Showing 60001 words to 63000 words out of 96447 words

Chapter 21 - Wata Soyayya Complete

03 Sep 2026

35

ya rud'e ya dinga tambayarta ko tanajin wani ciwo ne cikin dauriya ta nuna masa ba komai batason tun yanzu ta nuna gazawarta ta tayarwa da mutane hankali, tsugunawa yayi yayi kissing d'in cikin ya tashi yayi kissing d'in goshinta ya gangar

o kan dogon hancinta sannan ya dire kan bakinta doguwar sumba ya bata sannan ya saketa saidaya k'ara yin hugging d'inta sannan yayi mata sallama yana fad'in ta kular masa da kanta.

K'ofar daya fita tabi da kallo fuskarta d'auke da mad'aukakin murmushi

tana matuk'ar son Yah Abdallah yazama wani b'angare na rayuwarta a yanzun ALLAH ya bata ikon cigaba dayi masa biyayyar aure ninkin ba ninkin akan wadda take masa a da, siririyar k'ara ta saki tareda dafe k'asan mararta wadda ta tsinka mata idanunta ta rufe

gam tana ambatar sunan ubangiji so take ta d'aga k'afar taje ta zauna amma ta rik'e da k'yar taja k'afafun nata da sukayi mata matuk'ar nauyi ta nufi bakin gado ta zauna tana cije baki.

Ajiyar zuciya ta saki lokacin da ciwon marar ya saketa, nan ta ci

gaba da zama sai yayi kamar ya saketa saiya k'ara dawowa k'arshe dai k'asan tiles ta sauko ta durk'ushe nan k'asa tana salati idanunta a runtse, cikin haka ALLAH ya shigo da Ammi dan ta dubata taga halin datake ciki

nan taga yadda Janaan take da sauri ta

k'arasa inda take hankalinta a tashe ta dafa kafad'arta tana tambayar ta abinda ya sameta sam Janaan batayi magana ba sai cije baki datake ta faman yi na azaba hakan ya tabbatarwa da Ammi lallai nak'uda ce, da sauri taje ta sanar da Ayyah suka taho tare Ay

yah tace kamata yayi a tafi asibiti dan haka zataje ta sanarwa driver ya fito da mota itakuma Ammi ta shirya kayan da za'a tafi dasu.

Hakan kuwa akayi Ayyah ta fita Ammi kuma ta fara shirya kayan baby's dana Janaan d'in da duk wasu abubuwa datasan za'a

buk'ata acan a rud'e take yin komai cikin hanzari tana faman jerawa Janaan sannu wadda har lokacin take durk'ushe a k'asa idanunta a rufe tana ambaton ALLAH batayi zaton abun zaiyi worsting haka tun yanzu ba, sam Jauhar batasan bikin da akeba sai lokacin d

a Ammi ta kamo Janaan zasu fita itama ta fito falon suka had'u sosai hankalinta ya tashi ta shiga tambayar Ammi meya samu Janaan d'in Ammi tace mata haihuwa ce zasu tafi asibiti ne zasuje itada Ayyah itakuma ta zauna a gidan, Jauhar taso binsu Ammi ta hana

ta tace suma ba dad'ewa zasuyi ba insha ALLAH suna fatan ace da sunje ta haihu haka suka tafi suka bar Jauhar cikin jimami na ganin halin da y'ar uwarta ke ciki.

Suna zuwa aka karb'i file d'inta dama inda take zuwa ante natal ne aka shiga da ita labo

ur su Ammi na zaune gaba d'aya hankalinsu a tashe yake indai kanada mai nak'uda dama hakane hankali bazai tab'a kwanciya ba har sai kaga ALLAH ya bud'i ido lafiya fatansu ALLAH ya sauketa lafiya ya kawota mai sauk'i kuma.

Tunda aka shiga da Janaan take

faman abu d'aya haihuwa shiru ba ita ba alamunta sai tsabar wuya datake sha, a hakan kuma tayi matuk'ar dauriya duk da haihuwar fari ce sam bata irin ihuce ihuce nan sai salati da ambaton ALLAH kawai take amma fa tana shan azaba wadda tunda uwarta takawo

ta duniya bata tab'a jin irin misalinta ba.

