Showing 105001 words to 108000 words out of 132482 words
zuba ido tana mu,amala da k'awaye irin wad'annan.
Amma koma menene to dole yasan dalilin daya sa take mishi k'arya.
_Na dad`e ban ganta ba for long ko for years!!_
Shafshaf Hafsah tayi sallama da Jamila hankalin ta duk yayi wajen ukhasha, suka tsayar da Matsaya cewa Jamila zata dawo idan ta dawo daga Dubai.
Yanayinshi ya d'an nuna sanyi. D fara,a ta nufo shi sai yaji sanyi cikin zuciyarshi, tabbas Allah ne
yayi mishi gam da katar d`in samunta.. Hakika komai nata yayi mishi. Komai cikin nutsuwa da hankali..
Ahankali cike da kulawa yace mata "Sannu fah."
Muryar tayi tasiri wajen sata saurin amsawa tare da sakin murmushi.
"Yawwa ya kake ya hanya."?
Alha
mdulillah hope ban katse muku hira ba.
Hafsah ta girgiza kai.
Noo, dama gaisawa ta biyo mukayi."
Okey, ya fada sannan ya kauda zancen da cewa kamar rad'a. Kinyi min kyau matuk'a, kina da kyau masha Allah."
Hafsah ta saki murmushin jin dadi.
S
annan taji ya kuma cewa, "Ai da gaske you're beautiful shi yasa kika burkita min lissafi.!!
Hafsah ta saki murmushi, tana dan sunkuiyar da kai.
Bayan dan shuru sannan yace, ya mum ya family."?
Suna lafiya lau.
OK so ya kike kema."?
Ya fad'a cike
da kulawa wacce zaka karanta kai tsaye cikin idanunshi.
Ahankali tace "lafiya lau.!!
Alhamdulillah, Kinsan dole nayi taking care, na mai sunan Hajiyata.
Hafsah tayi murmushi, sannan ta gyara daidaitonta a kujerar.
"Sunan hajiyarka kenan.?
Ye
s my queen Hajiyata sunan ta kenan kuma tana so na."!!
Ya k'arashe zancen yana mata murmushi.
"Allah ya kara lafiya.
Ta fad'a a hankali shikuwa yaji ta tarr.
Cikin nuna jin dad`in adduar yace, "Amiin Queen."
Suka d'anyi shuru kafin Hafsah ta da
n daga mishi hannu, please "Ina zuwa.!!
Ya girgiza kai yana kallon ta. Ta mishi alamun tambaya da ido.
"Please kada ki tashi.!
"Tayi murmushi, i'm sorry yanzu zan dawo.!!
Yaji dad`in kalmar _i'm sorry_ d`in data ce. Ya saki tattausan murmushi.
"T
o kije.!
Sannan ya cukune fuska kamar yaron da aka kwacewa alawa.
π
Ta mik'e tana kunshe dariyarta.
Tana juya baya ya zuba mata ido yana k'arewa tafiyar ta kallo, _cikin nutsuwa take._ yana jin dad`in hakan har ta shige kofar cikin gidan.
Ita da
mufida suka dawo, ta rakota da try d`in lemo, ita kuma ta taho da snacks da dambun nama..
Suka mishi sallama dukkan su, ya amsa, suka ajye a kan table d`in, sai faman bin hafsah da ido yake.
Mufida ta gaida shi.
Ya amsa cikin sakin fuska sosai.
Ha
fsah taja kujera ta zauna, ta d'anyi kafin ta dago da niyyar mishi magana.
Karaf idanunsu suka had'u dama shi kallonta yake.
Ta dan kalleshi na seconni itama, shi ko ko kiftawa baiyi ba, hakan ya bata tsoro tayi saurin k'asa da ido ta fasa maganar.
"
Itama k'anwarki ce."?
Ta d'aga gira kawai.
Yayi murmushi.
Sannan yace, Hafsah.!!
Ta tsayar da duk tunaninta kanshi amma bata ko motsa ba bare ta amsa.
Ya dace kisan ko ni waye koh."?
Ta saki murmushin jin dad`in zancen.
Ya d'ora "Tun kafin ki gaji
dani."
Ta sake yin murmushin dai.
Ya jinjina kai yes, amma kafin in fad'a miki sai kin amsa min wata tambaya.
Ta kalle shi cikin ido tana sauraren shi.
Cikin nutsuwar daya tattaro ya had'a da rage sauti kai tsaye ya tambaye ta.
Zaki aure ni"
?... Ya d'an tsaya sannan ya k'arasa, don Allah ki fad`amin.
