Showing 63001 words to 66000 words out of 96447 words

Chapter 22 - Wata Soyayya Complete

03 Sep 2026

26

Abdallah sai daya bani tausayi saboda yadda naga ya zuge lokaci d'aya Abbie da Yah Ameen su kad'ai ne a d'akin kowa ya zuba tagumi sun rasa abinda yake musu dad'i a duniya

r nan dama haka lamarin ubangiji yake idan yaso jarabtar mutum fatansu dai ALLAH ya basu ikon cin wannan jarrabawar.

Abdallah ne yafara farkawa da kuka ya farka yana wasu maganganu dasu Abbie basujin abinda yake fad'a saboda k'asa k'asa yakeyi, da sauri

Yah Ameen ya fita kiran Dr ba jimawa suka dawo tare kamar yana jiran shigowar su ya fincike drip d'in ya fara k'ok'arin tashi wai zaije wajen Janaan Dr'n da Yah Ameen su suka dinga rirrik'eshi yana zamewa a dole saiya sauka Abbie dake kusa dashi yanata ma

sa magana amma yak'i kulashi burinshi kawai su sakeshi ya fita.

"Abdallah". Abbie ya fad'a da k'arfi sosai har d'akin yana amsawa, yaune karo na farko da Abbie ya tab'a ambatar sunan Abdallah gatsau ba tare dayace masa Modibbo ba kamar yadda suka saba

fad'a shida Ammi, tuni Abdallah ya nutsu ya k'urawa Abbie ido hawaye na sauko masa kan kumatunshi wani na bin wani tamkar an kunna famfo, a hankali cikin nutsuwa da tsananin tausayin Abdallah Abbie yace

"Abdallahi! ka nutsu ka bani hankalinka nan Hassan

a ta rigamu gidan gaskiya ta tafi gurin wanda yafimu sonta da k'aunarta shiya bamu ita kuma ya karb'i abarshi shin kanada ja ne akan hakan? kokuma dan wani yabaka aron abinshi yazo daga baya ya karb'a zakaji haushi? mutuwa gaskiya ce Abdallah kuma rigace d

ani dakai dasu da kowa da kowa saiya sanyata babu wata rai da bazata d'and'ani d'acin mutuwa ba kullu man alaiha faaan kowa saiya tafi mutuwa ta d'auki shugaban dayafi kowa ANNABI MUHAMMAD sallallahu alaihi wa sallam ta d'auki annabawa ta d'auki manya many

an sahabbai ta d'auki tabi'ai ta d'auki tabi'uttabi'ina ta d'auki manya manyan malamai da sauran muminai to waye bazata d'auka ba Abdallah? Hassana ta samu shaida da yabo ta mutu ranar juma'a ta cika da kalimatush shahadah me kuma musulmin k'warai yake fat

a banda wannan? kayi hak'uri mutuwa akwai d'aci kuma gyambo ne da warkewar shi sai a hankali kayi mata addu'a ALLAH yaji kanta yayi mata rahma yasa taje a sa'a ya had'a fuskokinku da alkhairi kaji Modibbo". Abbie ya k'arasa maganar cikin sigar lallashi yan

a kallon Abdallah wanda alamu suka nuna nasihar Abbien tayi matuk'ar tasiri a zuciyarshi da gangar jikinshi gaba d'aya.

Jauhar ma tun lokacin da ake fama da Abdallah na saiya fita itama ta farka, a hankali k'wak'walwar ta tafara tariyo mata abinda ya fa

ru wanda take fata da addu'ar ace mafarki ne ba gaskiya ba yanzu shikenan twin sister d'inta ta tafi ta barta ita kad'ai? shikenan bazata k'ara ganinta ba ta mata nisan da har abada bazasu k'ara had'uwa ba sai a darussalam? wani kuka tasaki mai k'arfin gas

ke harda shasshek'a kamar zata shid'e tareda dafe kanta dayake mugun sara mata wanda yayi mata mugun nauyi take jinshi tamkar ba nata ba da sauri Yah Ameen ya nufo wajenta.

Mrs Salees Mu'az

💝

3/11/22, 23:55 - Ummi Tandama

😇

: *WATA SOYAYYA*

💝

Pag

e 35.

Paid book.

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*.

©Oum Hanan.

