Showing 72001 words to 75000 words out of 96447 words
Abdallah adole kawai ta amsawa Daddyn danta faranta masa amma bawai dason ranta ba.
Bayan dawowar Abbie Jauhar taje ta gaishes
hi sannan ta bashi hak'uri tareda fad'a masa ta amince da zab'in da sukayi mata cikin hikmah Abbie ya bugi cikinta yana son yaji ko Daddy ne ya tilasta mata amincewar Jauhar ta nuna ba ruwanshi kawai dai tanaso ta kyautata musu ne hakan yayiwa Abbie dad'i
sosai ya shiga yimata addu'a tareda sanyawar albarka a rayuwar aurensu da Modibbo. Tana komawa bedroom ta fad'a kan gado ta shiga raira kuka wanda ita kanta batasan na meye ba na farin cikine ko akasin hakan ta rasa wanne take yi daga ciki farin cikinta b
ai wuce auren mutumin daya dad'e cikin rayuwar ta wanda tun tana k'wailarta take jinshi cikin ranta fiye da kowa tun bata gane meye ma'anar hakan ba harta fahimta shiyasa duk wani d'a namiji dazata gani indai zataga Abdallah kota tuna dashi saitaga wancan
d'in baikai ba Abdallah ya kereshi tako wane b'angare, bak'in cikinta kuma bai wuce aurenshi dazatayi a matsayinshi na mijin y'ar uwarta ba saidai kuma bazata ja da ikon ALLAH ba yafisu sanin hikmar yin hakan dama can ubangiji yayi sai Janaan ta fara zaman
aure dashi kafin ita koma dai meye ita zab'in ubangiji take nema.
An tsaida sa ranar Abdallah da Jauhar daidai lokacin bikin su Hassana suma za'a had'a ayi tare, Abdallah kasa b'oye farin cikinshi yayi lokacin da aka tsaida maganar auren ga d'okin
zuwan lokacin daya dinga yi kamar shine aurenshi na farko da zaiyi hakan yaba wasu daga y'an gidan mamaki sosai suka shiga tunanin kodai dama can Abdallah Jauhar yakeso aka bashi Janaan ba wanda dai ya fito da maganar suka barta cikin zuciyoyinsu.
K
wanakin biki nata k'ara matsowa yayin da Ammi ta shiga gyaran d'iyoyinta magungunan sanyi ne sadidan take d'ura musu wanda bazai cutar dasu da lafiyar jikinsu ba, saikuma gyaran jiki da shima aka samu wata y'ar maiduguri k'awar Aunt Deejah ce kuma mak'ociy
arta dan haka suke tafiya can gidan Aunt Deejahn itakuma take samun su a gidan duk nok'e nok'en da Jauhar take na ita batason wannan gyaran hakan baisa Ammi ta k'yaleta ba. Aikuwa cikin lokaci k'ank'ani duk suka canza kowacce ta k'ara yin kyau fatarsu ta c
anza gyaran ya karb'esu sosai.
Shiri sosai Abdallah yakewa wannan auren wannan karon ma Jeeddah yabawa kwangilar had'a lefen ya kuma sakar mata kud'i bana wasa ba yace bayason k'ananun kaya komai manya zatasa masa idan kuma yaga abinda baiyi masaba tas
an sauran dan haka Aunt Jeeddah ta dage sosai ta had'a masa lefe na garari set biyu masu shida shida kamar dai na Janaan saidai kayan ciki sun bambanta sosai ta wajen kyau da kuma tsada. Gidan Aunt Deejah aka kai kayan washegari aka kawosu a ranar ma aka k
awo na Hussaina shima Habeeb yayi k'ok'ari sosai kayane gasu nan tamkar za'a bud'e kanti, bayan kwana biyu kuma aka kawo na Hassana daga Yola itama d'in dai duk d'aya kaya sunyi masha ALLAH sai fatan zaman lafiya kuma.
Duk wata hanya dazata had'ata da A
bdallah bata binta dan bataso su had'un kuma shima d'in a y'an kwanakin yana busy sosai sam bai cika zaman gidan ba ko shigowa yayi baya dad'ewa yake k'ara fita batasan uwar dayake a wajen ba.
