Showing 69001 words to 72000 words out of 96447 words

Chapter 24 - Wata Soyayya Complete

03 Sep 2026

24

d'inshi da Daddy ya siya masa kafin yabar k'asar Nigeria lokacin yana Kaduna da zama wajen Mama (Su Madugu ashe an dad'e da folawa Jauhar almuri

🤣🤣

).

Sam fuskarshi ta ka

sa barin murmushin dayake ya cigaba da bud'o sauran hotunan yana kallo kowani k'asan hoto akwai zanen flower masu matuk'ar kyau da ban sha'awa had'i da special words na tsantsar soyayya da zallar k'auna cikin tataccen speech wani kuma da fulatanci da kuma

wani yare dana kasa tantance shi kamar chaina kamar indiyanci

😂

wani irin yanayi yakeji tattare dashi ya b'ata lokaci mai tsaho a haka batare daya sani d'in ba k'arshe ma daya gaji da zaman saiya zame ya kwanta kan pillow ya dora littafin a tsakiyar k'ir

jinshi ya rufe ido yana tunano yadda suke ada da irin tsananin shak'uwar da sukayi wanda idan bazai manta ba lokacin daya tafi outside karatu har rashin lafiya tayi sosai saboda kewarshi datayi yayi d'awainiya dasu Janaan sosai tun suna zannuwan goyonsu mu

samman Jauhar da tun farko tafi shiga ranshi har wankin kashi da fitsari ba wanda baiyi musu ba dan tare dashi Mama tayi jegonsu ya dad'e a haka yana tuna baya kafin barci yayi awon gaba dashi Abdallah dai an shiga shauk'i

🥲

🤣

.

Ya dad'e yana barcin k

afin ya tashi maida littafin yayi inda ya d'aukoshi ya k'ara kullewa sannan ya shiga bathroom danyin wanka.

Mrs Salees Mu'az

💝

3/13/22, 21:16 - Ummi Tandama

😇

: *WATA SOYAYYA*

💝

Page 38.

Paid book.

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*.

©Oum Hanan.



Yana cikin shiryawa bayan fitowar shi daga wanka yaji ya taka wani abu da k'afarshi daga bakin gado, sunkuyawa yayi yakai idanunshi kan abinda ya taka d'in abin d'aure gashi ne na yara mai kyau sosai pink color ido ya k'ura masa tabbas wannan beat d'in na

Jauhar ne kuma wajen d'auko littafin nan ya fad'o dashi bai saniba bazai manta ba lokacin dazai tafi k'asar waje had'uwarsu ta k'arshe yace tabashi abinda zai dinga tunawa da ita dube duben abinda zata bashi ta shiga yi saidai ba komai a jikinta wanda zat

a bashi dan haka kawai tasa hannu ta cire beat d'in da aka d'aure mata tulin gashinta a baya ta warware shi ta kama hannunshi ta damk'a masa murmushi yayi ya sumbaci goshinta a wancan lokacin, yanzun ma murmushin ne ya sub'uce masa yakai beat d'in bakinshi

yayi kissing d'inshi sannan ya maidashi inda yake ya tashi ya cigaba da shirinshi baisan abinda ya canza Jauhar ba ada tanada hak'uri ko surutu bata dashi kafin tafiyar shi amma yana dawowa da d'okin yazo ya ganta yaga gaba d'ayanta ta canza tazama fitina

nniya mara kunya ga tsiwar tsiya tun daga lokacin ya fita sabgarta.

Tsaf ya shirya cikin k'ananun kaya riga da wando farare tas na kamfanin ADIDAS wanda akayi musu ado da jan layi layi a gaban rigar dakuma gefe da gefen wandon Pcap yasa red colour ya z

ura farin slippers mai taushi sosai ya fesa turare ya fita yaja k'ofar. Kai tsaye cikin gidan ya nufa baisamu kowa a falon ba kuma dama sarakan rashin jin gidan basu nan Aunt Jeeddah ce tazo ta kwashesu wai zasuyi kwana biyu da k'yar ma Abdallah ya bari it

ama Jauhar jitake tamkar ta bisu gidan dama bada son ranta aka tafi dasu ba.

