Showing 54001 words to 57000 words out of 96447 words
hidimar ta.
Mrs Salees Mu'az
💝
3/2/22, 19:29 - Ummi Tandama
😇
: *WATA SOYAYYA*
💝
Page 30
Paid book
Oum Hanan
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*
^^√^^√^^√^^
"Saukomin dashi nan k'asa". ta tsinkayi muryar shi cikin kanta, amsawa tayi tareda tashi ta nufi dinning d'in shikuma ya cigaba da danne dannen waya.
Saidata sh
imfid'a sabuwar leda sannan ta jera masa komai a kai tana shirin barin wajen taji yace
"Nizan had'awa kaina kike nufi kokuwa?". juyowa tayi ta kalleshi taga har lokacin wayar yake kallo, dawowa tayi ta had'a masa tea ta zuba masa Irish d'in data soya da
stew d'in hanta sai wainar k'wai.
K'asa ya sauka ya tank'washe k'afafunshi yafara karyawa, Janaan dai tana rakub'e a gefe ta sunkuyar da kanta tanajin kanta duk wata iri kamar ba ita ba.
"Kinyi breakfast ne?". taji amon muryar shi yana tambayar ta.
Kai ta girgiza masa da sauri kuma tace
"A'a" ganin irin kallon dayake mata na zaici k'aniyarta.
"Taso kizo kiyi". abinda yace kawai kenan ya cigaba da juya tea d'in dake cikin mug, tanaso tayi masa musu tana tsoro dan sam batajin yunwa haka dai ta ma
tso ta zauna tafara had'a tea d'in itama haka ta dinga sha kamar bataso shikuma bai k'ara bi takan taba yana gamawa ya tashi yabar wajen.
Wajen ta gyara bayan tagama tayi wanke wanke ta k'ara gyara kitchen d'in sannan ta koma bedroom d'inta ta zauna tay
i shiru ita kad'ai duk kewar Ammi dasu Hassana ta cikata, tana nan zaune taji tashin motarshi daga cikin compound ta window ta lek'a taga ya fice daga gidan, dawowa tayi ta zauna ta cigaba da sak'e sak'e cikin zuciyarta.
Ba laifi tasha bak'i a ranar dan
akwai y'an uwansu na wajen uwa dana uba duk sunzo sun k'ara ganin gida da wad'anda ma basu samu zuwa ba a jiya da aka kawota, hakan ya d'ebe mata kewar datake fama da ita na kad'aitaka.
√√^^√√^^√√^^√√
Sai bayan sallahr Esha'e sannan Abdallah ya daw
o gidan lokacin tagama komai ta gyara gidan inda bak'in dasukazo aka b'abb'ata tayi wankanta ta shirya tsaf cikin wani yadin material mai rawa riga da wando rigar iya gwiwarta rapper blue black ne yadin da akayiwa ado da k'ananun flowers orange color tayi
rolling da k'aramin gyale kalar kayan tayi matuk'ar yin kyau duk da dai bawata kwalliyar kirki bace a fuskarta amma tayi kyau ainun, sai k'amshin turaruka masu dad'in gaske take wanda ya had'u dana asalin fatarta yabada wani kalar k'amshin mai dad'in shak'
a.
Sama sama ya amsa mata sannu da zuwan datayi masa ya wuce side d'inshi, bai dad'e ba sosai ya fito cikin riga da wando marasa nauyi na shan iska farare tas yanata k'amshi da alamu wanka yayi.
Ganin d'azu da safe yace ta sauko masa da breakfast k
an carpet hakan yasa yanzun ma tafara k'ok'arin dawo masa dashi k'asan nan kuma yace tabar masa shi akan dinning d'in ta d'auka ta k'ara mayarwa wato shidai ba'ayi masa gwaninta haka halinshi yake.
Kamar dai yadda Abdallah yayi alk'awarin bazai d'a
gawa Janaan k'afa ba hakan ce ta faru kuwa a daren ranar ya maida Janaan cikakkiyar mace tasha matuk'ar azaba a hannunshi duk da yadda taso daurewa hakan ya
gagara dan sosai tasha kuka abinta hakan kuma baisa ya sarara mata ba dan tamkar ma tana k'ara ingi
zashi ne.
