Showing 12001 words to 15000 words out of 96447 words
d'an girmanshi ba laifi, ido ya zaro ya mik'e da sauri ganin ya
fara shirin yowa wajenshi belt d'in hannunshi ya jefar yayi wata irin sufa kan gadon lokacin Jauhar ta mik'e tsaye akan gadon aikuwa yabi ta kanta suka fad'a kan gadon sai gashi d'are d'are akanta fuskarsu daf data juna idanunshi cikin nata idanun cikin za
ro ido yace
"Ke dan ubanki bakida hankali maciji fa nagani yanzu".
"Yah Abdallah kaine fa kace inyi na snake". tace tana b'ata fuska gefe d'aya kuma dariyar ta take matsewa ganin yadda ya tsorata ashe ba namiji bane bama sai afkin cika baki ya iya"
.
"Wawuyar yarinya kawai ke dan ubanki ba'ayi miki wasa?".
Baki ta tura tasa hannayenta a k'irjinshi tana turawa tace
"Nidai ka d'agani Yah Abdallah nauyi wllhy".
"Wancan snake d'in dake d'akin fa?".
Cikin dariya Jauhar tace
"Ka tashi
kagani Yah Abdallah ya tafi fa".
K'wafa yasaki ya tashi a hankali yakai dubanshi inda snake d'in yake yaga ba komai, kad'a kai yayi lallai ma yarinyar nan zataci ubanta belt d'inshi ya d'auka ya kalli Jauhar da har lokacin take kwance bata tashi ba sai k'
yalk'yalar dariya take abinta.
"Zanyi maganinki yarinya, sainasa an karya miki k'ofin naki inga ta yadda zaki dinga cutar da mutane shegiya muguwa". daga haka ya bud'e k'ofar ya fice, har lokacin Jauhar dariya take wlhy ya bata dariya sosai ganin yadda
yayi ashe duk kuri ne kawai irin na maza dama wani tym d'in mata sunfi mazan jarumta su sai afkin cika baki suka iya.
Falon ya fito yana maida belt d'in, tun daga nesa Hajiya Yaya take jefo masa harara murmushi kawai ya sakar mata ya zauna kujerar
dake facing tata yace
"Yadai hajjaju zaman me kike anan ne?". yayi maganar yana d'age mata gira
"Zaman k'aniyarka nake d'an banzan yaro kai bak'in mugu me Johar tayi maka ka daketa? kaidai wannan yaro anyi mamugunci wlhy".
Baki ya tab'e yace
"Tamu
ce ta had'omu dan haka ki zuba Ido kawai kiyi kallo wannan jikar taki batada kunya Abdallah kuma ba'a tab'a shi a zauna lafiya idan taimin ubanta zanci wllhy". ya k'arasa maganar yana mik'ewa tsaye da nufin barin falon, da kallo Hajiya Yaya ta bishi tace
"To zakabar gidan nan kuwa tunda cin zaline ya kawoka mara mutunci kawai".
"Idan nayi ra'ayin tafiya ba, ki share kawai hajjaju". yace lokacin dayake k'arasa ficewa daga falon yana k'ara gyara zaman belt d'inshi.
"Mtsww, ALLAH ya shiryaka". tash
i tayi ta tafi bedroom d'in Jauhar dan ganin abinda yayi mata wannan uban ihun dataji tanayi tasan ba banza ba yanzu haka ma tana nan kwance azzalumi kawai (kai Hajiya
π€£
).
^β^β^β^β^β^
Da Mama ta dawo Hajiya ta fara mata maganar.
"K
ijawa wannan mugun yaron naki kunne wllhy karya k'ara gigin tab'amin jikata idan ba hakaba kuma zamusa k'afar wando d'aya dashi". (Lokacin da Hajiya ta shiga bedroom d'in Jauhar itama munafukar bata nuna ba dukanta yayi ba harda hawayenta da k'yar Hajiya t
a lallab'ata tayi shiru).
"Me kuma yayi Hajiya?".