Bedroom d'in Jauhar ya wuce kai tsaye yana zuwa yakama handle d'in k'ofar ya bud'e ya shiga, tana zaune a gefen gado da waya a hannunta tana danne danne ta zame mayafin kanta

wanda ya bayyana da lallausar gashin kanta bak'a wuluk ta asalin fulani datayi doughnut dashi a baya, da sauri ta d'ago kai ta kalleshi lokaci d'aya tana laluben gyalenta a gefenta ta had'e rai sosai tana harararshi ta gefen ido, bai damuba ya cigaba da ta

kawa zuwa wajen gadon saida yaje daf da inda take sannan ya tsaya ya d'ora k'afa d'aya kan gadon d'ayar kuma tana k'asa ya d'an rank'wafa yana kallon Jauhar data had'e fuska take masa wani irin kallo tace

"Wai meye ma'anar haka Malam?". Wani d'an iskan

murmushi yayi tareda d'age kafad'a ya juya gaban Pcap d'in kanshi ya koma baya yace

Nima ban saniba kawai dai nazo in jaddada miki maganar aurena dake ne ba fashi dan haka ki shirya zan aureki zan kaiki gidana dolenki kuma ki zauna". Itama d'in murmushin

tayi cikeda rainin hankali tace

"Ana aure dole ne ko k'arfa k'arfa zaka nunamin ban saniba".

"Yeah! zan miki k'arfa k'arfa da k'arfin ikona a kanki, dan kin samu ma zan taimaka miki in aureki kike rainamin hankali shekararki nawa babu mashinshi ni ko

da sunzo ma bazaki iya kula kowa ba Jauhar saboda nine anan d'inki". ya ida maganar yana nuna saitin zuciyarta da d'an yatsanshi manuniya.

Sosai maganar ta daketa batada mashinshi fa yace yasan irin mazan dake kara kaina a kanta kuwa, a fusace ta mik'e

tsaye tace

"Yah Abdallah ka fita daga d'akin nan dan ALLAH ka fita na rok'eka kuma zan tabbatar maka da inada mashinshina bama d'aya ba ba biyu ba kawai ra'ayin kulasu ne daba nayi aure kuma bazan aureka ba kayi abinda zakayi".

Tsaye ya mik'e ya cusa

hannayenshi duka cikin aljihun wandonshi ya juya mata baya yace

"Mu zuba ni da ke Jauhar za'aga wanda zaici nasara". daga haka ya fice daga bedroom d'in da sauri, yana fita ta fad'a kan gadon tareda sakin wani irin kuka ranta na mata k'una ta rasa ta y

adda zatayi ta fito da soyayyar Yah Abdallah daga zuciyarta tun batasan mecece itaba batasan meye SO ba take jinshi cikin zuciyarta sunanshi kawai aka ambata yakan sata cikin farin ciki mara misali tanason Yah Abdallah kamar ranta lokacin da maganar aurens

u da y'ar uwarta ta taso k'iris ya hana zuciyarta fashewa ta tsinci kanta cikin wani irin mawuyacin hali ta danne ne dai kawai saboda kar mutane su ranfo ta amma a lokacin ko barcin kirki bata iyawa sai data kai zuciyarta nesa wajen ganin bata canzawa y'ar

uwarta ba a lokacin saboda yadda zuciyarta take mata zafi idan ta tuna masoyinta shi zata aura shikenan ita ta tashi a tutar babu duk dakon soyayyar nan tashi datayi tun tana k'aramar ta ta tashi a banza kenan a yadda yadawo mata a marar mutunci itama a h

aka ta karb'eshi a yanzu gani take koda ta auri wanin Madugu to gangar jikinta ya aura amma zuciyarta da dukkan wani tunanin ta suna wajen Abdallah batasan ya zatayi ba shin ta amsa tayin su Ammi ne kokuwa dai ta bijire kanta ya kulle itakam. Saida taci ku

kanta ta k'oshi ta rarrashi kanta da kanta ta fad'a tunanin abinda ya kamata tayi cikin haka barci ya kwasheta cikeda mafarkai kala kala kuma rabi duk na Abdallah ne.

**

★★

**

★★

**

Two days after.

