Showing 45001 words to 48000 words out of 132482 words

Chapter 16 - ZAZZAFAN SO COMPLETE

01 Sep 2026

66

lura da motar Abbansu dake bayansu.'

"Don Allah ki cire damuwa ki mai da komai kamar bai faru ba, please H. HAMID."

cewar Aysha kenan sanda a

kayi parking a k'ofar gidansu Hafsah.'

'Dak'yar Hafsah iya cewa, "Nagode, sosai Aysha ki gaida mamanku."

Tana fitowa daga cikin Napep, d'in motar Abba na sako kai, kuma ta tabbatar ya ganta.'

'Tayi saurin tura gate ta shige ciki tana k'ara goge fuskarta

.'

'Tun daga yanayin data ga mama tasan da akwai matsala, gashi kuma maman ta k'ura mata ido tun amsa sallamar ta.'

'Tasha jinin jikinta sosai, sai lokacin ta tuna cewa 'rufe gidan tayi ta fita.'

'Tayi hanyar d'aki kenan mama tace, "Ke, zonan."

Cikin r

awar jiki ta juyo ahankali take takawa takowa.'

"Daga ina kike"?

'Cikin tsawa maman ta tambayeta.'

'Nan ta hau kame- kame,..

"Um..wai ni..? in.. dama Aysha ce.."

'Mama ta daka mata tsawar data sata razana.'

"Zaki fad'amin min ko sai ranki ya b'aci."?

?

'Dai dai lokacin Abba ya shigo falon, jin mama na yin fad'a yasa yace, "Menene wai yake faruwa, lafiya."?

'Hmm inji mama, tare da yin kwafa 'k'

ta nuna Hafsah, da yatsa, gatanan sai ta fad'a maka tunda kazo kai.'

'Cikin rashin fahimta Abba yace,

"Me

yake faruwa ne ki fad'a min me ta yi kuma."??

'Mama ta nuna ta, ka ganta, wai na fita na bar mata jiran gida, shine ta fice ta kulle gidan ta fice yawonta.."

'Abba yayi dogon numfashi, ya zauna kan kujerar bayanshi, ya kalli, hafsah data durk'usa a k'as

a. cikin kaushin yace Ke, ina kika je. ehe"?

'Cikin rud'ewar murya tace "Abba dama Aysha ce tazo na rakata asibiti.."

"Shine kuma fuskar ki ta kumbura koh"?

'Ya katse hanzarin ta da tambayar.'

'Ta kai hannunta ta shafa fuskar, sai yanzu itama Mama ta l

ura da jan da idon Hafsah yayi.'

'Hafsah tayi kus, ta kasa bud'a baki tayi magana, sai hawaye ma da suka cika idanunta, na k'uncin da zuciyarta ke ciki.'

'Duka, da Abba da Maman ido suka zobo mata ta lura sosai da kallon tuhumar da dukkansu, suke mata.'

'Kwakwalwar ta chakud'e, gefe na k'okarin tariyo mata abinda ya faru da gidan su Yusuf, gefe na karanto mata tsoro da kuma neman abinda zata fad'awa Abba.'

'Ta d'an runtse idonta, kawai sai photon, abinda ta gani ya hasko cikin idonta, bata san lokacin d

a ta fashe da kuka ba, tama manta gabansu abba take.'

'Abba ya fusata, ya kawo mata duka, mama da zuciyarta ta shiga rud'u ta tare shi tana cewa, "Don Allah kada ka daketa ka kyaleta ta yi magana.'

Cikin fad'a Abba ya fara magana

"In kyaleta koh, kina s

angarta ta koh? "Don iskanci daga tambayarta sai ta hau yiwa mutane kuka"?

"Yayi kyau, shikenan ki goyi bayan ta!"

'Ya Mike fuu yayi daki, yabar Hafsa durk'ushe a wajen, har ya dakko abinda ya zo nema ya dawo ya fice cikin sauri.'

