Showing 15001 words to 18000 words out of 96447 words
da bayan hannunta ta shige bedroom d'inta tana k'ara yimasa ALLAH ya isa saboda hannayenta dataji suna amsawa dole saita musu
ruwan zafi kuma wllhy saita d'auki mataki akai kuma saita fad'awa Mama abinda yayi mata.
_D'inbin godiya gareku masoya hak'ik'a banida bakin magana, kunyi nagani na kuma yaba da irin soyayyar da kuke nunawa book din nan wanda har yaso ya zarta ta bo
ok din DR SAIF
π©Έ
nagode sosai ina ganin sak'onnin ku na gaisuwa ALLAH ya saka da alkhairi yabar mu tare ina yiwa kowa fatan alkhairi ALLAH yasa mudace Amin_.
π€©π
π₯°
*1luv*
Mrs Salees Mu'az
π
Maryam Ibraheem Aleeyuh
{Ummee}
*TOP 10
TAKUN HASKE BATCH A*
πͺ
*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAΖI SABON KARATU SABON AJI.*
*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA
7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*
*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*
*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*
*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI
π
*
*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU
π
*
*ZO GARE NI:- NA HAJJA
CE
π
*
*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*
*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*
*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*
KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*
SHIRIN
YADDA AKE H
ADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*
SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*
*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MA
TSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*
*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*
GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE
AKAN 500 naira only...Nair
Ι
ari biyal kacal.
*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*
*SAI YA TURA KUDINSA TA*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
*Seka tura shedar biyan kud'in
ka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number
ππΌππΌ
*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*
*Ζ³A
N NIGER
π³πͺ
, ZAKU IYA TURA KUΖINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
2/14/22, 08:44 - Ummi Tandama
π
: *WATA SOYAYYA* β₯
οΈ
π©Έ
β₯
οΈ
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
π‘
(Home of expert & perf
ect writer's)
*TAKUN HASKE BATCH {A} 2022*
Writer: Oum Hanan
From the writer of DR SAIF
π©Έ
Free page
Fiction story
08
Bedroom d'in Mama ta shiga bayan tayi wanka ta gasa hannayenta dasuke mata rad'ad'i ta shafa man zafi sai faman
jera masa ALLAH ya isa take cikin ranta.
"Waya tab'o min autata ne na ganta haka?"
Mama tayi maganar tana kallon Jauhar data b'ata rai kamar wadda zatayi kuka, zama tayi kusa da ita tana fad'in
"ALLAH Mama kiyiwa Yah Abdallah magana kar ya k'ara yimi
n irin haka wllhy".
"Me kuma yayi yanzu shida kullum sai ansamu laifin da akace yayi?".
Cikin tura baki tace
"Kawai fa yazo ya sameni da Saleem yazo ya wani zauna tsabar neman fitina ya hanamu sakat harda zuba drink yasha da snack saida yaji yace zai
tafi fa sannan ya tashi ya bar wajen".
Kai kawai Mama take girgizawa kafin tafara dariya.
"Mama dariya ma kikeyi?". tace tana tura baki kamar zata saki kuka.
"Abin ne ya bani dariya Jauhar lamarin Abdallah sai dua'e tun yana k'araminshi haka ake
fama dashi wllhy da rawar kai shikuma haka ALLAH yayi shi".
"Ni Mama ba ruwana da wani rawar kanshi kawai ayi masa magana ya daina shiga harkata wllhy".
"Taya kuwa zai daina shiga harkarki yana d'an uwanki zanyi masa magana dai ai ba'a haka tashi ki
je".
Tashi tayi ta fita daga bedroom d'in tana faman cika tana batsewa.
Washegari.
4:30pm.
Wasu y'an mata na hango a falon su Jauhar su uku kowacce taci ado na kece raini dukansu kyawawa ne masha ALLAH, gabansu kayan ciye ciye ne kal
a kala da lemuka.
Jauhar na hanga tana saukowa daga upstairs taci kwalliya cikin shadda ash color doguwar riga datasha aikin stone work sai walwali take d'aurinta data saba na malha siririn gyale data nad'e kanta dashi red colour sai takalmin k'afarta
Tom's shima red sai sauran abubuwan datayi using dasu irin su sark'a d'an kunne da abin hannu da zobe da agogo duk red colour ne tayi kyau k'warai masha ALLAH duk da dai ba wata kwalliyar kirki a fuskar tata powder ce kawai da kwalli sai lipgloss da eye sh
adow kad'an data goga saman idanunta ash color sai zuba daddad'an k'amshi take, hannunta rik'e da wayarta.