Ammi batayi niyyar kiran Abdallah ba karta tayar masa da hankali so tayi sai an haihu sannan ta kirashi tayi masa albishir amma ganin lokaci yanata k'ara shud'ewa abu yak'i ci yak'i cinyewa har lokacin bata ha

ihu ba yasa Ammi tace ta kirashi ta fad'a masa nan kuma ta dinga neman number tashi switch off sai Abbie ta kira ta fad'a masa.

Meeting d'in daya shiga yasa ya kashe wayoyin nashi bayan fitowar tashi kuma bai kunna wayar da wuri ba sai bayan wani lokac

i daya kunna yaga kiran Ammi rututu har dana Abbie 2miscal, Ammi yafara kira ta sanar dashi suna hospital Janaan zata haihu sosai hankalinshi ya tashi nan da nan ya tattara duk abinda yake ya ajiye a gefe kasancewar dama yasan asibitin dama nan yake kaita

ake duba lafiyar ta.

Da gudu ya figi motar shi ya nufi asibitin, a reception yasamu su Ammi da Abbie harma da Yah Ameen dan lokacin da Ammi ta kira Abbie ta fad'a masa suna tare dashi sai suka taho tare. D'akin da Janaan take yaso shiga su Ammi suka han

ashi nan suka cigaba da jira amma shiru sai shige da fice likitocin keyi a d'akin hakan ya k'ara d'aga hankalin su Ayyah.

Jauhar kasa hak'ura tayi gaba d'aya hankalinta yak'i kwanciya dan haka su Hassana na dawowa daga school data fad'a musu suka shirya

driver ya kaisu.

Kowa kagani a gurin yayi jigum al'amarin yafara basu tsoro, Jauhar kam tuni ta fara kuka gani take tamkar zata rasa y'ar uwar tata, bayan wasu awanni da suka shud'e babban likitan dayake tsaye a kanta ya fito ya nufo inda suke tun kafi

n ya k'araso wajensu su suka tareshi kowa da tambayar dayake jefa masa game da Janaan anan yake sanar musu da cewa dole saidai

ayi mata C.S haihuwar tazo mata da gardama bazata iya haihuwa da kanta ba, dan haka mijinta zaisa hannu ko iyayenta ayi mata abi

nda ya dace gaba d'aya sai jikinsu ya k'ara yin sanyi Abdallah kam tubure musu yayi harda cewa ba d'an iskan daya isa ya farka masa cikin mata zata haihu da kanta insha ALLAH sune dai basuyi abinda ya dace ba ya shiga masifa da bala'i ido kawai Dr Jabeer y

a k'ura masa yana kallon ikon ALLAH lallai wannan gayen d'an tujara ne duk da alamu sun nuna shine mijin nata yasan tsayin lokacin da suke kanta kuwa? yasan irin k'ok'arin da sukayi na ganin ta haihu da kanta kuwa amma abin yaci tura? kokuwa zai koya musu

aikinsu ne?.

A fusace Abbie yace

"Kai Modibbo banson shashanci da hauka mana kai wane irin yarone kasan tsahon lokacin da yarinyar nan ta d'auka cikin azaba kuwa tun safe ake abu d'aya ba irin k'ok'arin da basuyi ba ganin ta haihu amma shiru zakazo ka

yi mana buyagin naka daka saba anan karb'a kayi signing ko in b'ata maka rai yanzun nan". Abbie ya k'arasa maganar cikin tsawa, haka nan yana huci da kumbura baki ya karb'i takardar yayi signs ya koma gefe ya cigaba da kai kawo ranshi fal tausayin matarshi

.

Sunaji suna gani aka gangaro Janaan kan gadon da ake d'ora patient zuwa d'akin da za'ayi mata theater suka bita da addu'ar ALLAH ya raba lafiya Abdallah kamar zai bita d'akin haka yayi tsaye ya goya hannayenshi a bayanshi ya rasa abinda yake masa dad

'i, Jauhar kam wani kukan ta k'ara saki lokacin dataga an fito da Janaan su kansu su Hassana hawaye suke.

Abdallah tsaye yayi a k'ofar jiyake tamkar ya afka d'akin yaga halin da matarshi take ciki da k'yar Yah Ameen yaje ya dafo kafad'arshi ya dawo dash

i inda suke, nan ma zaune yayi kan kujera ya dafe kanshi da hannu bibbiyu wanda yake mugun sara masa.