Ta b'angaren Abdallah kam yayi matuk'ar farin ciki da yadda yasamu Janaan kuma ta kaishi wata duniya ta daban wadda bai tab'a shigarta ba kuma tasamu babban matsayi a cikin zuciyarshi. Sam batayi tsammanin samun rarrashi daga gurinshi ba bayan
wakanar komai amma ga mamakin ta sai taga ya zage yanata rarrashi da ban baki bayan ya k'ara shigar da ita jikinshi sosai, ganin haka tasamu damar k'ara shigewa jikinshi tanajin wani irin sanyi na ratsa zuciyarta duk da kuwa rad'ad'in dake ziyartar ta ta
k'asanta wanda take jin tamkar an watsa mata barkono.
A wannan daren suka tsarkake jikinsu sannan suka koma barci tana jikinshi duk da dai a d'ar d'ar take dashi dan tasan yanzun nan zai canza kamar bashi ba shiyasa take baya baya dashi.
******
Number Jauhar ta kira Janaan ta kira dan jin dalilin dayasa har yanzu batazo taga inda take ba tarasa meke damun y'ar uwar tata haka, tana picking kuwa ta sakar mata kuka, sosai Jauhar ta shiga tashin hankali ta shiga tambayarta abinda ya faru take kuka ha
la itada wannan mijin nata ne mara alk'ibla cikin kuka Janaan tace
"Ni karki k'ara sa mijina a ciki ba ruwanshi kuma inajin dad'in zama dashi".
"A hakan?". Jauhar ta fad'a cikin zaro ido kamar tana gabanta.
"Eh a hakan nakeji". Janaan ta fad'a tan
a share hawayen fuskarta, baki Jauhar ta tab'e tace
"Sannu fa, ALLAH ya had'aki da aiki wllhy nidai yanzu fad'amin abinda ya saki kuka malama".
Ajiyar zuciya Janaan ta saki tace
"Amma saboda ALLAH kin kyautamin kenan Bloody ba'a kawoni dake gidana ba
kuma har yanzu bakizo kinga inda nakeba why? meyasa kika tsani aurena da Yah Abdallah ne har haka Bloody?". ta k'arasa maganar cikin sanyin murya sosai.
"A'a fa karki k'alamin sharri malama yaushe nace banason aurenki dashi? bake kikaji kika gani ba in
a ruwana ni".
"To naji yanzu yaushe zakizo dan ALLAH". Janaan tace.
"Gobe dama zamu shigo dasu Hassana dan zuwa jibi nakesa ran komawa Ammi ce ma ta tsayar dani da tuni natafi wlhy". cikeda farin ciki Janaan tace
"ALLAH ya kaimu goben dan ALLAH ku
zo da wuri Bloody wllhy nayi missing dinku over".
"Insha ALLAH". Jauhar ta fad'a sannan suka katse kiran a tare.
Washegari tun sassafe Janaan ta fara shirye shiryen tarbar su Jauhar jitake tamkar taje ta taho dasu, dama da wuri Abdallah ya fita ranar
. Ganin shiru shiru har kusan sha biyu na rana basu zoba hakan yasa ta kira layin Hassana ta tambayeta ko sun fasa zuwa ne tanata jira tun d'azu tace gasu nan yanzu suka fito driver zai kawosu sai lokacin taji dad'i a ranta dan duk zaton ta sun fasa zuwane
.
Da sauri ta nufi k'ofa lokacin dataji ana knocking ko tsayawa tambayar waye ma batayi ba ta bud'e cikeda tarin farin ciki da Jauhar ta fara cin karo cikin tsananin murna ta rungumeta kafin sukayi joining gaba d'ayansu dasu Hassana suka rungume jun
a ALLAH nagani sunyi masifar kewar y'ar uwar tasu, daga nan kuma suka rankaya suka shiga cikin falon suka zazzauna sam bakunansu sun kasa rufuwa musamman ma Janaan nan fa suka
shiga hira baji ba gani da k'yar ma ta tashi ta kawo musu abin tab'awa suka d'or
a daga inda suka tsaya bayan sunje sun zazzagayo gidan sun k'ara gani.