"Hi guys get up". ta fad'a lokacin data k'arasa saukowa downstairs d'in.
"Wow! kinyi kyau sosai fa Jauhar". d'aya daga cikinsu mai suna Abeeda
h ta fad'a kafin sauran ma su fara yaba kyawun datayi bayan sun tattashi tsaye cikin murmushi tace
"Thank you so much my friends". tayi maganar tana shiga gabansu tareda d'aga wayarta suka shiga yin selfie, kaloli daban daban sukayi sannan kowa ta d'auk
i bag d'inta suna shirin tafiya. ALLAH ALLAH take subar gidan kafin wannan mai almatsutsan yadawo yazo yawani tare musu a gida ya takura musu kawai.
A hankali yake takowa zuwa cikin falon yana sanye da riga da wando farare k'al rigar mai gajeren han
nu hakan yabawa cikakkun fararen damatsen shi damar fitowa k'afarshi sanye da bak'in boot Rolex watch ne black color d'aure a tsintsiyar hannunshi sai bak'ar P cap d'inshi ta gado dake sanye a kanshi, cikin takunshi na mai cikakkiyar lafiya ya shigo falon
kanshi a k'asa yana danna waya sai d'aya hannun daya sokeshi cikin aljihun wandon, cak ya tsaya yana kallonsu lokacin daya gansu suma d'in tsayawar sukayi suna kallonshi dukansu lokaci d'aya suna yaba kyau da tsari irin na gayen a zuciyoyinsu, Jauhar kam t
uni tayi kicin kicin da fuska dan bataso yace zai kawo mata k'auli a gaban k'awayenta tasan k'aramin aikinshi ne yace ba inda zata fita, kamar yasan abinda take tunani kuwa ya shiga takowa inda take bayan ya zura wayarshi a aljihun wandonshi, wata irin tsa
yuwa yayi yai bake bake a gabanta ya soke hannu d'aya a aljihu yayin da d'ayan kuma ya dafa bayan wuyanshi yana kallon Jauhar data had'e rai tana tura baki sudai k'awayenta Abeedah da Maryam da Ameerah tsaye sukayi suna kallonsu, cikin tsare gida yace
"
We're are you going?". kai ta juyar tana tura baki gabanta sai fad'uwa yake tsoronta d'aya kar ya dizgata gaban su Abeedah.
"I said we're are you going?". ya fad'a cikin d'aga murya yana k'ara matsawa daf da ita, baya ta d'an ja cikin tura baki tace
"Bikin friend d'inmu zamuje".
"Bikin friend d'inku?". ya maimaita yana mata wani irin kallo.
Kai kawai ta d'aga masa tana satar kallon su Maryam da suka maida gaba d'aya hankalinsu kansu suna mamakin waye kuma wannan? sudai Ja'afar kawai suka sani a mats
ayin yayanta to waye wannan kyakkyawan handsome man d'in?.
"To bazaki ba". ya fad'a kanshi tsaye.
"What?". Tace cikin yatsina fuska tana d'an hararar shi.
"Baki buk'atar maimaici kinji me na fad'a, kewai baki gajiya da yawo ne uban me kike fita ki
yi a wajen?". Dire diren k'afafu tafara kamar zatayi kuka take fad'in ita wllhy saitaje, Ameerah datafi sauran son iyawa da neman suna ta matso inda yake cikin kwarkwasa da yanga tana wani kashe murya tace
"Please mai kyau a taimaka a bar k'awarmu taje
mana bawani dad'ewa zamuyi ba, uhmm?".
Inda take tsaye ya juyo ya kalleta sama da k'asa yace
"Wace ke?".
"I'm Ameerah Muhammad Ali Jauhar is my best friend".
"Ware daga nan to uwar shisshigi ko kinji nasaki a maganata". kunya ce ta kama Ameer
ah sosai jin abinda yace mata, a kunyace ta koma gefen da sauran suke tsaye tanajin tamkar ta nutse k'asa saboda kunya wane irin mutum ne wannan?
Kallon Jauhar yayi datake ta faman jijjige jijjigen jiki tana itafa bai isa ya hanata fitaba,yana shirin m
agana Hajiya Yaya ta shigo falon jin maganganu.
