Showing 24001 words to 27000 words out of 96447 words

Chapter 9 - Wata Soyayya Complete

03 Sep 2026

6

tayi picking ta kaita kunnenta lokacin data k'arasa shiga motar ta zauna kan kujerar.

"Perfect! shigar tayi

". taji an fad'a daga d'aya b'angaren, sai lokacin ta ciro wayar taga number data kirata tsaki kawai tasaki tareda katse wayar ta d'orata kan cinyar Hassana tayiwa motar key sukabar gidan sai faman k'ink'uni take.

Sai bayan magreebah suka dawo gidan.

^√^√^√^√^√^√^

Washegari juma'a ranar za'a gabatar da dinner tun safe gidan yafara d'aukar bak'i na nesa dana kusa Momy Maryam ma ta k'araso itada nata yaran Abdallah da Hannah sai Aunt Zakiyyah da Aunt Hameedah ita Aunt Kulthum bata samu zuwa ba

saboda tsohon ciki datake d'auke dashi. Hakama Mama ta k'araso itada Aunt Zaleehah babbar yayar su Jauhar da mai binta Aunt Fatee sai sauran mazan daza suzo ranar asabar wato ranar d'aurin aure.

Tunda suka k'araso gidan ya k'ara kacamewa Abdallah Madu

gu da Abdallahn Momy Maryam dama bayan y'an uwantakar abokai ne sosai jininsu yayi bala'in had'uwa shima d'an warai ne irin Abdallah Madugu yanada wasa da dariya kuma shi idan bawai ka shiga harkarshi ba ba ruwanshi dakai sab'anin Abdallah d'an neman fitin

a da abokin fad'a ga tsokana.

Su hud'u ne a falon Abdallahn Ja'afar sai H.U Marafa wato babban aminin Abdallah saikuma shi Madugu uban tafiyar sai Abdallahn Momy Maryam gaba d'aya sun hargitsa falon da plate plate na abinci da sukaci da cups da suka sh

a ruwa da lemuka sun baje sai hira suke kafin ka shigo falon zakayi zaton sunkai kusan su goma a ciki saboda yadda hayaniya ta cika ko ina Ja'afar nema mai d'an sauk'i a cikinsu danshi bai cika hayaniya ba sosai.

Bayan magreebah aka fara tafiya hall d

'in da za'ayi dinner dama iya ta y'anmata da samari ce dinner ko ina ka waiga a cikin gidan y'an uwa ne maza da mata y'an matan su da samarinsu kowa yaci ado mai k'ayatarwa sai walwali suke suna haskawa, Janan, Jauhar, Hassana, Hussaina da Hannah shigarsu

iri d'ayace wani had'add'en material ne mai tsada dark peach color da adon tsalli tsallin flowers green color Ammi ta d'auki nauyin siyanshi da d'inkinshi gaba d'ayansu d'inki iri d'aya akayi musu riga da siket sai head d'in kansu da akayi musu d'auri gree

n kowacce tasha makeup masu ra'ayin heavy makeup anyi musu hakama wad'anda light sukeso duk ayi musu sunyi kyau sosai sai selfie suke kashewa yayin da k'amshi ke tashi duk ta inda suka gifta.



Can part d'insu Ameen ma haka yana d'akinshi da abokans

hi suna shiryawa shima Abdallah yana nashi d'akin shida Habeeb da Ja'afar da Abdallahn Momy Maryam sai wasu y'an uwa da ba za'a rasaba da suke d'akin, had'add'un shaddoji kuma tsadaddu kawai kake gani a d'akin kowa da yanayin shigarshi wadda ta dace dashi,

Abdallah wata bugaggiyar shaddace

a jikinshi rantsattsiya sai k'yalli take zubawa da d'aukar ido maroon color daya ciza sosai kasancewar shi fari yasa kalar ta haskashi sosai anyi masa d'inki irin na zamani daidai jikinshi harda babbar riga k'arama irint

a samarin zamani da akeyi yanzu ya murza hula zanna bukar data hau da shaddar sosai hatta links d'in dayayi amfani dashi ya shiga da kalar shaddar sai bak'in takalmi halfcover da bak'in agogon fata daya haska farin hannunshi mai cikeda gargasa, madarar kya

u dai yayita a wannan lokaci sai k'amshin Arabian perfumes ke tashi a jikinshi duk da suma sauran ba bayaba wajen kyawun da sukayi saida suka shiga yana kyawun da Abdallah yayi shi d'in na daban ne a cikinsu.

^√^√^√^√^√^

Taheer guest palace.



Hall d'in wajen aka kama inda yasha adon decorations masu kyau da d'aukar ido da k'ananun fitilu da aka mammak'ala jikin fulawoyi da suke bada haske kala kala red, green, purple da sauran kaloli masu kyau da ban sha'awa gurin ya k'ayatu matuk'a.



