Showing 33001 words to 36000 words out of 96447 words

Chapter 12 - Wata Soyayya Complete

03 Sep 2026

18

mata cikin sakin fuska tana dafa kafad'arta akwai kyakkyawar alak'a da fahimtar juna tsakaninta da surukar tata.

"Oyoyo Ayyahnmu". Hassana da Hussaina suka had'a baki wajen fad'a tareda rungumeta, Janaan dai tana

gefe tana murmushi cikeda sha'awarsu.

"A'a ya kika tsaya taho mana Hassana". Ayyah ta fad'a cikin murmushi tana kallon Janaan bayan su Hussaina sunbar jikinta, a hankali Janaan ta k'araso inda Ayyah take rungumota Ayyah tayi jikinta haka nan take k'aun

ar yarinyar ALLAH ya had'a jininsu kuma sau d'aya ta tab'a ganinta wani hutun semester da suka samu driver ya kaisu itada Hassana da Hussaina tun daga lokacin taji yarinyar tayi mata musamman saboda hak'urinta dakuma sanyin halinta, kwanansu biyu suka dawo

.

Cikin gidan gaba d'aya suka rankaya suka shiga bayan Hassana ta karb'i jakar kayanta da drivern yabata, saida suka rakata har wani k'aramin part da aka tanadar mata wanda zata zauna yasha gyara sosai sai tashin k'amshi yake duk fita sukayi sai Ammi d

a aka bari sai data shiga bathroom ta had'a mata ruwan zafi ta fito ta sanar da ita tayi wanka saitayi sallah sannan tazo taci abinci.

Sai data shimfid'a mata pray mat sannan tabar bedroom d'in.

Tana kan dardumar bayan ta idar da sallahr Janaan

tayi sallama Ayyah ta amsa tare da bata iznin shiga, kusa da ita ta tsuguna tace

"Ayyah Ammi tace ki fito ga abincin angama shiryawa".

"Gani nan zuwa Hassana bari in shirya".

"Toh Ayyah saikin fito". Janaan ta fad'a cikin murmushi tareda fita da

ga d'akin Ayyah ta bita da kallo.

Bayan wani d'an lokaci Ayyah ta fito falon duk a dinning table d'in ta samesu dan dama suma basuyi launch d'in ba, tana isa Janaan tayi hanzarin tashi taja mata kujera ta zauna.

"ALLAH yayi miki albarka". Ayyah

ta fad'a bayan zamanta, da Amin suka amsa gaba d'ayansu sannan Hussaina ta tashi suka shiga yin serving d'insu itada Janaan, kasancewar ansan Ayyah da son tuwo hakan yasa akayi mata tuwon masara lafiyayye dayake kona semovita bataso tafison na masara kokum

a na shinkafa miyar busasshiyar kub'ewa akayi mata wadda taji naman rago da man soyayyen man shanu duk k'amshin miyar ya cika wajen, Hassana ma da tuwon yabata sha'awa tace shi zataci, hararar wasa Ayyah ta jefa mata tace

"Magulmaciya". Y'ar dariya ka

wai Hassana tayi tana janyo plate d'in da aka zuba mata tuwon gabanta ta fara ci.

Bud'e k'ofar falon da akayi ne duk yaja hankalinsu Ammi bakin k'ofar dan ganin waye duk da dai sun d'auki haske saboda jin k'amshin mayen turarenshi daya fara gauraye

ko ina na cikin falon Abdallah Madugu ya bayyana sanye cikin bak'in wandon jeans da white shirt long sleeve mai round neck dayasa wadda ta fito masa da faffad'an k'irjinshi ya nad'e wuyanshi da wani dogon abu mai taushi na sak'a black color farin takalmin

sawu cikine sanye a k'afarshi ya manna farin glasses na gayu a idanunshi yayi matuk'ar yin kyau duk da dai fuskarshi a tamke tam ya shigo saidai ganin wadda ke dinning wato Ayyah yasa ya saki fuskar tashi ya nufi dinning table d'in.

Yana k'arasawa ya

ja kujerar kusa da Ayyah ya zauna yana fad'in

"Hajjaju mutan makkah saukar yaushe?".