Ya saki hannayen shi ya ware su, "nayi miki kalar wanda zaki iya rayuwa dashi."?
Hafsah tayi saurin kawar da kai gefe, bata son wannan titsiyan nashi, yau wato bama a waya ba a fili yake mata
wannan zancen."?
Sukayi shuru, sai iskar Yammar dake kad'a su.
"Please ki fad'amin. Don Allah.!
Hafsah ta yi ajiyar zuciya a hankali kafin tace, "Please ka bari mu bar wannan magana kashe lemon ka ga snacks nan."
Yayi mata murmushi, "Nagode
da hidima. Sannan ya kalli abincin ya k'ara kallon ta, Babu abinda zaki bani nak'i ci, amma bani da nutsuwa idan banjin amsar tambayata ba please."
I will tell you ai." so take subar zancen a yanzu don haka ta fad'i haka.
"Okay you promised koh."?
Tan
a murmushi ta girgiza kai.
Hmm, Allah sai kin fad`amin. Ya fad'a sannan babu jira ya shiga zuba lemon a cups. Yau ma guda biyu ya zuba nata da nashi, ya mik'a shi gabanta sannan ya d`auki nashi ya fara sha haka, kafin ya fara had'awa da cake."
Kallonsh
i Hafsah kawai take yi da wani shauk'i. Kadan yaci ya koma ga dambun naman, ya fara ci yana mata hira.
"Mama na tana son abin nan, gaskiya yayi dad'i thank you my queen."
Ya d'ago ya kalle ta, "Kisha mana."
Ta girgiza mishi kai.
Why."?
Naka ne ai.
!!
Nawa ne to ai nina baki."
Hmm, nima ai nina baka."
Baisan sanda ya sa dariya ba. _Dama tana magana haka kamar shi."?_
A fili yace, "Hmm kina da wayo... Kin fi ukhasha wayo.
Tayi murmushi itama.
Ya d`auki toilet paper ya goge hannunshi.
Bayan ya motsa bakin shi azuci yayi hamdala sannan ya zubo mata idanu.
Nagode Hafsah na, na gode da hidima, duk da ke bakya min karar na baki abu kici.!!
Tayi murmushi ta kawar da kai.
"Ai baka ci da yawa ba."
"Ya isheni, nagode, ganinki yana k'a
ra min koshi.!!
Suka yiwa juna dariya.
Kafin ya tattaro nutsuwa yace, "Hafsah.!!
Itama ta bada hankalinta kanshi.
Zan fad'a miki gaskiya tsakani ga Allah ina sonki, kuma ina son in aure ki...
Yayi shuru yana karantar yanayinta.
Kinyi min
a matsayin mata komai da komai.
"Ni ba wani bane, haka mahaifi na, sunan mahaifina Khady Abubakar, yana aiki da ma,aikatar shari,a. Hafsah banyi zurfi a boko ba masters kawai gareni..Sannan ina aiki a wani company, civil engineering shi na karanta.!!
Ya tsahirta anan yana kallonta sosai, Hafsah tayi shuru ita dai, bata da dogon buri akan auren hamshakin mai kud'i, amma tana da burin samun miji wanda yasan darajar ta, wanda zai kula da ita.
A ganinta ukhasha zai iya hawa wannan matsayin.. Tabbas bataj
i makusa a tattare dashi ba sam.
"Ban miki ba ko Nayi miki."?
Ya kalleta da wani salo yana tambayar ta.
Murmushi tayi.
Indai banji amsa ta ba nan da gobe, to banyi miki ba. Ya fad'a yanayinshi na bayyanar da gaskiyar abinda yake cikin zuciyars
hi.
Hafsah ta yi Jim, sai ta kau da zancen da cewa, "K'annenka nawa toh."
Ta bashi dariya ma, sai ya kalleta da murmushi, ke naki guda nawa ne.
Kai tsaye tace "Four.
Ya jinjina kai, "Tab ni kam tsoho ne.
Ta zuba mishi ido.
"Ni ina da ya ma."
Y
a fad'a.
Hafsah ta tsare shi da idanu.
So take ta gane ko da wasa yake.
Sai taga ya nuno mata photon a wayarshi, sun d'auka shida wata akan kujera, 'yar wacce bazata wuce shekaru biyu da rabi ba, ta zagayo ta bayansu ta dafa shi.
Hafsah ta zaro ila
hirin idanunta.
Sunyi kyau matuk'a, amma sai kishin macen kusa dashi ya hanata ganin haka.
