Showing 6001 words to 9000 words out of 96447 words
da niyyar komawa inda ta fito taji yace
"Come here dan u
banki". a haka yayi maganar batare daya d'ago kaiba.
"Innalillahi wa inna ilaihi rajioun, wllhy sam ta manta yau mutumin nan zai dawo da gidan Aunt Deejah zata wuce inyaso ta dinga zuwa school d'in daga can.
Kamar kazar da k'wai ya fashewa a ciki
ta fara takowa inda yake kanta a k'asa tana wasa da yatsun hannunta, gefe tasamu ta tsuguna a hankali cikin sanyin muryar ta dayake halittarta tace
"Yah Abdallah sannu da zuwa".
Sipping d'in lemon dayake sha ya k'ara yi sannan batare daya d'ago daga k
allon wayar dayake ba yace
"Sai yanzu kikaga damar yimin sannu da zuwan dan ubanki? tun k'arfe nawa na dawo gidan nan saboda bakida mutunci ko?
Ji take tamkar tasaka kuka, ta tsani wannan zagin dayake musu wllhy gashi hakan kamar wata d'abi'ar shic
e ya zagi mutum shiba komai bane a wajenshi.
A marairaice tace
"Wllhy Yah Abdallah bana gidan tun 7@m natafi school sai yanzu nadawo".
Zaune ya tashi ya aje lemon kan k'aramin center table dake gefen kujerar dayake zaune, crossing legs d'inshi yay
i yana kallonta yaga kanta a k'asa.
"Munafuka, nasan har cikin ranki bakiso nadawo gidan nan ba ko? so kikayi flight d'in ya tarwatse dani a sama ko? muguwa".
Haka ALLAH ya yita da saurin kuka hakan yasa yanzun ma hawaye suka taru cikin idanunta s
aidai bata barsu sun kai ga zubowa ba dan suma d'in idan yagani saiya sauke mata wani bala'in nashi, ko wanda ba musulmi ba dai bazata yimasa wannan fatan ba bare shi dayake matsayin musulmi kuma d'an uwanta na jini sai neman jafa'in tsiya ya iya dan wanna
n neman jafa'ine wani time d'in idan yasaki magana fitar tusa ma tafita dad'in ji wllhy. Ganin yadda ya tsura mata ido yasa ta girgiza kai tace
"ALLAH Yah Abdallah ba haka bane".
"Koma dai meye nadawo fece daga wajen nan". Tashi tayi ta koma bedroom h
aka ta matse yunwarta saidata lek'o taga ya fita sannan taje ta zuba abincin bata zauna a falon ba ta shige bedroom a can taci abincin.
^√^√^
∿
Da dare Habeeb yazo ya d'aukeshi suka fita suka d'anyi yawo sukaga gari, gari ya gansu, sai wajen k'arf
e 10pm Habeeb ya dawo dashi ya tafi. Sai a lokacin suka gaisa da Abbie.
Tunda ya dawo ya hana su Janan sakat gashi haka zai baro part d'insu yazo yayi zaune a falon duk abinda zasuyi idonshi akai, kuma bazai gani ya k'yale ba saiya tanka, hakan yasa
duk suka daina zaman falon da sun dawo school kowacce zata shige bedroom indai ba dole ce zata fito dasu falon ba.
^√^√^√^√^
∿
Duka baifi sati da dawowa ba yafara shirin zuwa Kaduna gidan yayar Ammi mamansu Janan hajiya Ameenah wadda suke k
ira da Mama, yana matuk'ar son zuwa gidan saboda yadda Mama take nuna masa k'auna yasamu labarin tunda aka haifeshi take nuna masa soyayya ALLAH ya had'a jininta da nashi hakama mijinta Alh Isma'eel yanason Abdallah sosai saboda yana yawan zuwa gidan tun y
ana yaro hakan yasa suka shak'u sosai.