Da gawar tata suka tafi duk wanda ka kalla idanu sunyi ja sun kumbura wasu kam suna kan yine har yanzu irinsu Jauhar da Hassana da Hussaina da kuma Aunt Deejah wadda bata dad'e da zu

wa ba baby girl d'in na hannunta shikuma namijin yana hannun Ammi har suka k'arasa gida Abdallah yayi shiru kamar mai nazarin wani abu kallo d'aya zakayi masa kasan yana cikin tsantsar tashin hankali da rashin nutsuwa sai wata irin ajiyar zuciya yake sauke

wa akai akai Yah Ameen ne dake zaune kusa dashi yake yawan dafa kafad'arshi alamun rarrashi bai tab'a tunanin haka Abdallah yake son Janaan ba sai ayau da babu ranta.

Suna komawa aka fara shirye shiryen had'ata ayi mata sallah a mik'ata gidanta na gaski

ya, sai bayan la'asar sannan al'ummar annabi masu d'imbin yawa suka sallaci gawarta sannan aka d'auketa zuwa gidanta na gaskiya tafiyar da babu dawowa ALLAH yasa muyi kyakkyawan k'arshe dan sayyadil wujuud

🙏

.

Abdallah kamar zaiyi hauka a lokacin dan m

akarar ya rirrik'e yana kuka da k'yar aka b'amb'areshi ya durk'ushe a wajen ya cigaba da kukan Habeeb da Abdallahn Momy Maryam wanda ya samu isowa yanzun suka kamashi suka d'agashi suna rarrashi duk da suma hawayen suke hak'ik'a mutuwar Janaan ba mutum d'a

ya ta tab'a ba kowa jimantawa yake kuma tasamu shaida mai kyau a wajen mutane da dama, daga nan suka nufi inda mak'abartar take suna rik'e dashi.

Mama tayi dauriya sosai ko d'igon hawaye babu a idanunta sai na zuci datake itace ma take rarrashin Ammi,

Hajiya Yaya kam kuka ta dingayi sosai lokacin da suka k'araso abu d'aya kesa zuciyar mutane karyewa idan aka kalli jariran data bari wanda basu san komaiba shikenan sun rasa gatan UWA, UWA ta daban ce a rayuwar nan kowa tausayin yaran yakeji, musamman da

akaga sunata neme nemen abinci zam-zam aka basu sannan aka tauna dabino aka basu ruwan daga nan kuma Habeeb yaje ya siyo madara bayan an dawo daga kai Janaan.

An cigaba da karb'ar gaisuwa mutane tako ina b'arkowa suke b'angaren Abdallah ne Abbie Ammi Ma

ma Yah Ameen da sauran y'an uwa da abokan arzik'i hak'ik'a Janaan tana shan addu'o'e daga bakunan mutane da dama duk wanda ya santa alkhairinta yake fad'a kowa ya bud'i baki saidai ya yabeta ko hakan da Ammi da Mama sukeji yana d'an rage musu rad'ad'in ras

uwar Janaan Hafsat Yusuf ma k'awarta ta school tazo itada mahaifiyarta tasha kuka ba kad'an ba tanajin wata irin kewar k'awar tata ALLAH yayi bazasu gama karatun tare ba.

Jauhar kullum tana k'ule a d'aki sam ko fitowa batayi bedroom d'in da Janaan ta s

auka lokacin data dawo gidan nan ne yazama wajen zamanta ta tasa kayan Janaan d'in a gaba tana kallonsu tana kuka ratuwarsu ta baya tana dawo mata kafin Janaan d'in tadawo gidan Ammi takan tuna irin hak'uri da kawaicin da ALLAH ya azurta ta dashi ko takala

rta tayi da fad'a bata kulata sau dayawa wani abun na Janaan d'inne amma saitayi ruwa tayi tsaki tace natane haka zata bar mata batare data damuba ALLAH yasa hak'urinta ya amfaneta, cikin kwana biyu Jauhar ta rame saboda tunani datasa a ranta da kuma rashi

n cin abinci batacin komi sai ruwan Lipton shima sai wani daga cikin Aunt Deejah ko Jeeddah ko Aunt Mabrookah ko sauran yayyensu sunzo sun tasata a gaba sannan za'a samu tasha da k'yar duk tabi ta tsangwami kanta.

