Showing 45001 words to 48000 words out of 96447 words

Chapter 16 - Wata Soyayya Complete

03 Sep 2026

34

/>
sai boxer ya d'ora farar jallabiyyah akan gajeren wandon ya d'auki wayarshi ya fita bayan ya kulle part d'in.

Da sallama ya shiga falon Alh Hamisu da Ayyah ne kawai suka amsa masa sallamar da k'arfi Ammi da Abbie kuwa ciki ciki suka amsa suna binshi d

a harara, gefe d'aya yasamu ya zauna k'asan carpet yana k'ara bin Alh Hamisu da kallo ko ba'a fad'a masa ba yasan mahaifin yaron nan ne duk da bawai wani tsayawa yayi ya kalli Anas d'in sosai ba amma yaga kamarsu tattare da mutumin dake zaune.

Rai a ha

d'e Abbie yace

"Modibbo! ga Alh Hamisu nan mahaifin yaron d'azu da rashin hankali yasa ka dakeshi dan haka saika bashi hak'uri kan laifin dakayi musu".

"Hak'uri kuma Abbie?". Abdallah yace yana d'an tura baki.

""Eh, hak'uri idan kuma zaka nuna bamu

isa dakai bane to". Ammi ta fad'a tana hararar shi.

"Zaka bayar ne kokuwa?". Abbie ya fad'a.

"Kayi hak'uri". yace yana juyar dakai gefe.

"Ba komai Abdallah ya wuce sai a kiyaye gaba, bari inkoma Alh Basheer". Alh Hamisu ya fad'a yana mik'ewa tsaye, g

odiya Ammi da Ayyah suka k'ara yimasa sukace kuma zasu shiga su duba Anas d'in daga nan ya fita Abbie yabi bayanshi danyi masa rakiya.

Abbie yana fita yadawo, zama yayi ya shiga yiwa Abdallah fad'a ta inda yake shiga bata nan yake fita ba daga k'arshe

kuma ya koma nasiha da rarrashi dan lamarin na Abdallah saida rarrashin.

Upstairs Abbie ya hau yabar Abdallah dasu Ammi da Ayyah suma suka d'ora da tasu nasihar, a haka dai kamar ya d'auka dan harda yimusu godiya

😅

sannan ya tashi zai fita har yaje ba

kin k'ofar falon ya tsaya tareda waigowa yace

"Ayyah zan samu damar ganin amaryar tawa kuwa?". takaici ya hana Ammi cewa komai Ayyah kam dak'uwa ta jefa masa tana fad'in

"Gidanku, saikace gaske kamar ba d'azun nan kagama bata kashi ba to kasha zaman

ka bata buk'atar ganinka". Baki ya d'an tab'e tareda d'age kafad'a yana murmushi ya ida ficewa daga falon dama neman magana ne kawai irin nashi.

√^^√^^√^^√^^√^^



Kusan kwance Janaan ta yini ranar zazzab'in dai ya sauka sai ciwon kan dake damunta w

anda yak'i sauka ga jikinta da sam batajin k'warinshi, gefe d'aya kuma tararrabin yadda zasu k'ara had'uwa da Yah Abdallah ne cike da zuciyarta.

Ayyah duk bayan y'an mintuna saita lek'ata hakama Ammi tanajin dad'in yadda suke bata kulawa sosai gasu Hass

ana ma dasuke ta nasu k'ok'arin ganin ta manta da damuwarta.

After Asr.

K'arar wayar tace ta tasheta daga barcin daya fara surarta, wayar ta janyo a k'asan pillow ta duba mai kiran sunan My Bloody ya bayyana bisa screen d'in wayar, murmushi ta d

'anyi sannan tayi picking takai kunnenta lokaci d'aya tanayin sallama, amsa sallamar Jauhar tayi tana tambayar Ammi da sauran y'an gidan Janaan ta amsa mata tana k'ara jan blanket d'in data lullub'a saboda zazzab'in dataji yana son dawo mata itama ta shig

a tambayar su Mama da Hajiya.

"Amma dai bakida lafiya My Bloody naji muryar ki haka?".

Murmushin k'arfin hali Janaan tayi kamar tana gabanta tace

"K'alau nakefa kawai dai gajiyar school ne ke aiki dani". bataso ta fad'a mata abinda ya faru d'azu d

an tasan tsaf zata iya kiran Yah Abdallahn suyi ba dad'i.