Alhmdulillah cikin ikon ALLAH ubangiji ya basu nasarar ciro baby's d'in baby boy da baby girl, kyawawan yara manya manya farare tas masu kama da ub

ansu sak tamkar Abdallah yayi kaki ya tofar tamkar yaran larabawa masha ALLAH duk nurse's d'in sun rikice sai santin yaran suke.

Nan da nan aka shiryasu cikin fararen kayan sanyi aka fito aka sanar dasu Ammi fad'ar irin farin cikin da wannan ahali suka

shiga a wannan lokacin b'ata bakine gaba d'aya wajen ya rikice sai tashin hamdala kakeji musamman da sukaga yaran, suna fitowa suka shiga tambayar nurse's d'in lafiyar maijego suka shaida musu tana nan lafiya ba wata matsala bata farka bane dai har yanzun

an kaita d'akin hutu. Ba kunya Abdallah ya had'a yaranshi ya rungume kyawawan yaranshi yanajin wani irin farin ciki mara misaltuwa yana ratsa k'wak'walwar shi zuwa gangar jikinshi wai yau shine da yara har biyu lallai wannan kyauta ce wadda ba wanda ya isa

yayiwa wani mutum ita sai jallah wa azzah wanda kud'i ko mulki na mutum basu isa su siyeta ba alhmdulillah kawai yake jerawa cikin ranshi yayin da idanunshi suka ciko da k'wallar farin ciki, Ayyah ce ta karb'i baby girl d'in tana fad'in

"Bani ita nan f

itsararre".

"Barni inji d'uminsu please Ayyah". yace yana kallon Ayyah.

"Shima kawoshi zakayi mara kunya". Ammi tace tana kawo hannu ta karb'i baby boy d'in ba yadda ya iya amma yanajin tamkar a bar masa su cikin jikinshi su dawwama a haka, bisa kujera

ya zame yana sakin wani murmushi lokaci d'aya yana shafa sumar kanshi yanzu kuma burinshi yasa Janaan a cikin idanunshi yaga halin datake ciki.

Bayan wani lokaci Janaan ta farka, saidai farkawar tata tazo da matsala.

M&S

💝

.

3/9/22, 20:15 - Um

mi Tandama

😇

: *WATA SOYAYYA*

💝

Page 34.

Paid book

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*.

©Oum Hanan.

_I'm sorry reader's yanayin labarin ne yazo da haka dazan iya dana canzashi tun farko so sorry mutuwa rigace da kowa saiya sakata a jikinshi, ni k

aina page din nan ya tab'a min rai sosai ina ganin abin tamkar gaske

😭

ubangiji ALLAH yasa mu cika da Imani yabamu sa'ar tafiya alfarmar annabi rahma (S.A.W.)

🙏

._

Wani azababben ciwon ciki ta farka dashi wanda irin zaburar data dinga yi sai dayasa gado

n datake kai ya dinga jijjiga kamar zata fad'o k'asa, ba k'aramin tashi hankalin likitocin yayiba abin ya matuk'ar tsorata su. Su Ammi ma basu san abinda yake faruwa ba dan basu fad'awa kowa ba burinsu kawai Janaan d'in ta tashi suga lafiyar jikinta, da k'

yar da taimakon ALLAH suka samu suka shawo kan al'amarin ta d'an samu nutsuwa kad'an amma jikinta wani irin rawa yake kamar mazari ga wani irin numfarfashi datakeyi sun rasa daga ina matsalar take sister d'inta kawai take ambata da Yah Abdallah dan haka d'

aya daga cikin likitocin yazo ya tambaya waye Abdallah dakuma sister d'inta a rud'e suka shiga tambayarshi lafiya kuwa ake nemansu? Anan ya sanar dasu maijegon ce take ta ambatarsu cikin sauri Abdallah da Jauhar sukabi bayan likitan zuwa d'akin da Janaan t

ake ciki lokaci d'aya suka isa inda take da mugun sauri suka tsuguna gabanta a tare zuciyarsu tayi mugun rauni ganin yanayin halin datake ciki kuka Jauhar ta fashe dashi ta kama hannunta ta damk'e cikin nata hannun tace

"Meya sameki haka Bloody?".