"Meye ma baiyi ba? yaron nan dan tsabar zalunci yasamu yarinyar nan ya dinga duka ba laifin zaune bana tsaye saboda mugunta to wllhy nagaji ai ba jaka bace dazai dinga kilarta haka nan batare da wani d
alili ba".
"Hajiya yarinyar nan fa ita take jan abinda Abdallah yake mata ko meye shifa idan ba'a shiga harkarshi ba baya kula mutum duk ita take ja".
"Dama haka zakice mana saboda bakison laifin shi, idan ance Johar tanada tsokana itakuma Janan fa?
yarinyar daba ruwanta itama nasamu labarin takura mata yake".
"Ayi hak'uri Hajiya zan masa magana".
"Atoh dan bazan lamunci hakaba". tayi maganar tana gyara medical glass d'in dake idonta.
Tun daga ranar Abdallah da Jauhar basu k'ara had'uwa ba
har akayi kwana biyu.
Tun safe ya fita daga gidan yaje wajen wani friend d'inshi da sukayi school tare a outside Khaleel dama d'an Kaduna ne shine yakai mashi ziyara can suka yini sai yanzu da yammacin nan yadawo gidan.
Tunda ya danno hancin mota
r shi ya hango Jauhar itada wani saurayi a compound d'in gefen wasu flowers akan fararen kujeru sai k'aramin table a tsakiya da aka jera drink's kaloli daban daban da snacks.
Parking yayi ya k'ura musu ido ta glass d'in gaban motar zuciyarshi na masa wa
ni irin tuk'uk'i, ido ya lumshe ya k'ara bud'esu akansu Jauhar da suke hirarsu cikin nishad'i da farin ciki, lips d'inshi ya cije yana kad'a kai bari yaje ya d'an tab'a tsokana ko kad'an ce yaga ta yadda za'ayi zancen dan ubansu itada saurayin.
Fita ya
yi ya rufe motar, yana sanye ne cikin bak'in wando da red colour d'in riga sai black tied daya matse wuyanshi dashi ya matse k'ugunshi da bak'ar belt bak'in takalmi sawu cikine a k'afarshi sai black
watch dake d'aure a tsintsiyar hannunshi mai cikeda kwant
accen gashi sassanyan k'amshi ke fita daga jikinshi.
Kai tsaye ya nufi inda su Jauhar suke yana kad'a key d'in motarshi, saidaya fara d'auko wata kujerar sannan ya k'arasa inda suke daf da saurayin ya aje kujerar ya zauna tareda sallama yana mik'awa sa
urayin hannu sukayi musabaha, sosai Jauhar ta b'ata fuska tasan tunda wannan mutumin yazo yanzu zai b'ata gayyar duk saita rasa abinyi.
Shima saurayin mai suna Saleem mamakin abinda ya zaunar da Abdallah yake a wajen duk da dai bai sanshi ba amma koma w
aye ai kamata yayi ace suna gaisawa yabar wajen amma harda neman wajen zama
π€π¬
.
Kallon Jauhar Saleem yayi data kasa samun nutsuwa sai hararar Abdallah take ta gefen ido tana d'an tura baki.
"My love yayanki ne wannan?".
"Nabi My love da gudu uban
ka zakaci". Abdallah yayi maganar cikin ranshi a fili kuma yace.....
Mrs Salees Mu'az
π
Maryam Ibraheem Aleeyuh
π‘
*DAGA TASKAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*
π‘
π‘π‘π‘π‘π‘π‘π‘π‘π‘
*_OHH NI IBTISAM WANNAN SOYAYYAR TA YAYA UMAR ITA AKE KIRA
DA WATA SOYAYYA DUK DA HALIN ABDALLAH YA BANBANTA DA WASU MAZAN, KUKAN ZUCIN DA AZAAD JUNAID YA JIMA YANA YI AKAN SALIMA YAYI KAMANCECINIYA DA NA HAKEEM TAURARON NIDA RAHIMA BURINSA DA KALAMANSA AKODA YAUSHE ZO GARE NI.....TOP 10 KENAN DAGA ΖUNGIYAR HASKE
YAR UWA KAR KI SAKE KI BARI AYI BABU KE_*
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*
πͺ
*HAKA KUMA ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALAR JINI, DA MA MATSAL
OLI DA DAMA.*
*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*
GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair
Ι
ari biyal kacal.