Mrs Salees Mu'az
💝
HASKE WRITERS ASSOCIATION
💡💡💡
TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A
ZAFAFAN LITTAFAI MASU SAKA SHAUK'I, FADAKARWA K'AYATARWA NISHADANTARWA HAR GUDA 7!!!
GA SHIRI NA MUSAMMAN
INA M
ASU SON KOYAN GIRKUNA DA MASU SON KARA SANIN SIRRIN MALLAKE MAI GIDA
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
KUDIN RAJISTA - 500 (NAIRA DARI BIYAR GABA DAYA)
*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*
GARABASA MAI CIKE DA ALB
ARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair
ɗ
ari biyal kacal.
*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*
*SAI YA TURA KUDINSA TA*
2083371244
Zeni
th Bank
Aisha M.Salis
*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number
👇🏼👇🏼
*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA
TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*
*ƳAN NIGER
🇳🇪
, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
2/14/22, 08:41 - Ummi Tandama
😇
: *WATA SOYAYYA* ♥
️
🩸
♥
️
HASKE WRITER'S ASSOCIATION
💡
(Home of expert & perfect writer's)
TOP TEN TAKUN HASKE BATCH {A}
Writer: Oum Hanan
From the writer of DR SAIF
🩸
Free page
Fiction story
04
A ranar dazai tafi bayan ya gama shirinshi ya shigo cikin
falon dan yiwa Ammi sallama shi Abbie tun safe dazai fita sukayi sallama dashi.
Ash color d'in wandone a jikinshi da black color d'in riga round neck mai dogayen hannu wadda ta d'ameshi ta fito da cikakken k'irjinshi, wani siririn abune mai d'an fad'i
na sak'a ash color mai taushi ya nad'e wuyanshi dashi, d'aya yayi gaba d'aya yayi baya, agogon sark'a ne a hannunshi shima kalar ash sai bak'in takalmi dake k'afarshi na zallar fata, ya toshe idanunshi da bak'in glasses k'amshin Arabian perfumes kawai ke
tashi daga jikinshi.
Anan falo ya samu Ammi dasu Hassana harda Janan a d'arare suka had'a baki suka gaisheshi baima amsaba ya zauna kusa da Ammi yana fad'in
"Ammi ni zan wuce".
"To a gaishe mana dasu kwana nawa zakayi?".
"To gani dai Ammi amm
a bazan dad'e ba". yayi maganar yana d'an sosa kanshi da key d'in motarshi dake hannunshi.
"To ALLAH ya kaimu, kadawo dai da wuri kaga ga shirye shiryen bikin d'an uwanka da za'ayi".
"Insha ALLAH Ammi". daga haka ya mik'e tsaye yana jan wandon dake j
ikinshi sama, Ammi ma tashi tayi ganin haka yasa suma su Janan suka tattashi da niyyar rakashi, ganin yadda suketa fara'a yasa har yayi gaba saikuma ya juyo ya kallesu.
D'an yatsanshi manuniya ya d'ora kan bakinshi kamar mai tunani kafin yace
"Kamar
fa murna kuke zan tafi ko?".
Tuni kowacce ta d'inke fuskarta daga yanayin murmushi dasuke a da sukayi saurin girgiza kai
Kad'a kai yayi yace
"Duk zakuci ubanku ne zan dawo ai".
K'aramin tsaki Ammi taja tace
"Dan ALLAH ya isa haka wuce katafi ALLAH
ya kiyaye murna kuwa ai dole suyita a yadda kake takura musu d'in nan".
Saidaya hararesu sannan ya fice daga falon basu bishi bama suka koma suka zauna suna k'usk'us a tsakaninsu itadai Janan tana gefe ALLAH nagani tayi murna da barinshi gidan kafin k
uma ya dawo ya d'ora daga inda ya
tsaya duk rashin son hayaniyar ta saiya samu abinda ya lak'aba mata yace tayi.
