Showing 66001 words to 69000 words out of 96447 words

Chapter 23 - Wata Soyayya Complete

03 Sep 2026

3

ne ba mazauni bane kuma batason Ammin ta tambayeta wani abu a matsayinta na y'ar uwarta jininta ta hanata amma dai zata yiwa Daddy maganar duk abinda ya yanke shikenan duk da tasan dai da wuya ya hana d'in inyaso ita saita d'auko Kauthar babbar d'iyar Z

aleeha babbar yayar su Jauhar dama tana yawan zuwa tayi kwanaki kafin takoma gidansu.

Hakan ta fad'awa Ammi tace yadda sukayi da Daddyn zata kira ta fad'a mata, godiya Ammi tayi sannan sukayi sallama kowa ya kashe wayar.

Kamar yadda Maman tayi alk'

awari bayan dawowar Daddy tayi masa zancen, shikam baima ja da nisa ba yace tayi zamanta a can d'in nan da can d'in duk d'aya ne ALLAH yasa zaman nata a can shine mafi alkhairi, Hajiya Yaya ce dai dataji maganar tayi k'orafin nata data saba ya za'ayi ace d

uk yaran can zasu tare taso hanawa Daddy ya lallab'ata da k'yar ta yarda amma fa tana ta faman maganganu da mitarsu ta tsaffi musamman idan Mama tana wajen itadai uffan bata cewa harta gaji ta daina.

Lokacin da Jauhar taji labarin da Ammi take fad'a ma

ta tayi matuk'ar farin ciki da murna itafa burinta kasancewa da yaran nan batason abinda zai rabasu ko kad'an su kansu yaran da ita suka bud'i ido dan haka suka fara sabawa da ita.

Tsakaninta da Abdallah ido ne babu mai cewa d'an uwanshi kanzil kowa har

kar gabanshi yake hakan yana mata dad'i sosai da baya takalarta duk da dai tun kafin bikinshi da Janaan ta lura ya janye mata.

Yah Ameen Ammi tayiwa maganar karatun Jauhar dan haka yafara yimata cuku cukun samar mata gurbin karatu a Bayero University Ka

no, ba'a d'auki dogon lokaci ba komi ya kammala harsun fara tafiya tare dasu Hassana da k'yar take tafiya tabar yaran saikuma d'awainiyarsu takoma kan Ammi saidai idan tadaw ta d'ora.

Abdallah sai gani yayi tafara zuwa school kai kawai ya jinjina yana t

ab'e baki lokacin daya hangosu ta windown bedroom d'inshi driver zai kaisu wato tadawo nan kenan gaba d'aya shima d'in kai tsaye bazaice bayason zamanta anan ba ko dan yaranshi abu d'aya dai yasani wanda yakejin baison ta zauna anan wanda shi kad'ai ya bar

wa kanshi sani.

1Yrs After.

Cikin ikon ALLAH su Jauhar har sunyi graduation itada su Hassana dama classmate ne, twins suna gudunsu ko ina dole subawa mutum sha'awa idan ya gansu sunyi mugun sabo da Jauhar abin nasu har mamaki yake bawa mutane sa

boda tsananin yadda suka shak'u. Auntie Fareedah ma matar Yah Ameen sun samu k'aruwar baby boi wanda yaci sunan Abbie suke masa alkunya da Aabeed.

Abdallahn Momy Maryam dai yayi wuff da Hassana

🤣

yayin da Habeeb shikuma ya kafa ma Hussaina k'ahon zuk'

a tun tana d'ari d'ari dai dashi harta amince dan farko tsoron Yah Abdallah ne yasa tak'i yarda to shi ranar daya gansu ma a compound ko bi takan su baiyiba sai bayan da suka gama zancen ne Habeeb ya shiga side d'in Abdallah anan yake tambayar shi meye had

'inshi da Hussaina ya gansu tare bayani Habeeb yayi masa tsaki yayi yace

"Banzaye haka zaku k'are naji ma wancan shegen wai Hassana yakeso yara k'ananu ku auresu kuce kun auri me?". had'e rai Habeeb yayi yace

"Ba ruwanka malam a haka muka gani mukac

e munaso kasa ido kawai kayi kallo".