Hidima akewa auren nan sosai baga b'angaren amarya ba bag
a na angwaye ba anata shirye shiryen yadda bikin zai kasance, wannan karon ma tare dasu Hassana sukaje Kaduna sukayi kwana biyu suka dawo saboda lokaci daya k'ure ga kuma gyaran jikin da Ammi takeso a k'arasa musu.
Ana saura kwana biyar biki Ammi ta aik
i Jauhar gidan wata aminiyarta zata kai mata wani sak'o kasancewar su Hassana basa nan yasa ita kad'ai ta fito zata tafi, riga da siket ne a jikinta na atamfa sun d'an kamata kad'an tayi rolling da k'aramin gyale light purple kalar atamfar kenan tayi matuk
'ar yin kyau fatarta sai wani glowing take tana shek'i ga k'amshin daya zauna a jikinta dama kayan sawarta gaba d'aya.
Tana shirin bud'e k'ofar motar taji kamar an tsaya an bayanta juyowa tayi dan ganin waye tayi tozali da Abdallah yayi mata k'erere a g
abanta sama da k'asa ta kalleshi yana sanye da farin wandon three quarter da ash color d'in riga mara hannu mai hula k'afarshi sanye da farin takalmi sandals mai mad'auri, kallonta yake sosai hannayenshi zube cikin aljihun three quarter'n dake jikinshi.
"Lafiya?". Jauhar tace tana wani yatsina fuska, Kai ya d'age shima yana wani kallonta up and down matuk'a gaya kwalliyar ta tafi dashi ga atamfar tayi mugun haskata ga wani kyau data k'ara na musamman ga kuma daddad'an k'amshin dayake buso shi wanda yasa
shi d'an lumshe ido ya bud'e yana kallonta da shanyayyun idanunshi.
"Ina zakije?".
"Inda ka aikeni". Tabashi amsa kai tsaye batare da shayin komaiba mamaki yasashi zaro ido ya ciro hannu d'aya daga aljihun wandonshi ya nuna k'irjinshi dashi yana fad'in
"Ni kike fad'awa haka Jauhar? sa'an wasanki ne ni? kan bala'i, yace yana rik'e k'ugunshi da duk hannayenshi bayan ya tamke fuska sosai ya nuna mata hanyar komawa cikin falon tareda fad'in
"To shige ki koma ba gidan ubanda zakije".
"To wai ina ruwan
ka da fitar da zanyi ka takurawa rayuwata fa Malam". Tace cikin tsiwa tana harararshi.
Batayi aune ba kawai taji ya finciki hannunta da k'arfi yayi hanyar komawa da ita tutturjewa ta shiga yi tana son k'wace hannunta amma ta kasa saboda irin rik'on da y
ayiwa tsintsiyar hannun nata wanda har zafi suka fara yimata saboda tsabar damk'a tana tutturjewar tana komai sai daya kaita har cikin falon ya wurgata kan kujera.
"Subhanallah! Meye haka Modibbo? Lafiyarka kuwa?". Ammi da fitowarta kenan daga kitchen
ta fad'a tana kallon Abdallah dake tsaye akan Jauhar ya kama k'ugunshi, a fusace yace
"Ammi ki gayawa yarinyar nan kija mata kunne ta daina fad'ar duk abinda yazo bakinta a kaina idan ba hakaba wllhy wataran zan raunata ta a banza Ammi".
"Innalillahi
me yayi zafi haka, me kikayi masa Jauhar?". Ammi ta tambaya tana kallon Jauhar daketa harare harare tana tura baki, kamar zatayi kuka tace
"Wai Ammi kawai daga ganina zan fita ba tambayar ina zanje wai indawo ba inda zani".
Goshi Ammi ta dafe tace
"
Haba Modibbo nice fa na aiketa gidan Hajiya Zuhra zata kai min wani sak'o meyasa kai baka tsayawa yin bincike akan komai ".
"To kuma Ammi daga tambaya saita fad'amin magana dan ubanta abokin wasanta ne ni? Kuma saboda tsabar batada hankali da wannan shi
gar zata fita tana yawo a gari".
Cikeda tsiwa Jauhar tace
"To ina ruwanka da fitar da zanyi inba sa ido ba kuma meye laifin shigar danayi kai idan baka takurawa mutane ba bakajin dad'i".
