`ame yana kallonta yana ta qyaqyata dariya yana nuna ta ha

r Hafsah ta tsorata.

Sannan ya gimtse ya fara magana, cike da shaqiyanci,

"La-la-la-la, gaskiya kina so mama ta zane ni kenan.

ta kalleshi ad`an tsorace sannan ta qara kallon tray d`in.

Ya sa Hannu ya amshi tray d`in ya ajye sannan ya cigaba da magana

k`asa-k`asa.

"Wa yace miki anan Mama ke zuba min abinci."?

"Ai Matsayina bai wuce wannan ba."

Ya d`auki plate daga kan tray d`in yana nuna mata.

"Anan ake zuba min abinci kin manta bani ne mai gidan ba." Ya Qarashe zancen yana zaro idanunshi.

D`an mur

mushi tayi a qagauce, saboda gaba d`aya ji take kamar akan qaya take.

"Bata saba ba sam, ace wai gata ga wani namiji, tsaye irin haka daga ita sai shi, idan aka cire Yusuf, da shi kuma ta bashi wani Matsayi na daban.

Bata da yayye maza, sannan ba wasu ma

zaa ke shigo musu gida ba har su sami damar hira dasu, idan ka d`auke auncle Abdullah, sai shi Nazeer d`in, sai wad`and`a ba,a rasa ba cikin `ya`yan `yan uwa suma kuma jefi-jefi ne. Su a familynsu ma mata sunfi yawa.

Sannan bata son maman ya Nazeer, taga

ta dad`e, don haka ta motsa K`afarta da niyyar juyawa ta tafi amma sai ya katse mata hanzari da cewa.

"Ni al,majiri ne a gidan." Ya fad`a da marainiyar murya.

"Please zubamin, a plate sai ki tafi da sauran."

Ranta bai so hakan ba amma bata da zab`i tana

bashi girma a matsayinshi na Yayansu.

Ta tsuguna, da sauri sauri, take zubawa, ta cika plate d`in.

"Kaii ai bazan cinye ba rage min."

Ta kwashe wajen kwatar (quarter) abincin.

"Yawwa ko kefa."

bata ce komi ba tasa mishi miya da nama tasa mishi salad.

Sannan ta d`auke ruwan da ke kan tray d`in ta ajye mishi sannan ta d`auki tray d`in.

Tana lura da kafe ta da Ido da yayi.

"Thank you Qanwaty!

Taji ya fad`a

Bata ce komai ba ta juya tana sak`e sak`e a ranta.

_"Anya kuwa zata yarda, tayi koda kwana

uku ne agidan nan bare kuma sati, matuqar za,a dinga zata ayyukan hidima irin wad`annan."??_

📝



*HAJEEYA KHAREEMERH*

















*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*

💔💔

*By*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Khareemerh)*

*Dedicated to unique in your love heart*

📄

*39*

*Tana* komawa palour, fateema ta shigo ita ma da sallama, Hafsah ta amsa cike da farin cikin ganinta.

Itama da gudu ta qaraso ta rungume Hafsah tana murna da gan

inta.

"Hafsy yau kece a Gidan namu."?

Hafsah tayi murmushi ita ma, Nice wallah auntie Fateema."

Fateema ta sake ta tana fad`in "Gaskiya naji dadie."

A palourn suka zauna suna hira, Fateema ta miqe taje ta zubo abinci ta dawo tana fad`in.

"Wata irin yu

nwa nakeji wallah."

"Sannunki.!!"

Hafsah ta fad`a tana qara kallonta.

"Level 3 kike koh auntie."?

( _Da ke ta girmi Hafsah da wajen shekaru uku._)

Eh, wata test mukayi mai zafi wallah."

Ta fad`a tana kai lomar abinci bakinta.

"Ke fa, kinyi candy kem

a koh."?

"Eh result nake jira."

To Allah ya bada sa,a.

"Amin."

Suna hirar, Ya nazeer ya qara shigowa, kamar tare suka shigo shida ragowar yaran gidan. Wad`anda murnar ganin Hafsah yasa suka cika gidan da hayaniya.

Ya Nazeer, shima da tashi hayaniyar

ya fara musu magana, "Haba cai cai cai cai, kun dawo ai."

Mama ce ta fito itama, lokacin Fateema na tambayar Hafsah.

Amma dai kwana zakiyi koh."?

Mama ta cafe, "Ai Hafsah nan da sati biyu ma tana nan."

Wani murmushi Nazeer yayi, "Kice mun qaru a gidan

."