Jauhar tasamu wani sabon saurayi da suka had'u a shoppin

g malls taje yiwa su Irfaan siyayyar sweet da chocolate suka had'u shikam dagani ya girmewa Abdallah sosai kawai dai irin y'an boko d'in nan ne wanda ya dad'e baiyi aure ba sunanshi Auwal zarewa tunda ya ganta yabi ya rud'e bataja da tsayi ba tabashi phon

e number d'inta tareda address din gidan shiya biya kud'in datayi siyayyar sai dayaga tashin motar ta sannan shima ya shiga tashi motar yabar wajen.

Su Ammi basu k'ara tada maganar ba hakan yasa Jauhar tayi tunanin ko sun bar maganar ne gaba d'aya shik

am Abdallah hankalinshi yana kai kuma yayi alk'awarin koda su sunbar maganar saiya k'ara taso da ita dan a yanzu burinshi bai wuce yaga ya mallaki Jauhar a matsayin matarshi ba dan haka kota yayane yanajin saiya mallaketa.

Sau biyu suna waya da Auwal

zarewa kuma ya nemi zuwa gidansu dansu gana da ita bataji ko d'ar ba tabashi damar zuwa ranar dazai zo ta sanar da Ammi ga mamakin ta kuma Ammin batace komaiba tace ALLAH ya kawoshi lafiya.

Sai yamma yazo bayan sallahr la'asar anan compound suka zauna k

usa da wasu shuke shuken furanni kan fararen kujerun roba dake wajen ta kawo masa ruwa da lemo da snacks bayan sun gaisa ya bata yabata tarihinshi in brief da kuma aikin dayake tunda suka zauna Jauhar ta lura shegen surutu gareshi gashi bataso wannan mara

mutuncin yadawo gidan ya sameshi batasan abinda zai masa ba bataso a dalilinta aci masa mutunci shikuma ya dage sai zuba yake sam batayi zaton zai dad'e hakaba horn d'in dataji daga bakin gate ne yasa gabanta ya fad'i cikin ranta ta shiga addu'ar ALLAH yas

a Yah Ameen ne ko wani dai ba Abdallah Madugu ba, aikuwa dai addu'ar tata bata ciba dan ana bud'e gate d'in motar Abdallah ta danno cikin gidan.

"Innalillahi wa inna ilaihi rajioun". ta fad'a cikin ranta tana k'ara gyara zamanta duk ta tsorace kuma bada

n komaiba saidan gudun cin mutuncin da Abdallah zai iya yiwa Auwal tasan da wuya yagani bai tanka ba sai yanzu take dana sanin yarje masa datayi yazo gidan data sani gidan Aunt Deejah ko Jeeddah ko Mabrookah taje suka had'u tsaki ta saki tana d'an dukan g

oshinta, jin tsakin datayi yasa Auwal tambayar ta lafiya kuwa? murmushin yak'e kawai tayi tace masa lafiya k'alau ba komai hankalinta gaba d'aya yana kan Abdallah dake k'ok'arin fitowa daga mota bayan yayi parking, kasancewar shi Auwal d'in ya bashi baya h

akan yasa baiga mai shigowar ba baikuma juya dan ganin waye d'in ba. Had'add'en farin yadin filtex ne a jikinshi riga da wando rigar iya gwiwarshi

shara shara ne yadin hakan yasa har singlet d'inshi fara tas bata b'uya ba k'afarshi ma farin takalmi ne na z

allar fata sai farin agogon fata daya d'aura a tsintsiyar hannunshi ta gadon ce dai a kanshi itama fara da adon bak'i a gaban (Nasan dai kun fahimta

🤣

).

Tsaye yayi bayan fitowarshi daga motar yayi crossing hands d'inshi a k'irjinshi ta k'asa ma yayi cr

ossing legs d'inshi ya zuba musu ido yana kallonsu ransa na masa zafi meyasa Jauhar batajin magana ne? duk hak'urinshi saitaja abinda zaizo yana bambami da tada jijiyar wuya dan me zata kawo wani cikin gidan da maganar aurenshi a kanta, ido suka had'a da J

auhar tayi hanzarin kauda nata idanun cikeda fargaba addu'ar ta d'aya ALLAH yasa yayi wucewar shi salin alin batare daya kulasu ba wanda tasan mawuyacin abune hakan ta faru Abdallahn ne zaiga abinda baiyi masaba ya kauda kai bai tanka ba aikuwa da an canza

masa suna saidai kuma wani ikon na ALLAH.