*GA MAI BUKATAR BI
YAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*
*SAI YA TURA KUDINSA TA*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin way
a na MTN ta wannan number
ππΌππΌ
*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*
*Ζ³AN NIGER
π³πͺ
, ZAKU IYA TURA KUΖINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BEN
IF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
*HASKE MAGANIN DUHU*
π€π»
2/14/22, 08:42 - Ummi Tandama
π
: *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
π‘
(Home of expert & perfect writer's)
*WATA SOYAYYA* β₯
οΈ
π©Έ
β₯
οΈ
Writer: Oum Han
an
From the writer of DR SAIF
π©Έ
Free page
Fiction story.
07
^β^β^β^β^β^
"Baki tab'a bashi labarina ba? baki tab'a fad'a masa waye ni a wajenki ba?".
Yayi maganar yana k'ank'ance idanunshi akan Jauhar.
Murmushin yak'e kawa
i Jauhar tayi tace
"Amm Saleem wannan kamar yaya yake a wajena da Maman mu da mamanshi ya da k'anwa ne so yazo kawo mana ziyara ne a Kano suke da zama". ta k'are maganar tana d'an hararar Abdallah da yaketa sakin murmushi yana wani tsotsar baki kamar mai
shan sweet, shima Saleem murmushin yak'en yayi yace
"Eyyah ALLAH sarki". daga haka yaja bakinshi ya tsuke yana satar kallon Abdallah ta gefen ido wanda ya sunkuyar da kanshi yana danna waya, ido suka had'a da Jauhar data had'e rai sosai sai faman harar
ar Abdallah take ta gefen ido.
Shiru gurin ya d'auka, kafin Abdallah ya d'ago kanshi ya kallesu duk sai suka bashi dariya y'ar dariyar iya shege ya saki yana d'an tab'e baki ya matso inda drink's da snacks d'in suke wanda da alamu ma ko tab'a su ba'ayi
ba ya bud'e ya tsiyaya a glass cup dake wajen ya koma yayi relaxing kan kujerar yayi crossing legs nashi yafara shan lemon yana danna waya, wani takaici ne ya kama Jauhar wllhy abinda mutumin nan yake sam baya kyautawa taya zaizo ya sameta da saurayi suna
hira yazo ya wani
zauna tsabar neman bala'i irin nashi wllhy ta gaji da zamanshi a gidan nan jitake tamkar ta iza k'eyarshi ya koma garinsu.
Saleem dai kallon ikon ALLAH kawai yake zuwa yanzu dai ya tabbatar bawai iya gaisuwa bace ta kawo mutumin nan
harda neman masifa da biyu yazo wajen kuma, haka suka cigaba da zama ba wanda ya k'ara magana Abdallah daya shanye lemon ya ajiye cup d'in ya d'auki lafiyayyen meat pie ya fara ci, Saleem dai mamaki yagama cikashi itakam Jauhar kome akace Abdallah zaiyi ba
zatayi musu ba gashi dai One in town, first class handsome guy duk inda ake neman cikakken saurayi mai cikar sura kyawun fuska dana jiki Abdallah ya had'a ga brain ga ilmi ga kud'i dan yana samun kud'i sosai a sana'ar shi, amma wani time d'in idan yayi wan
i abun zakace bai tab'a shiga class ba shiyasa dayawa daga cikin y'an uwansu wad'anda suka san halayyarshi basu cika damuwa ba idan yayi musu w
ani abun, shi kawai haka ALLAH yayi shi baya d'orawa kanshi pressure yana da hawa kai ga wanda zama ya had'asu ta
re, amma wani lokacin yanada dad'in zama idan akayi sa'a y'an buyagin nashi basu kusa
π€£
.