"Wayyo sannu Bloody haka muketa fama wllhy muma, bari in barki haka to ki gaida su Ammi da twins".

"Zasuji insha ALLAH take care love you".

"Love you too". Jauhar ta fad'a tareda datse kiran,

haka nan jikinta yabata y'ar uwar tata ba gaskiya ta fad'a mata ba kamar yau tafara yin school d'in? itadai bata yardaba dan haka ta kira number Hassana dan jin gaskiyar lamarin.

Lokacin suna kitchen suna shirye shiryen d'ora dinner itada Hussaina da

kuma Atika dasuke yi tare kiran ya shigo wayarta barin yankan salad d'in datake tayi ta d'auki wayar dake saman drawer a kusa da ita ta d'aga, bayan sun gaisa Jauhar take tambayar Hassana ko akwai wani abu dake damun Janaan sunyi waya taji kamar tana ciki

n damuwa kuma ta tambayeta tace ba komai shiyasa ta kirata ta tambayeta.

Lek'e lek'e Hassana ta shigayi tana hango falon ta k'ofar kitchen d'in dan wani lokacin kamar aljani haka yake saidai kawai ka ganshi a gabanka.

"Munafunci ya tashi kenan". Huss

aina ta fad'a cikin dariya tana kallon Hassana, dak'uwa Hassana ta jefa mata tana hararar ta itama Hussaina ta rama dak'uwar ta juya ta cigaba da aikinta.

K'asa Hassana tayi da murya tace

"Bawani gajiyar school datayi Yah Abdallah ne ya daketa".

Ido

Jauhar ta zaro sosai cikeda mamaki tace

"Duka kuma Hassana? me tayi masa to?".

"Hmm bari kawai sister Yah Abdallah saidai addu'a, dayake yau ita kad'ai taje school saboda mu bamuda lectured so da aka tashi bata jira driver ba saita biyo wani Anas d'an

layinmu sukayi dropping d'inta to data fito saita manta handout d'inta a motar shine ya fito ya kawo mata sai suka tsaya suna y'ar hira saiga Yah Abdallah yadawo wllhy ingaya miki haka yakama yaron mutane yayi masa lilis wai wayace ya tsaya masa da iyalin

shi da k'yar maigadin gidanmu da drivern su yaron suka k'waceshi.(Kai Hassana

🤦

kamar a gabanta akayi komai).

Cikin b'acin rai Jauhar tace

"Shine itama ya daketan?".

"Wllhy ingaya miki lafiyayyun maruka yayi mata saida fuskarta ta d'aga ya fasa mata b

aki kuma, gata can kwance yau yini tayi zazzab'i da ciwon kai". Hassana ta bata amsa.

"Shikenan sister sai anjima ki gaida su Ammi da Abbie sai munyi waya". bata jira abinda Hassanar zata fad'a ba ta kashe wayar saboda ranta dayake a b'ace wllhy Yah Abd

allah mugune kawai dan yaga su k'annen shine saiya dinga zalintarsu ai ALLAH yana nan kuma saiya saka musu ita kad'ai ta dinga zazzaga masifa a d'aki daga k'arshe dataga ba amfanin masifar

tunda wanda ake domin shi bai saniba dan haka ta rarumi wayarta dat

a aje bayan gama wayarsu da Hassana ta lalubo number Abdallah ta danna masa kira.

Lokacin yana kwance tsakiyar gadonshi ya tada kanshi da pillow da laptop akan ruwan cikinshi yana duba tsarin wasu new design d'in wasu company's da suka shigo a k'asar A

merica, three quarter ne kawai a jikinshi ko riga babu sai P cap d'inshi ta gado

🤣

dake sanye a kanshi, k'amshin nan dai daya tsumu dashi shike ta faman tashi kowane lungu da sak'o na d'akin, hannu yakai ya d'auko wayar datake ajiye a gefenshi kan gadon y

a duba mai kiran nashi sunan dana ganine yana yawo saman screen d'in yasana zaro ido saboda mamaki har yayi picking yakai kunnenshi ina can ina tunanin ma'anar sunan maganar daya fara ce tasa nadawo hankalina na cigaba da d'auko muku rahoto.