Ta d`auke kanta, ukhashatu ya lura da yanayinta da ya sanya shi cikin wani nishad`i mara misaltuwa. _Ashe ana kishi nah."!_
Ya fad'a a zuciyarshi a fili kum
a ya kuma hasko mata photon.
"Kinga mamanta."
"Bata kalla ba tare Allah ya raya.!!
"Amin Nagode.
Yace mata.
Sukayi shuru babu magana tsahon muntuna.
Sannan ta ji shi yana cewa, k'annena suna da yawa nine na uku a gidan mu.
Hmm, tace mishi
kawai.
Kin zaci nine dan fari koh."?
Yace da ita, azahiri haka ne amma saboda takaicin shi take yasa tace, "Noo, ni bana raya kai na nawa ne a gidanku, kamar yadda banyi hasashen kana da aure ba.!!
Ba k'aramar jarumta ukhasha yayi wajen hana kanshi
tintsurewa dadariya ba.
Kiyi hakuri, mantawa nayi ban lissafo miki da shi ba.
Takaici ya hana ta tanka mishi.
Suka k'ara yin shuru, sannan yace, kin gama service d`in koh.
"Um."
Amma naga kamar still kina aiki a wajen.
"Sun d'auke ni ne.!!
Ta
fad'a mishi kai tsaye.
"Okay Masha Allah Allah ya sanya alkhairi."
"Amin."
Ta fad'a fuska babu annuri, tunda ta d`auke shi tun d'azu bai dawo ba.
My queen, ukhasha ya fad'a yana yar dariyar da ya rik'e.
Sai taji ya bata haushi ma.
Sun dad'e ci
kin shuru kafin yace a hankali, _ina sonki wallahi."_
Taji ya k'ara bata mata rai, Azuciyar tace, _k'arya ne.!!_
_Agurin Hafsah gani take Soyayyar mutum biyu bata had'uwa azuciya lokaci d'aya._
"Please ki fad`amin." Ya katse mata tunani da cewa haka
.
A dakile tace mishi what."?
"You loves me, ba kin fad'a min ba rannan inaso ne na tabbatar."
Da k'yar Hafsah ta mayar da k'wallar da ta cika mata idanu.
Ukhashatu ya fuskanci raunin da tayi sosai don haka ya tausasa murya.
"Please inason naj
i don Allah please I love you my queen."
Maimakon ta ba amsa sai ta sunkuyar da kanta tana dan cije leb'e.
Ukhashatu ya shagala da kallonta a haka.
Kyakykyawar farar mace, komai nata madaidaici, ga yangar halitta komai cikin nutsuwa, sai raunin da
yayi zuciyarta yawa, ga _k`i fad'i_
A hankali taji shi yana wata Siririyar dariya me jan hankali.
Ta d'ago a hankali.
"Kiyi hakuri na daina.!! Ya fad'a yana daga mata hannu alamun rok'o.
Bata fahimci me yake ce mata ya daina ba amma zafinshi da
takeji bazai barta ta iya mishi magana ba.
Suka sake yin shuru dai, ya dakko wayar shi yana dannawa.
"Ki tura min photonanki please koda ta Whatsapp ne inason na dinga ganin ki Hafsah na.!!
Taji yace haka.
Bata tanka mishi ba.
"Ya share
babin ya k'ara cewa, Ki fad'a min abubuwan da kike so da wanda bakya so."
Ya fad'a a k'ok'arinshi na kawar da wannan Yanayin da ta shiga, wanda a bad'inin zuciyarshi ba k'aramin kona mishi zuciya shurun nata yake yi ba, dauriya kawai yake, don yana son
jarraba ta sosai.
"Bana son k'arya!!
Yaji ta fad'a kai tsaye baiyi zaton zatayi magana ba sam, sai gashi tayi cikin d'aure fuska.
Ya saki tattausan murmushi, yana girgiza mata kai, don yasan dalilin ta na fad'ar haka.
Nima haka Hafsah, bana son
karya kuma in sha Allah ba zaki same ni maiyi miki itaba..
Ya tsura mishi ido, Shikuma ya d'aga mata gira, cikin k'asa da sauti yace, _"sai dai ina da zolaya.!!_
Ba tayi dogon tunani kan abinda ya fad'a mata ba, banda haka da ta d'ora wasu zantukan
nashi a ma,aunin zolayar dayake yana dashi.
_Misali auren daya ce mata yana da.._
Hmm, tace mishi kawai. Sai ya kalleta itama ta zuba mishi ido sai ya b'ige da yi mata wasu dogayen zantukanshi masu sanyaya mata jiki.