'Mama da tun sanda ya

shige tayi shiru ta rasa abin da zata cewa Hafsah ma.'

'Har wajen tsawon minti biyu, sannan maman ta k'irkiro abin cewa, cikin tsawa ta yi mata magana.'

'Zaki fad'i inda kika je ko sai nayi ball da ke anan wajen.'?

Hafsah ta d'ago a razane, har yanzu k'

wallar bata daina d'iga ba.'

"Basma aka kwantar um.. a asibiti shine aysha,mukaje..Asibiti duba ta.."

'Tana dire zancen mama ta d'auka.

"Karya kikeyi"

"Wallahi Hafsah idan baki fad'amin gidan uban da kika je ba sai na k'arya ki anan."

"Wallahi, Mama c

an muka.."

Ta, doka mata tsawa.'

"Dubiya da tsakar ranar nan koh,?.. To uban meye ya kumbura miki ido, fuskarki tayi ja ehe."

"Um, wallahi tun jiya mama nake ciwon ido dama."

'Mama tayi shiru, ba, wai don ta yarda da shiryayyen zancen Hafsah ba, kawai

dai ta shiga rud'ani ne.'

'Kuma akace,' 'Mace' tana da rauni.' To agurin mama, raunin shine yayi tasiri, sai tunanin ta ya chanja gabad'aya zuwa wani layi daban.' Bisa wani karatu da zuciyarta tayi mata.'

'Ta fara tuno abubuwan da suke faruwa tun had'uwa

r Hafsah da Yusuf.'

'Zuwan Hafsah gidan Hajiyah na k'arshe, sai babban tashin hankalinta 'ranar bikin uncle abdallah, fitar da hafsah tayi ita da wani.'.. To yau ma gashi ta fita ba,a sani ba, kuma yadda mama ta kiyasta tafi awa d'aya bata gidan.'

'Don i

ta kanta maman wajen awarta d'aya da dawowa. Mamaki da tsoro suka mamaye ta data ga gidan a k'ulle.'

'Duk da tana da 'Spare' na muk'ulli acikin jakarta, hankalinta bai kwanta ba sai da tayi ta zagayen mak'ota tana cikiyar ko Hafsah ta shigo.'

'A farko tu

naninta ko ta gaji da zaman shiru ta shiga mak'otan, duk da tasan Hafsah bata da tsoron zama ita kad'ai cikin gida sannan kuma bata da shige shigen mak'ota.'.

'Ashe ita Hafsan ta tafi wani wuri can abinta.' To ina taje kenan,? Ita da wa,?

'Allah ya kiyay

e kada dai Hafsah na k'okarin kama wani layi na daban ne.' idan ta duba zata ga gaba-d'aya Hafsah ta canja dabi,u.'

'Zaman shiru

yawan tunani sai kuma b'oye b'oyen da ta tsiri yi mata yanzu, sai fita bada saninta ba.'

'Wanda ada ba haka bane.'

'To Mey

ake faruwa? ka da dai ace ansami wani ya gurb'atawa 'yarta tunani da kuma tarbiyyar da suka dad'e suna tattalinta.'

'Wannan tunanin na Mama, ya jawo abubuwa da dama..'

'Sallamar Hajiya ita ta farko da Mama daga dogon tunanin da ta tafi.'

'Ta amsa cikin

sanyi, ta fara yiwa Hajiya sannu da zuwa.'

'Yawwa inji Hajiya, Hajiya ta zauna, sai lokacin ta lura da Hafsah, zatayi magana Mama ta hau gaisheta.'

"Sai da ta amsa, cikin sakin fuska, sannan ta juyo ga Hafsah,

"Ke kuma fa?

'Kinyi wani jugum dake ba kya

gaida mutane"?

'Hafsah ta d'ago tare da dai dai ta fuskarta.'

'Hajiya sannu da zuwa, ina wuni.'

"Lpia lau"

'Hajiyan ta amsa, sannan ta dire tambayarta,

"Me akayi miki ne.'