Yadda ake fama da Jauhar haka Habee

b Yah Ameen Abdallahn Momy Maryam suke fama da Abdallah yazama kurman k'arfi da yaji sam ya daina magana saidai yaita bin mutane da kallo, ko gaisuwa akayi masa saidai ya amsa dakai gashi baya cin komai duk ya zabge ya lalace duk faman da sukayi dashi kuwa

k'arshe ma sai tashi yayi ya shige bedroom d'inshi ya rufo k'ofar saida takai sun had'ashi da Abbie yazo har d'akin bayan yasa an had'a masa tea mai kauri sosai yataho dashi, yanaji ana bugawa yayi kunnen uwar shegu dasu yak'i bud'ewa duk a zatonshi su Ab

dallah ne sai dayaji muryar Abbie sannan ya bud'e.

A hankali cikeda da rarrashi Abbie ya fara yimasa nasiha da nuna masa wannan abinda yake duk bashi bane addu'a ya kamata ya dinga yimata ALLAH ya sadata da rahmarshi cikin hikmah irin tasu ta manya yasa

mu Abdallah yasha tea d'in sosai shik kanshi yayi mamakin wanda yasha daga nan Abbie ya k'ara d'ora masa da wata nasihar mai shiga zuciya saida Abbie yaga ya k'ara samun nutsuwa sosai sannan yabar bedroom d'in, maganar bacci kuwa babu ita yadda ya kwanta h

aka yake tashi ganin baccin ba samuwa yakeba kawai saiyayi alwalah yayi sallah tareda rok'arwa Janaan da sauran musulmi gafara da rahmar ubangiji.

Wani lokacin Abdallahn Momy Maryam da Habeeb sukan zauna suyita kallon Abdallah yadda ya canza lokaci d'ay

a mutum magananne ga masifa da bala'i da shak'iyanci kala kala amma dubi yadda ya koma wani salihi kamar bashi ba lallai idan ubangiji yaso zai iya canza mutum lokaci d'aya kokuma ya canza mutum ta sanadiyyar wani kamar yadda Abdallah ya canza sanadin rasu

war Janaan.

Abdallah taron mata dake cikin gidan baya hanashi shiga yaga yaranshi haka yake ketasu har saiya dangana da inda suke sun zama sanyin idaniyarshi yana jinsu fiye da komai a cikin zuciyarshi a yanzu baahi kad'ai ba kowa na familyn yana nunaw

a yaran soyayya suna iya bakin k'ok'arinsu wajen ganin sun basu kulawa tamkar mahaifiyarsu na raye.

✓✓✓✓✓✓✓✓

••••••••••••

✓✓✓✓✓✓✓✿

Ranar Bakwai.

A yau Janaan take kwanaki bakwai da rasuwa yayin data kama ranar rad'in sunan twins anyi yanka kamar y

adda addini ya tanadar ba'a canza musu sunaba an barsu da sunansu dama ance twins da sunansu suke zuwa, saidai ita Hussainar duk Janaan suka fara kiranta dashi a tak'aice dai Janaan ta tafi Janaan ta dawo fata dai ALLAH yasa tayi d'abi'un mai sunan. A rana

r Habeeb da Abdallahn Momy Maryam suka lodowa yaran siyayyar kayayyaki kala kala masu kyau da tsada.

Washegari Mama da sauran yayyen su Jauhar da Hajiya Yaya suka fara shirin komawa Mama taso Ammi ta bata little Janaan ko Hassan wanda suke cewa Irfaan

ta tafi da d'aya daga cikinsu Ammi ta rok'i alfarmar abar matasu duka dan ALLAH bataso a rabata da yaran nan ganin yadda duk ta damu yasa Maman tace shikenan a barsu d'in, Ammi taji dad'i sosai sam bataso a raba yaran nan tafiso su tashi tare.

