Showing 102001 words to 105000 words out of 132482 words

Chapter 35 - ZAZZAFAN SO COMPLETE

01 Sep 2026

29

ciki, ta nunawa Jamila gefen gado, "Zauna mana."

Jamila tayi murmushi sannan ta nemi guri ta zauna.

Hafsah cikin rawar jiki

ta fito don nemawa Jamila ruwa.

Tana fitowa palourn kai tsaye hanyar kitchen tayi. Basheer ya bita da kallon Takaici, ta zubo mata snacks da dambun nama da basa rabo dashi a, ta had'o da lemo da ruwa. Sai da tazo zata wuce su Bashir yayi mata magana mur

ya a dak'ile.

"Yaya.!

Bata amsa ba ta juyo.

"Yanzu sai da kika gayyato wannan gidannan koh..."?

Jin abinda yake fitowa daga bakin shi ya sata yin gaba, don bata son ma ta saurare shi.

Basheer ya cije leb'e don matuk'a ta bata mishi rai, ya zabu

ra zai mik'e ya bi bayanta amma mama ta hana shi.

Ta daga mishi hannu, "Bari Basheer kada ka bita."

Ranshi ya k'ara b'aci ya zauna shuru ya jingina sosai jikin kujera, bai fi minti d'aya ba, ya mik'e yayi waje mama ta bishi da kallo.

Niyyar fice

wa yayi daga gidan gaba d'aya don haka ya nufi hanyar waje kai tsaye.

Yana bud'e k'ofar gate d`in wani Napep na tsayawa a k'ofar gidan nasu.

Bashir na k'arasa fita yaga kamar ana d'ago mishi hannu ta ciki. Don haka ya dan dakata har mutumin ya fito, m

e Napep yayi gaba, shi kuma mutumin ya nufo wajen Basheer.

Basheer yaso gane shi, sannan yana mamakin irin murmushin da yake mishi.

Yana k'arasowa ya k'ara fad'ad'a murmushinshi, sannan ya mik'wa Basheer hannu suka gaisa.

Cikin fara,a yace mis

hi, Allah ya sake had'amu koh."?

Basheer yayi murmushi tana kallon shi da mamaki.

Kafin yace, "Ai ni sai yanzu na gano ka."

Shima murmushin ya mayar mishi.

Bashir dai kallonshi yake da buk'atar k'arin bayani, kuma yaga kamar bai da niyyar k'ara cew

a komai. Don haka yayi gajen hakuri yace. "Ka kira number ta baka samu ba koh."?

"Hmm, kai dai bari nasha wahala fah,

Ya dafa kafad'ar Basheer, yana murmushi, "Ka wahalar dani abokina, meya faru ne."? Cewar Ukhasha.

Bashir ya taya shi murmushin,

"Wa

llah a ranar aka d`auke min waya."

Ayya Allah ya kikaye gaba. Ukhasha ya fad'a cike da alhini.

"Amiin inji Bashir, sannan cikin son tabbatar wa yace, "Naga kamar nan gidan kazo koh."?

Ukhashatu yayi murmushi mai sauti, sannan yace, "Eh."

"Nan na

zo."!!

Bashir ya mishi kallon mamaki kafin yace, "Gurin abbanmu,? kar dai ka sanshi dama."

Ukhasha yayi 'yar dariya, sannan yace, kai tsaye, "A,a gurin Hafsah nazo.!!

Bashir najin haka ya fad'ad'a murmushi sannan ya mishi nuni, "Aa shigo, zo mu shiga

ciki don inason k'arin bayani.

Sukayi dariya dukkansu, sannan yabi Bashir suka samu kujeru suka zauna, Bashir ya bude baki zaiyi magana Ukhasha ya dakatar dashi.

"Eh dama na santa, na ganta wajen bikin aboki na, so ta hanyar shi na sami contact d'int

a a wajen matarshi, bayan na kasa samunka a waya."

Tare suka sheke da dariya, don yanayin amsar tashi ya baiwa Basheer dariya.

"Ai nasan abinda zaka tambaya kenan a ina na santa koh."?

Cewar Ukhasha.

Basheer ya jinjina kai "Yes.!

Basheer nason yi

mishi k'arin tambayoyi amma baya son ya dameshi.

Da kanshi ya kuma cewa, "Ai nazo wajenta fiye da sati d'aya daya wuce, kawai dai bamu had'u da kai bane."

Bashir yace, "Hakane, sai yau Allah yayi.

Sosai Basheer yake yi mishi wata fara,a ta musamma

n domin har cikin ranshi murna yake kuma yana godiya ga Allah da Hafsah ta samu Ukhasha a matsayin mai sonta, don komai ya had'a, kudi, kyau, ga ilimi.