"Ka ganni nan dai ban dad'e da zuwa ba maigidan". Ayyah tabashi amsa fuskarta a sake cikeda jin dad'in ganin Abdallahn dan duk a cikin jikokinta kaf mata da maza ba w

anda take nunawa so irinshi hakan ya samo asaline kuma saboda sunan Malam Abdullahi Modibbo da aka maida masa wato mijinta saikuma Abdallahn Momy Maryam da shima take kulawa dashi sosai duk dan saboda sunan maigidanta da suke dashi, dan ma dai wani lokaci

n halinshi na had'ashi da ita haka take biye mashi suyita fad'a wani lokacin ma fad'an nasu abin dariya.

Tunda ya zauna wajen su Janaan duk sukasha jinin jikinsu kowacce ta sunkuyar da kai tana juya spoon cikin plates d'in abincin har Hassana datake ta

faman yiwa Ayyah surutu saitaja bakinta ta tsuke, plate d'in Ayyah ya kalla ya wani yatsina fuska yace

"Kinji matsalarki Ayyah dan ALLAH meye daga zuwa zaki fara wani cin tuwo? Dan ubanku wayace kuyi mata tuwo?". Yayi maganar yana rarraba idanunshi ka

nsu Hassana da Janaan wanda duk suka tsure kowacce kanta a k'asa.

"Modibboo, waye baisan Ayyah da son tuwo ba? shiyasa fa akayi mata".

"Rabu da wannan maigidan nawa d'an rigima, ina ruwanka ninake so nace ayimin". Ayyah tayi maganar tana kallon Ab

dallah.

Plate d'in tuwon ya janye yana fad'in

"Ayyah baza kici tuwon nan bafa".

"A'a nikam dawo min da abuna". Tace tana k'ok'arin amsar plate d'in, kallon Hassana yayi ya zabga mata harara yace

"Kema dan ubanki mayar da tuwon nan ki ajiye munafuk

ai na k'ara ganin kunyi mana tuwo a gidan nan sainaci ubanku dukanku".

"Yaa salam! Wai meyake damunka ne haka Modibbo? Dan ALLAH tashi kabar wajen nan kuma kabawa Ayyah tuwonta tun kafin ranka ya b'aci". Ammi tayi maganar a fusace tana kallonshi.

Pl

ate d'in ya tura mata yana wani yatsina fuska, itadai Ayyah murmushi kawai take gamida girgiza kai, Ammi kam k'wafa tasaki ta maida kanta kan abincin datake ci, har yanzu tamkar yaro haka Abdallah yake wani lokacin ALLAH dai ya shirya mata shi.

"

Bani abinci". Abinda kawai yace kenan yana kallon Janaan, da sauri ta mik'e kuwa kamar wadda ke jira ta zuba masa dambun shinkafa dayaji vegetables da spices sai hanta da aka yanka hanta k'ananu a ciki ta tura masa plate d'in gabanshi bayan tasa masa spoon

, su Janaan dai sai tashi sukayi suka bar wajen dan gaba d'aya zamanshi a wajen ya takura musu, kad'an ya tsakuri abincin ya ture plate d'in coconut juice d'in da aka zubawa Ayyah a glass cup shiya d'auka yana shirin kaiwa baki Ammi tayi saurin cewa

"A

h meye haka wai Modibbo? tashi kabar wajen nan tunda neman magana ya kawoka". Ganin ba alamun wasa saman fuskar Ammi yasa ya ajiye ya yagi tissue ya fita yana goge bakinshi, duk da kallo suka bishi Ayyah ta girgiza kai tace

"Halin dai yana nan har yanz

u".

"Me za'a fasa Ayyah? Modibboo ai sai addu'a har yanzu bai daina halayyar shiba".

"Zai daina ne Hafsat". Ayyah ta fad'a tana murmushi, kai kawai Ammi ta girgiza itadai taga ranar dazai nutsu ya daina wannan harigidon nashi amma tasan idan ALLAH ya

taimaka yayi auren maybe ya daina.



√^√^√^√^√^



Yau sati d'aya kenan da zuwan Ayyah gidan sun shak'u sosai da Janaan kullum suna tare da ita a bedroom d'in Ayyahn suna hira indai ba school dan yadda suke zama suyi hira ma basuyi dasu Hassan

a.