'Kunya ta hana Hafsah amsawa, ita da tayi laifi kuma ake tambayarta me akayi

mata'??

'Mama ta cafe zancen'

"Laifi tayi."

'Hmm ko da naji, sai wani wuk'i wuk'i kike da ido kamar mara gaskiya."

"Ashe kuwa baki da gaskiyar."

'Mama taji gabanta ya fad'i rashin gaskiya kuma.'? To me Hajiya take nufi,?

'Kada dai ta gano wani abu,

game da Hafsah, tun da dai ita Babba ce.'

'Nan lissafin Mama ya k'ara jagule wa.'

'Ta mik'e ta nufi kitchen don debowa Hajiyah abinci.'

'Lokacin kuma aka kira sallar la,asar, saboda haka Hajiya ta mik'e don yin alwala, ta kalli Hafsah,

"Ja,ira sai ki

tashi an kira sallah.."

"Naji yace kin k'are boko koh."?

"Ai, ashe bokon naku bana k'arau bane, kin gama secondira"

'Hafsa ta gyad'a kai.

"To Allah yasa albarka."

'Ta mik'e ta nufi d'akinta, tana godewa Allah, da Hajiya tazo da tuni har yanzu Mama na

faman tuhumar ta.'

'Maimakon tayi alwala, sai alhinin abinda ya faru ya danne k'arfinta ta kwanta ta fashe da wani matsanancin kuka, tana jajanta wa kanta, wannan cin amana da aka dad'e anayi mata, da sai yau, Allah ya nufa ta sani.'

'Taci kuka ta goge A

llah har ta tausaya wa kanta, babban abinda yafi tasar mata da hankali shine,

'Yanzu a wanne matsayi take gun Yusuf.'?

'Ashe Yusuf duk soyayyar da yake karanta mata ta k'arya ce.'?

Ita data rik'i Basma aminiya, shine zata ci amanarta.'?

'Ashe da gaske

ne sauyin data dinga gani a wajen Basma.'.. Wayasan lokacin da suka d'auka suna aikata haka,?

'Sun ninke ta abai-bai.. 'Ta k'ara rushewa da kuka, har da dukan 'pillow' saboda alhinin raina mata tunani da akayi.'

'Gaskiya sun raina tunaninta, takaicinta

ajinta da aka zubar mata ranar birthday d'in Basma.'

'Ta tabbatar rabin 'yan class d'insu sun je, kuma an kira Yusuf da saurayinta, amma saboda su tabbatarwa da mutane sun rainata, kuma ita ba komai bace a wajen yusuf.'.

Yasa suka yi hakan.. '

'Tayi kuk

a har kanta ya fara ciwo, idanunta, sukayi jajir kamar an watsa mata barkono.'

'Har kiran sallar magariba bata fito ba, tana ta aikin kuka, amma babu shashsheka sai hawaye dake fitowa daga cikin idanunta, wand'a kana gani kasan tana cikin k'uncin zuciya,

da taikaici.'

'Tana jiyo tafiyar hajiyah, amma ko lek'awa parlour bata yi ba.'

'Ta dai tashi tayi sallah sannan ta koma ta kwanta.'

'Mama kuma fushi take da ita, don haka ko lek'o ta batayi ba.

'Can kuma bangaren, mama tunani tayi kamar bata kyauta ba

data hana abban hafsah dukan Hafsar, bai dace ta dinga katse mishi hanzarin ba, akan dukkan matakin daya ga ya dace ya d'auka akan Hafsar tun da ita ta gaza.'

'Ta saba tun da can bata dukan Hafsah, bare kuma yanzu da ta zama budurwa sosai.'

'Ba kuma, do

n hafsan tafi k'arfinta bane, sai don shi dukan bashi da amfani.'.