"Kina jinta ko Ammi? Kinajin abinda take fad'amin ko". Yayi ma
ganar yana nuna Jauhar da d'an yatsanshi tareda sakin k'wafa yana jijjiga kanshi.
"Kai dallah ku rufewa mutane baki shashashai kawai aure fa kuke shirin yi amma bazaku bar wannan abinda kukeyi ba zan sassab'a muku yanzun wllhy ke kuma Jauhar banason ras
hin kunya Modibbo yayanki ne kuma yake shirin zama mijinki dan haka ki dinga saita bakinki a kanshi kinji na fad'a miki, Kai kuma nasha gaya maka ka dinga kama girmanka wannan abinda kakeyi shike k'ara janyo maka raini a wajenta kullum kamar k'ananun yara
ku dinga saka mutane magana wuce ka tafi naka waje".
"Ki kawo sak'on inkai miki". Yace yana kallon Ammi.
"Ka wuce kayi tafiyarka banaso". Baki ya bud'e zaiyi magana Ammi ta dakatar dashi tana kallon Jauhar dake ta faman ture turen baki tace
"Tashi
ki maida min sak'ona bedroom d'ina idan su Hassana suka dawo su saisu kai".
"An fasa kaiwa Ammi?". Jauhar ta tambayeta, cikin gatse Ammi tace
"Eh tunda wanda yafi kowa iko dake ya hana ai dole ki hanu tashi ki maidamin abuna. Abdallah daya san dashi
Ammi take baiyi magana ba sai sajenshi daya shiga shafawa yana tattare fatar goshinshi sama.
Tashi Jauhar tayi ta kalli Abdallah da shima yake kallonta wani irin kallo tayi masa sannan ta nufi upstairs dan maidawa Ammi sak'on nata, saida taje tsakiyar s
tairs d'in sannan ta waigo taci sa'a kuwa idanun Abdallah na kanta wata k'atuwar harara ta sakar masa tareda murgud'a masa baki, baki ya bud'e yana zaro ido kafin cikin hanzari ya haura ta bayan kujerar inda yake tsaye ya bita da gudu kan upstairs d'in da
gudu itama ta kwasa, Ammi kam zaune tayi kan kujera tana kallonsu itada su Irfaan da suka shigo yanzu daga wajen Ayyah suna kallon mahaifinsu na gudu akan stairs
🤣
Ita ta rasa ma abinda zatace musu wllhy.
Da gudu ta k'arasa bedroom d'in ta banko k'ofar
da k'arfi shikuma daidai lokacin daya k'arasa, tsayawa yayi cikin haki ya rik'e k'ugu yana kallon k'ofar, kai ya jinjina yana shirin barin bakin k'ofar yaji tace
"Kuma bazan yafe gudun daka sani ba Abdallah".
Murmushi yayi yana kad'a kai gamida cij
e lips d'inshi na k'asa yace
"Abdallah kai tsaye ko? Zan rutsaki ai kin kusa shiga hannuna, kwarkwar d'in yarinya kawai". Daga haka ya sauka downstairs, sumar kanshi ya shiga shafawa yana kallon Ammi da itama take kallonshi ya bud'ewa su little Janaan h
annayenshi sun san ma'anar hakan dan haka da gudu suka nufoshi suka rungumeshi suna masa surutunsu irin na yara wanda abubuwa dayawa ba'a sanin abinda suke fad'a.
"Sannu, ALLAH ya shiryeka Modibbo ka gama gudun?".
"ALLAH Ammi yarinyar nan batada kunya
kiyi mata fad'a".
Baki Ammi ta tab'e tace
"Matsalarku ce kuje can ku k'arata bazaku dinga sani magana ba kamar k'ananun yara".
Y'ar dariya kawai yayi ya sunkuyo ya sumbaci forehead d'insu sannan ya fice.
Mrs Salees Mu'az
💝
3/16/22, 20:39 - Um
mi Tandama
😇
: *WATA SOYAYYA*
💝
Page 40.
Paid book.
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022.*
©Oum Hanan.
Tun daga ranar Jauhar bata k'ara bari sun had'u da Abdallah ba duk hanyar datasan zasu had'u kauce mata take har zuwa lokacin da y'an biki suk
a fara hallara a gidan.
