Showing 18001 words to 21000 words out of 96447 words
amma bata bud'e ba bugun duniyar nan tayi amma Jauhar tayi shiru abinta dan tasan kan abinda ake mata bugun kuma wllhy bazata sakeshi yanzu ba saiya d'and'ana kud'arshi, Hajiya ma
dataji bugun yayi yawa ta fito ta tambayi Mama abinda yake faruwa Mama ta sanar da ita itama d'in da ita akaita bugun tana faman lallab'a Jauhar kan ta bud'e duk a banza dole haka suka hak'ura suka bar k'ofar d'akin.
Komawa Ja'afar yayi side d'inshi y
asamu Abdallah yaja k'afafunshi ya koma kan gadon ya rufe k'afafunshi da blanket yana danne danne a waya, dariya ce sosai ta kama Ja'afar aikuwa ya shiga k'yalk'yala ta harda dafe ciki, d'agowa Abdallah yayi a fusace ya kalli Ja'afar yace
"Na rantse id
an natashi sainaci ubanka cikin d'akin nan Ja'afar wato dariya ma kake min ko?".
"Yo taya bazan maka dariya ba da alamu dai yau nan zaka yini dan wllhy munje ba irin bugun da ba'a yiwa yarinyar nan ba tak'i bud'e k'ofar".
"Haba dai?". Abdallah yace
yana zaro ido
"Wllhy da gaske nake maka bansan dai ya za'ayi ba amma dai yanzu ba wannan ba bari in kawo maka breakfast kayi d'an gurgu". ya k'arasa maganar cikin dariya, throw pillows dake kan bed d'in Abdallah ya rarumi
d'aya ya jefa masa yana zaginshi
, fita yayi yaje dinning ya had'o masa breakfast ya kawo masa kan bedside ya ajiye yana fad'in
"Gashi nan".
"Bani brush".
Toilet Ja'afar ya shiga ya matso masa maclain a toothpaste ya kawo masa da wata roba da ruwa yayi brush d'in sannan yayi breakfa
st d'in.
Komawa Mama ta k'arayi ta bubbuga amma Jauhar tak'i bud'ewa sosai ran Mama ya b'aci da wannan iskancin na Jauhar.
Wasa wasa dai har kusan Azhar Abdallah na nan zaune, ya cika yayi famm sai faman masifa yake daga zaunen Ja'afar namas
a dariya dayaga bazai iya zaman d'akin ba saiya fice ya bar masa d'akin yayi alk'awarin bazai k'ara shiga harkar taba tunda batada mutunci muguwa kawai, gobe goben nan ma zai koma Kano yabar mata gidan dan ubanta
ALLAH ne ya jefo da Daddy gidan yazo d
'aukar wasu file daga office anan Mama take sanar dashi abinda ke faruwa da kanshi yaje ya buga d'akin yayi magana, sai dataji maganar shi sannan ta bud'e bedroom d'in Mama tamkar zata rufeta da duka saboda fad'a Daddy ma fad'an ya shiga yimata da dalilin
dayasa tayi masa haka cikin tura baki ta fad'a musu abinda yayi mata Daddy da kanshi ya tasata yace taje ta bashi hak'uri.
Yana zaune har lokacin da kayan barci a jikinshi, suka shiga bedroom d'in tunda suka shiga yake hararar ta harta k'arasa bakin g
adon ta tsaya Daddy ya k'araso shima yana fad'in
"Ashe sai k'anwar taka tamaka tsiyar tasu My son".
"Ai wllhy Daddy ko? bai cigaba ba sai k'wafa daya saki yana jijjiga kai.
Murmushi Daddy yayi tareda dafa kafad'arshi yace
" I'm sorry d'an g
idan Daddy Jauhar tayi laifi bashi hak'uri Jauhar". Daddy yayi maganar yana kallon Jauhar dake tsaye tana faman d'add'age hanci cikin tura baki tace
"Kayi hak'uri Yah Abdallah". banza yayi bai kulataba Daddy yace
"Ka amsa mana Abdallah ka hak'ura?"
"Saboda kai Daddy dasai nakusa targad'a yarinyar nan wllhy". ya fad'a kanshi tsaye (Kutt lallai Abdallah a gaban mahaifin yarinya kace zaka targad'a ta
π€π
saboda bakada man kai
π
π€£
).