Kai Jauhar ta sunkuyar lokacin daya fara tahowa.

"Shikenan ta faru ta k'are". tace cikin ranta time d'in daya k'araso inda suke shima ya janyo wata kujerar ya zauna bayan ya mik'awa Auwal hannu sunyi musabah

a a mutunce Jauhar har yanzu bata d'ago kaiba.

"Ahmm dalilin daya kawoka gidan nan nakeso inji Malam". yace idanunshi akan zoben azurfar dake hannunshi na dama yana wasa da ita.

Ko bai tambaya ba yaga kamanni na jini tsakanin Abdallah da Jauhar yasan

yayanta ne shiyasa cikin girmamawa yace

"Nazo wajen Jauhar ne dan mu gana saboda inaso in aureta idan ALLAH yayi".

Kai kawai Abdallah ya shiga jinjinawa kafin yace

"Bakasan matar aure bace ne tanada miji?". Da sauri Auwal ya zaro ido ya shiga bin

Abdallah da Jauhar da kallo itama Jauhar da sauri ta d'ago kai ta kalli Abdallah daya maze kamar wanda ya fad'i gaskiyar nan cikeda mamaki yace

"Tanada aure fa kace?".

Wani kallon rainin hankali Abdallah yake masa kafin yace

"Kana tantama ne? to ni

ne mijinta yau kwana biyu da d'aura mana aure bata tare bane saboda wani dalili fatan kagane?".

Kallon Jauhar Auwal yayi wadda tayi wuri wuri tamkar hakane d'in gaskiya Abdallahn ya fad'a kai ta shiga girgizawa tana fad'in

"Wllhy Auwal ba haka bane k

arka yarda da abinda ya fad'a yana jin haushi ne ance za'a had'amu aure nace bana sonshi". Yaa ALLAH yau kuma ta nan Abdallah ya b'ullo tayi zaton zaizo a fusace yaci masa mutunci saikuma taji akasin hakan.

Shidai Auwal saiya rasa maganar wazai kama taw

a kuma zai bari, ganin kamar Auwal ya yarda da maganar Jauhar yasa Abdallah tashi tsaye yace

"Bari inyi abinda zaisa ka yarda tunda naga tantama kake". gani kawai sukayi ya nufi Jauhar basu san me zaiyi ba yana zuwa yasa hannu ya janyo nata hannun ya mi

k'ar da ita tsaye kafin tayi tunanin abinda zaiyi mata taji ya zura bakinshi cikin nata ya shiga kissing d'inta.

"Innalillahi wa inna ilaihi rajioun". Amma dai wannan yarinya ta cuceshi wllhy yanzu ashe da matar aure yake tare bai saniba ALLAH zai saka

masa kuma yasan bazai kamashi da laifin kula matar aure ba tunda bai saniba me yake damun matayen yanzu ne sam babu tsoron ALLAH a lamuransu. Auwal ne ke wannan zancen zucin ranshi a b'ace sosai gameda abinda Jauhar tayi masa ita ko tsoro ma bataji a gansu

?

Tamkar ta mutu saboda tsananin b'acin rai wani dunk'ulallen abu ya tsaya mata a wuya idanunta suka cika da k'wallar bak'in ciki me Yah Abdallah yakeso ya zama ne shi idan zaiyi abu kawai gaba gad'i yake yin abinshi ba tunanin komai ko abinda zaije yaz

o, k'ok'arin k'wacewa ta dinga yi da kici kici ya saketa amma saboda irin rik'on tsauri dayayi mata hakan yasa ta kasa k'wacewa, Auwal dai yana zaune shi bai tashi ya tafi ba bai kuma kallesu ba ya sadda kanshi k'asa yana dana sanin zuwanshi gidan nan.



Saida yayi iya son ranshi sannan ya saketa sai wani lumshe ido yake yana murmushi, dab'ar takoma ta zauna kan kujerar d'aya fincikota ta tashi sai lokacin hawayen da suka taru cikin idanunta suka samu damar zubowa kan fuskarta.