Kiyi hak'uri idan a zuwan nan
da nayi nayi wani abu daya bata miki rai, babu zuciyar da zan so in sata farin ciki kamar taki, sai dai idan ina tare da ke bana iya control d`in kaina, ina iya yin komai ne domin na burge ki, sai dai a samu akasin ke a wajenki ba abin burgewa bane, tunda
ban kware wajen karantarki ba tukuna.
Nagode, da irin hidimarki gareni, amma ina son inji amsata ko da a waya ne, don Allah idan banyi miki kalar wanda zaki aura ba ki sanar dani.!!
Ta bi shi da kallo, shima ya k'ura mata ido.
Bari na barki kada
na cika ki da surutu, Nagode Allah ya huci zuciyarki..
Lokaci guda ya mik'e itama sai ta mik'e d'in. Ji tayi zuciyarta na tafasa, sam bata tsammaci tafiyar shi yanzu ba,
Ji tayi kamar, hasken wajen ne zai d`auke idan ya tafi..
Bata ankara ba ta
ji yana ce mata kiyi hakuri ki karb'i wannan, ta dawo da kallonta gunshi, kud'i ne sababbin 'yan dariya biyu, _wrapper_
Ta tsaya sororo tana kallon shi, kafin tayi yunkurin yin magana ya rigata.
Bance don kina da buk'atar su ba ko wani abin, sai dai
inason na dinga kyautata miki nima da iya abinda nake da iko, kamar yadda kike min.
Ya ajjye su akan table d`in sannan ya daga mata hannu yana murmushi mai tsaya mata a rai.
"Bye bye.!!
Ya juya ya nemi hanyar shi ta fita ya barta daskare a wajen ta
zubawa kud'in idanu....
π
*HAJEEEYAH KHAREEMERH*
[17/03, 2:54 p.m.] UMAIMA BASHEER: β₯
οΈ
β₯
οΈ
β₯
οΈ
β₯
οΈ
*ZAZZAFAN SO*
(Masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*
ππ
*By*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Khareemerh)*
*Dedic
ated to unique in your love heart*
*IN SHA ALLAH ZAN TAKAITA BOOK D`IN CIKIN 3PAGES. DALILI SHINE MUN KOMA MAKARANTA KUMA KARATU YA KANKAMA..*
_SAI AYI HAKURI DA YADDA LABARIN ZAI ZO ATAKAICE._
ππΌππΌππΌππΌ
π
*59*
Ukhashatu na f
ita motar Abban su Hafsah na sako kai, don haka ya dakata aka bud'e mishi ya shigo, lokacin ita kuma Hafsah lokacin ta gaji da tsaiwar ta wuce ciki cikin sanyin jiki..
Abba yaga ukhashatu kuma ya yayi mamakin ganinshi tunda yasan ba abokin Basheer b
ane.
Sai da yayi parking ya fito, ukhashatu dake rakabe a gefe ya k'arasa wajen shi.
Har k'asa ya tsuguna ya gaida shi, Abba ya amsa cikin sakin fuska yana mishi alamu da hannu 'da ya mik'e.'
Ukhashatu cikin ladabi ya mik'e zai juya. Abba ya buda
baki ya mishi magana cikin sakin fuska. "A to ai a shigo mu k'ara gaisawa koh."?
Ukhashatu cikin ladabi ya dawo yana murmushi, Abba yayi gaba, shi kuma yabi bayan shi.
A sit room suka yada zango, bayan dukkansu sun zauna a gurin da shi abba yaiwa kan
shi mazauni, da kuma gurin da yayi wa ukhashatu nuni daya zauna tun f
Kafin shi Abban ya zauna, amma sai da ukhashatu ya bari Abba ya zauna sannan ya zauna a k'asan kujerar da aka mishi nuni da ita.
Abba yaji dad`in wannan ladabin. Ya fuskace shi kum
a da murmushi a fuskar shi.
"Ya mutanen gidan suna lafiya."
Ukhashatu yayi murmushi, yana dan sunkwi da kai.
Lafiya lau Abba.
Abba ya d'anyi gyaran murya.
"Sai dai ban shaida fuskar ba daga ina ake."
Ukhashatu ya k'ara k'asa da kanshi.
Nassara
wa."
"To Masha Allahu." yana murmushi yace, "Za,a fad'a mana sunan mai Gidan ko nafi ganewa."
Ukhashatu yayi murmushi shima, Eh, "Alhaji Abubakar Khady."
Abba ya fad'ad'a fara,arshi.