Baki ta murgud'a masa ta juya tayi ficewarta yabita da kallo yan
a kad'a kai.
Bayan fitar Daddy ya tashi yayi wanka ya d'aura alwalah ya fito ya canza kaya ya gabatar da sallahr Azhar dan tuni masallatai sun riga da sun idar.
Tun daga nan basu k'ara had'uwa da Jauhar ba washegari yayi shirin tafiya Kano.
Ja
uhar na zaune a falo kan kujera ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana sanye cikin riga da siket na atamfa Cote d'ivoire tayi d'aurin ture kaga tsiya
π
da waya a hannunta tana buga candy crush saga, daga upstairs ya sauko sunyi sallama da Daddy yaudai shigar
manyan kaya yayi riga da wando na shadda sea green mai matuk'ar tsada sai walwali take tana d'aukar ido bai dai saka hula ba sai takalmi da agogo duk kalar shaddar yayi matuk'ar yin kyau wannan mayen turaren nashi dai na biye dashi ta bayanta ya zagayo kaw
ai ji tayi an dungure mata kai har d'an kwalinta na fad'owa kan cinyarta da sauri ta waiga dan ganin waye duk da bata raba d'aya biyun idan ba Abdallah bane shine kad'ai zaiyi mata haka a gidan, tsaye ta
ganshi a bayan kujerar ya kama k'ugunshi da hannayen
shi duka biyun yana kallonta, d'an kwalinta ta d'auka ta fara k'ok'arin d'aurawa tana tura baki tace
"Dan ALLAH meye haka Yah Abdallah?".
"Ture kaga tsiya naga kinyi shine na ture inga tsiyar taki".
K'aramin tsaki taja cikin ranta tace
Banida loka
cinka ni ayi mutum ace bashida aiki sai jan masifa ALLAH yayi mata maganin mutumin nan.
Yana shirin k'ara yin wata maganar Mama ta fito Ja'afar ma ya shigo janye da trolley d'in Abdallah, farin cikine ya kama Jauhar sosai dan ita sam batasan yau zai taf
iba to umma ta gaida assha ALLAH raka taki gona, Hajiya ce ta fito falon itama ta zauna Abdallah ya kalleta yace
"Hajjaju zan wuce saina k'ara kewayowa kuma zanyi missing d'inku wllhy musamman ke Hajiya".
"Kasha zamanka dan ALLAH ka dinga kiran wa
ya ana gaisawa kawai nikam bawani mussun d'inka da zanyi".
"ALLAH Hajiya? anya bazan fasa tafiyar nan ba".
"Ka fasa kuma?". Jauhar ta fad'a da sauri tana zaro ido waje.
"Nasa dake ne malama?". yace yana hararar ta, baki ta tab'e tana yatsina f
uska ta maida kanta kan wayarta Hajiya kam cewa tayi
"A'a Modibbo kaje kawai ALLAH ya kiyaye hanya yabada ladar zumunchi". daga jin yadda tayi maganar kasan kora da haline take masa
π€£
.
Dariya Ja'afar da Mama suka sa shikuma gogan ya wani tab'e bak
i yana d'age kafad'a yayi hanyar fita daga falon Hajiya da Jauhar suka rakashi da murmushin farin ciki, kai Abdallah case ne yasin
π
kazo gidan mutane ka addabesu yaudai Jauhar ranta fari k'al Hajiya ma na tayata murna wannan jaraba har ina.
Har bakin
motarshi sukayi masa rakiya Mama tace sai biki idan ALLAH yakai rai amma Jauhar da Jauhar zasu fara tahowa kafin bikin, back seat Ja'afar ya bud'e yasa masa trolley d'inshi yabashi hannu sukayi musabaha sannan ya shiga motar ya tayar yabar gidan suna d'ag
awa juna hannu duk sai Ja'afar yaji ba dad'i abokin fad'an nashi ya tafi dan Abdallah ba wanda ya ragawa gashi dai bak'unta yazo amma duk sai daya addabi y'an gidan
π
Ja'afar d'inma ba tsira yayi ba to yau dai Kano ta d'auka za kuma a komawa Janan dasu H
assana.
Sauka lafiya Abdallah Madugu
π€©
.