"Saikuyi tayi ai manyan banza". yace tareda zamewa ya kwanta kan kujerar dayake kai zaune.

Cikin kwanakin kuma saiga maganar Ja'afar ta b'ullo shikuma wai Hannah yakeso k'anwar Abdallahn Momy Maryam, hak'ik'a y'a

n uwa dayawa sunji dad'in wannan al'amari ganin zumunchi zai k'ara had'uwa kenan kowa fatan alkhairi yake da addu'ar ALLAH yasa aga lokacin.

Ganin abu duk na gidane yasa aka had'e bikin kawai lokaci d'aya kuma gaba d'aya angwayen a shirye suke dan duk c

ikinsu ba wanda bashida gidanshi duk angama komai sai lefe da sauran abubuwan da ba za'a rasaba. Duka watanni hud'u aka tsayar idan ALLAH yakai rayuwar, su Hassana fa ansamu dama soyayya ba kama hannun yaro musamman data samu d'an soyayya haka suke zuba lo

ve abinsu Hussaina kuma itace mai kunyar saikuma ALLAH ya bata marar kunya dan shima Habeeb d'in duk jirgi d'aya ya kwasosu dasu Abdallahn.

Jauhar dai har yanzu ba tsayayye sam bata ma kula masu son nata duk wanda yayi mata maganar aure sai tace ita ba

yanzu zatayi aure ba ba soyayya ce a gabanta ba haka nan take jin duk soyayyar ta fita a kanta anya Jauhar

🤔🤣

.

Abbie da kanshi ya kira Abdallah ya nuna masa ya kamata fa yasamu wadda zai aura bai kamata yayi ta zama haka ba, ya amsa da to ne kawai a

mma shikam bai shiryawa yin aure yanzu ba bai saniba dai ko nan gaba, Jauhar saidai taje Kaduna da ziyara shima kuma saidai su tafi dasu little Janaan suyi kwana biyu su dawo Kano, Abdallah ya tab'a yunk'urin hanawa saida Ammi taci mashi shi ganinshi dan m

e za'a dinga kwasar yara ana faman yawo dasu ko a cikin Kanon indai zataje gidajen su Aunt Deejah dasu Jeeddah dasu take tafiya, Abbie yana yawan tuntub'arta batun aure sai tace masa ba yanzu ba shidai koda yaushe lallashinta yake da nuna mata zuwa yanzu y

a dace ace tana d'akin mijinta saidai tace masa kawai zata duba insha ALLAH shiyasa take jin kunyar had'uwa dashi bataso ya kalleta a matsayin wadda batajin maganar shi ko marar jin maganar na sama da ita.

★★★★

"Nifa Ammin yara akwai wani tunani d

aya fara d'arsuwa a raina amma ban saniba ko abinda nake tunani kema kinyi hasashen hakan". Abbie yayi maganar yana rufe laptop d'in dake kan cinyarshi tareda k'urawa Ammi ido danjin abinda zatace.

"Wane tunani ne wannan Abbie?". Ammi ta tambaya.

Gya

ran murya yayi yace

"Game da Modibbo da y'ar uwar mai rasuwar nan Hassana bakya wani tunani a kansu?".

"A'a Abbie wani tunani kayine a kansu?". ta fad'i hakan ne kawai danjin abinda zai fad'a amma tunda taji yafara maganar tasan tatsuniyar gizo bata wu

ce ta k'ok'i.

"K'warai kuwa Ammin yara ina ganin ta inda aka hau ta nan ake sauka Abdallah ya rasa matarshi itakuma wannan yarinyar har yanzu tak'i tsayawa ta saurari masu son nata bare harta fitar da wanda take so shine nake ganin mezai hana a karo na

biyu a k'ara aura masa ita kinga zai dinga ganinta kamar Janaan tunda kamarsu d'aya kuma komai nasu iri d'ayane shi kanshi sai hankalinshi yafi kwanciya idan ita d'in ya aura ko don saboda yaranshi itace kawai bazaiyi d'ar ko tararrabi ba dan yaranshi suna

hannunta itama kuma yanzu rabata da yaran nan ai yak'i ne babba inaga shine musabbabin ma da har yanzun tak'i fitar da wanda zata aura d'in amma idan itace muma hankalinmu kwance munsan wadda suke hannunta yadda mahaifiyarsu zata rik'esu da tana da rai it

ama haka zatayi

musu amma ke meye shawarar ki akai".(Kai Abbie wannan magana haka ba jan numfashi duk nagaji

😬🙃

).