'Amma to ya ta iya, wani lokacin dole sai an had'a da dukan, musammaman yanzu da Hafsah ke neman 'bujirewa, ta kama wani layi na daban.' A tunin maman, 'Wanda zancen Abba da mutane yayi ta

siri akanta har ta ke zargin wani mummunan abu ayau ga Hafsan wato fad'ar da ake na,

πŸ‘‰πŸ»

'BA,A SHEDAR YARAN YANZU'..

B'angaren zuciyar mama na wassafo mata wani abu, wani b'angaren na k'okarin korewa.'..

'Haka ta tilasta wa zuciyarta sai ta binciko gaski

yar zarginta. Hafsah ta gudu gidan Hajiyah tayi zance kuma ta tabbatar a d'akin uncle abdallah tayi zancen.' sanan ta fita da saurayi bada sanin kowa ba ranar biki, yau kuma ta fice yawonta (idan ma ita kad'ai d'in ta fita) batare da sanin kowa ba. 'Wanda

dukka wad'annan halayen ba nata bane ada ba zata iya koda kwatanta yinsu ba, to Yanzu to 'Me TAKE SON ZAMA.'?

'Wai don ma mama bata ji halin da uncle abdallah ya gansu ba ranar.'

'Da akwai matsala inji Mama.'

'Iya k'arfin tunanin mama kenan..'

πŸ˜‡πŸ‘πŸΌπŸ‘ŒπŸΌ

#Hajeeyah Kareemerh.'

'Shiko Abba sai bayan anyi sallar magariba, sannan ya shigo gida.'

'D'akin shi ya wuce maman ta kai mishi abinci can, bai nuna mata komai ba ya saki jiki da ita har sukayi hira.'

'Bai sako mata zancen Hafsah ba sam, kuma tasan hali

nshi so yake ya barta tayi nata k'okarin, don haka tayi azamar chanja hirar tasu ta sako ta abinda yafi damunta ayanzu wato 'lamarin Hafsah.'

"Am Abban Hafsah baka tambayeni ya mukayi da Hafsah taka ba."?

'Cikin rashin bawa zancenta muhimmanci yayi d'an

murmushi mai sauti.'

"Hmm to ai wannan ke da ita ne.

"Me yayi wa Abba zafi,? 'Bake tayiwa laifi ba, kin barta jiran gida ta fice nata sabgar,? to ni me ye nawa kuma ciki."??

'Nan da nan fuskar Mama ta sauya taji zafin kalamanshi fiye da tunani. 'Da baza

ta tanka ba sai kuma taga asarar hakan, don haka ta had'iye fushinta, tace,'

"Idan tamin laifi ai kaima ai tayi maka, kuma ko ba haka ba ma ai kafi kowa iko da ita."

"Hmm, ta yaya? Bayan gaki, kefa kika haifeta."

"Haba Abban Hafsah don Allah ka daina fa

d'ar haka."

"Hmm da Hakane Amina, ai da baki nuna min wai kada in tab'a miki 'ya ba koh'?

'Subhaanallah, wallahi ba haka bane, wallahi bada wani manufa bada manufa nayi hakan ba.'

"Hmm to ai shikenan nima bacewa nayi wani abu ba.

'Ki mata abinda ya dac

e kawai."

'Yana fad'a ya mik'e don fita masallaci sallar isha'i.'

'Hankalin mama ya tashi, tayi da na sanin hakan data mishi, data bari ya d'auki mataki akanta, ita gani tayi dukan bai da anfani, kuma ta tsorata da dukan da yayi wa Hafsan kwanaki.'

'Shi

abinda kake tunanin zaiyi fushi akai to, ba,a kanshi yake fushin ba.'

'Yanzu ya zatayi idan ya zare hannun shi daga kan Hafsah'??

😳

πŸ˜€

'Mama kenan'!

πŸ‘πŸ»

'To shima abba, a b'angaren shi, ba wai cire, hannun nashi zai yi ba.'

'To idan yayi haka mekenan

yayi, ai kanshi yayiwa.'