Ammi ma daga bakin k'ofar falon sukayi sallama tadawo shikuma ya nufi wajen motarshi da Isya ya goge masa ya shiga saida yayi addu'o'e sanna
n ya tada motar ya fita dama already maigadi ya bud'e masa gate.
Sauka lafiya Abdallah madugu
🤩
.
Ana yin sallahr la'asar ya shiga unguwar, bai shiga gidan ba saida ya tsaya yayi sallah a masallachin dake jikin gidansu Maman sannan ya shiga bayan
an idar, Maman na zaune a falo itada Hajiya Yaya wato mahaifiyar Alh Isma'eel d'in dake zaune a gidan Hajiya Yaya akwai fad'a kuma dama basu cika shiri da Abdallah ba saboda yadda idan yazo yake cin zalin Jauhar gashi y'ar gaban goshinta ce.
Tashi Mama
tayi ta tareshi da murnar ta sam bakinta ya kasa rufuwa Hajiya Yaya kam kicin kicin tayi da fuska ta juyar dakai gefe.
Zama yayi kusa da kujerar da Mama take yana gaisheta cikin farin ciki ta amsa tareda tambayarshi mutanen gidan ya amsa yana kallon H
ajiya Yaya data b'ata fuska, tashi yayi ya nufi wajenta yana dariya gamida fad'in
"Hajjaju ikon ALLAH, wai bakiyi murna da ganina bane? yayi maganar yana zama kusa da ita.
"Banyi ba". ta fad'a kanta tsaye.
Dariyar ya k'ara saki tareda zaro ido na
iya shege yace
"Why Hajiya?.
Banza tayi masa, hakan yasa yace
"Ohhh na manta fa bakyajin turanci, cewa nayi saboda me bakiyi murna da ganina ba".
Mama dai dariya kawai take ta tashi da kanta ta nufi kitchen dan samar masa abinda zaici.
"Ka
fini sani ai fitinanne yanzu zakazo ka takurawa yarinyar nan Johar".
Baki kawai ya tab'e ya tashi ya koma inda ya taso ya zauna yana fad'in
"Shine damuwarki?. K'ala batace masa ba shima saiya tattarata ya watsar, Mama ta fito daga kitchen d'in hann
unta d'auke da tray da warmer guda d'aya sai plate da spoon sai kuma drink da cup, gabanshi ta ajiye da kanta tayi saving d'inshi dambun shinkafa dayaji vegetables da spices sai k'amshi yake tashi kad'an ta zuba masa saboda tasan yanayin cikinshi bai wani
cika cin abinci sosai ba barshi dai da kayan k'walam saikace wani mace, had'add'en lemon ayar dake cikin jug ta zuba masa ta ajiye a gabanshi, itadai Hajiya Yaya sai kallon Mama take tana tab'e baki shiyasa yake tata rashin mutuncin shi yadda yaga dama tun
da duk abinda yayi Maman bata gani, daga k'arshe ma tashi tayi tabar falon ta shige d'akinta.
Abincin yafara ci ya d'auko wayarshi ya kira number Ja'afar, bata dad'e da fara ringing ba akayi picking.
"Yane wai kana inane?". Abdallah ya fad'a bay
an ya amsa sallamar Ja'afar.
"Ka ganni nan a hanyar gida na kusa k'arasowa ka iso ne?".
"Eh mana nazo, saika k'araso d'in".
"Okay Tam". Ja'afar ya fad'a sannan sukayi hang up a tare.
Hira suka cigaba dayi da Mama har lokacin da Ja'afar ya k'ar
aso, hannu ya bashi suka gaisa ya d'auki trolley d'in Abdallah na kayanshi suka wuce part d'in Ja'afar d'in tare.
Dukansu wanka suka k'ara yi suka shirya cikin k'ananun kaya suka k'ara ficewa ganin gari a motar Ja'afar saidai Abdallah ne yake driving.