Batay

i magana ba sai kallonta data maida kan Abdallah wanda ya k'ura mata ido cikin rarraba maganar saboda hakin datake tace

"Yayanah! ina yaranmu da muka haifa inaso in gansu please". juyawa Abdallah yayi ya kalli Dr'n dake tsaye shikuma ya kalli wasu nurse

's biyu dake tsaye a gefenshi sun san ma'anar kallon dan haka suka nufi inda yaran suke a wani gadon daban suka daukosu suka kawosu aka sa mata su gefe da gefenta, duk da irin rawar da jikinta yake da numfashin ta daketa faman kaida kawo bai hanata rungume

yaran sosai a jikinta ba wata irin k'aunar su da soyayyar su na ratsata saidai a yadda take jin jikinta tamkar bazata rayu dasuba, kuka kawai Jauhar take mai shiga rai Abdallah kam bakinshi ya mutu uffan ya kasa cewa sai idanunshi da suka kad'a sukayi jaw

ur jijiyoyin kanshi sun tashi rad'a rad'a wani dunk'ulallen abu mai tauri ya tokare masa mak'oshinsa yak'i gaba yak'i baya.

"Suna kama da Yah Abdallah nah ko?". Janaan ta fad'a da k'yar tana kallon Jauhar fuskarta d'auke da kuka mai had'e da murmushi it

a kad'ai tasan azabar datake ji cikin jikinta, Kai kawai Jauhar ta jinjina mata yayin da wasu sabbin hawayen suka shiga rige rigen zubowa kan kumatunta cigaba Janaan tayi da fad'in

"Bloody ga amanar yarana a hannunki duk da nasan zaki basu gata fiye da

wanda zan basu inajin alamun rayuwata tazo k'arshe dan ALLAH ki kulamin da Yah Abdallah nah ki.......Da sauri Abdallah yasa hannu ya rufe mata baki yana girgiza mata yayin da idanunshi suka cika taf da k'walla.

"I'm sorry N00R kiyi shiru dan ALLAH insh

a ALLAHU zaki tashi kar zafin ciwo yasaki sambatu mana zaki tashi mu cigaba da rayuwar mu cikin farin ciki da yaranmu zaki k'ara haifa min wasu twins d'in please *JANAAAN* kiyi shiru da bakinki kinga numfashin ki ba daidai yake ba stop crying please inane

yake miki ciwo yanzu?". ya k'arasa maganar yana share mata hawayen da suka fara zubowa a idanunta yana share mata shikuma nashi hawayen na d'iga a fuskarta batare daya saniba saboda yadda idanunshi suka rufe fuskar tata ma dishi dishi yake ganinta.

"Ba

zafin ciwo bane Yah Abdallah bakusan ya nakeji bane inajin kamar ana huramin wuta a cikina Yah Abdallah ko ina na jikina ciwo yakemin". da k'yar ta k'arasa maganar tana fashewa dawani irin kuka tareda kamo hannun Abdallah ta kifashi akan fuskarta tana ciga

ba da kukan wanda sanadin hakan yasa numfashin ta sark'ewa tuni likitocin sukayo kanta dama tuni an kwashe yaran an maidasu gadon da suke da, da k'yar suka samu Abdallah da Jauhar suka matsa gefe farko ma cewa sukayi su fita tamkar kurame ba wanda ya kulas

u dole suka k'yalesu wani irin kuka Jauhar take tamkar zata shid'e, basu san ya akayi ba waye ya fad'awa su Ammi sai ganinsu kawai sukayi sun shigo d'akin kowa hankali a tashe lokacin ansa mata oxygen dan taimakawa numfashin nata amma ina duk da hak

a fama

take Abdallah kasa hak'uri yayi ya ratsa ta tsakiyar likitocin da suke kanta ya isa inda take ya durk'ushe a gabanta hannunta ya kama ya damk'e gam yana kuka sosai basuyi aune ba sukaga tasa d'aya hannun ta fincike oxygen d'in ta cillata k'asa a hankali b

akinta yafara fad'ar kalimatush shahadah wanda k'arasowar Abbie wajen ya cigaba da d'ora mata tana fad'a har takai ga fad'in sallallahu alaihi wa sallam daga nan kuma komi nata ya tsaya cak (Ubangiji kabamu ikon cikawa da mafificiyar kalmar nan

😭🙏🙏

).