Gidanshi da suka zauna da Janaan nan aka k'ara gyarawa sosai gaba d'aya kayan ciki fitar dasu akayi aka zuba wasu sabbi komai da komai wadancan kuma na Janaan d'in aka dawo dasu gidan Ammi aka zubasu a wani d'aki daba komai anan
cikin compound.
Ranar alhamis da safe sukaje akayi musu gyaran gashi sannan akayi musu k'unshi.
Da yamma kuma akayi kamu anan compound d'in gidan wanda aka k'awatashi sosai inda ya cika da mutane mak'il kamar irin ranar yinin nan amare sun fito d'as
inda sukayi kwalliya da kayan sak'i wanda amare kesawa kalar ja da adon bak'i a jiki light makeup akayiwa kowacce sai tashin k'amshi suke, an gabatar da kamu lafiya k'alau aka tashi daf da magreebah bayan anyi rabon abubuwa masu tafiya suka tafi masu shiga
ciki suka shiga.
Jauhar harta fara gajiya duk tayi tib'is da ita tana kwance saman gado bayan tayi wanka ta d'an tsakuri abinci y'an mata ne birjik cike da d'akin y'an uwansu. Hassana da Hussaina kam ansamu dama suna can wajen angwayen su dan Abdallah
n Momy Maryam ma tun ranar yazo shida wasu daga cikin abokanshi sauran mutanen kuma sai ranar d'aurin aure zasu biyo baya.
Kan dole Habeeb yayi sallama da Hussaina ya tafi saboda kiran da babanshi yake masa, wajen shiga gidane Hussaina ta had'u da Abdal
lah yace ta kira masa Jauhar a cikin gida da sauri ta amsa da to ta wuce kafin ya tuhumeta fitowar datayi ta tsaya da Habeeb dan tasan sarai zai iya ba ruwanshi da amintakar dake tsakaninsu da Habeeb d'in.
"Auntie Jauhar angonki fa na kira a waje". Huss
aina ta fad'a lokacin datake zama gefen gadon da Jauhar take.
"Waye haka kuma?". tace cikin yatsina tana b'ata fuska bayan ta d'ago kanta.
"Ke kuji min y'ar rainin hankali angon naki ne baki saniba?". wata y'ar uwarsu ta fad'a, tsaki taja ta maida ka
nta tana fad'in
"Kice masa bazanzo ba". kai tsaye.
Ido Hussaina ta zaro da wasu na kusa da ita da hankalinsu ke kansu da sauri Hussaina tace
"Bazakije bafa kikace?".
"Eh ki fad'a masa haka kedai ai y'ar aike ce". Kai Hussaina ta jinjina ta tashi tan
a fad'in
"Kin fad'i gaskiya ni y'ar aike ce amma Yah Abdallah ba lallai ya tuna da hakan ba shiyasa zan tsaya daga baya baya in fad'a masa". ta fita daga bedroom d'in.
Tana zuwa ta fad'a masa abinda Jauhar tace, kai ya shiga kad'awa kafin yace ta tafi
, wayarshi dake hannunshi yana danne danne yafara nemo number ta ya danna mata kira, Itama wayar na hannunta lokacin kiran ya shigo dayake da wani sabon sim card ya kirata bata gane number shi ba tayi picking takai kunnenta tareda yin sallama saboda masifa
dake cinshi da k'yar ya amsa sallamar datayi ya fara balbala mata bala'in ta rainashi har ya aiko a kirata tace bazata zoba saboda batada mutunci, itama a fusace take fad'in
"Wai to idan nazo me zanyi maka haka nan zaka damu mutane da jarabar aike".
K'wafa yayi yace
"Haka kikace ko to ki shirya zuwana yanzun nan kinsan ba gudun abin magana nake ba wllhy tsaf zan d'auko ki kowa ya ganki kafin in fito dake nan inci uwaki tunda bakida kunya".
K'aramin tsaki taja tace
"Ina jiranka idan kuma bakazo ba
baka cika sunanka Abdallah Madugu ba". daga haka ta katse wayar.