Yauma suna cikin bedroom d'inta, Ayyah na zaune kan gado ta mik'e k'afafuwanta Janaan tana zaune daga wajen k'afafunta tana shafa mata man zafi a k'afafun saboda takura mata d'in da suke cikin kwana biyun nan da ciwo, tuni Ayyah take faman kissima

abubuwa da dama akan Janaan da Abdallah a cikin ranta saidai bata saniba ko akwai wanda yake nemanta dan haka ta bugi cikinta da fad'in

"Nikam Hassana wai yaushe za'a kawomin jikana mu gaisa ne bake d'in ba basu waccan uwar surutun ba(Hassanar Ammi). M

urmushi kawai Janaan tayi a kunyace tace

"Ayyah ai babu kowa fa".

Cikin jin dad'i Ayyah tace

"Kina nufin bakida tsayayye?".

Cikeda sanyin muryarta na halitta tace

"Ayyah karatu mukefa nibana kula kowa har gara su Hassana suna d'an kula samari". K

ai Ayyah ta shiga jijjigawa tana murmushi da yardar ALLAH zata isar da k'udurin zuciyarta.

"ALLAH ubangiji ya kawo mafi alkhairi". Cewar Ayyah, Janaan bata amsaba sai k'asa data k'ara yi da kanta cikeda kunya.

K'ofar bedroom d'in aka bud'e Abdallah

ne ya shigo bakinshi d'auke da sallama sanye cikin blue black d'in jallabiyyah mai hula wadda tayi mugun haska farar fatarshi, kai Ayyah ta d'aga tana amsa sallamar tashi, bakin gadon ya k'arasa ya d'auke wata ledar magunguna dake kan bedside drawer

ya za

una, tunda ya shigo Janaan tabar abinda take gabanta sai fad'uwa yake bataso taga sun had'u waje d'aya da Yah Abdallah zuciyarta wani irin bugu take.

"Ke! tashi kibar wajen nan". Yayi maganar cikin had'e rai yana kallon Janaan.

"Ina ruwanka da ita?

kaidai rigimarka tafi k'arfinka wllhy maigidana". Janaan kuwa kamar jira take dama ta rufe bottle d'in man zafin ta sauka daga kan gadon cikin rawa rawar murya tacewa Ayyah

"Ayyah bari inje in dawo". Bata jira komaiba ta fice daga bedroom d'in, Ayyah ta

bita da kallo kafin tadawo da kallonta kan Abdallah tace

"Zamusa k'afar wando d'aya dakai fa tunda nazo na lura kana takurawa yaran nan musamman ma Hassana".

"Nifa raini ne banaso Ayyah, suna ganin kafara sakar musu fuska zasu rainaka nikuma cin u

ban yarinya zanyi". Ya ida maganar yana zame hular jallabiyyahr dake kanshi. Tsaki kawai Ayyah taja tana girgiza kai, nan ya cigaba da zama yana tayata hira duk rabin hirar fad'a ce kuma yak'i tashi ya tafi sai daya dad'e sannan ya fita yayi shirin fita o

ffice.

2/16/22, 07:41 - Ummi Tandama

😇

: *WATA SOYAYYA*

💝

Page 19

Oum Hanan

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*

Bayan sallahr la'asar ya shigo gidan bayan yadawo office yayi wanka ya huta. Pen da paper ne a hannunshi ya shigo falon Ayyah kawa

i ya samu a falon ta k'urawa TV ido wanda ake haska news na turanci kusa da ita ya zauna yana fad'in

"Tsohuwar nan akwai fitina wllhy saikace wadda ke gane abinda ake fad'a".

"Aifa kadawo kenan d'an nema". Tayi maganar tana kai masa rank'washi a kan

shi yayi saurin gocewa yana dariya bata sameshi ba, bata k'ara bi takan Abdallah ba ta cigaba da kallon news d'inta tana k'ara gyara zaman farin medical glasses d'in idonta itadai kawai hotunan da ake haskawa take kallo.

Zamanshi ya gyara yafara zane a

paper daya shigo da ita sai jefi jefi dayake satar kallon Ayyah data maida hankalinta gaba d'aya kan kallon datake, dan haka batasan bikin dayake ba.