^β^β^β^β^β^
KANO.
Babu wadda gabanta bai fad'i ba cikinsu Janan lokacin daya dawo dama duk suna zaune a falo ya shigo dan haka al'adar gidan take ana yawan zama a falo ayi hira harda Ammi da Abbie
aji matsalar kowa ayi wasa da dariya, a d'arare suka yimasa sannu da zuwa da d'ai d'ai da d'ai d'ai kowacce ta samfe daga falon dan karma sutafi lokaci d'aya yace kamar sunga wani dodo dayake hankalinshi ma nakan Ammi suna gaisawa da tambayar yadda yabaro
su Mama yasa baima lura da fitarsu ba.
Anata shirye shiryen bikin Yah Ameen su Abdallah sune kan gaba a komai yaso ya wakiltashi ma shida Habeeb suje su tattauna da y'an mata k'awayen amarya kan events d'in dazasu gabatar da tsare tsarensu da ku
d'in da za'a basu Yah Ameen yace sam
π€£
Abdallah bazai jeba yaje ya kwanto masa ruwa dan kad'an daga aikinshi idan sukayi abinda bai
gamsheshi ba ya k'ukk'urma musu zagi
π
abokanshi na jiki sosai Sameer da Miftahu su sukaje suka zauna da k'awayen Fareedah
sukayi tsare tsaren bikin.
Ana sauran kwana biyar bikin Ja'afar da Jauhar sukazo Kano saboda wani aiki dazai kawo Ja'afar d'in lokacin sai Mama tace kawai sutaho da Jauhar itakuma sai ana gobe d'aurin aure sannan zata taho.
Janan tayi murna k'
warai da ganin y'ar uwarta suka rungume juna cikeda farin ciki sunyi missing d'in juna sosai su Hassana ma sunyi murnar ganinta nan fa suka zauna aka shiga chapter dariyarsu kawai kakeji da shewarsu Janan dai yawanci saidai tayi murmushi kawai idan abu yab
ata dariya saboda ita sam batada hayaniya kuma batada surutu kamar sauran.
Duk yinin ranar datayi a gidan bataga Abdallah ba ita hakan ma saiyafi yimata dad'i dan tasan indai suka had'u tofa sai ansamu abinda zai had'asu.
Koda dare ma da za'ayi di
nner badashi akayi ba wai sun fita shida Habeeb da Ja'afar. A ranar da daddare sukayi waya da Abeedah itama ta shigo Kano bikin wata cousin d'inta tana gayyatar ta nan tayi mata alk'awarin insha ALLAHU zatazo ta fad'a mata address d'in gidan sukayi sallam
a.
Washegari ita kad'ai aka bari a gidan daga ita sai Ammi su Janan duk sun tafi school, bayan ta tashi barci tayi wanka ta shirya cikin jallabiyyah k'irar Turkish red colour mai adon duwatsu masu k'yalli a gaban rigar ta yafa mayafin rigar ta zura bak'
in plat shoe ta fito bayan ta fesa turare.
Mrs Salees Mu'az
π
Maryam Ibraheem
_
π³π³
KIN SIYE 'YAR UWA?, KINA DA TANADINKI AHANNU?, KINA SO?, ZAKI KI KOYA?, SHIN KE CIKAKKIYAR MACECE? IDAN AMSARKI ITACE *EHHH..
π
* 'YAR UWA INA YIMAKI SAMBARKA, I D
AN KUMA AMSAR ITACE *A'A
π₯
* TO MAZA KI HANZARTA KIYI REGISTER DA
π
_
*TOP 10, TAKUN HASKE, BATCH A, INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI, 1-ZO GARENI NA HAJJACE, 2-IBTISAM NA AYUSHA MOH'D,
3-WASU MAZAN NA BILLY S FARI, 4-AZAAD JUNAID NA JEEDDAH ALIYU, 5-WATA SOYAYYAR NA OUM HANAN, 6-NI DA RAHEEMAH NA ASMY B ALIYU, 7-KUKAN ZUCIYA NA SLIMZY,
πππ
KAI KA KAI....!