Bari naje na kira maka ita koh."?

Inji Bashir.

Ukhasha yayi murmushi, "Nagode dama na kira numbe

r ta tun kafin na sauka ba,ayi picking ba.

Bashir yayi shuru yadai mik'e, amma a zuciyar shi yana cewa, _"Ya zaayi tayi picking tana tare da wannan banzar kawar tata.?_

Ya nufi ciki Ukhasha ya bishi da kallo, gaba-d`aya yaron yayi mishi kuma yaji ya

k'ara samun nutsuwa da Hafsah dama gidansu da komai nata..

Allah-Allah yake kawai ta fito ya k'ara ganinta yaji sanyi a ranshi, don tunda ta tabbatar mishi ta amshi soyayyarshi, yake jin wani irin abu na musamman game da ita fiye da na da..

_____

___________________

A cikin gidan kuwa, komawar Hafsah d'akin kenan ta ajyewa Jamila kayan data kawo mata tana murmushi take ce mata, "Ga ruwa fah."

Jamila tayi murmushi, ta k'ara bin Hafsah da kallon da take ta bin ta dashi tun zuwanta gidan.

"Thank

you! tace mata, sannan ta d'ora "Nayi missing dambun nama nan naku da snacks d'innan."

Jamila mamaki ta bawa Hafsah, amma sai tayi, murmushin yak'e kawai tanajin ciwon abin cikin zuciyarta.

"An kira wayarki fah." Jamila ta fad'a sanda ta debo dambun

nama zataci.

Hafsah ta d`auki wayar tana dubawa,

sai taga sunan Ukhasha, ta tsaya jimm, da zata bi kiran amma sai ta fasa. Don tana da yak'inin zai sake kira kuma bata son katse hirar su, kuma bata son tayi waya dashi a gaban Jamila.

"Kinsan da agid

anmu aka bani abubuwan nan bazan ci ba.."? Ta dan tsaya, Hafsah kuma ta zubo mata ido.

"Nan ma don na mugun yarda da ke neh."!!

Inji Jamila tana wani irin murmushi.

Lamarin daya bawa Hafsah matuk'ar mamaki ta kalli Jamila da neman k'arin bayani.

Jamila ta jinjina kai. "Yes, ba komai ake bani a ko'ina nake ci ba musamman ma idan nazo gidanmu, don zan iya ce miki rabona da ko da ruwan gidanmu ne za,ayi shekara biyar ko shidda."

Hafsah ta zaro ido, lamarin ya ba ta mamaki, mamakin dalilin Jamil

a na kin yarda da abincin gidansu. _Wannan wacce irin jaraba ce!!_

Ta fad'a a zuciyarta.

Kafin tayi magana, Jamila tace, _"Saboda zasu iya min kiranye ni kuma ban shirya komawa gidan ba.!!_

Hafsah ta dan zaro ido, abin yafi k'arfinta. Ashe duk abinda

take tunani mafarki ne kawai, Jamila bata da tunanin sauyawa. Saitaji tana shakkar yi mata wasu tambayoyi da, da tayi niyyar duk randa jamilar tazo zatayi mata su. Don a ganinta Jamila Itace dai wacce ta sani a da, kuma tafi kowa sanin ta, sannan tana ga

nin ta isa da ita da har zata yi mata kowacce irin tambaya.

Ashe ba haka bane, tunaninta ne ita a haka, Jamila tayi nisa kuma ta riga ta chanja tsarin rayuwa.....



πŸ“



*HAJEEEYAH KHAREEMERH*

[17/03, 2:53 p.m.] UMAIMA BASHEER: β™₯

️

β™₯

️

β™₯

️

β™₯

️

*Z

AZZAFAN SO*

(masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so*

*(Guba ne)*



πŸ’”πŸ’”

*By:*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah khareemerh )*

*Dedicated to Unique in your love heart group members.*

*HELLO FANS KU K'ARA HAKURI DANI BISA RASHIN POSTING

... IN SHA ALLAH, ZAN TAK'AITA LITTAFIN*

_BANA SAMUN LOKACIN TYPING NE SOSAI._

πŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌ

*NOT EDITED*

✏

️

πŸ“„

*58*

*Suka* shuru ita da Jamila na dan wani lokaci kafin Jamila ta k'ara kallon Hafsah.

"H. hameeed, naga kamar shirin fita

kike yi koh."?

Hafsah ta d'anyi jimm, kafin tace, "Eh akwai wanda zan gani ne."