Ji kawai sukayi ya k'yalk'yale da dariya har yana d'an dukan goshinshi, shidai Saleem zuwa yanzu ya daina mamakin Abdallah ya zura masa ido kawai yana kallon ikon
ALLAH ya kuma fara tunanin ya tashi yayi tafiyarshi idan ALLAH yasa Abdallah yabar gidan yadawo wannan jaraba dame tai kama yazo ya musu katak'e katak'e a waje suna tsaka da soyayyarsu.
"OH my God, wllhy ana tsiya a media dan ALLAH abokina duba wani
posting da akayi a Facebook yanzu". Cikin dariya Abdallah yayi maganar yana karkatowa kusa da Saleem tareda haska masa screen d'in had'add'iyar wayarshi a fuskar Saleem d'in daya shak'a ya tumbatsa kamar zai fashe tsakani da ALLAH wannan guy d'in bai kyaut
a masa ba yazo yana cikin tsinkar fulawarshi ya katse masa komai jiyake kamar ya tashi yaita dukan Abdallah
π
cikin had'e rai Saleem yakai idanunshi kan wayar batare daya karanta abinda yake nuna masa d'in ba ya kauda kanshi yana fad'in
"Zan wuce My l
ove sai mun k'ara had'uwa".
"Buk'atar maje hajji sallah". Abdallah ya fad'a a ranshi dama so yake ya tafin, dan haka yanajin ya fad'i haka ya mik'e tsaye yana gyara zaman tied d'inshi fuskarshi d'auke da wani shegen murmushi ya mik'awa Saleem hannu ala
mun su gaisa, da k'yar yabashi hannu suka k'ara yin musabaha har lokacin da murmushi saman fuskarshi, ledar da aka rufe snacks d'in ya bud'e ya d'auki doughnut da samosa guda d'ai d'ai yayi gaba yana dariya.
Duk da kallo suka bishi Jauhar kamar idonta
zai fad'o saboda harara, kallonta tadawo dashi kan Saleem da shima ya dawo da nashi idanun kanta.
"Wai dan ALLAH My love wannan guy d'in waye? meyake nufi da wannan abinda yayi?".
Tsaki taja cikin jin haushi tace
"Dan ALLAH kayi hak'uri Saleem mut
umin can fa da kake gani bawai k'alau yakeba yanada d'an tab'in hankali a k'wak'walwar shi".
Cak ya tsaya tareda runtse Ido lokacin dayake daf da shigewa cikin falon ALLAH ya hore masa ji kamar maciji hakan yasa har yaji abinda ta fad'a wato ma mahauka
ci ta d'aukeshi? kai kawai ya kad'a ya ida shigewa falon yana cije lips d'inshi tamkar zai huda.
"A'ah no wonder mana haba shiyasa naga abin yayi yawa to ki dinga dai taka tsantsan dashi My love duk da dai ni ban gama ma yarda wai tab'in hankali garesh
i ba tsabar tantiranci ne kawai yake d'awainiya dashi". ya k'arasa maganar yana shirin tashi tsaye.
"Yanzu tafiya zakayi kenan?". tace cikin tura baki kamar zatayi kuka.
"I'm sorry Jauhar munada appointment da wani da zamu had'u kinga ma yafara call
ing d'ina, yace yana
nuna mata wayarshi dake hannunshi wadda ta tafara ringtone.
Mik'ewa tayi ta taka masa har wajen motarshi sukayi sallama ya shiga ya tayar tana nan tsaye har saida ya fice daga gidan sannan ta juyo a fusace ta nufi falon bata tsaya
bi takan kayan dake kan table d'in ba ta shige falon.
Tana shiga ta sameshi akan kujera 2sitter ya mik'e k'afarshi akan k'aramin center table da labtop akan cinyarshi dama nan ya barta kan kujera lokacin dazai fita ga dukkan alamu wani binciken yake
saboda yadda ya maida hankalinshi sosai kai dan baisan ma ta shigo ba saiji yayi an tsaya masa akai ana huci, d'agowa yayi ya kalleta cikin fushi ta fara magana
"Gaskiya Yah Abdallah ka dainamin irin wannan ya za'ayi kazo wajen bak'o na kayi masa haka
yanzu gashi nan kaja ya tafi kuma daga gani ranshi ya b'aci wllhy".