Jinjina kai kawai Ammi take alamun gamsuwa da maganar Abbie itafa koda sau d'aya bata tab'a kawowa ranta wannan maganar ba cikeda jin da

d'i tace

"Gaskiya ne Abbie wannan tunanin naka yayi daidai wllhy kuma shawara ce mai kyau fatanmu dai ALLAH yasa su amince dan dukansu ba kanwar lasa bane dan ma rasuwar Janaan tasa duk sun d'an rissina ba laifi".

"Insha ALLAHU zasu amince kuma insha

ALLAH alkhairi ne zan kira Alh Isma'eel d'in a waya mu tattauna batun ALLAH ya zab'a abinda yafi zama alkhairi".

"Amin Amin Abbie". Ammi ta amsa cikin farin ciki dagani maganar da Abbie yazo da ita ba k'aramin dad'i tayi mata ba.

A hasashenku waye z

ai bada mtsl tsakanin Madugu da Jauhar? A kafta

🤣

.

Mrs Salees Mu'az

💝

3/13/22, 07:08 - Ummi Tandama

😇

: *WATA SOYAYYA*

💝

Page 37.

Paid book.

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*.

©Oum Hanan.

Cikin kwana biyu maganar duk ta karad'e kunnuwan

manyan cikin familyn na son had'a Abdallah da Jauhar aure da Abbie yake sonyi a karo na biyu kuma kowa yayi na'am ya bada goyon bayan yin hakan, sudai kam ma basu san wainar da ake toyawa ba ba sai a yau ne da Abbie yayi shirin sanar dasu dan yana sone a

had'a bikin gaba d'aya danasu Ja'afar ayi a huta gaba d'aya.

Kamar yadda akayi lokacin Janaan hakan ce ta k'ara kasancewa wannan karon akayi zama irin wancan tarihi zai maimaita kanshi kenan

😅

har Jauhar ta hallara kiran da akayi mata Madugu ne kawai

baizoba, Abbie yana shirin k'ara kiranshi a waya saikuma ya bud'e k'ofar falon ya shigo yana sanye cikin bak'in wando plain da farar riga mai dogayen hannuwa wadda ta d'an kamashi kad'an ya nad'e wuyanshi da abubuwan daya saba nad'ewa black color sai bak'

in agogon fata dake d'aure a hannunshi wanda ya haska farar fatarshi sosai sai k'amshi yaketa uban zabgawa wanda har yanzu Jauhar bata san wani irin mayen turare bane wannan mai masifar k'amshi haka gashi k'amshin mai sanyi bamai hawa kaiba har wani irin y

anayi take shiga mai wahalar fassararuwa idan taji wannan k'amshin na Abdallah, guri yasamu ya zauna yana k'ara gaishesu kowa ya amsa fuska a sake tunda ya shigo Jauhar ta kauda kanta dan karma yasa ran zata gaisheshi, shima d'in sau d'aya ya saci kallonta

ta gefen idonshi yayi saurin kauda idanunshi wani abu na k'ara taso masa game da ita gashi ta k'ara zama big girl kyawunta ya k'ara fitowa ga tsabar gayu da iya kwalliya daya zauna mata.

Shiru wajen ya d'auka kafin Abbie yayi addu'a yafara sanar musu a

binda ya tarasu a wajen, cikin sauri Jauhar ta d'ago kai tana kallon su Ammi yayin da gogan ya wani maze sam babu alamun maganar ta girgizashi hankalinshi kwance har wani wasa yake da bezar abinda ke nad'e a wuyanshi yake wanda ya sauko kan k'irjinshi ta k

'asan ido yake kallon Jauhar dan ganin wani irin action zata d'auka, b'ata fuska tayi sosai a shagwab'e tana d'an yatsina fuska tace

"Aure kuma Abbie da Yah Abdallah?".