Ameen ne yayi sallama ya shigo falon yaci gayunshi sosai cikin bugaggiyar shadda mai kyau da tsada sai

k'yallin amarci yake ga k'amshi dayake ta zubawa, kusa da kujerar Ayyah da Abdallah ya zauna yana gaida Ayyah ta amsa masa tana tambayarshi lafiyar Fareedah.

"Lafiya k'alau wlhy Ayyah tace a gaisheki". Yayi maganar yana lek'a paper'n da Abdallah yake

zane dan ganin abinda ya d'auke masa hankali haka baki ya bud'e tareda zaro ido yace

"Lallai Abdallah Ayyah kinga iskancin da yaron nan yake miki kuwa?". Ya k'arasa maganar yana warce takardar daga hannun Abdallah dake ta dariya ya nunawa Ayyah zanenta

ne rad'au a jikin takardar tamkar ka kirata ta amsa hatta irin d'aurin d'ankwalin dake kanta iri d'ayane saidai dan iya shege yadda ya zana glass d'in fuskarta k'ato wanda har ya kusa cika rabin fuskar, karb'ar takardar tayi ta shiga dukanshi da ita tana

fad'in

"Amma kai dai anyi d'an k'aniyar yaro wllhy shine dan wulak'anci ka zanani haka, dariya kawai Abdallah yake yana kare dukan datake kai masa da hannunshi Ameen ma dariyar yake tayashi dan ba k'aramin dariya zanen

yabashi ba lallai ALLAH yayiwa k'a

nin nasa wata baiwa ta musamman indai zane mutum keso ya fita sosai to ya nemi Abdallah shiyasa manyan masu kud'i da masu kamfanoni da sauran wad'anda za'a yiwa gine gine suke yawan nemanshi saboda yadda ya iya tsara gini har outside ake d'aukarshi yaje ya

gano gida ko kamfani yazo ya zana irinshi kuma sak batare dawani bambanci ba.

Ana cikin haka Abbie shima ya shigo falon tareda sallama, ganin yadda Ayyah take faman dukan Abdallah da takarda yayi dariya yana fad'in

"Meyake faruwa ne? Ayyah yau ked

a mutumin naki ne kuma". Juyowa Ayyah tayi tace

"K'yaleni da wannan maigidan nawa kaga tsiyar daya min yanzun nan". Tayi maganar tana nunawa Abbie takardar hannunta, karb'a yayi ya duba yaga abinda aka zana d'agowa yayi ya kalli Abdallah daya sunkuyar

da kai yana shafa sumar kanshi yace

"Gidanku Modibbo tsohuwar tawa kayiwa haka dan k'aniyarka". Dariya Abdallah yayi ya d'ago yace

"I'm sorry Abbie color kawai za'asa mata kaga yadda zata k.....ganin Abbie yayo kanshi yasa cikin sauri ya mik'e tsaye

ya dira ta bayan kujerar ya fice daga falon yana dariya dama tsokanace kawai ta kawoshi ba wani abu ba, da kallo duk suka bishi Abbie ya girgiza kai yana murmushi ya zauna kusa da Ayyah yana mata sannu da gida kafin su shiga gaisawa.



√^√^√^ Ammi ce

kawai da Ayyah a falon a zaune dan su Hassana duk suna school.

"Nikam Hafsat akwai mata muhimmiyar magana danake so muyi dake ina fatan zaki bani had'in kai da goyon baya akan maganar". Ayyah ta fad'a tana kallon Ammi.

"Insha ALLAHU Ayyah me kikeso

ayi miki?". Ammi tace tana maida hankalinta gaba d'aya kan Ayyah.

Shiru Ayyah ta d'anyi kamar bazatayi magana ba kafin tace

"Maganace kan maigidana da wannan yarinya Hassana y'ar wajen yayarki, nutsuwa Ammi ta k'ara yi sosai jin Ayyah ta d'auko ma

ganar data dad'e tana ranta takeso kuma tayiwa Abbie maganar duk da dai bata tabbatar da abinda Ayyahn zata fad'a ba maybe ba abinda take hasashe bane, cigaba Ayyah tayi da fad'in

"Na yaba sosai da halayyar yarinyar nan hak'uri da kawaicinta da kuma sa

nyin halinta na burgeni matuk'a wanda har hakan yasa nayi kwada'yin shigarta cikin zuri'ata kuma bada kowaba da mai sunan Malam dan k'ara k'arfafa dank'on zumunchi tsakaninmu Ina fatan zan samu had'in kanki".