Cike wajen yake wanda ya had'a wayayyun y'an mata da samari y'an boko kowa kagani yaci ado na kece raini kowa yanason nuna shi wanine a wajen.

Ango da amarya suna zaune a inda aka tanadar musu inda akafi k'ayatawa amarya tasha kyau harta gaji ciki

n bride gown white color shima Yah Ameen d'in shigar farar shadda yayi sai murmushi yake faman saki bakin sam yak'i rufuwa.

Babban abokin ango Sameer shi aka kirawo ya bada d'an tak'aitaccen tarihin ango da turanci sai babbar aminiyar amarya Nusaiba d

a itama tazo ta bada tarihin amarya a tak'aice, daga nan aka shiga gabatar da abinda ya tara mutane a wajen, tuni wajen ya hargitse saboda music d'in da aka saki aka fara gwangwajewa.

A.B Madugu, H.U Marafa, J.I Turaki da kuma A.A Zakeer su kad'ai

aka bawa filin cashewa nan fa suka fara kwasar rawa musamman Abdallah Madugu dayafi kowa zak'ewa rawarshi yake bil haqqi da gaskiya Ja'afar ne kad'ai yake d'an takawa a hankali.

"Anya mutumin can baici kaiba kuwa dan ALLAH dubi irin rawar dayake, wai A

mmi bata tab'a baku labarin ya d'an samu matsala a brain d'inshi ba tym d'in dayana yaro?". Jauhar ce tayi maganar bayan taja tsaki idanunta akan Abdallah dayake ta d'iban shokky

😂

.

Sosai Hassana ta k'yalk'yale da dariya tace

"Wllhy sis bawata mats

ala dake k'wak'walwar shi kawai shi haka yake in kikace zaki biyewa Yah Abdallah da abinda yake zaki iya kamuwa da hawan jini ma wllhy shiyasa tsakaninmu dashi ido". ta k'arasa maganar tana kai hannu kan idanunta, wani tsakin Jauhar ta k'ara saki tana tab'

e baki.

Cikin rawar ya hango Jauhar da wani saurayi sun fita daga cikin Hall d'in baki ya cije yana binsu da kallo kafin ya zame jikinshi ya fita daga filin rawar da zuwa yanzu aka cikashi sosai yabi bayansu cikin takunshi na k'akk'arfan namiji d

a ubangiji ya azurta da cikakkiyar lafiya.

Gaba d'ayansu basu san da tahowarshi ba bare zuwanshi saboda sun juya bayansu sai saukar wani azababben rank'washi da Jauhar taji a tsakiyar kanta, ba shiri tasaki k'arar azaba tareda dafe wajen da hannunta ta

na

juyawa dan ganin waye duk da dai zuciyarta bata raba d'ayan biyun wannan fitinannen ne, k'ik'am ta ganshi yayi mata tsaye yana k'are mata kallo hankalinshi kwance bakace shiya aikata ba, cikeda mamaki saurayin yace

"A'a Malam lafiya kuwa? ya zakazo

ka sameni da yarinya ka daketa meye had'inka da ita?".

Zagaye Jauhar yayi ya k'arasa gaban saurayin yai masa tsaye akai ya kama k'ugunshi da hannayenshi duka biyun yana wani kallonshi a d'age yace

"Zaka rama mata ne?".

"Ba zancen zan rama mata bane

amma meye dalilinka nayin haka?". saurayin yace yana wa Abdallah wani irin kallo na mamaki.

Gabanshi ya k'ara matsawa sosai yana wani irin murmushi gamida shafa sajen fuskarshi yace

"Ko zamuyi fad'a ne?".

"Fad'a kuma? me yai zafi? akan me zanyi fad

'a dakai?". lokaci d'aya saurayin ya jero masa tambayoyin yana kallon shi.

Tsayuwar shi ya gyara gaban saurayin yace

"Karka damu ganina dakayi da wannan babbar rigar zan iya cireta mu bugi juna dakai yanzun nan d'an saurayi".

Shidai zuwa yanzu sa

urayin ya fara tunanin duk yadda akayi Abdallah baida cikakkiyar lafiya ta k'wak'walwa gashi dai very handsome guy fari kyakkyawa dan haka yafara masa kallon tsoro yana girgiza masa kai.

"Saita hanya". Abdallah ya fad'a yana kaucewa daga gabanshi tared

a nuna masa hanya da hannunshi, da sauri kuwa saurayin yabar wajen yana waiwayen inda yabarsu tsaye.

Takowa ya shiga yi inda Jauhar ke tsaye har lokacin hannunta dafe da kanta dan harga ALLAH ba k'aramin shigarta rank'washin yayiba ga takaici daya cika

ta kamar ta mutu dan haushi.