"Malama me

ye na kirana?". yace yana cigaba da duba pictures d'in dayake gani da hannu d'aya.

"Dalilin dayasa ka tab'amin y'ar uwata nakeso inji". tayi maganar cikin tsiwa da rashin kunya.

"Dalili kikeso kiji?". ya tambaya

Kai tsaye tace "Eh" harda murgud'a ba

ki kamar yana wajen ne.

Murmushi yayi yana wani cije lips ya rufe laptop d'in ya ajiyeta gefe tareda kai hannu kanshi ya zame P cap din ya shiga yamutsa lallausar sumar kanshi yace

"Kibari mu had'u Jauhar zan fad'a miki dalilina".

Tsaki tasaki ta

ce

"Mugunta dai batada kyau, kawai dan kaga yarinya tana da hak'uri saika dinga cin zalinta kum....."Koke dabaki da hak'urin bakifi k'arfin insa bulala in miki dukan tsiya ba yarinya". ya katse maganar data fara.

Wata irin dariyar rainin hankali tayi

tace

"Wa? ai wllhy ko a mafarki karkayi tunanin dukana duk ranar dakayi gigin tab'a lafiyar jikina kuwa to kaima bazaka kwana da lafiya ba".

"Haka kikace ko? to muzuba mugani ni da ke har yanzu sunan Abdallah Madugu kikeji bazaki tabbatar da sunan ba

sai ranar dana miki kamun kazar kuku wllhy". yayi maganar yana cije baki tareda gyara kwanciyarshi daga rigingine zuwa rufda ciki.

Cikin tab'e baki tace

"Kai kasan duk wannan kuma damuwarka ce batawa ba nidai abinda nasani karka k'ara gangancin tab'am

in y'ar uwata wllhy".

"Idan ba'ayi hakan ba kuma fa? me zakiyi? zaki d'auki mataki ne?".

"Matakai ma ba mataki ba wllhy". tace kanta tsaye.

"Zaki cimin uwa Jauhar, koni zakici mu had'u a......."Tirrr ALLAH wadaran naka ya lalace". ta fad'a da saur

i tareda jan tsaki ta kashe wayar batare data bari ya k'arasa abinda yayi niyyar fad'a ba.

Mrs Salees Mu'az

💝

3/2/22, 08:20 - Ummi Tandama

😇

: WATA SOYAYYA

💝

Oum Hanan

Page 26

*TOP TEN TAKUN HASKE BATCH A*

Tasan shi sarai yanzu saiya

fad'i maganar dazata dad'e tanajin kunya tunda shi ba kunyar ce ta isheshi ba.

Dariya kawai yayi lokacin dayaga tayi hanging call d'in wani irin nishad'i da farin cikine masu tarin yawa yaji suna ratsashi cikin b'argo da zuciyarshi harma da ilahirin j

ikinshi baki d'aya ya lumshe ido yana jin yadda zuciyarshi ke harbawa da sauri sauri, laptop d'in dabai k'ara dubawa ba kenan ya cigaba da kwanciya a haka idanunshi a rufe yana sauke numfashi a hankali a hankali muryar ta kad'ai dayaji ta haddasa masa shig

a wani hali mai wuyar fassara.

√^^√√^√^^√√^



A ranar da daddare Ammi da Ayyah da Hassana datayi musu rakiya sukaje suka duba Anas wanda ke kwance ciwon k'irji ya sakoshi gaba saboda dukan da Abdallah yayiwa k'irjin nashi, sun dubashi tar

eda k'ara bada hak'uri sannan suka dawo gida.

Abbie ma saidaya tasa k'eyar Abdallah a gaba suma sukaje suka duboshi, farko ma togewa yayi bazashi ba saida Abbie yayi masa tsiya tsiya sannan ya bishi sukaje tare.

A cikin halin zazzab'in da Janaan ta

ke ko sannu bai mataba lokacin ita kad'ai ce a d'akin yazo ya titsiyeta lallai saita fad'a masa dalilin dayasa ta fad'awa Jauhar abinda ya faru, cikin rawar jiki data murya wanda zazzab'i da kuma tsoron Abdallah ya haifar mata ta shiga yimasa rantsuwa ita

sam basuyi maganar da Jauhar ba batasan kuma wanda ya fad'a mata ba yak'i yarda wai k'arya take, ana haka Ammi ta shigo duba jikinta ta ganshi yana tuhumarta yayi mata tsaye akai aikuwa Ammi ta hau kanshi da fad'a ta korashi daga bedroom d'in.