Jamila ta kafe ta da ido tana mata wani irin kallo, "Hmm kice an kusa mu fara shiri."

Hafsah ta d'anyi wani d'an murmushi. "Hmm Jamila kenan ina fah.."? Wannan _manage

r_ inda nake aiki ne, zaizo zamuyi wata magana."

Sanin Hafsah bata k'arya yasa Jamila yarda da zancenta.

Kafin daga bisani Jamila tace, "To gaskiya kiyi kwalliya a fuskar ki don naga bakiyi kwalliya ba."

You know mazaa akwai rainin hankali, musam

man manyan ma,aikatan nan."

Abin ya bawa Hafsah dariya.

Yes nake fad'a miki, inji Jamila tana zuge jakarta ta dakko wata powder.

Ta mik'e tana cewa, "ungo shafa ko in shafa miki."!!

Kawai sai ta hau shafawa Hafsan. Haka kawai Hafsah taji tana d'a

rd'ar d`in hakan, taji tana kyankyamin Jamila ta tab'a ta amma babu yadda zatayi.

_Powder ce mai tsada Jamila ta shafa mata wacce a k'alla kud'inta zai kai 5k, ta kuwa amshi fuskar Hafsah sosai, dama ta farare ce, tunda Jamila ta zama fara sosai itama d

uk da dama can tana da hasken fata._

Jamila ta ajye powder a gefe, ta kwance daurin d'ankwalin kan Hafsah, bak'in gashin ta mai tsaho ya bayyana.

Jamila ta yarfe dan kwalin tana cewa, "Gashin nan dai na nan yadda na sanshi sai baki daya k'ara.!!

H

afsah tayi dariya, sosai.

Jamila kenan, kina son gashin nan, gashin da naki ma yafi shi yawa "?

"Ta fara zarga mata d'auri tana cewa, Hmm ai nawa fushi ne dashi gashi ba gaba-d`aya ya tafi ba wani yafi wani tsaho."

Ganin suna hira haka ya ba

wa Hafsah k'warin guiwa wajen yin tambayar data dami zuciyarta. Dama bata son had'a ido da Jamila tayi mata ne, yanzu kuwa tana mata d'auri.

"Jamila wa zaki raka Dubai please."

Hafsah ta dake murya ta tambaye ta.

Jamila tayi murmushi.

"Hmm, H ham

eeed kenan."

________________________________

A parlour, Basheer ne ya shigo, har yanzu mama na zaune a parlourn, ita kanta ji take bata aminta da shigewar Hafsah da Jamila d'aki ba. Tunda bata san me Jamilan zata fad'a mata ba.

Sallama Bashee

r kawai yayi ya nufi inda d'akin Hafsah yake.

Mama ta kira sunan shi, "Basheer."?

Ya dakata, sannan ya juyo, "Naam mama."?

"Me zaka shiga d'akin kayi."?

Ya dan shagwabe murya, Kai mama babu komai fah, Ya Hafsah ce tayi bak'o zan fad'a mata."

"H

mm, da gaske."?

Ya saki murya.

"Allah mama.!

Mama ta maimaita, Bak'o."? "Jeka fad'a mata toh.

Mama a ranta itama bata so bakon Hafsah yaga Jamila ba.

Basheer ya wuce, ya nufi k'ofar d'akin.

_____________________________

"Ai Hafsah badon

kina da abinyi ba akwai labari.. Cikin muryar tausayi ta cigaba.

"Bansan ya akayi na yada ke ba, amma cikin in sha Allah idan na dawo daga tafiyar nan zanzo zamu tattauna don ke kad'ai ce zan fadawa magana ki yarda kuma ki bani Shawara tsakani da Allah.

"

Hafsah tayi shuru tana sauraron ta jikinta ya k'ara sanyi.

Ita har yanzu Jamila bata bata amsar abinda take son ji ba.

Sai ta ji Jamila na cewa,

"Aunty zan raka, Kinsan yanzu duk duniya bata da kamata Nima bani da ya ita sai dai akwai Matsal

a guda d'aya nida ita.."!!

Ji sukayi an turo k'ofar babu ko sallama.

Jamila ta juyo, Hafsah kuma ta d'ago.

Yaya."?

Kira sunanta rai a cunkushe.

Ran Hafsah ya b'aci.

Mene."?

Tace mishi.

Ita kuma Jamila ta cigaba da gyara mata d'aurin.

"To kiz

o kiji mana."

Inji Bashir.

Hafsah ta bude baki cikin fushi.

Bazan zo ba, Basheer ni kake disgracing koh agaban kawata koh ni kake wa haka."?