Gaba d'ayansu suka shiga kitchen lokacin lunch, ganin sunada yawa
yasa suka tarki yin sakwara aikuwa cikin k'ank'anin lokaci suka kammala ta da miyar ganye ragowar doyar da suka k
irb'a kuma sukayi yam balls sai had'add'en kunun aya da kwakwa da sukayi suka jera komai bisa dinning table bayan sun gyara kitchen d'in sannan sukaje sukayi sallahr Azhar da aka kira tun d'azun banda Jauhar datake fashin sallah. Bayan duk sun idar suka ha
u kan dinning dan yin lunch sunaci suna hira har suka gama suka gyara kan dinning d'in suka k'ara bajewa nan cikin falon suka cigaba da hirarsu.
K'arar bud'e k'ofar falon ce tasa duk suka maida hankalinsu kan k'ofar da aka bud'e, Abdallah ya bayya
na sanye cikin riga da wando farare na kamfanin POLO takalmin k'afarshi ma POLO shima fari kayan sunyi matuk'ar amsarshi yayi kyau ainun, tuni falon ya d'auki shiru kamar basu bane masu dariya da shewa saboda dad'in hira, kauda kai Jauhar tayi tana wani me
le baki kamar wadda taga kashi.
A hankali ya shiga takowa har zuwa tsakiyar falon sannan ya tsaya tareda bud'e hannayenshi yana kallon Janaan da bata fahimci abinda yake nufiba sai kallonshi da itama take yi.
"Taso mana". yace yana murmushi gamida w
are manyan idanunshi akan Janaan, tanaso tayi masa musu ga kuma tsoro fal cikinta ga kunya data dabaibayeta haka dai ta tashi kamar kazar da k'wai ya fashewa cikin ciki ta nufeshi kanta a k'asa tana zuwa tayi yunk'urin tsugunawa shikuma ya hanata ta hanyar
kamota ya sanyata cikin k'irjinshi ya maida hannayenshi ya rufe, lamo tayi tareda lumshe ido tana shak'ar daddad'an k'amshin dake tashi a jikinshi wani sanyi na ratsa zuciyarta wanda ya aikawa dukkan sassan jikinta, Hassana da Hussaina kam tamkar zasu nut
se tsabar kunya data mamayesu duk k'asa sukayi da kansu dan bazasu iya ganin wannan tab'arar ta Yah Abdallah ba, Jauhar ma da akayi sa'a ta waigo da kanta inda suke tsaye suka had'a ido da Abdallah dayake ta wani lumshe ido yana bud'ewa hannu ya d'aga mata
tareda d'age mata gira yana wani munafukin murmushi tareda shafa bayan Janaan da d'ayan hannun, wani k'ululun bak'in cikine yakama Jauhar tamkar ta tashi ta kama dukansu da duka takeji, k'aramin tsaki kawai taja tana tab'e baki ta k'ara maida kanta inda y
ake da farko, kan Janaan ya d'ago yana fad'in
"Daga yau irin wannan oyoyon nakeso koma a gaban waye kinji HASKEN ANNURI". Kai kawai Janaan ta d'aga masa ba kuma dan zata iya d'inba sai dan gudun laifi, gefe d'aya na zuciyarta kuma mamakin sunan daya kir
ata dashi take uwa uba kuma dad'in da sunan yayi mata.
Hannunta ya kamo har zuwa inda su Jauhar suke zaune, har lokacin Hassana da Hussaina basu d'ago kansu ba a hakama suka gaisheshi ya amsa sama sama, Jauhar kam dama batayi niyyar gaisheshi d'in ba y
aja hannun Janaan.
"Mtsww, kunya tayi a rayuwa gaskiya kuma wanda baida ita baiji dad'in shiba wlhy". kunnenshi ya d'auko masa sautin muryar Jauhar ta fad'a k'asa k'asa, murmushi yayi tareda sakin hannun Janaan yadawo inda Jauhar take zaune rank'wafawa
yayi samanta cikin d'age mata gira yace
"Yadai yarinyar nan kamar kinajin ba dad'i fa".
Waigowa tayi ta sakar masa wani irin kallo tace
"Kamar ya inajin ba dad'i akan wane dalilin?".