"Meyake faruwa ne anan naketa jin surutai d'an lazumin danake ma kun hanani". kafin ta k'araso wajen Jauhar ta k'arasa wajenta tana fad'a mata Yah Abdallah ne yace wao bazata fitaba.
"Yau naji jaraba,
waikai Modibbo meyake damunka ne? kai a rayuwar duniyar nan idan baka takurawa yarinyar nan ba bakajin dad'i akan wane dalili zaka hanata fita?". cikin fad'a tayi maganar suna k'arasowa inda yake tsaye itada Jauhar d'in data fara matso k'wallah.
"Sabod
a bai dace taje wajen ba". yace yana kallon Hajiya.
"To saitaje kuwa inga mai hanata fita dan k'aniyar mutum haba wannan bala'i har ina kai idan bakaja abinda aka tada jijiyar wuya ba bakajin dad'i ku wuce kuyi tafiyarku inga mai hanaki".
"Yeeee I
love you so much Hajiyata muaahhhh". ta fad'a cikin murna tana sakarwa Hajiya kiss a kumatunta.
"Wuce kuje ALLAH ya kiyaye". Hajiya ta fad'a tareda juyawa ta koma d'akinta tana cigaba da mita.
Gaba su Maryam sukayi suka fita falon, ta kusa dashi Jau
har tazo ta wuce tana wani taku d'ai d'ai tana yatsina fuska saidata harareshi sannan sannan ta fita.
"I like this". ya fad'a yana wani murmushi gamida fad'awa saman kujera.
A motar Abeedah da sukazo a ciki suka fita, Abeedahn ke driving sai Ja
uhar a front seat Maryam da Ameerah a back seat, suna d'aukar hanya suka fara tambayar Jauhar dan ALLAH waye wannan? sai santin shi suke suna ya burgesu wllhy harda Ameerah wadda gayen yayi matuk'ar tafiya da ita duk da irin gwanya mata d'in datayi.
Cik
in tab'e baki tace
"Hmmm wlhy yaron k'anwar Mama ne yazo ya gallabeni bayajin magana wllhy ni kad'ai ke taka mashi birki dan ni bana yarda ya nunamin wani iko da Saleem yazo ma kinsan meyayi masa kuwa? Kai suka girgiza gaba d'ayansu anan tabasu labarin ya
dda akayi ranar dariya sukasa gaba d'aya Abeedah harda dukan sitarin motar tana fad'in
"So funny, amma dai wannan gayen yasan takan tsiya wlhy amma fa very very handsome guy ne wllhy ya had'u over".
"Bakiji komaiba indai Yah Abdallah ne wllhy". Nan
ta shiga basu labarinshi aikuwa sukaita dariya suna fad'in wllhy yanayin actions d'inshi na burgesu daga yadda take basu labarin nashi. Har suka kusa k'arasawa hirar Abdallah suke ita Jauhar ma shiru tayi ta k'yalesu kafin daga bisani kuma su fad'a wata hi
rar daban.
Wajen Hall d'in da ake kamun k'awar tasu suka isa, tayi parking suka fiffito suna shirin shiga cikin Hall d'in Maryam ta dafe k'irji tareda k'walalo ido ta tsaya tana kallon can gefen Hall d'in daba kowa a wajen, suma tsayawar sukayi su
na mamakin abinda ya tsayar da ita d'in
"Wai meye kika tsayar damu anan Maryam? mu shiga ciki mana". Abeedah tayi maganar tana kallon Maryam dan su duk hankalinsu baikai kan abinda Maryam d'in tagani ba.
"Wancan ba Yah Abdallahn da muka gani a gidan
ku bane da kike bamu labarinshi ba".
Duk kallon inda take nuna musu sukayi aikuwa idanunsu suka hango musu Abdallah d'are d'are a saman motarshi harda wani kishingid'a hankalinshi kwance kayan d'azu ne dai sai bak'in glass kawai daya b'oye k'wayar idan
unshi dashi sai jefa car key d'inshi yake sama yana cafewa, gaba d'ayansu saida gabansu ya fad'i musamman Jauhar suka zaro ido suna kallonshi mutum saikace aljani yaushe yazo wajen nan kuma ya akayi yasan inda zasuzo?