"Munafuka da kukazo nan d'in uwar mi zakuyi?". baki ta tura gamida sakin tsaki ta juya da shirin barin wajen ya fincikota ya matso da ita daf dashi har sunajin hucin numfashin juna da k'amshin turarukan juna da suka cika k'o

fofin hancinansu.

"Ba'a tafiya idan ina magana, ya kamata kisan wannan".

Wani k'ululun abune ya tokare mata a wuyanta baiyi gaba ba haka kuma baiyi baya ba ALLAH nagani Yah Modibbo yana mugun takurawa rayuwarta batasan ya zatayi dashiba ya zamar ma

ta alak'ak'ai.

"Bakya jine". yace yana k'ara matsar da fuskarshi kusa da tata tamkar mai shirin had'esu.

Da k'yar ta had'iye abinda ya tokare mata batason su raba abin fad'a a cikin mutane ita yau batajin fitina gashi kanta na mata ciwo saboda hay

aniyar wajen datayi yawa.

"Kayi hak'uri to". ta fad'a tana cije lips jitake tamkar tai ta wanka masa mari tsabar haushin da datake ji.

Sakinta yayi yace

"Wuce muje".

"Kaje zan taho". tace cikin had'e rai tana hararar shi ta gefen ido

Cikin za

ro ido yace

"Inje ina? k'afata k'afarki wuce ko in d'auke ki kuma kinsan koban rantse ba zan iya ko?".

Gaba tayi batare datayi magana ba tasani sarai tsaf zai iya d'aukar nata kamar yadda ya fad'a d'in yabi bayanta yana murmushi.

M&S

💝

*TOP

10 TAKUN HASKE BATCH A*

💪

*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*



*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*

*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI G

UDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*

*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*

*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*

*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI

💎

*

*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU

👄

*

*ZO GARE NI:- NA HAJ

JA CE

👈

*

*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*

*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*

*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*

KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*

SHIRIN

YADDA AK

E HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*

SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*

*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA

MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*

*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*

GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU

NE AKAN 500 naira only...Nair

ɗ

ari biyal kacal.

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244

Zenith Bank

Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud

'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number

👇🏼👇🏼

*

07043079282

*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*

2/

14/22, 08:59 - Ummi Tandama

😇

: 14.

Tana gaba yana biye da ita a baya.

"Bakiji ba". ya fad'a daga inda yake, banza tayi masa tamkar bataji abinda yace ba ta cigaba da tafiyarta k'wararan taku biyu yayi sai gashi ya taddo ta gefenta ya tsaya suka je

ra yace

"Nace ba". Nan ma shiru tayi kamar bata jishi ba a fusace yace

"Jauhar zanci ubanki a wajen nan wllhy ya ina miki magana kinyi banza dani kurma ce ke kome".

Sai data harari gefen dayake tana tura baki tace

"To wai ba kunne ne yake jiba,

zaka ishi mutane jarababbe". ta k'arasa maganar k'asa k'asa cikin k'unk'uni yadda bazai jiba.

"Idan an tashi kar kibi motar kowa sai tawa kin gane".

"Why?". tace tana tsayawa.

Shima tsayawar yayi a gabanta ya d'age kafad'a yana d'an tab'e baki yace

"Haka dai na fad'a idan kuma kikayi gigin bin wata mota ba tawa ba kinsan sauran ki gwada kigani". bai bata damar magana ba yayi gaba yana wani irin taku. Da wata muguwar harara tabi bayanshi jitake tamkar ta janyoshi taita dukanshi batasan ya zatayi d

a wannan bawan ALLAHn ba, tsaki taja tabi bayanshi lokacin harya shige cikin Hall d'in.

Tana komawa su Hassana suka fara tambayar ta inda taje ba wanda ta kula a cikinsu dan a wuya take ranta a b'ace yake suma da suka gaji sai suka k'yaleta suka maida

hankalinsu kan ango da amarya da aka taso suka fito filin rawa dan takawa.

An rak'ashe sosai anyi nishad'i anci ansha da abinci da abinsha masu dad'i da akayi order, k'arfe sha d'aya da y'an mintuna aka tashi daga dinner cikin rububi Jauhar tabi danta

gujewa Madugu saidai abinda bata saniba hankalinshi gaba d'aya yana kanta saiji tayi caraf an rik'e hannunta an fita da ita daga taron mutanen, kamar sakara haka tabishi batare datayi magana ba to tace me? shifa hayaniyar mutum da wani bore da mutum zaiyi

bashi zaisa ya fasa abinda yayi niyyar yiba.