Yawo sukayi sosai cikin garin daga k'arshe suka yada zango wajen shan ice cream, sun dad'e a wajen suna hira ayi ta arzik'i ayi ta tsiya kuma duk Abdallah ne ke takalar fad'an.
Tafe suke a hanyar dawowar su yanzun ma Abdallah ke tuk'in anci sa
'a a hankali yake tuk'in dan sam Abdallah bai iya bin mota a hankali ba sharara gudu yake yadda ranshi keso.
Da uban gudu wata mota ta taho tamkar zata tashi sama duk yadda Abdallah yaso kauce mata sai data gogi motar su dan dama ya hangota ta mirror,
batare da mai motar ya tsaya ba ya k'arawa motar tashi gudu, a fusace Abdallah ya mulmulo wani uban ashar ya k'unduma masa tare da k'arawa motarsu gudu shima dayake titin ba yawan motoci hakama ba mutane sosai.
Wuta yake bawa motar sosai kamar yadda w
ancan mai motar ma yake k'ara nashi gudun, sai masifa yake yana sakin zagi ganin haka yasa Ja'afar ya fara fad'in
"Dan ALLAH Bros kabari tunda dai ba abinda ya samemu".
Baki Abdallah ya cije yace
"Bazan barshi d'in ba dan ubanka gobe ma yaji dad'i
n yiwa wasu haka".
"Dan ALLAH nace fa kasani ko yanada wani uzurin ne, duk da uban gudun dayake saida ya juyo ya harari Ja'afar kafin yace
"Uzurin yaci ubanshi kasamin ido kawai malam tunda kai banza ne mara zuciya, ido kawai Ja'afar yasa masa yasan
Abdallah farin sani wata magiya da ban baki bayi masa sukeba idan ba niyyar yin abu yayi ba, duk gudun mutumin nan saida Abdallah ya k'ureshi yana zuwa yasha kan waccan motar ya taka wani wawan birki jikake k'uuuuuuu wanda daga shi har Ja'afar saida sukay
o gaba sukayi baya, dan dole motar ta tsaya cikin hanzari Abdallah ya bud'e murfin motar ya fita a fusace ya nufi gurin motar yayin da shima mai motar ya bud'e ya fito daidai lokacin da Abdallah ya k'arasa yana zuwa ya d'aga hannu da nufin kaiwa wannan sau
rayin mai motar mari Ja'afar daya k'arasa wajen yayi saurin rik'e hannunshi yana fad'in
"Dan ALLAH Abdallah kayi hak'uri ayi magana ta fahimta".
"K'yaleshi ya mareni ya marowa kanshi bala'i dan duk danginka sainasa an d'auresu wlhy". wancan saurayi
n ke fad'ar haka yana wa Abdallah wani irin kallo.
Hannunshi ya warce daga rik'on da Ja'afar yayi masa, ya wani kad'a kai tareda sakin wani d'an iskan murmushi ya dafe k'ugunshi da hannu d'aya d'ayan kuma ya shiga nuna k'irjinshi yana fad'in
"Ni? n
i zakasa a d'aurewa dangi? kabar bala'i ya kwana lafiya d'an samari bank'i mu kwana muna bala'i dakai a wajen nan ba bakasan waye Abdallah ba amma bari in fara marin naka idan ka d'aure min dangin daga nan zakasan waye ni". ya k'are maganar yana cije baki
gamida d'aga hannu zai kai masa mari Ja'afar ya k'ara hanzarin rik'e hannun yayin da wancan saurayin yaketa balok'ok'on Ja'afar ya saki Abdallah ya mareshi, a fusace Abdallah ya juya ya kalli Ja'afar yace
"Idan banci ubanka anan wajen ba kace d'an isk
a ne ni Ja'afar dallah malam sakarmin hannu, wani dattijo dake can gefe a wajen yin sana'ar shi ta faci yake kallonsu tun d'azu ganin abin yak'i ci yak'i cinyewa ne yasa ya tsallako titi hannun da suke inda suketa faman tada jijiyar wuya kamar zasu fara ko
kawa, yana zuwa Abdallah ya fara janyewa dan yaga kamar yafi wancan zafin zuciya.