Da Jauh

ar aka shirya tafiyar amma jin ance yaran anan za'a barsu saita tubure ita wllhy ba inda zata bazata tafi tabarsu little Janaan ba abin yabawa kowa mamaki amma duba da yadda tayi mugun sabo da yaran ba abin mamaki bane kullum tana mak'ale dasu ta goya wanc

an data saukeshi ta maida d'ayan gaba d'aya rabin d'awainiyarsu itace Mama ta kanyi mamakin hakan sosai a yadda tasan Jauhar da d'an banzan son jiki da lalaci ko aiki sai anyi fama da ita takeyi amma dubi yadda ta zage hidimar yaran kaf ta d'auketa batare

da nuna k'osawa ba duk yadda aka kad'a aka raya Jauhar tace ba inda zataje bamai rabata da yaran nan k'arshe ma kuka ta saka musu saboda mutuwar Janaan data dawo mata sabuwa fil a cikin zuciyarta, ido kawai kowa na wajen ya zuba mata kafin Hajiya Yaya tace

"Ke bamuson sakarci mana kin tashi kin shirya kokuwa kinata b'ata mana lokaci tun d'azu ku kiramin Abdullahi yazo yayi mana maganinta yanzu tunda batajin magana". ta k'are maganar tana kallon Hassana.

"Hmmm Hajiya Yaya ko Abdallah yazo yanzu ba abin

da zai iya yimata kura tayi lafiya ai rasuwar Janaan duk ta canzashi". cewar Ayyah, cikin kuka Jauhar tace

"Wllhy ko yazo ba inda zanje saidai idan dasu zamu tafi Kadunan". ido kowa ya zuba mata lallai abin na Jauhar da gaske take, cikin lallashi Mama t

ace

"Haba auta ta kinga kina zuwa school idan kika zauna nan ya zakiyi da makarantar gashi hutun da kuka samu ya kusa k'arewa ki shirya mutafi idan aka samu wani hutun sai Ja'afar ya kawoki kinji". kafad'a Jauhar ta nok'e alamun a'a har hakan ya basu da

riya murmushi Ammi tayi tace

"Dan ALLAH Yaya a barta d'in har hutun nasu ya k'are sai Modibbo ko Aminu wani a cikinsu ya maida ita".

Kan dole dai Maman ta amince bataso kad'aici yayi mata yawa.

Abdallah ne yayi sallama ya shigo falon yana sanye da

farar jallabiyyah da dogon wandon shadda fara, fuskar nan tashi fayau saboda ramar dayayi waima a hakan yadan ciko sai dogon hancinshi daya k'ara fitowa sosai ga uwar k'asumba data fara cika fuskar tashi wadda bata samun wani gyaran kirki, Kai tsaye kusa

da Mama ya nufa ya zauna batare daya yiwa kowa magana ba.

"Yadai mai sunan manya?". Mama tace tana kallonshi fuskarta d'auke da murmushi, kanshi ya kwantar a kafad'arta yana sakin ajiyar zuciya duk binshi akayi da kallo Jauhar kam kukan datake ta daina

ta kalli yadda ya wani shasshake tsaki taja cikin ranta wai yaushe mutumin nan zai girma ne fisabilillahi ya rasa ina zai kwantar da kanshi sai wajen surukarshi ALLAH dai ya kyauta masa ya girma baisan ya girma ba, d'agowa yayi ya kalli Ammi yace

"Ammi

ina suke?". kowa yasan suwa yake nufi dan haka Ammi ta bashi amsa da

"Suna d'aki barci suke".

"Ke kuje ku daukomin su duk yau bamu gaisa ba". ya ida maganar yana kallon Hassana da Hussaina da suke kusa da Ayyah.

"Ban gane a d'auko masa suba yaran su

na barcin za'a tashesu". Hajiya Yaya da bata gani ta k'yale ta fad'a tana masa wani irin kallo.

"Hajiya banason magana please a fitomin da yarana in gansu". yace cikin sanyin murya da rasuwar Janaan ta haddasa masa ita. Baki kawai Hajiya Yaya ta tab'e c

ikin ranta take ayyana wannan yaro dai bazai tab'a canzawa ba, kallonshi ya maida kansu Hassana ranshi a had'e sosai hakan yasa cikin sauri suka tashi suka tafi bedroom d'in Ammi inda su little Janaan suke, Ammi da Ayyah dai basu tanka masa ba su Aunt Deej

ah ma basu kulashi ba.

Basu dad'e ba sai gasu sun d'auko su anyi musu shigar kayan sanyi overrole da hulunansu an nad'esu da shawul mai taushi gaske sai k'amshi suke zabgawa, zamanshi ya gyara suka d'ora masa su a cinyarshi har lokacin basu tashi ba sai

baccinsu suke sha, tuni yanayin fuskarshi ya canza ta washe lokaci d'aya duk saiya manta da kowa na wajen ya shiga yimusu wasa kamar sunsan abinda yake, sudai mutanen dake wajen sai suka tsaya kallon ikon ALLAH gaskiya Abdallah bashida kunya.