"Woww like sweet". Yace

yana murmushi gamida tsotsar bakinshi yabar wajen da sauri, da k'yar ta d'ago kai ta kalli Auwal tana shirin yin magana ya d'aga mata hannu batare dayace komi ba ya tashi yabar wajen da sauri, batayi yunk'urin binshi ba harya shiga motarshi maigadi ya bud

'e masa gate ya fice daga gidan da sauri

(Maigadi dai baiga aika aikar da Abdallah yayi ba lokacin ya zagaya band'aki).

A hankali tasa hannu ta goggoge idanunta a fusace ta tashi bata nufi cikin gidan ba sai side d'in Abdallah data nufa, tana zuwa

ta banka k'ofar falon a shiga baya ciki dan haka kai tsaye ta nufi bedroom d'in tasan dai bazai wuce can ba.

Yana tsaye gaban mirror yana cire links d'in hannunshi ta shigo bedroom d'in, kai tsaye inda yake ta nufa tana zuwa tasa hannu ta turashi tana

fad'in

"Me kake tak'ama dashi ne Yah Abdallah meyasa kakemin haka ne? nace me yasa kakemin haka idan baka b'ata raina ba bakajin dad'i ko nace bakajin dad'i ko. Ta k'are maganar cikin k'araji tamkar wata zararriya, dariya kawai yayi ya zagayeta da nufi

n komawa wajen mirror n ta k'ara turashi ya had'u da bango taje daf dashi tamkar zata shige jikinshi hakan daya gani yasa ya d'age hannayenshi sama tareda zaro ido waje yace

"Fyad'e zakimin Jauhar?".

Cikeda b'acin rai tanajin tamkar taita marinshi ko

zata huce daga iskancin dayake mata tace

"Y'ar iska ka maidani Yah Abdallah? Nace y'ar iska ka d'aukeni? Eh fyad'en zan maka Tayi maganar da k'arfi tana k'ara turashi, ido ya k'walalo waje na shak'iyanci ya k'ara d'age hannayenshi yana wani d'an runtse

Ido da kauda kai gefe yace

"Wayyo Ammi kizo zatamin fyad'e wayyo Ayyah". Ya fad'a da k'arfi yana y'ar dariya

Ganin kamar ma ya maida ita wata sha ka tafi mara hankali yasa kawai ta sakeshi tabar bedroom d'in da gudu tana hawaye.

Dariya ya k'yalk'

yale da ita kafin yace

"I love you so much Jauhar har k'arshen numfashina muaahh". Yace yana jefawa hanyar data fita kiss ya cigaba da rage kayan jikinshi yana murmushi.

Mrs Salees Mu'az

💝

3/16/22, 11:24 - Ummi Tandama

😇

: *WATA SOYAYYA*

💝

Page 39

.

Paid book.

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*.

©Oum Hanan.

Tun daga lokacin Jauhar take baya baya da Abdallah tsoron had'uwarsu dashi take gani take tamkar zai k'ara yimata kiss ne agaban y'an gidan shiyasa ko suna zaune a falo ana hira dataji

alamun shigowar shi zata tashi da sauri ta shige bedroom d'inta kar yaja mata abin kunya tunda dai shi ko d'igo bashi da ita.

Abbie sunyi waya da Daddy ya fad'a masa duk abinda ya faru lokacin da sukayi musu maganar auren dan haka gara a hak'ura kawa

i har ALLAH ya fito mata da miji tayi aurenta shima Abdallahn haka, sam Daddy baiji dad'in hakan ba yace kuma a barshi da Jauhar d'in zaiyi mata magana, shidai Abbie har sukayi sallama yana k'ara nanatawa Daddy da rok'on alfarmar kar yace zai takurawa Jauh

ar ta auri Modibbo idan bata yardaba kawai a k'yaleta Daddy yace ko d'aya ba matsa mata zaiyi ba abarshi dai da ita.

Jauhar Daddy ya kira bayan ta gaisheshi yafara mata nasiha da rarrashinta akan maganar auren Abdallah tareda nuna mata alfanun wannan

had'in da suke son suyi karta bashi kunya dan ALLAH taje tasamu Abbie ta bashi hak'uri ta kuma sanar masa ta amince da auren

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login