Kai Abbie ya jinjina mata yana murmushi cikin ranshi yana addu'ar ALLAH yasa ta am

ince dan indai bataso bazai mata dole ba ya d'ora da fad'in

"K'warai yarinyata munga hakan shine maslaha abinda kuma yafi dacewa kenan ki maye gurbin y'ar uwarki dan kulawa da yaranta da kuma basu ingantacciyar rayuwa fiye da kowace mace a duniyar nan m

e kikace?". ya k'are maganar da sigar tambayarta dan jin ta bakinta.

To Jauhar dai ta gado yayanta Abdallah

🤣

dan itama ba b'oye b'oye ba kunya da kawaici a al'amurata dan haka tayi k'asa da kai duk da tanajin kunya da nauyin abinda zata fad'a d'in a ga

bansu Abbie wasa ta shiga yi da y'an yatsun hannunta da sukasha jan lalle wanda saboda kamun dayayi yazama maroon color ya zauna sosai a farin hannunta, jin tayi tak'i magana Abbie yace

"Karfa kice zakiji kunya Hussaina kuma kar kiyi la'akari damu muk

a haifi Modibbo ki fito ki fad'a mana gaskiyar abinda ke cikin ranki kinji autar Mama". Baki ta d'an tura kafin tace

"Ni gaskiya a'a Abbie bana sonshi".

Ido suka zaro dukansu musamman Ayyah da kamar ya fad'o k'asa, Abdallah kam ido ya lumshe cikeda b'a

cin rai yana taune lips d'inshi tamkar wanda yake shirin hudashi lallai yarinyar nan batada mutunci a gaban idanun su Ammi take cewa bata sonshi ta kalli tsabar idanunshi tace bata sonshi a gabanshi zata gane dashi take magana shi tayiwa haka dan mai garin

su.

"Murmushi kawai Abbie yayi duk da dai cikin ranshi sam baiji dad'in abinda ta fad'a d'in ba yace

"Kikace bakya sonshi ko?". Kai ta d'aga tace

"Eh Abbie bana sonshi". tace hankalinta kwance dan ita bata d'auki hakan wani abu ba a ganinta tambayar ta

akayi ta bada amsa kuma ance ta fad'i abinda ke ranta Abbie yana shirin yin magana yaji Abdallah cikeda bala'i yana fad'in

"Ki kalli tsabar idanuna saboda bakida mutunci kice baki sona dan ubanki me kike tak'ama dashi? nace me kike tak'ama dashi ne Jau

har". Kallon sama da k'asa tayi masa tana wani yatsina fuska tace

"Abinda kake tak'ama dashi kaima kuma na fad'a d'in bana sonka ko ana so dole ne?". tayi maganar cikin rashin kunya da tsiwa tana kallonshi, wani irin numfashi ya zuk'a tareda lumshe shan

yayyun idanunshi cikeda b'acin rai da k'uncin zuciya datasan irin halin da zuciyarshi ke shiga idan ta furta wannan kalmar ta BANA SONKA da bata fad'eta ba yanajin tamkar zuciyarshi zata fashe tayi bindiga ne, itama a fusace tace

"Nace bana sonka d'in Y

ah Abdallah akwai abinda zakayi ne? banayi a k'ara gaba ko za'a samu wadda zata taya".

Huci yaja sosai sosai yana cije leb'e tareda jinjina kai yace

"Okayyyyy haka kikace ko? good nikuma zan aureki kota tsiya ne inga matakin dazaki d'auka stupid d'i

n yarinya kawai". ya ida maganar yana fincike abinda ya nad'e wuyanshi dashi ya cillar dashi a k'asa tamkar shine mai laifin ranshi na masa suya da tuk'uk'i.

Baki Jauhar ta bud'e da niyyar maida masa martani Ammi ta daka musu wata tsawa ranta a matuk'a

r b'ace tace

"Ku rufa mana baki shashashan yara kawai yanzu a gaban mu kuke wannan musayar yawun ko kunya bakuji, ke Jauhar ba sama yake dake ba da har kike bud'e baki kike fad'a masa maganar da duk tazo bakinki". Kamar Jauhar zatayi kuka ta bud'e baki

zatayi magana Abbie yace su tashi dukansu subar wajen kar wanda ya k'ara magana a cikinsu, a tare suka tashi tsaye kamar kububuwa haka Abdallah ya fice daga falon da sauri tamkar zai tashi sama Jauhar ta rufa masa baya.