Mrs Salee

s Mu'az

💝

3/13/22, 07:08 - Ummi Tandama

😇

: *WATA SOYAYYA*

💝

Page 36.

Paid book.

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*.

©Oum Hanan.

Takaici yasa Jauhar jan tsaki batare data san tayi d'inba, in banda shirme na Yah Abdallah ya za'ayi ka ding

a yiwa yara y'an 8dys wasa a hakan ma kuma barci suke inyayi maka wani abun kamar d'an fari.

D'agowa yayi da sauri ya kalli Jauhar wadda suna had'a ido tayi saurin kawar da nata ido ya k'ura mata sosai harya bud'e baki zaiyi magana kome ya tuna saikum

a yayi shiru ya maida kanshi kan yaran yana taune lips d'inshi na k'asa, ya dad'e a zaune a wajen har wasu daga cikin y'an falon suka tattashi shi yana zaune hankalinshi gaba d'aya yana kan twins.

Dole haka su Mama sukayi sallama suka tafi batare da Ja

uhar ba tace babu mai rabata da twins d'inta.

******

Jauhar tana burge Ayyah da Ammi sosai harma da Abbie saboda yadda take yiwa yaran nan matuk'a take nuna musu tsananin so da k'auna bataso ko k'uda ya tab'asu duk wata d'awainiya da hidimar su ta

d'auketa tsaf kamar irin dama can ta saba da rainon yara ko taimakon su Ammi wani lokacin saitace bataso saitaji uwar bari sun caza mata k'wak'walwa sannan take nufo Ammi dasu waya gaya miki Jauhar

🤣

rainon twins wasane is not easy fa aradu

😪

.

Abdall

ah kanshi yana matuk'ar jin dad'in yadda Jauhar d'in take yiwa yaran nashi ya fito ya nuna ne dai bai tab'a ba amma yana yaba k'ok'arin ta a zuciyarshi dan duk lokacin daya shigo gidan ganinsu zai samesu a wajenta tana hidima dasu.

***

★★☿

***

To

haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya yau da gobe kayan ALLAH gidan yafara komawa kamar da sun fara sabawa da rashin Janaan walwalar gidan tafara dawowa duk da dai sai a hankali har yanzun twins sun fara girma madarar ta karb'esu sosai sunyi dumi dumi dasu

gwanin sha'awa kullum kyawunsu k'ara fitowa yake haka kuma kamanninsu da Abdallah na k'ara bayyana shak'uwar Jauhar da yaran na k'ara k'arfi kowa nan nan yake dasu suna ganin gata sosai kuma har yanzu basu daina basu tausayin rashin UWA da sukayi ba duk da

ba abinda suka nema suka rasa kullum Abdallah ya fita da kalar abinda zai shigo musu dashi na daga kayan sawa masu kyau da tsada dana kwalliyar yara da kayan wasa duk da har yanzun basu gama sanin menene wasan bama.

Daf da hutun su Jauhar zai k'ar

e Mama tayiwa Ammi waya ta fad'a mata ya kamata Jauhar ta dawo haka nan tafara shirin komawa school dan Monday zasu koma saura kuma kwana uku litinin d'in, Ammi na fara yiwa Jauhar maganar tafiyarta ta nuna sam batasan zancen ba inkuwa aka tilasta mata ta

tafi saidai ta tafi da twins d'inta ba kalar lallashin da Ammi batayi mata ba amma ta tubure gashi sam Ammi batada zafi bare ta b'ullo mata ta bayan gida sai Maman ta k'ara kira ta fad'a mata yadda sukayi da Jauhar d'in ta kuma kawo shawarar me zai hana ab

ar musu Jauhar d'in sai a samar mata gurbin karatu a B.U.K inda su Hassana suke ta cigaba dayi anan, shiru Mama tayi tana tunani shikenan fa idan Jauhar ta koma can batada wani yaro kenan a gabanta sai Ja'afar shikuma ba za'ayi la'akari dashi ba tunda nami

ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login