Durowa yayi daga kan motar ya zar
e abin sauraron dake mak'ale a kunnenshi ya ratayashi a wuyanshi ya k'araso inda suke tsaye cirko cirko kamar zakaru
π€£
sai wani d'an banzan murmushi yake yana tsotsar baki.
"Surpriiiise". ya fad'a lokacin daya k'arasa daf da Jauhar, da bak'in ciki kamar
zai kasheta. Had'e rai yayi kamar bashi ke murmushi yanzu ba ya kalli Jauhar yace
"Wuce mutafi gida".
Sanin halinshi datayi shi wani tutsu da bore da mutum zaiyi bayi masa sukeba yasa tayi tunanin kawai bari ta bishi ta lalama yadda zai barta dan ha
ka ta kwantar da murya a marairaice tace
"Dan ALLAH Yah Abdallah kayi hak'uri I promise you bazan dad'e ba zan koma gida dan ALLAH".
"Da zan barki da banyi wahalar zuwa nan ba oya let's go malama".
"Please Yah Abdallah". tace kamar zatayi kuka ta
na karyar dakai.
Hannayenshi ya zube duka cikin aljihun wandonshi ya k'ara matsawa daf da ita ya had'e rai sosai yace
"Zaki wuce muje ne kokuwa sokike saina d'auke ki yanzu a gurin nan?". Ganin abinda yayiwa Ameerah d'azu yasa yanzu sukayi gum dasu b
a wadda tayi k'ok'arin tanka masa karya dizgasu gaban bainar jama'a.
"Naga alamun d'aukar kikeso ko". Yace yana k'ok'arin sunkuyawa tasan kad'an daga cikin aikinshi ya sungumeta yasa tayi saurin matsawa ta fara tafiya a fusace dan takaici harda k'walla.
Mrs Salees Mu'az
π
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*
πͺ
*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAΖI SABON KARATU SABON AJI.*
*INDA SUKA ZO
MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*
*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*
*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*
*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI
π
*
*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY
B ALIYU
π
*
*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE
π
*
*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*
*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*
*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*
KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DE
EJARH BERVER*
SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*
SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*
*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA
SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*
*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*
GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA
. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair
Ι
ari biyal kacal.
*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*
*SAI YA TURA KUDINSA TA*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Sa
lis
*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number
ππΌππΌ
*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZAT
A BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*
*Ζ³AN NIGER
π³πͺ
, ZAKU IYA TURA KUΖINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
2/14/22, 08:57 - Ummi Tandama
π
: *WATA SOYAYYA* β₯
οΈ
π©Έ
β₯
οΈ
*HASKE WRITER'S AS
SOCIATION*
π‘
(Home of expert & perfect writer).
*TOP TEN TAKUN HASKE BATCH A 2022*
_Sa kud'i kad'an ki debi hani'an
ππ
_
Writer: Oum Hanan
From the writer of DR SAIF
π©Έ
Free page
Fiction story
*Na sadaukar da wannan page d'in ga d
uk wani masoyin book din nan wanda nasani da wanda ban saniba alkhairin ALLAH ya kai muku a duk inda kuke nagode ALLAH ya saka da alkhairi β₯
οΈ
π©Έ
β₯
οΈ
*.
_Gaisuwa ta musamman ga kungiyata ta haske da duk wani member dake cikinta ALLAH ya barmu tare ya k'a
ra dank'on zumunchi Ameen
ππ
π₯°
_
```Sak'on gaisuwa daga Abdallah yace a sanar daku masu zaginshi da masu cewa bashida hankali duk yana nan juyowa gareku
π
yanaso yagama da Jauhar ne ya dawo kanku saikun jishi lol.
Sako daga Abdallah Madugu (Mo
dibbo).```
10
Dariya Ja'afar yayi yace
"Abu d'aya ne kawai a sameta a bata hak'uri kawai".
Cikeda rainin hankali yace
"Waye zai bata hak'urin?".
"Waye kuwa banda kai". Ja'afar ya mayar masa da amsa.
"Saidai inci ubanta dai wlhy
amma bazan bata hak'uri ba taimin laifin kuma inbata hak'uri?".
"To yazaka yi? haka nan zaka daure yanzu dai bari inje in fad'awa Mama". nan Ja'afar ya fita yabar Abdallah sai faman cije baki yake yana sakin k'wafa.
Koda Ja'afar yaje ya fad'awa Mam
a abinda Jauhar tayi ranta b'ace ta nufi bedroom d'in Jauhar ta shiga bugawa