Showing 96001 words to 96447 words out of 96447 words
kulawa duk wani hakk'insu yana iya bakin k'ok'arin shi wajen ganin ya s
auke shi kuma a ko ina Jauhar tana alfahari da mijinta dan d'ayane tamkar da dubu yasamu cigaba ta b'angarori da dama kuma yanada zuciyar taimakon al'umma musamman gajiyayyu masu rauni da marasa lafiya musamman ya kafa wata k'ungiya ta taimakon marasa k'ar
fi da marayu shiyasa ako yaushe yake k'ara ganin bud'i da alkhairai a sana'arshi.
Dama masu iya magana kance barewa batayi gudu d'anta yayi rarrafe ba kuma kamar kumbo kamar katan ta dan Irfaan kaf halayen Abdallah lokaci dayana yaro ya kwashesu tsaf sh
ima idan yayi wani abun saidai kawai Ammi ta bishi da ido dan yana tuno mata da k'uruciyar Abdallah ne fatan ta dai ALLAH yasa yabi k'uruciya karya d'ore har girmanshi dan ga babanshi nan yara hud'u gana biyar a ciki amma har yanzu Jauhar fama take dashi i
dan ya rikice mata idan yayi wani abun ko k'aramin yaro bazaiyi ba saidai ta kalleshi kawai tasa masa ido, amma fa yana da dad'in zama ita kanta tasan da haka kawai dai wani lokacin ne sai a hankali kuma dama zaman tare saida hak'uri bawai duk abinda mutum
yakeso yake samu ba ALLAH ya k'ara mana hak'uri da juriyar zama da mazajen mu lafi
ya
🙏
.
Mace ta haifa lokacin data haihu ita kuma saita biyo kamannin Jauhar d'in sunan Ammi taci wato Hafsat suke mata alkunya da Mahnoor.
Yah Ameen ma yanzu haka ya
nada yara uku itama dayake matar bata haihuwa akai akai su Hassana ma kowacce ta ajiye iyali, abokantakar Abdallah da Habeeb da d'aya Abdallahn tana nan saima abinda yayi gaba suma sun sa hannu tare suke tallafawa al'ummar musulmi.
Bayan haihuwar ta daw
asu watanni ya shirya musu tafiya yawon bud'e ido k'asashen waje shida iyalanshi gaba d'aya da Irfaan aka shirya tafiyar amma k'ememe yace shifa ba inda zaije kawai a k'yaleshi Abdallah yaso tursasa shi Ammi tace ya k'yaleshi d'in kawai tunda yace bazaije
ba.
Fatan dawowa lafiya ABDALLAH BASHEER MADUGU FAMILY
💝😍
.
Alhmdulillah
Alhmdulillah
Alhmdulillah
ALLAH nagode maka daka bani ikon sauke wannan nauyin dake kaina, abinda na fad'a daidai ubangiji ya had'amu cikin ladar wanda nayi kuskuren
rubutawa ya yafemin ina rok'on afwar duk wanda na b'atawa yayin rubuta wannan littafin kuma mun gode sosai da had'in kan da kuka bamu ALLAH yabar zumunchi ya had'amu a aljannah kamar yadda ya had'amu a nan
🙏👏👏
Ina yiwa kowa fatan alkhairi
Bissalam.
Maryam Ibraheem Aleeyu
Mrs Salees Mu'az
💝
(Oum Hanan)