"Kutt shikenan Jauhar kin kwanto mana kura bala'i da kanshi ai bakeba muma nan idan har yazo d'akin nan tamu ta samemu dan haka wllhy ba abinda zai zaunar dani a d'akin nan karku babbaka m
u da ranmu gara tun wuri in fece". wata y'ar yayan su Ammi Aliya ta fad'a tana mik'ewa tsaye tareda kama hannun Hussaina suka fita daga bedroom d'in, dayake sauran bawani cikakken sani suka yimasa ba itama d'in wani zuwa ne daya tab'a yi Yola yakai musu z
iyara aikuwa duk saida ya gallabi y'an gidan akwai yayyenta mata masu jida kansu marasa jin magana duk saidaya saita musu zama a lokacin tun daga nan suke shakkar shi, Abdallah case
🤦😂
.
D'an yatsanshi ya ciza lallai ma yarinyar nan baisan meyasa ta
rainashi har haka ba bari ta shigo hannunshi zatasan da wanda takeyi, cikeda karsashi ya tashi ya nufi hanyar dazata sadashi da cikin falon zai nuna mata shi Abdallah Madugu ne, yana shiga falon yaga mata da yawa wasu na kallo wasu cin abinci yayin da was
u sukayi group sai zabga hira ake ta y'an uwantaka, bai tankawa kowa ba ya nufi hanyar dazai isa bedroom d'in Jauhar sukaci karo da Ammi itakuma zata fito baya yayi yana y'an kame kame ganin yadda Ammi ta tsura masa ido da alamun tambaya a fuskarta.
"In
a zakaje da daren nan Modibbo?".
Hannu yakai kan lallausar sumar kanshi ya shiga shafawa d'ayan kuma ya cusashi a aljihun wandonshi yace
"Ammi wajen yarinyar nan mana wai har in aiko a kiramin ita tace bazata zoba tsabar ta raina ni Ammi". galala Ammi
ta tsaya tana kallonshi kafin tace
"To daka taho nan zuwa zakayi ka d'aukota kokuma dai me zakayi?".
Ba rissinawa ba komai yace
"Eh Ammi zan gyara mata zamane naga rainin hankalin nata ya wuce misali". Tsaki Ammi taja ta nuna masa hanyar fita tana f
ad'in
"Dallah malam wuce ka tafi harkar ka kiran uban me kake mata da daren nan harda tasowa wai kazo ka d'auketa saboda bakada kunya wai dan ALLAH Modibbo yaushe zaka girma ne ka daina abinda kake?". Baki ya tura yace
"Dan ALLAH Ammi ki k'yaleni da..
.....hanyar fita data k'ara nuna masa yasa yayi shiru ya juya ya fita daga falon, da kallo Ammi ta bishi tana girgiza kai tasan halin kayanta shi yanzu ba abin kunya bane a gurinshi ya d'auko Jauhar duk uban mutanen nan yazo ya keta ta cikinsu ba ALLAH dai
ya zaunar dasu lafiya inba hakaba wllhy za'a ga kwamacala kala kala ita Jauhar rashin kunya shikuma ba hak'uri da rangwame ko yaya akayi masa abu saiya rama haka zaije yaita wahalar da ita a banza indai bata daina yimasa rashin kunya ba zata sameta kuma t
ayi mata magana rashin kunyar datake masa tayi yawa inzata gyara ta gyara idan kuma bazata gyara ba to itace a wahale.
Yana fita yaga har lokacin Abdallah da Hassana suna nan anata lobayya, wajen ya nufa a fili yake fad'in
"Kaima tashi zakayi dan uba
nka tunda nima ban yiba, tunda Hassana taga ya nufosu gabanta ya shiga fad'uwa tun kafin ya k'araso ma ta mik'e tsaye dan tasan sauran zancen yana zuwa kuwa yace mata
"Ke dan ubanki wuce ki shiga gida". da sauri kuwa tabar wajen jikinta na rawa, harara
Abdallahn Momy Maryam ya zabga masa yace
"Malam ya haka daga zuwa zaka korar min mata bayan bamu gama soyayyar mu ba".
"Ai yadda banyi ba ba ubanda ya isa yayi wllhy shima wancan d'an iskan daya nan wlhy saina koreshi". ya fad'a yana zama kusa da Abda
llahn, tsaki Abdallahn Momy Maryam yayi cikeda jin haushin korar masa