Mama, tace sosai ma, ai kasan tayi candy fah."

Ya qara yin murmushi "Allah Mama."?

Sannan ya kalli Hafsah, sam bashi take kallo, ba. "Congratulations sister."

"Thank you."

Tace mishi nan aka barke da hira.

Mama ta kalle su, zan d`an fita.

"Fateem

a, Hafsah ku kula da gidan."

"To mama a dawo lpia."

"Tare Mama suka fice, ita da Nazeer don shi zai driving dinta.

Fateema taja Hafsah d`akin ta suka kule suna hirar Yaushe gamo."

Har dare mama bata dawo ba, sun gaji da hira sun dawo palour, suna kallo

.

Sai can maman tayi sallama ita da Nazeer da kayi niqi niqi irin na amfanin gida.

Mama kenan _mace me kamar mazaa_, a kalla zatayi shekara Arba'in da biyar.

Mijin ta Alhaji Dalhatu ya rasu shekaru uku kenan da suka wuce, ya barta da yara biyar,

uku mata biyu mazaa.

To kasancewar a gajiye maman ta dawo bata samu zaman hira sosai da su Hafsah ba, taje ta kwanta babu jimawa bacci ya d`auke ta.

Da daren Hafsah suna kwance a d`akin Fateema, Hafsan tai jugum tana tunanin Basma da Yusuf. Su su

na can suna jin dadin rayuwar su ita kuma sun barta nan cikin k`uncin zuciya.

"Aunty Fatee, Don Allah ara min wayarki."

Hafsah ta miqe kamar an tsikare ta tare da fad`in hakan.

"Okey ungo."

Fateema ta miqa mata wayar.

Hafsah ta zana number Yusuf a cik

i sannan tayi saving. Kafin tace, "So nake kawai naga mai number d`innan a online."

"Hira zakuyi"?

Cewar Fateema.

Hafsah ta girgiza kai, "Aa dai kawai sa number zanyi, idan lokacin da za,ayi magana yayi zan miki magana.

"Tom."

Inji fateema.

Ai kuwa s

ai ga photon, shi a profile.

"Aa wannan ne me number."?

Fateema ta tambaya cikin zumud`i.

Hmm kawai Hafsah ta fad`a ta kafe photon da ido zuciyarta fal da bak`in ciki yaya ma za,ayi tayi sakacin da zata barwa Basma Yusuf, ai impossible.

"Gaskiya ya had

u fah."

Cewar Fateema, wacce fad`in hakan ya qara tun zira, Hafsah. Sai kawai ta miqa mata wayar ta kwanta cike da tashin hankali.

Dole ta nemi mafita, kuma ta tashi tsaye, tunda ana nema afi k`arfinta.

Wani abu ya maqale mata a mok`ogoro, zuciyarta ke

wassafo mata basma, da irin rainin da tayi mata har yasa ta mata _Snatching_ mafi muni.

A kullum ta tuna bak`in ciki ne ke qara cika mata zuciya had`i da wata qiyayyar basma mara misaltuwa, bata taba jin ta tsani wani ba sai a kanta.

Nunkuwar tsanar kuma

yana da alaqa da rashin samun damar daukar fansa _revenge_ ko yaya neh." Shiyasa abin ya tsaya mata arai, data tuna bata da wata dama fa. Kawai sai ta fashe da wani kuka me cin rai."

Fateema ma na cikin qarewa photon kallo kafin tabi Hafsah da kallo ciki

n mamaki, da damuwa, gaskiya akwai abinda ke damunta.

Cikin in,ina take fad`in "Ha.. Hafsah me menene."? Me akayi miki don Allah kiyi shuru.

Kukan take sosai ko zata sami relief.

Fateema tayi cilli da wayar ta matso kusa da ita tana lallashinta.

"Kiyi

hakuri don Allah, me aka miki ko nice."?

Hafsah ta girgiza kai.

Mama ce."?

Nan ma ta girgiza kai.

Ya Nazeer ne."? Shima ta girgiza kai.

Sai da ta tambayeta

kowa na gidan amma tace babu kowa.

To wanene."?

Fateema an cuce ni, anzalince ni.!"

Ta

kuma rushe wa da kuka.

Hakan ya qara rud`a

Fateema.

To wanene Hafsah kodai in kira mama ne."? Ta fada tana qoqarin miqewa.

Hafsah ta ruqo ta.

Cikin kuka tace, kada ki fada mata don Allah ki kyaleni kawai nina san abinda aka min."

"To ki daina kuka,

ki fad`amin menene, ko kuma in kirata."