π±
TIRQASHI, DUKA FA WANNAN GARA'BASAR ZA'A BAKU ITA AKAN N500 KACAL, GA KUMA SHIRE
-SHIRE HAR GUDA UKU DA ZAMU KOYAR DOMIN YABAWA, JINJINAWA DA KUMA FARANTAWA AGAREKU DA KUKA ZABEMU, 1- SHIRIN KOYAR DA GIRKE-GIRKE DOMIN ZUZUTA MAIGIDA
π
DAGA CHIEF DEEJARH BARVER, 2-SHIRIN KOYAR DA YANDA ZAKI HA'DA MAGUNGUNAN NI'IMA DANA KARIYA DAGA CUTAR
INFECTION DA ZAKI HAD'A DA KANKI ACIKIN GIDANKI DOMIN MAQALEWA A ZUCIYAR MAIGIDA DAGA MAMAN KHADIJA, 3-SHIRIN KOYOR DA TSAFTA, GYARAN JIKI, GYARAN GIDA, SAMUN WARAKA DAGA MATSALTSALUN JINI DA SAURANSU DOMIN ZAMOWA FITILAR GIDANKI DAGA UMMI A'ISHA*
_WOHO
HOOO..DUKA FA AKAN NAIRARKI 'DARI BIYAR KACAL ZAKI MALLAKI REGISTERΒ A *TOP 10, TAKUN HASKE BATCH A* SAI KIGA KIN ZAMA QASAITATTAR MACE, ISASHSHIYA KUMA ZINARIYA AWAJEN MIJINKI!_
_GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N500)TA W
ANNAN ACCOUNT
ππΌ
_
2083371244
ZENITH BANK AISHA M. SALIS
SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
ππΌ
+447894142004
IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA WANNAN LAMBAR
ππΌ
07043079282
SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
ππΌ
07065283730
Β Β _GA MUTANENMU NA QASAR NIGE
R
π³πͺ
ZAKU IYA TURA KUDINKU 550F TA NITA, AMANA, ALI'ZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR
ππΌ
_
+227 96 91 36 36 RAHINA daga niamey.
MUN GODE.
2/14/22, 08:57 - Ummi Tandama
π
: 11.
^β^β^β^β^
Dinning table taje tayi breakfast ta taso kenan Ammi t
a shigo falon inda take taje ta gaisheta kafin ta fara kame kamen tambayar unguwar datake so tayi hakan da Ammi tagani ne yasa tace
"Yadai Jauhar me kikeson tambaya ne kiketa faman kwana kwana?".
"Wllhy Ammi wata k'awata ce itama jiya ta shigo Kano b
ikin cousin d'inta shine ta gayyaceni dama kuma tun a KD ta fad'amin shine nakeso inje".
"Jauhar nifa banason wannan yawace yawacen kosu Janan dakike gani ba inda suke zuwa daga school saikuma idan fita ta kama dole".
A marairaice tace
"Dan ALLAH A
mmi ki barni please ALLAH ko magreebah bazan kaiba dan ALLAH".
Shiru Ammi ta d'anyi kafin tacee
"Toh naji amma kifara zuwa ki tambayi Modibbo naga shine yake a gida idan yabarki sai kije".
"Kai Ammi dole saina tambayeshi?". ta fad'a a shagwab'e ta
na b'ata fuska.
"Eh, haka tsarin gidan yake y'an uwanki ma haka suke idan Daddy yana gida a tambayeshi idan kuma baya nan toga wakilanshi nan Ameen ko Modibbo dan haka indai kinason zuwa to kije ki tambayeshi tunda Ameen baya nan".
Baki ta tura ta
tashi ta gyara gyalen jallabiyyahr jikinta ta zura takalminta ta fita daga falon dan dole zata tambayeshi wllhy kawai dan tanason zuwa ne amma ita harga ALLAH batason su had'u ma so tayi har a gama biki su tafi bata ganshi ba.