Baki ya tab'e tareda d'age kafad'a alamun shima bai saniba,
tsaki Jauhar ta saki cikeda k'unar rai, murmushi yayi ya tashi yabar wajen ya koma inda Janaan ke tsaye ya kama hannunta suka nufi side d'inshi.
Tunda ya dawo ya hana Janaan sakat tanaso ta fito wajen su Jauhar ya hanata sunyi bulunbuk'wi a d'aki ba da
mar kuma ta fito ta barshi. Su kad'ai suka cigaba da hirarsu duk da dai can cikin k'asan ran Jauhar abin ya k'ona mata rai wanda batasan dalilin jin hakan ba.
Sai lokacin da aka fara kiraye kirayen sallahr Asr sannan suka fito.
Mrs Salees Mu'az
💝
3/5/22, 18:40 - Ummi Tandama
😇
: *WATA SOYAYYA*
💝
Page 31
Paid book
Oum Hanan
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*
Yayi shirinshi na zuwa masjeed jallabiyyah black color sai k'amshi yake, lokacin suma su Jauhar sun tashi da niyyar zuwa yin sallah
r akayi sa'a idanunsu suka had'u ya kashe mata ido kuwa yana wani murmushi data kasa fassarashi ya fice daga falon.
Tsaki kawai taja ta juya ta nufi bedroom danyin alwalah duk suka bita da kallo kafin suma su mara mata baya.
Daya dawo daga masallacin
ma ba wanda ya nema ya shige side d'inshi ya rufe.
Sai daf da sallahr magreebah sannan su Jauhar suka tafi cikeda alhinin rabuwa Janaan harda y'ar k'wallarta.
√√^√√^√√^√√^√√
A gurguje please
🙇
.
Kwanaki sunci gaba da gangarawa inda kai tsa
ye Janaan bazatace tanajin dad'in zama da Abdallah ba hakama bazatace bataji ba saboda shi wani irin juyayyen mutum ne mai wuyar ganewa bashida hagu bare dama sau tari abune zatayi masa na kyautawawa amma saiya juya abun ya maidashi baibai yazama laifi a w
ajenshi amma duk da haka dai bata gaza ba kuma bata fasa yimasa d'in indai ta tabbatar tayine dan ta kyautata masa kuma tanada lada a gurin ALLAH duk wani abu da zaiyi baya damunta.
Babu wata sakewa a tsakaninsu sosai kuma ta kasa daina tsoronshi wanna
n kam a jinin jikinta yake bata saniba dai ko nan gaba.
Ta cigaba da zuwa school d'inta, kullum tare suke tafiya saiya ajiyeta sannan ya wuce office idan antashi kuma tadawo a napep ranar da y'an kirkin kuma suke kanshi saidai ta ganshi kawai yaje d'auk
arta.
******
Jauhar dai ansamu matsala tsakaninta da Saleem kuma bawani abune ya had'asu ba kawai dai mahaifinshi ne ya nuna ra'ayin aura masa d'iyar k'aninshi lokacin dashi Saleem d'in ya gabatar da Jauhar a gurinsu a matsayin wadda yakeso ya aur
a.
Yaji ba dad'i sosai kuma yayi iya bakin k'ok'arinshi wajen ganin mahaifin nashi ya barshi ya auri zab'in ranshi amma fur Alh Kabiru yak'i farko yaso ya bijire daga baya kuma da ya hak'ura.
Ga mamakin Jauhar sam bata wani damu da rabuwar tasu ba d
ama can batajin wani feelings a kanshi batasan meyasa ba kawai dai suna soyayya ne har wani lokacin takan zauna tayi ta tunanin meyasa batajin sosai cikin ranta kuma yadda take tuna Abdallah shi bata tunanin haka duk da dai aduk lokacin data tuna Abdallahn
saitayi tsaki saboda yadda yake shiga harkarta ya takura mata koda yake yanzu abin ya ragu sosai ba kamar da ba tarasa dalilin dayasa take yawan tunawa da wannan d'an buyagin mutumin.