"Ya dad'e ran nashi bai b'aci ba dan ubanshi, ke ki bini fa a sannu wllhy".
Ido ta zaro jin kai tsaye ya zagar mata saurayi
"Kai kai kai ka zageshi?".
Dama a kusa yake k'iris y
ake jira dan haka da sauri ya dangwarar da labtop d'in ya mik'e a zafafe ya matsa daf da inda take tsaye har sunajin hucin numfashin juna yace
"Na zageshi d'in akwai abinda zakiyi ne? nace na zageshi Jauhar zaki da'u mataki ne". ya k'arasa maganar yana
turata da k'irjinshi tayi baya kamar zata fad'i ya k'ara binta yana fad'in
"Nace zaki d'auki mataki ne Jauhar?"
A tsorace tace
"ALLAH saina had'aka da Daddy idan ka k'ara". juyawa tayi tana cigaba da fad'in
"Aikin banza aik.......ba zato ba tsammani
taji ya fisgota haka yasa ta katse maganar dataso fad'a ba shiri kafin tayi tunanin abinda zai mata taji ya zuro hannayenshi ya kamo nata hannayen ya bank'aresu baya ba shiri tasaki k'arar azaba tana runtse idanunta kanshi ya zuro ta gefen wuyanta ya d'or
a hab'arshi akan dokin wuyanta ta yadda kwantaccen quarter million d'in dake hab'ar tashi yasamu damar tab'a wuyanta ta k'ara tamke idanunta kamar zata saki kuka saboda zafin da hannayenta ke mata.
"Dan ubanki wa kike cewa yanada tab'in hankali d'azu?"
.
K'asa k'asa yayi maganar cikin kunnenta yana k'ara matse hannayenta dake rik'e cikin nashi hannun tabbas da wani zaizo a lokacin zaiyi tsammanin wata maganar arzik'i yake fad'a mata, ido ta zaro gabanta na fad'uwa dama yajita ne shikenan ta shiga ukun
ta.
"Baza kiyi magana ba saina karya wad'annan hannayen naki?". yace yana k'ara bank'aresu harda cije baki.
"Wayyo ALLAH dan girman ALLAH Yah Abdallah kayi hak'uri na rantse maka bazan k'ara ba wayyo ALLAH nah". da k'yar ta harhad'a kalmomin ta fad'a
saboda azaba hawaye har sun cika idanunta suna daf da zubowa.
Wata y'ar dariya yayi yace
"Wai ni Abdallah nine mahaukaci ko to kibari in k'ara ganinki da wannan ramammen saurayin naki ko wani daban anan ne zakiga tsantsar hauka da tashin hankali dan
ubanki b'ace daga nan". yayi maganar tareda sakar mata hannu ya d'aga kanshi daga wuyanta.
Kamar wadda ke jira tabar wajen harda had'awa da gudu hawaye shab'e shab'e a fuskar ta, k'ugu ya kama da hannayenshi duka ya bita da kallo.
Saidata tabbatar
takai kusa da bedroom d'inta sannan ta leqo da kanta tace
"ALLAH ya isa mugu kaidai anyi azzalumi wllhy bazan tab'a yafewa ba kuma".
Inda ya tashi ya koma ya zauna ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana girgizasu idanunshi akanta yace
"Uwarki zanci la'ad
a waje wllhy kibari mu k'ara had'uwa Jauhar".
Fuska ta yatsina tana d'an tab'e baki tareda kwaikwayar sunan Jauhar d'in daya fad'a
"Wai Jauhar, dan ALLAH wai yaushe zaka iya R ne Miss Abdallah Madugu".
Baice komaiba sai dariya kawai dayayi ya d'auki
labtop d'inshi ya k'ara mik'e k'afarshi ya cigaba da aikinshi.
"Mugu kawai". Tace cikin tura baki tana share hawayen fuskarta