√^√^√^√

^√^√^√^√√^√^√^√^√^√^√^√^√^√^√^



Tun daga wannan lokacin Janaan ta daina kula kowa a makarantar tasu dama kuma bata shiga harkar kowa inba karatu dake had'asu da wasu mazan ba shima saita daina ta shafawa kanta lafiya dan gani take tamkar Yah Abdallahn zai

zo har school d'in ya ganta, harkar lafiya a bita da shekara tunda shi bayayin uzuri a rayuwa.

A gurguje please

🙇

Kwanaki sunata k'ara tafiya yayin da bikin Abdallah da Janaan keta k'ara matsowa, kuma har a yanzun koda sau d'aya bai tab'a gwada

kiran Janaan sun keb'e sunyi magana ba a matsayinta na wadda zai aura, ita kanta Janaan d'in bawai son had'uwarsu take dashi ba harga ALLAH ma batason ya nemeta d'in. Ammi ma bata matsa masa lallai saiya dinga kiranta suna zance ba saboda wasu dalilanta da

ita kad'ai ta barwa kanta sani.



A yanzu baifi saura 3wks da y'an kwanaki ya rage biki ba, Abdallah ya gama gininshi tsaf wanda dama ya dad'e yanayi a unguwar zoo road ginine na musamman daya zana abinshi da kanshi inda ya d'auko tsarin gidan a

k'asar Cyprus dayaje gano wani ginin company wanda mai kamfanin ya d'auke shi, anan yaga gidan kuma yayi masa kyau matuk'a dan haka ya d'auko hotonshi plat house ne gidan bashida irin girman nan sosai amma dole

tsarin gidan ya burge mutum ya narka dukiya d

ashi kanshi baisan adadinta ba kuma alhmdulillah kwalliya ta biya kud'in sabulu dan duk wanda ya shiga gidan kokuma yaga hotonshi saiya burgeshi yayi santin shi Habeeb Marafa ma da Abdallahn Momy Maryam sunce irinshi zasuyi Abdallah yace ba d'an iskan daya

isa yayi irinshi suma suje sugano kalar n

asu suyi amma dai ba irin wannan ba sukace tunda ubanshi ya basu kud'in yin ginin ai saiya hanasu, kai wad'annan yara ALLAH shirya

🤦

.

Ko lefe baiyi tunanin had'awa ba kawai harkokin gabanshi yake saida Ammi

tayi masa maganar tace ya tura mata kud'i za'a had'o kayan lefen, mak'udan kud'ad'e ya turawa Ammin dan bashida matsalarsu ubangiji ya hore kuma ya sawa sana'ar tashi albarka, yana tura mata kud'in ta turawa Hauwa'u k'anwar Abdallahn mai binshi a haihuwa

wadda su Hassana ke kiranta da Aunt Jeeddah ita zata had'o lefen komai da komai dayake tana yin order na kayayyakin na mata kasuwancin datake kenan hakan yasa Ammi ta wakiltata kan had'a lefen. Wannan karon da kanta ta shirya tafiya had'o kayan bayan ta ne

mi yarjewar mijinta ya amince.

Cikin y'an kwanaki kad'an kuwa Aunt Jeeddah ta had'o komai harda k'arin tata gudunmawar data saka a ciki set biyune na akwatinan masu shida shida set d'aya peach color d'aya set d'in kuma ash color mai haske su kansu jaku

nkunan abin tsayawa a kalla ne bare kuma kayan dake dank'are a ciki kowacce saida aka shak'eta da kaya na alfarma masu matuk'ar tsada da asalin kyau, kai tsaye gidan Ammi aka wuto da kayan tunda itace uwar y'a nan fa aka baje kaya ana kallo dama su Aunt De

ejah da Aunt Jeeddahn da Mabrookah wadda su Hassana sukebi duk suna gidan da sauran y'an uwa da abokan arzik'i da suka zazzo.

"Masha ALLAH" kalmar da kowa ke fad'a kenan lokacin da ake ganin kayan kowa santi yake tareda yabawa Aunt Jeeddah data zab'o ka

yan, ba abin kushewa sai san barka tareda zaman lafiya mai d'orewa ga ma'auratan.