Side d'insu shida Yah Ame
en ta nufa k'ofar Yah Ameen a kulle tashi kuma a bud'e take saidai an d'an karota kad'an, saidata harari k'ofar kafin ta tura ta shiga bakinta d'auke da sallama can ta hangoshi zaune a tsakiyar doguwar kujera ya d'ora wata k'atuwar farar paper akan k'arami
n table d'in dake gabanshi sai pen da color kaloli daban daban masu yawa cikin wani farin abu dogo kamar cup na roba, duk wani hankali da nutsuwar shi ya maidasu kan zanen dayake, yana sanye da 3 quarter bak'i da farar
riga mai hula marar hannu green colo
r yasa hular a kanshi saidai ya d'anyi baya da ita kad'an wanda hakan ya bayyanar da kyakkyawar tattausar sumarshi daga gaba, sai data k'are masa kallo sosai yadda ya nutsu idan ka ganshi a haka zakayi zaton ko d'an yatsa akasa masa a baki bazai ciza ba na
n kuwa sai tsabar rashin ji da d'aukar magana tamkar wani k'aramin yaro.
A hankali ta taka ta isa kujerar dake gefenshi ta zauna bai waigo ya kalleta ba kamar ma baisan an shigo falon ba zanen dayake kawai ne a gabanshi, baki ta d'an tab'e kafin tace
"Yah Abdallah Ammi ce tace inzo in tambayeka zan fita idan ka yarda".
Baice uffan ba bai kuma juyo ya kalleta ba yadai d'ago kanshi ya k'urawa zanen dayayi kan takardar gabanshi ido ya d'ora pen d'in akan lips d'inshi.
"Kaji Yah Abdallah". ta k'
ara fad'a tana kallonshi da alamu yau y'an mulkin ne a kanshi, bayanshi ya kwantar a bayan kujerar dayake zaune ya shiga girgiza k'afa kamar bazai tanka bama yanzun saikuma yace
"Bazaki jeba Jauhar".
"Dan ALLAH Yah Abdallah". ta fad'a da siyar shagwab
'a kamar zatayi kuka.
Ido ya bud'e mata sosai yace
"Nace bazakiba wai dan ubanki ke amarar inace dabaki da aiki sai zuwa biki to bazaki jeba get out of my room".
Tana shirin k'ara yin wata maganar yayi mata wani kallon dayasa dolenta ta had'iye ab
inda tayi niyyar fad'a, a fusace ta mik'e tsaye tana huhhura hanci kamar wadda zata d'auki wani mataki a kanshi, kai ya d'age yana kallonta kafin yace
"Zaki dakeni ne?".
Tsaki kawai taja a hankali ta fice daga falon nashi da sauri kafin ya yunk'uro ya
ci k'aniyarta, da kallo ya bita yana girgiza k'afafunshi har yanzu kan yarinyar nan rawa yake ya kamata ya saita ta bai saniba ko shiga harkarta da yake ne yasa ta rainashi haka k'wafa yayi sannan ya taso ya cigaba da duba art d'in d'inshi ko zaiga wani gy
aran.
A bakin k'ofar falon ta tsaya tana shirya k'aryar dazata yiwa Ammi dan dole saitaje bikin nan fa abu d'aya zatayi tacewa Ammi yabarta zuwan to idan kuma Ammin ta tambayeshi fa? wani sashen na zuciyarta ya tambayeta, kai ba lallai bane ta tambaya
hakan kawai zatayi dan haka ta nufi falon su Ammi ta canza fuskarta daga b'acin rai zuwa murna, da murnar ta ta shiga falon kamar gaske tasamu Ammi anan inda ta barta kusa da ita ta zauna tace
"Ammi ya barni zuwa amma yace indawo da wuri". sam Ammi bat
a kawo k'arya take mata ba tace
"To barkan ki kinci sa'a indai Modibbo ne ba k'aunar fita yakeba haka su Hassana ke fama dashi dama Janan wannan fice ficen bai dameta ba, saiki tashi kije ki shirya".
"Yanzu kuwa Ammi". ta fad'a da sauri tareda bari
n falon ta shige bedroom d'in su Hassana inda kayanta suke, dama a shiryen ta take tsaf dan haka bata buk'atar wani shirin saidai kaya dazata canza.
Wani dakakken lace tasa lemon green rigar bubu ce tayi mata kyau sosai d'aurinta data saba tayi, ta yaf
a k'aramin gyale kalar lace d'in a gefen kafad'arta agogo da d'an kunne duk lemon green ne sai bak'in takalmi mai d'an tudu datasa da k'aramar jaka itama black color sai datayi selfie kala kala sannan ta fito tana zuba k'amshi, bata samu Ammi a falon ba da
n haka ta