Gaba d'aya d'akin rud'ewa yayi Abbie ne kawai da Yah Ameen masu dauriya duk da suma d'in k'arfin haline kawai amma can k'asan ransu wani irin d'aci sukeji mara misali ganin abin suke kamar a mafarki wai Janaan ce ta rasu? ALLAH Al HAKEEM shi kad'ai yasan

hikmarshi tayin hakan duk abinda ubangiji yayi to lallai akwai hikmah a cikinshi. Saida sukayi aune aunensu dan tabbatar da gasken ta rasu kuwa? abu d'ayane dai binciken nasu yake nuna musu Janaan lokaci yayi ubangiji yayi ikonshi akanta.

Mayafin dake j

ikinta babban likitan yaja ya rufe mata gaba d'aya jikinta sannan sukabar d'akin kowanne da y'ar guntuwar k'wallarshi hak'ik'a sun tausayawa ahalin mai haihuwar nan suna tayasu jimamin rashinta tareda fatan ALLAH yabasu hak'urin rashi.

Duka gaban gadon

suka k'arasa gaba d'ayansu kuka suke mai cin rai musamman Jauhar wadda muryarta tafi ta kowa d'agawa tana rungume jikin Ammi da itama take kukan bata tab'a tsintar kanta a cikin makamancin halin nan ba jitake dama itama ALLAH ya d'auki rayuwarta a yanzun t

abi y'ar uwarta ta huta, tamkar k'aramin yaro haka Abdallah ya dinga kuka yayi zaman dirshan a gabanta kanshi akan cikinta yana fad'in shi matarshi bata mutu ba likitocin ne munafukai kuma duk saiya d'auresu sai sunyi shari'a dasu kai daga jin irin maganga

nun dayake na rashin kan gado kasan bawai a cikin hankalinshi yake yinsu ba kamar wani zautacce, ganin hakan yasa Abbie ya d'agoshi ya rungumoshi jikinshi

"Abbie Janaan ta mutu da gaske? Kai kawai Abbie ya gyad'a masa zuciyarshi tafara rauni da ganin ha

lin da yaronshi yake ciki shima kamar yayi kukan yakeji saidai kuma shi namiji ne sunada dakakkiyar zuciya fiye data mata kuma bai kamata ace shida zai rarrashesu ba shima yanayi amma hak'ik'a rasuwar yarinyar nan ta tab'ashi fiye da tunanin mai tunani.



"No Abbie nooo matata bata mutuba dan ALLAH kuce ta tashi please". yayi maganar da k'arfi yana kallon gadon Janaan bai jira abinda Abbie zaice ba ya zame daga jikinshi ya nufi inda Yah Ameen yake tsaye yana fad'in

"Please Brother kayi wani abu mana ka f

ad'amin da gaske Janaan ta rasu?". k'wallar data taho masa yayi saurin maidawa ya kamo hannayen Abdallah yace

"Janaan ta amsa kiran ubangiji Abdallah ka nutsu ka fahimta Janaan bata raye kayi mata addu'a ALLAH yaji kanta ya raya abinda tabari". Kai Abda

llah ya shiga kad'awa kamar irin ya fahimta d'in nan ya bud'e baki zaiyi magana kenan sai gani sukayi yayi luuuu jikin Yah Ameen idanunshi a k'akk'afe cikin hanzari Abbie ya k'araso suka tareshi daidai lokacin da itama Ammi taji Jauhar dake jikinta ta lang

ab'e mata duk jikinta ya saki hakan ya tabbatar mata da itama ta suma kamar Abdallah salati gurin ya d'auka yayin da tashin hankalinsu ya k'ara nunkuwa fiye da da, da k'arfi Yah Ameen yacewa Hussaina wadda keta gurshek'en kuka kamar ranta zai fita taje ta

kira musu Dr, da gudu tayi hanyar fita daga d'akin sukaci karo da Dr'n zai shigo suka dawo ciki tare.

•√•√•√•√•√•√•√•√•√



Gado biyune kawai a d'akin na marasa lafiya suna facing d'in juna Abdallah da Jauhar ne kwance akan gadon kowanne hannunsh

i mak'ale da drip, tashin hankali ba dad'i jama'a iya yanzu kawai dana kalli fuskar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login