Janaan dai tana mak'ure a gado tanajin hayaniyar mutane tareda sa albarka ganin abin take tamkar a mafarki wai itada Yah Abdallah ne zasu zama k'ark'ashin inuwar aure ta

na rok'on ALLAH ya bata hak'uri da juriyar zama da Abdallah, Hassana ce taje ta tsegunta mata yadda lefen yake tanata faman santi itadai murmushi kawai tayi tana sauraron Hassana.

Haka Abdallah da suka shigo gidan da Habeeb bayan tafiyar bak'in ya rag

e sai y'an gida kawai ba kunya ya zauna ya baje kayan ya musu filla filla yana gani harda cewa Aunt Jeeddah idan baiga abinda yayi masa ba saiyaci ubanta kuma saita biyashi kud'inshi ko mijinta ya biya a hakanma wai tasu tazo d'aya dashi yana d'an mata mut

unci, duk dariya akayi a falon Aunt Jeeddah tace

"To gasu nan dai ko kai iya zab'en dazakayi kenan Yah Modibbo".

Baki ya tab'e yana cigaba da d'add'aga kayan Habeeb na tayashi gani.

"Very good thank you so much, kinyi k'ok'ari sosai". yayi magana

r yana cigaba da dubawa, mamaki ne ya kama kowa a wajen dan sunsan halinshi sarai ko godiya bai cika yiwa mutane ba.

"Nagode Yah Modibbo". Aunt Jeeddah ta fad'a tana murmushi, d'agowa yayi ya kalli Hussaina yace

"Ina Janaan? kirawota taga kayan, idan

akwai abinda baiyiba a canza".

"Haba Yah Abdallah ina kaga an tab'a yin haka? cikin mutane amarya tazo tana ganin kayan lefenta". Aunt Mabrookah ce tayi maganar tana kallon Abdallah.

"Ina ruwanki? banason shisshigi malama". ya fad'a yana hararar ta, ba

ki ta d'an tab'e tana juyar da kai gefe.

""Wai dan ubanki ba magana nayi miki ba". yace a fusace yana kallon Hussaina, da sauri ta zabura ta nufi bedroom d'insu inda Janaan take.

Kallonshi Aunt Jeeddah tayi tace

"Haba Yah Modibbo dan ALLAH ka k'yaleta

kunya kawai zaka bata wllhy kasanta akwai kunya". Harara ya zabga mata yace

"Wato nine sarkin marasa kunya kenan ko, to ko itace sarkin kunya na duniya saitazo ta gani dan ubanta salon nan gaba tace wasu abubuwan basuyi mataba".

"Dama ina kaga kunyar?

". Aunt Deejah tace tana hararar shi, baice uffan ba ya cigaba da dubawa.

Har lokacin Janaan tana kwance kan bed da waya a hannunta kamar ma wani assignment take dubawa a ciki Hussaina ta shiga ta zauna bakin gadon tana kallon Janaan tace

"Aike

daga angonki sister yace wai kizo kiga kayan lefen yanzu".

"Inzo inga lefe kuma?". Janaan ta tambaya cikin mamaki tana kallon Hussaina tareda ajiye wayar hannunta.

"Eh wllhy, haka yace". Hussaina ta bata amsa.

"Amma dai da wasa yake ko?". Janaan t

a k'ara tambaya gabanta yana fad'uwa, dariya Hussaina tayi tace

"Wllhy bawani wasa kinsan dai ba wasa yake damuba bare kice kitaho kawai muje a wuce wajen".

"Amma saboda ALLAH Hussaina cikin mutane sai inje in fara kallon kayana saboda nice k'arshen

mara kunya duk gasu Ammi da Ayyah a falon". A marairaice tayi maganar kamar zatayi kuka.

"Ammi da Ayyah fa basu falon Aunt Deejah ce kawai saisu Aunt Jeeddah saikuma Aunt Fareedah su kad'ai ne".

"Duk da haka dai Hussaina nidai dan ALLAH kibashi hak'

uri dan ALLAH kice masa kunya nakeji".

Tashi Hussaina tayi tana fad'in

"Bari inje to zagi ne dai zamusha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login