'Dole ne ya sa ido akanta ko dan hak'k'insu akanshi yake, bare kuma yafi sonta akan dukan 'ya'yanshi.'

'Kawai ya kyale mama ne, don kuma da gaske abinda ta mishi ya b'ata ranshi sosai.'

'Amma shima da akwai nashi tunanin akan

matakin daya dace kan Hafsah.'

'Koda aka idar da sallah bai nemi hanyar gida ba, ya jima yana addu,a kan Allah ya taimake shi akan tarbiyyar Hafsah, 'Don yasan addu,ar ita ce komai bawai wani k'okarinshi ko fad'anshi ba..'

'Yasani tarbiyya da akwai wuya

amma, kuma yasan yayi iya kokarinshi, sai kuma yanzu da wani keson wargaza mishi komai.'

'Shi dake tuninshi daban da na mama, yayi amanna tabbas 'Soyyaya' ce ke dawainiya da Hafsah har bata tsoron fushinsu yanzu, ya lura tanayin duk abinda zai zamar mata

maslaha ne ga soyayyar ta ko menene kuwa zai biyo baya.'

'Shi abba ba takaicinsa bane soyayyar data fad'a, a,a abinda yake b'ata mishi rai shine kalar yaron data nacewa.'

'Ya tabbatar ba na nunawa bane in banda haka meyasa ya kirashi, yak'i zuwa.'?

'Amm

a yanzu ya zamar mishi wajibi ya nemi yaron koda a waya ne, don maslahar shi.'

'Saboda haka yasa a ranshi gobe zai kira shi..'

'Da wannan tunanin ya kamo hanyar gida.'

'A gidan kuma, yaran ne suka dami mama bayan ta fito daga d'akin Abba, 'Wai ina yaya.

'?

'Nace muku tana d'aki meye zaku dameni.'?

"Mama bata da lafiya ne..?"

'Inji Mufida.

"Ban sani ba, kije ki duba mana." 'Cewar mama cikin fushi.'

'Mufida ta mik'e ta nufi d'akin Hafsar.'

'Tana kwance sai juyi take.' Bayan ciwon kan daya addabeta yan

xu kuma ciwon mara take fama.'

'Ga kuma uwa uba ciwon da aka haddasa mata cikin zuciyarta.'

"Yaya, Yaya, wai baki da lafiya ne?

'Ta d'ago jajayen idanunta, ahankali ta bud'e baki murya a dashe saboda kuka tace, "Eh Mufida, bani da lafiya."

"Kaii, amma

baki fad'awa mama ba.?

Bari inje to in fad'a mata.

'Tana yunk'urin ce mata a,a, amma ina, ai tuni ta fice.'

'Daidai sanda ta dawo falo lokacin Abba ya shigo yaji tana cewa.'

"Mama Mama yaya bata da lafiya kuka take tayi ma."

'Mama ta d'an rud'e ta ta

bbatar kenan tun la,asar Hafsah keyin kukan nan, idan kuwa haka ne, to da akwai babbar matsala tabbas akwai abin da ya faru da Hafsan ayau d'innan kuma ta tabbatar mummunan abu ne, sai zarginta ya k'ara samun wuri.'

'Bata nuna damuwarta afili ba, ta dai m

ik'e ta nufi d'akin.'

'Abba ya jinjina kai sannan ya bita.'

'A kwance ta sameta sai juyi takeyi.'

'Maman tazauna, a gefen gado, ta tab'a k'afarta, abinda yasa Hafsah ta d'ago da idanunta, ahankali tace bani da lafiya.'

"To meya yake damunki"?

'Sai da

tayi jinkiri, sannan tace, "Ciwon kai, kuma marata ciwo take."

'Mama tayi azamar k'ara yi mata tambaya, kana ji kasan a rud'e take matuk'a, kuma tana cikin tsoron faruwar wani abu.'

"Ke.. ke Haf..sah dazu ina kika je ehe.?