Da kyar dai Fateema ta samu Hafsah tayi shuri amma fir tak`i fad`a mata komai sai ajiyar zuciya take. "Ki bari kawai, take iya ce mata.

A haka sukayi bacci, wanda ga Hafsah ba bacci ne kad`ai ba, bacci ne me cike d

a mafarkai, na Yusuf da Basma, marasa dad`i.

Da safe Fateema, tayi shirin makaranta, dukan su na palour banda Hafsah da take ta bacci.

Fateema taso fad`awa mama as abinda Hafsah tayi da dare amma tana sauri.

Sai da yamma bayan ta dawo suna zaune a

na hira kawai mama, ta tashi ta shige d`aki, minti kad`an kuma sai ta k`wallowa Fateema kira.

Fateema ta miqe ta bita d`akin.

"Ina son dama inja miki kunne tun jiya sai kuma na manta."

Maganar da mama ta fara da ita kenan.

Bbu shiri Fateema ta tattara

dukkanin nutsuwar ta ga Maman.

Mama ta d`ora, "Koda wasa kada ki sake ki ara wa Hafsah wayarki ta kira wani, saura kuma kiyi sakaci ta d`auka."

Dam! gaban Fateema ya fad`i jin wata doka mai tsauri irin ta mama.

Anya ta sanar da ita gaskiya kuwa, cew

a Hafsah ta riga da ta ari waya."?

Bare har ta fad`a mata zancen Kukan da Hafsan tasha jiya.

Idan hakane da akwai alamar tambaya kenan game da zuwan Hafsah gidansu, dama abin ya bata mamaki, don Hafsah bata wuce kwana d`aya a gidansu amma wannan zuwa na

bazata, don mama sam bata musu zancen zuwan hafs

Idan haka ne Akwai abinda ya faru.

Don haka ta yanko tambaya tare da d`agowa don yiwa maman amma sai ta d`aga mata hannu.



📝



*HAJEEYAH KHAREEMERH*

















*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin kwarai)

*Ci

gaban littafin Zazzafan so.*

*(Guba ne )*



💔💔

*By:*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah khareemerh)*

*Dedicated to Unique in your love heart group members.*

📄

*40*

*Kada* ki tambayeni komai."

Kawai ki bi abinda nace.

"To mama.

"

Fateema ta amsa cikin ladabi.

Tashi kije ki turo min Hafsan.

To mama.

Ta miqe ta fita, ta sanar da Hafsah kiran mama.

Ta shigo cikin nutsuwa, doguwar riga ce a jikinta ta atampha.

Ta durk'usa a gaban maman.

Mama gani.

Hajiya Nafeesa ta fad`ad`a f

ara,arta sosai.

"Hafsa na. Ya naga duk kin fad`a"?

Bata jira amsarta ba tace, "Ki saki jikinki kinji kuma ki daina sa damuwa a ranki.

Sannan ta qara kallonta, "Ai babu wanda yake takura miki a gidan nan koh."?

Hafsah ta girgiza kai da sauri. "Aa mama

babu kowa."

Tayi murmushi, Yawwa idan ma akwai ki fada min duk wanda kika ga yana damunki ko da kuwa Nazeer ne."

Mama ta qarashe zancen tana dariya Hafsah ma dariya tayi.

So Maman take Hafsah ta saki jikinta da ita tana so ne ta saba hira da ita sosai a

haka har ta saki jiki ta fada mata damuwar ta."

Tana son ta gano Menene matsalar ta ita da yaron.

"Ki bani labarin makarantar ku kinji Hafsah."?

Hafsah tayi d`an

Murmushin jin kunya.

Ko bazaki bani ba"? "Ba mamanku tace ke kike daukar 1st position b

a ko ba haka bane."?

_Duk cikin sigar wasa take mata tambayoyin._

Hafsah ta d`aga kai.

"Gud girl.!!.

baki tab`a zuwa ko ta biyu bane."?

Ta girgiza kai.

"Kin taba zuwa."?

um, sau nawa sau biyu."

Na uku fa."?

Aa.

"To na hudu fah."?

Nan ma Hafsah

ta girgiza kai.

Mama tana dariya tace "To sai na biyar."?

_Tana sane tayi mata tambayar don maman Hafsah ta fada mata komai._

Sai Hafsah taji kunya ta shiga boye fuskar ta cikin cinyoyi."

"Ahh, Hafsa kice kin taba zuwa ta biyar d`in."

"To garin yaya."

?

Shuru babu amsa.

"Wasa kika tsaya."?

Nan ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login