To Masha Allah, Khady dai da na sani mai sharia na majestry cour
t"?
Ukhashatu ya jinjina kai cikin ladabi.
Abba cikin fara,a Alhamdulillah. "Ai Khady na mu ne, Allah ya k'ara mishi lafiya."
"Amin Abba."
Cewar ukhasha.
Sannan Abba ya d`an shaki numfashi kafin yace, "To wajen Basheer aka zo ne."?
( _baya son ya
mishi tambayar gurin wa yazo cikin yayanshi mata kai tsaye._)
Ukhashatu ya sosa k'eya yana gyara zama cikin jin nauyin abba yace, "Eh Abba mun gaisa dashi kuma nazo wajen mun gaisa da Hafsah ma."
Abba jira kawai yake yaji alak'ar Basheer da Hafsah.
Cikin son mishi wayo irin nasu na manya yace, "Wajen aikin ku d'aya kenan."?
Ukhashatu ya girgiza kai, fata yake kawai Abba ya fahimta basai ya fito b'aro-b'aro ba.
"Am um dama ina zuwa ne muna gaisawa."
Abba yayi murmushi, cikin matsanancin far
inciki, "Alhamdulillah ya furta a fili."
Yana yiwa Allah godiya, da ya bawa Hafsah miji irin wanda yake mata fata. _(Dan gidan manyan mutane ba girma irin na naira ba, sai dai duka kuma Allah yayi an had'a kudi da sanin yakamata ga kyakykyawan asali)_
Ukhashatu yana iya karantar irin farin cikin daya bayyana kan fuskar Abba.
"Masha Allah, Allah yayi albarka."
Kai tsaye yace, Za,a iya yiwa manyan magana sai a zo agaisa koh."?
ukhashatu ya gane me Abba yake nufi, cikin farin ciki, shima ya ke zub
a godiya.
"Nagode Abba Allah ya saka da alkhairi."
"Amin Amin."
Sai a bani number shi Abban naka koh."?
Abba ya ciro wayar shi ya mik'o.
Ukhashatu ya karb'a da hannu biyu ya rubuta number, sannan ya mik'awa Abba.
Abba yayi saving, sannan zana tashi
number akan wayarshi, ya k'ara mik'awa ukhashatu.
"To gashi, koh sai a d`auki tawa saboda a sanar idan an shirya zuwan."
Ukhashatu ya karba yasaka, a wayarshi.
Sannan ya mik'awa Abba wayar.
Yana fad`in "Angode Abba."
Abba yayi murmushi sannan ya
mik'a mishi hannu sukayi musabiha, yana fad`in agaida mutanen gidan, naga magriba ta k'arato.
Ukhashatu ya mik'a bayan sun saki hannun juna, "Na Barka lafiya Abba."
Ya fita cikin matsanancin farin ciki, ji yake kamar ango ne shi.
Godiya yake ga Al
lah daya sauk'ak'a mishi komai. Ya sani ba dabarar shi bace Allah ne ya saukaka mishi komai yadda zai sanya mahaufanshi cikin farin ciki.
*______________*
A wani masallaci ya tsaya a hanya yayi sallar magriba inda babu wani jira ya, k'ara tarar napep Kai
tsaye ya wuce gidan abokin shi, da k'yar ya lallabashi kan ya taso ya raka shi gadon k'aya gidan Baffa..Babu irin mitar da Mubarak bai mishi ba a mota. _kai ka cika zumudi daga haka sai ayi haka, wa yaga farin shiga."? Banda na matsu kayi aure nima da ba
bu abinda zai hana ni zamana a gada. Kawai ka taso mutane suna hutawarsu._
Shidai ukhashatu kus yayi yana jinshi don yana cikin farin ciki, baya son ya tanka mishi ya ce bazai raka shi ba.
Yanayinsu da Baffa ya gani ya tabbatar mishi da akwai magana,
kuma shima ya sakar musu fuska kamar yadda ya gansu cikin farin ciki.
Bayan gaisuwarsu kamar ko yaushe, _ta musabiha._
Baffa cikin fara,a yake tambaya.
Ya akayi ne, ya Abban naku."?
"Yana lafiya lau Baffa."
"To Masha Allah." Suka k'ara yin shuru.
Baffa ya k'ara tambaya.
Komai kalau dai koh."?
"Lafiya lau Abba suka fad'a cikin ladabi, Mubarak ya gyara zama, ganin dare ya farayi ya fara magana.
"Baffa ayi mana afwa munzo da daddare."
Baffa ya gyada