'Wani abu da Mama bata sani, b

a shine da zarar tayi wa Hafsah tambayar 'inda taje, tana k'ara tuno mata da abinda ya faru ne.' sai taji bazata iya fad'a musu ba, kuma bazata iya rik'e kukanka ba.'

'Ta, rantse idonta don wani irin suka da taji zuciyarta nayi.'

'Wai shin Gaske ne yau t

aje gidan tayi Yusuf, har taga wannan mummunan al,amari.'?

'Tsawar mama ta firgitata da tace, bazaki fad'i gidan uban da kika je ba koh, cikin raunin murya tace, mama dubiya muka je.."

"K'arya kike.. Zaki fad'amin gurin wanda kika je idan na tattaka ki a

nan."

'Dam gaban Hafsah ya fad'i, har rawa jikinta ya fara yi, ka da dai mama tasan inda sukaje.'

'Muryar Abba taji da yake tsaye abakin k'ofa, yana cewa "Meye haka Amina, wacce magana kike yi ne ehe"?

"Yarinya bata da lafiya kina wani tuhumar ta da wan

i zancenki."?

'Ya juya kan Hafsah "Ke tashi maza, zaki iya tashi koh"?

"Ta gyad'a kai."

To tashi ki shiga toilet kiyi wanka, kisa ruwan 'Heater' dayawa kinji? Idan kin shirya kizo ki sameni.'

'Ahankali ta d'aga mishi kai.'

Gaskiya taji dad'in abinda A

bba yayi yanzu.'

'Ahankali ta mik'e tana bin bango saboda dad'ewa da tayi a kwance har jiri takeji.'

'Mama ta daka mata tsawa,

"Zakiyi tafiya daidai, ki daina bin bango ko sai na ci ubanki!"?

'Babu shiri ta dawo kan doka da oda, inda ita kuma mama ta

k'ura mata ido.'

πŸ˜…πŸ˜„πŸ˜„

πŸ€”

To wai me Maman ke nufi ne.'???

πŸ˜’

'Ruwa mai zafi ta had'a, tayi wanka dashi, tanayi tana hawaye, wanda sun ma k'afe sai rad'ad'i cikin zuciyarta.'

'Ga takaicin abinda mama take mata, sai taga wannan karon tafi Abba ma d'aukar z

afi.'

'To meye dalili??

'Wata zuciyar tace,

"Hafsah kina jawo mata magana ne da yawa..!

'Da tayi wankan taji dad'in jikinta sosai, kuma taji, zuciyarta ta rage k'una, sai ajiyar zuciya da take ta faman yi.'

'Ta tarar da Abba a falonshi, yana zaune kan

kujera. Zata zauna a k'asa yace ta tashi, ta zauna a kujera itama, sanan tace Abba gani.'

'Memakon ya amsa mata sai yace mata, "Kin ci abinci"?

"Ta girgiza kai."

Ya nuna mata tray da mama ta shiryo mishi abincin daya ci d'azu, gashi nan ki zuba kishi k

inji.'

'Ta, gyad'a kai'

'Madaidaici ta zuba sannan, ta fara ci ahankali, abba na kallon 'television' jefi jefi yana kallonta.

"Kici fa abincin nan sosai."

"To"

'Ta fad'a.'

Taci fiye da rabin abinci ta sha ruwa, sai ya nuna mata apple da aka yanka aka

n wani k'aramin 'plate' ta, d'auki guda d'aya ta fara ci."

'Gaskiya taji dad'in jikinta, cikin abinda suka addabeta har da yunwa.'

"Kin fad'a wa maman naki inda kika je."?

Tambayar da Abba yai mata kenan babu wasa a fuskanshi.'

'Ta d'aga mishi kai, "Eh

"

'To fad'amin'

"Dubiya muka je ni da k'awata"

"Ina kenan."

"A asibiti aka kwantar da ita."

"To ya sunan asibitin a ina yake"?

'Tayi d'if, to fa anzo wajen'

Sai da yace "Uhum"?

'Sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login