Ajiyar zuciya Abbie ya sauke yace

"Anya kuwa wannan had'in zai yiwu kuwa Ayyah Hussaina ba irin y'ar uwarta bace zamansu bazaiyi dad'i da Modibbo ba".

Jinjina kai Ayyah tayi tace

"Hak'ik'a tun farko sai danayi wannan tunanin kar azo ayi abu daga baya kuma azo ana dana sani ya kamata

dai a k'ara duba lamarin gaskiya".

"Insha ALLAH ba wata matsala Ayyah sai alkhairi dazai biyo baya da anyi auren zasu daidaita tsakaninsu ne duk wadda Modibbo zai aura bayan Jauhar ne muyi musu kyakkyawar addu'a kawai ALLAH ya basu zaman lafiya ya rage

musu zafin zuciyar nan tasu". Duk sunyi na'am da maganar Ammi daga nan kowa ya kama gabanshi saikuma zama na biyu idan buk'atar hakan ta taso.























Kai tsaye side d'inshi ya nufa ya tura k'ofar da k'arfi ya shiga bai tsaya a falon ba ya wu

ce bedroom d'inshi yana shiga ya fad'a bisa bed yayi ruf da ciki idanunshi a rufe zuciyarshi na masa wani irin zafi wai shin Jauhar tasan tsahon lokacin daya d'auka yana dakon soyayyar ta kuwa? shin batasan itace BUGUN NUMFASHI DA ZUCIYARSHI BA? duk abinda

yake mata kawai yana yine saboda alamunta daya gani batada kunya bazasu tab'a daidaitawa da itaba, Jauhar tun tana y'ar shekara hud'u zuwa biyar ya kware mata a soyayya a lokacin dayaso bayyana mata kuma aka shigo masa da zancen auren Janaan bai tab'a kaw

owa zuciyarshi auren wata ba bayan Jauhar ko a kanshi bai tab'a kawowa zaiyi rayuwar aure da wata d'iya mace ba sab'anin Jauhar amma saboda lamarin ubangiji juya

k'addara da sarrafata ba'a hannunmu yakeba sai gashi rabon su little Janaan yasa sunyi aure da

Janaan sun samu kyakkyawar shekara d'aya a matsayin ma'aurata daga baya ubangiji yazo yayi ikonshi akanta ta tafi ta barshi da yara biyu, koda su Abbie basuyi masa tayin auren Jauhar ba shi zai nemi hakan lokaci yayi dazai fallasa sirrin zuciyarshi lokaci

yayi daya kamata ya bayyana mata ciwon daya dad'e yana fama dashi a zuciyarshi dama gangar jikinshi ya daina k'warar kanshi haka saigashi a gabanshi take ta maimaitawa da nanatawar bata sonshi saboda ita d'in batada mutunci aikuwa zai nuna mata kalar nash

i rashin mutuncin dama yayi k'aurin suna a wajenta dole ma saita aureshi (Tsohon k'ok'ari

🤔🙄

).

Tsaki ya dinga ja daga kwancen dayake kafin daga bisani ya tashi ya nufi wata drawer sai daya lalubo key d'inta cikin wata drawer ta kusa da ita sannan ya bu

d'e ya d'auko wani k'aton dairy ya koma kan gadon ya zauna tsakiyar gadon sannan ya fara bud'e littafin shafi na farko yana bud'ewa na fara cin karo da hotunan wata kyakkyawar yarinya y'ar kimanin shekaru biyar fara tas da ita wajen guda goma k'ananu kalo

li daban daban wasu sanye take cikin k'ananun kaya wasu kuma manya gasu nan dai dayawa wani tana rik'e da teddy bear wani tana dariya wani ta shagwab'e fuska ta turo baki kamar zatayi kuka style kala kala wani ma dana gani kukan take ta cika bakinta da Pop

corn ta bud'e bakin gaba d'aya abin dariya, saidana k'ura mata ido sannan nagano ashe Jauhar ce

ta hoton, sassanyar ajiyar zuciya ya saki tareda lumshe ido yakai hannu kan hotunan yana shafasu daki daki yake tariyo lokacin da akayi kowane hoto shi kad'ai

yake murmushi yana hango time d'in dayake d'aukarta kowane pic da digital camera

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login