Muryata tayi rauni, "Shikenan bazan zo ba, ko ma mene bazan zo ba inyaso ka rufe ni da duka.."

Bashir ya

san hali don haka ya k'araso cikin d'akin.

Lokacin Jamila ta k'arasa mata d'aurin ta zauna.

"Am sorry my yaya, ba abin zafi bane, kiranki ake a waje."

"Shine Bazaka fadamin ba kake kirana kamar nice mufeeda koh."?

Shidai Bashir shuru yayi, Jamil

a kuma ta zuba musu ido bata son tasa musu baki.

Please Yaya ki zo dai jiranki ake."

Yana gama fad'ar haka ya fice.

Yana fita Jamila tayi magana.

"Ki tashi Hafsah, kinga may be ya dad'e yana jiranki, kinga _no wonder_ ma tun d'azun nan ma shi ya

kiraki so kada yace kina mishi wulak'anci don ya biyo ki har gida."

Jamila ta mik'e ta d`auki Jakarta ta bud'e, ta zaro wani pink jambaki da powder nan ta d'azu.

Ta mik'awa Hafsah, Ki shafa wannan lipstick, zai miki kyau, wannan powder shima kuma ki r

ik'e yana da kyau.

Hafsah ta tsaya saroro tana mamakin Jamila.

Jamila tayi murmushi, ki amsa mana."

Ta ajyewa Hafsah a gefenta.

Nagode Jamila.

Hafsah ta fada, sannan ta d`auki jan bakin ta mik'e ta, Kalli mudubi.

Ta dinga murmushi ganin yacce ta

yi kyau matuk'a.

Ta dan goga Jan bakin tana murmushi azuciyarta tana godewa Jamila, don yau tana da burin ta yanki ukhasha da yawa.

Wow Jamila thank you fah, dama kefa kin iya kwalliya, amma wanna daurin like irin makeup artist ce

ke.!!

Ta bude

drawer zata dakko mayafi.

Jamila tayi murmushi.

Hmm, H hameeed, da gaske d`in ita ce.

Hafsah ta juyo da mamaki.

Jamila ta jinjina kai, Hmm, H. Hammed sana,ar da ake zaton inayi ba ita nake ba yanzu, Allah ne shaida ta, shiyasa nace miki zanzo zuw

a na musamman ina so ki bani shawara, inaso na inganta rayuwata nima."

Jikin Hafsah yayi sanyi ta matso a hankali ta kamo, hannun Jamila.

Sam Jamila batayi irin raunin da Hafsah tayi ba, Hafsah har kwalla ce ta cika mata ido.

Jamila ta lura, sai tay

i murmushi kawai, ta yarda cewa a duniya bata da kamar Hafsah H hameeed.

"Ki saka kwalli mana."

Jamila ta share zancen da fad'ar haka.

Hafsah ta juya ta d'auka.

Jamila ta sa hannu ta d'akko turaren data gani cikin drawer, sannan ta rufe drawer da m

urfinta.

Aka kuma turo d'akin, wannan karon mama ce.

Fuska babu annuri sosai ta leko d'akin ta k'are musu kallo, Hafsah nasa kwalli Jamila tsaye.

Jamila tayi saurin cewa, "Sannu mama."

Lokacin ta bude baki zata fara magana.

Maimakon ta amsa ta sai k

awai ta fara maganar ta.

"Ke Yaya ba cewa akayi kinyi bako ba."?

Kafin Hafsah ta amsa mata. Ta kalli Jamila "Yawwa."

Hafsah ta juyo.

Mama gani nan fah.

"Zo ki wuce toh."

Sannan ta kalli Jamila. Ki jirata kinji."

Aa mama nima ina sauri ne bari

mu fita tare."

Mama bataji dadin hakan ba, kawai sai ta juya tabar musu d'akin.

Jamila ta fesawa Hafsah turare itama ta fesa.

Hafsah ta dakko takalmi a hannu suka fito.

Jamila ta durkusa da suka iso palour, "Mama, sai anjima.!

"To ki gaida g

ida."

Zasuyi gaba, mama ta kira Hafsah.

Suka fara tafiya sun fita kofar palourn har sun nufi hanyar waje, mama ta kira Hafsah.

Hafsah ta dawo tana mamakin kiran.

"Zauna kiji."

Hafsah ta zauna.

Mama tayi shuru, ta shiga wata sabgar ma.

Kusan minti biyu, suna shurun.

Awaje kuma Jamila na tsaye.

Hafsah ta rasa dalilin kiranta da mama tayi, gashi bata mata magana ba kuma.

"Tashi kije ma kawai .!!

Mama ta fad'a mata.