Ajiyar zuciya Ammi ta saki tareda fad'in Al

hmdulillah cikin zuciyarta kamar Ayyah tana zaune sukayi wannan tattaunawar itadasu Deejah, cikin murmushi tace

"Wllhy Ayyah na dad'e da wannan tunanin cikin raina kuma ma har munyi maganar dasu Aminu nace zan samu Abbien su da maganar kuma har yau ALL

AH bai bud'i bakina na masa zancen ba, had'in yayi sosai Ayyah ubangiji ALLAH yasa alkhairi zamu k'ulla".

"Amin Amin, saidai kuma wannan rikitaccen maigidan nawa nasan da k'yar zai amince sai ankai ruwa rana dashi".

Murmushi Ammi tayi tace

"Karki

damu Ayyah insha ALLAHU Modibbo bazai bamu matsala ba nasan halinshi sarai duk abin nan nashi yanajin maganar mu sosai kuma bayason ranmu ya b'aci".

"To masha ALLAH, ALLAH yasa muga alkhairi". Ayyah ta fad'a cikin jin dad'i daga nan suka d'ora da hirar

su ta surukai masu ganin mutuncin juna.

Da dare lokacin da Abbie yaje gaida Ayyah a bedroom d'inta bayan sun gaisa ne ta d'auko masa maganar shima yaji dad'i sosai yayi murna ya kuma d'ora da addu'ar fatan alkhairi,anan suka tsayar da maganar za'a sam

u Abdallah da maganar da ita kanta Janaan d'in.

Ko Madugu zai karb'i tayin Ayyah, Ammi da Abbie?.

Two days after.

Tunda Janaan taji an aiko Hassana wai su Ayyah na nemanta a falon Abbie gabanta yaketa faman fad'uwa batasan dalilin kiran

ba tanada matuk'ar tsoro da gudun laifi dan haka tsoronta d'aya kar ace ko wani laifin tayi wanda bata saniba, doguwar rigar abayah ce a jikinta black color sai k'aramin hijab iya kafad'arta datake sanye dashi white color da akabi ko ina na jikin hijabin d

a stones masu k'yalli.

A d'arare tayi sallama ta shiga falon nan ta hangi Abbie da Ammi akan doguwar kujera a zaune Ayyah ma zaune kan kujera 1sitter da carbi a hannunta tana ja kamar yadda koda yaushe zaka sameshi dashi a hannunta, da k'yar ta k'arasa

inda suke ta zauna a k'asa saitin inda k'afafun Ammi suke ta sunkuyar da kanta tana musu barka da hutawa cikin rawar murya duk suka amsa mata cikin sakin fuska, baifi minti d'aya da shigowarta ba aka k'ara bud'e k'ofar falon aka shigo tareda yin sallama,

k'amshin turaren shi kawai daya baza musu a falon Janaan ta shak'a ta gane wanda ya shigo bai wuce Yah Abdallah ba tuni gabanta ya k'ara tsananta fad'uwa itafa harga ALLAH bata son abinda zai dinga had'asu ita dashi batak'i bama idan cikin mutane ne shima

d'in saiya zama dole kamar wannan lokacin.

Coffee color d'in yadi ne a jikinshi mai kauri riga da wando wanda aka yiwa aiki da bak'in zare wanda ya zauna sosai jikin yadin da kad'an rigar ta wuce cinyarshi, sumar kanshi tasha gyara sosai anyi mata wan

i style na gyara mai k'ayatarwa kasancewar shi fari yasa yadin yayi matuk'ar haskashi, hannunshi d'aya soke cikin aljihun wandonshi d'ayan kuma yana rik'e da wayarshi ya k'arasa inda suke shikuma kusa da k'afar Ayyah ya nema ya zauna ya gaishesu kawai ya c

igaba da latse latse a wayarshi kanshi a k'asa,wani aiki sai Abdallah Madugu

🤔

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login