"Dan ALLAH kayi hak'uri saurayi tunda dai ALLAH yasa ba abinda ya sameku ka kyaleshi kuyi tafiyarku".
"Dan ALLAH Baba ka sakeni sonake ya fad'amin waye uban nashi a g
arin nan kamar yadda yake ik'rari angaya masa ina gudun bala'ine k'aramin aikina ne in tub'e anan mu bugu dashi wllhy, yaci darajar ka kawai tsoho naci uwarshi a rashin mutunci wllhy".
Murmushi kawai dattijon yayi yana nan shima da irin Abdallahn a gid
a mai shegen zafin ran tsiya.
"To nagode sosai dayaci darajar tawa yaro kamashi ku tafi ALLAH ya huci zuciyarshi". yayi maganar yana kallon Ja'afar daketa kallon ikon ALLAH ko fiye da haka akace Abdallah zaiyi bazaiyi musu ba yasan shi kamar yunwar ciki
nshi.
Hannunshi ya kama ya nufi inda motarsu take ya shigar dashi driver seat dama a bud'e take dan lokacin daya fita baima tsaya rufe murfin ba. Komawa Ja'afar yayi inda dattijon yake yayi masa godiya harda alkhairi yayi masa na kud'i, shima dattijon
godiya yayi sosai, a fusace wancan saurayin ya shiga motarshi ya bata wuta ya zagaye motarsu Abdallah yabar wajen da gudu da kallo Abdallah yabi motar yasaki k'wafa yana jijjiga kai zuciyarshi sai zafi take masa.
Dawowa Ja'afar yayi ya shiga motar ya k
alli Abdallah daketa cije lips yana rurrufe ido baki ya bud'e da nufin yin magana Abdallah ya dakatar dashi da fad'in
"Uwarka zanci wllhy idan kasake kai min magana wllhy banza mara zuciya".
Murmushi kawai Ja'afar yayi yana d'an tab'e baki yace
"To naji bazanyi magana ba kar aci uwata yanzu dai ka tuk'a mutafi gida kaga magreebah takawo kai".
"Bazanyi driving d'inba, kai zakayi". yace kanshi tsaye yana wani girgiza k'afa
"A kanka zan zauna to inyi tuk'in". Ja'afar ya fad'a yana dariya.
Mrs Salees Mu'az
💝
Maryam Ibraheem Aleeyuh
(Ummee)
HASKE WRITERS ASSOCIATION
💡💡💡
TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A
ZAFAFAN LITTAFAI MASU SAKA SHAUK'I, FADAKARWA K'AYATARWA NISHADANTARWA HAR GUDA 7!!!
GA SHIRI NA MUSAMMAN
INA MASU S
ON KOYAN GIRKUNA DA MASU SON KARA SANIN SIRRIN MALLAKE MAI GIDA
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
KUDIN RAJISTA - 500 (NAIRA DARI BIYAR GABA DAYA)
*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*
GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA
DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair
ɗ
ari biyal kacal.
*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*
*SAI YA TURA KUDINSA TA*
2083371244
Zenith Ba
nk
Aisha M.Salis
*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number
👇🏼👇🏼
*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA S
AN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*
*ƳAN NIGER
🇳🇪
, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
2/14/22, 08:41 - Ummi Tandama
😇
: *WATA SOYAYYA* ♥
️
🩸
♥
️
*HAS
KE WRITER'S ASSOCIATION
💡
(Home of expert & perfect writer's)
*TOP TEN TAKUN HASKE BATCH {A}*
Writer: Oum Hanan
From the writer of DR SAIF
🩸
Free page
Fiction story
05