Da sauri Hafsah ta mik'e ta f

ita.

Jamila ta tsargu da kiran da akayiwa Hafsah. Amma da Hafsan ta fito bata nuna mata komai ba. suka had'u a harabar gidan.

Ukhasha tun sanda Jamila tazo ta tsaya ya lura da ita, dake suna daga gefe shida Basheer.

Don ya hana Basheer tafiy

a sai janshi yake da hira.

Acikin hirar ne ya gane cewa Basheer k'anin Hafsah ne, kuma ya ji cewa Basheer ba anan yake karatu ba, kuma shima engineering yake karantawa.

Sannan daga baya yaga Hafsah ta fito, Basheer na ganin fitowarta ya mik'e y

ayi waje Ukhashatu sallama,

"Agaida gida yaya nah.!"

Ukhashatu ya tsaya yana kallon shi, "Haba aboki ya zaka tafi kuma."?

"Dama zani wani waje ne."

Ukhashatu ya mik'a mishi hannu sukayi musabiha.

"Okey thanks alot, zan kiraka in sha Allah tunda kayi

swapping layin."

"Okey nagode ka gaida gida." Inji Bashir.

Hafsah niyya tayi da ta wuce shi, ta raka Jamila in yaso idan ta dawo taje wajenshi. Amma sai ta kasa samun nutsuwa da hakan.

Tana ji ajinkinta kallontan da yake. Kawai sai ta nufi wajen

shi. Ganin haka Jamila ma ta bita amma sai ta tsaya daga can gefe.

Wani shudadden murmushi suka dinga yiwa juna, ukhashatu yaji zuciyar shi fes, kamar an wanke mishi, ganinta yake kamar wata sabuwa, yau tayi mishi wani kyau ne na musamman daya tafi da

tunaninshi..

Assalamu alaykum.

Cikin sakin murmushinya amsa mata yana k'ara kallon cikin idanunta.

Hafsah ta kawar da kai tana murmushi.

Tana tsaye har yanzu. Ahankali taji yace "Queen!!

Ta amsa mishi da idanu.

Yayi mata nuni da kujera. Sai ta

girgiza kai.

Ya kalleta cikin kwayar ido, cikin marairaice fuska yana neman dalili.

Tayi mishi nuni da Jamila.

"Kawata ne mun dad'e bamu haduba for years yau tazo min so zan dan taka mata ne."

Hafsah ta manta da ukhasha take magana, sannan kafe

ta da ido da yayi yaja tayi saurin furta wad'annan kalaman babu shiri.

Ukhashatu ya lumshe ido a hankali, sannan ya zuba su can Wajen da jamila take. Hakika farkon tahowarsu tafi mishi kama da k'anwar babar Hafsah, amma da suka doso shi, xubinta da Yana

yin shiga yasa yaji ya kori wancan tunanin kuma yaji yana bukatar jin wacece ita."?

Murmushin ya saki, sannan yace "Okey, kuma ba zaki kawota mu gaisa ba."?

Ya fad'a da zolaya.

Hafsah tayi murmushi sannan ta matsa ta kira Jamila.

Cikin yauk'i ta

zo amma yin tozali da idon ukhasha sai da yasa ta gyara tsayuwarta. Shikuma ya sami dama yayi mata cikakken kallon na seconni a lokacin.

"Sannu Barka da yamma."

Cikin sakin fuska yace "Barka dai."

Hafsah koh sai murmushi ta ke.

Daga nan Jamila ta n

emi zata tafi, ta hanyar kallon Hafsah sannan batayi magana ba ta fara tafiya.

Hafsah ta d'agawa ukhasha hannu alamun yayi hakuri tana zuwa. Ta bi bayan Jamila tana murmushi.

A hankali ya sauke ajiyar zuciya. sannan a zuciyarshi ya furta k'awarta

."?

Hakika dole yayi nazarin akan al,amran. Kada dai ace Hafsah nayi mishi rufa-rufa ne. Banda haka kawayenta biyu kenan wad`anda kana kallon su zaka d'ora zuciyarka _a layin shakku game da su._ Amma me yasa take ce mishi ta dad'e rabon da ta had'u dasu

."?

Me take nufi."?

Anya bata zo da rainin hankali ba.?

Ita kanta tasan basuyi kama da qawayen kirki ba sam shiyasa bata son a ganta dasu, shine dalilin kenan daya sa take yunk'urin kare kanta, ko nisanta kanta dasu idan ya ganta dasu.!!

Ahankali ya fu

rta, _dole na nemi sanin dalili._

Baya mata mummunan zato, amma baya jin zai iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login