*NOTE* I'm sorry reader's! nasan da yawanku kunso kuji irin rayuwa
r da za'ayi a gidan Abdallah Madugu tsakaninshi da Janaan da irin dramar da za'a buga saidai kuma dole in tak'aita saboda tun farko an tsara kowa zaiyi gajeren labarine ta yadda masu karatu zasu karanta cikin marmari batare da abin ya gunduresu ba, kuma mu
gama cikin lokaci so shiyasa na tak'aita shi ba lallai saina fito nace ga abinda ya faru a gidan ba anyi kaza kaza kawai dai inaso ku kimanta a cikin ranku ku k'iyasta maza masu hali irin na Abdallah duk da dai nasan basuda yawa amma dai za'a iya samu ya a
uri mace mai hak'uri da kawaici irin yadda zaman zai wakana da irin hak'urin da zatayi basai lallai na fito na bayyana komaiba saboda hakan zai daukemu lokaci mai tsawo gaskiya kuma ba'a son hakan ta kasance fatan zaku duba mun gode sosai da had'in kanku w
ajen yimana comments ALLAH ya sakada alkhairi ♥
️
.
Nagode.
Bayan wasu watanni.
Zaman Abdallah da Janaan yayi dad'i sosai Janaan tayi matuk'ar k'ok'ari wajen ganin ta canza Abdallah kuma alhmdulillah cikin kaso 100 ya rage wajen kaso 80 na abubu
wan dayake ita kanta tayi mamaki k'warai amma idan ta tuna irin jajircewar datayi saitaga hakan ba abin mamaki bane dan sai datayi ta maza ta rage tsoronshi hakan yasa idan taga yayi abinda ba daidai ba harta gyara masa tun yana d'ura mata zagin daya saba
yimusu da masifa da buyaginshi daya saba harya dawo ya fara d'auka ganin bata fasa ba.
Cikin lokaci k'ank'ani Janaan ta siye zuciyar Abdallah tsaf da kyawawan halayenta gamida ladabi da biyayyar datake masa tasamu babban matsayi cikin zuciyarshi wanda
bai tab'a tunanin zata sameshi a gurinshi ba,haka itama Janaan d'in mamaki take ganin yadda Abdallah ke nuna mata tsananin kulawa da soyayya wadda bata tab'a samunta a wajen rikitaccen mutum irin Yah Abdallah ba sai gashi kuma komai yazo mata da sauk'i ba
yadda tayi zatoba tasan kuma hakan bazai rasa nasaba da yadda ta dage da addu'o'e ba dama ance addu'a takobin mumini tayi yak'inin da bata had'a addu'a ba zaman nasu sai a hankali duk da dai farkon auren tasha wahalar shi, a yanzun ma bawai ya daina bane g
aba d'aya ance mai hali baya fasa halinshi ana d'an tab'awa
😀
.
Ta b'angaren su Ammi ma abin ya basu mamaki ganin Abdallah yana zaune lafiya da matar da suka zab'a masa koda yake y'an uwa da dama basu yi zaton hakan ba ALLAH natuba Abdallah ko wadda ya
keso ce ya zab'a da kanshi ai zamansu sai addu'a bare kuma wadda ba zab'inshi ba, daidai da sau d'aya bata tab'a kawo masu k'arar shiba kuma kallo d'aya zakayi mata
kasan tana cikin kwanciyar hankali da nutsuwa abin ya matuk'ar yimusu dad'i suka cigaba da
binsu da addu'ar zaman lafiya mai d'orewa da tarin albarka a rayuwar su.
Har zuwa yanzu Jauhar tak'i sakarwa kowa fuska danyin soyayya da ita, duk da yadda samari ke bibiyarta tak'i ba kowa dama haka nan take jin tagama soyayya a duniya duk wanda zasu h
ad'u dashi yayi mata maganar soyayya saitaga baiyi mata ba bai kuma kai quality'n irin namijin datake da burin aure ba dan haka ta ajiye maganar soyayya a gefe ta maida hankalinta kacokam kan karatun ta. Kullum ta ALLAH sai sunyi waya da Janaan idan ita Ja
naan d'in bata kiraba ita Jauhar d'in zata kira danjin lafiyar juna.
********
★★☿
Janaan na hanga zaune a falonta dayasha gyara sosai sai k'yalli yake yana tashin k'amshi tako ina, Sosai nake k'are mata kallo ganin yadda ta k'ara kyau sosai
kan wanda take dashi ada hasken fatarta ya k'aru sosai kuma fatar ta k'ara