Can gefe inda ba yawaitar mutane suka nufa inda motarshi take, suna zuwa yaga yaga Abdallahn Momy Maryam da Habeeb Umar Marafa suna tsaye jikin motar suna jiranshi, front seat ya bud'e yayi mata alamun ta s

higa da hannunshi ba musu ta shiga ya rufe ya zagaya yaga Habeeb Marafa ya shiga back seat Abdallahn Momy Maryam ma na shirin shiga hannu yasa ya janyo rigarshi ta baya yana fad'in

"Wai ina zaku? dallah malamai ku fito". juyowa A. Zakeer yayi yace

"

A'a ban ganeba ba tare mukazo dakaiba".

"Eh tare mukazo amma ba d'an iskan dazan maida yanzu kowa yaje ya nemi mai maidashi gida kaima fito dan ubanka". yayi maganar yana cakumo Habeeb Marafa ya fito dashi shima, sakato sukayi suna kallon wannan d'an juj

un abokin nasu.

"Amma kaidai anyi mara mutunci wllhy kasan fa bamuzo da mota ba a motarka mukazo shine zaka mana iskanci A.B Madugu?". Habeeb Marafa ne yayi maganar yana hararar Abdallah daya juya baya yana shirin bud'e driver seat, juyowa yayi yace



"Kuje ku nemi Ja'afar ubanwa yace karku d'auko mota niba d'an iska bane dazaku maidani wani direbanku". bai saurari abinda zasuce ba ya bud'e ya shiga ya yiwa motar key yabar harabar hall d'in suka bishi da kallo harya fice, k'wafa A. Zakeer yayi yace

"

Gayen nan fa ya raina mana hankali Habeeb".

"Rabu da d'an iska bashi da mutunci fa zo muje ga Ja'afar can da alamu ma mu yake nema". ya fad'a yana jan hannun A. Zakeer suka nufi inda Ja'afar yake tsaye yana dube dube suna k'arasawa Ja'afar yace dama su

yake nema yayi zaton sun tafi da Abdallah tsaki A. Zakeer yayi yace

"Rabu da mara mutuncin can yayi tafiyarshi wai bazamu maidashi driver ba".

Kai kawai Ja'afar ya girgiza yana murmushi ya shiga motar suma suka shisshiga ya tayar sukabi sahun sauran

motocin daketa ficewa daga wajen.

Tunda suka tafi ba wanda yayi magana saida suka d'an fara yin nisa sannan ya juyo inda Jauhar take taci d'aci tana faman harare harare murmushi yayi ya juya ya maida hankalinshi kan driving d'in dayake kafin yace

"Ya kikaga rawar d'azu?".

'Ji wani shirme kuma dan ALLAH' tace cikin zuciyarta tana jan k'aramin tsaki.

"Kinji". ya k'ara tambayar ta, takaici kamar me Jauhar kamar ta daddalla masa mari meye abin burgewa a rawar? baisan ma haushin shi taji ba d'az

un lokacin da yake rawar.

Kai tsaye tace

"Batai ba". harda tsartar da yawu dan k'arin bada haushi.

Maimakon taga yaji haushi sai taga yayi murmushi ya juyo ya kalleta ya k'ara maida kanshi kamar bazaiyi magana ba saikuma taji yace

"So tired wll

hy jikina duk ciwo yake".

"Saikace wani yasashi yayi rawar". ta fad'a cikin ranta tana hararar shi ta gefen ido, bai k'ara magana ba itama ta maida kanta kan wayarta dake hannunta har suka k'arasa gida, yana yin parking tayi hanzarin ficewa ta shige falo

bata saurari cewar dayake ba wai bazata tsaya tayi masa godiya ba saboda mutuncinta ragaggene, tsaki kawai taja lokacin datake k'arasa shigewa cikin falon.

Wanka kawai tayi tasaka nyt dress tabi lafiyar gado dan cikinsu ma ita kad'ai ce ta dawo, ta g

aji matuk'a dama ga kanta dake ciwo dayake ba k'aunar magani take ba yasa bama ta nemeshi ba tayi kwanciyar ta.

Yana shiga part d'inshi A. Zakeer da Ja'afar suma suka shigo dama saida suka biya suka ajiye Habeeb Marafa a gida sannan suka wuto, b

ai kalli inda sukeba ya cigaba da cire kayan jikinshi tunda suka shigo A. Zakeer yake hararar shi ba kallonshi yayi ba baima san abinda yakeba sai daya d'ago kai yaga yadda yake hararar shi dariya yasaki yace

" Ya Broth har kun dawo?".

"Ban saniba d'a

n iska mara mutunci yanzu daka taho ka barmu bambancin mu kad'an ne dakai ai".

Baki ya tab'e yana zame wandon shaddar jikinshi yace

"Bakasan wadda na d'auko bane da baka zageni ba".

"Tafimu muhimmanci kenan?". A. Zakeer ya tambaya.

"To dama

kunada wani muhimmanci ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login