Showing 3001 words to 6000 words out of 96447 words
dan in bakayi musu cikakken sani ba to kuwa bazaka iya bambance su ba , ba kamar na Ammi da sam basu kama kamar ba twins bama idan ba an fad'awa mutum ba. ta b'angaren halayyar sune kawai ake ganesu dan ita Janan tanada sauk'in kai da sanyin hali g
a hak'uri da kawaici sab'anin Jauhar datake matsiwaciya ga rashin kunya da d'an banzan surutu, suna first year d'insu ne a higher level inda Janan take kano gidansu Abdallah tana karatunta a B.U.K wato Bayero university Kano itada Hassana da Hussaina, itak
uma Jauhar acan Kadunan take nata karatun a poly. Sunada kyau mai d'aukar hankali ga diri da ALLAH yayi musu da kyan sura komai nasu iri d'ayane.
Itama Maryam wadda suke kira da Momy a yanzu ta aurar da Zakiyyah Hameedah da Kulthum d'in sai auta H
annah datake gabanta a yanzu tana karatu saikuma Abdallahnta da shima baiyi auren ba yake aiki a wani babban company na babansu wanda ake sarrafa fata.
Wannan shine tarihin madugu family a tak'aice ga kuma su Jauhar dasu Abdallah suka had'a alak'a ta j
ini dasu ta b'angaren Ammi.
A yau alhamis Abdallah yake dawowa daga k'asar Italy wani course dayaje duka na wata biyu duk akan aikinshi na zane a yaune kuma yake dawowa k'asar.
Tun safe Hassana da Hussaina ke kaida kawowa wajen yin girke girke
kasancewar basuda lecture ita Janan tun 7@m tabar gidan.
"Dan ALLAH sis ya kikaji gidan nan da Yah Abdallah baya nan?". Hussaina ce tayi maganar tana blending aya da coconut a blander.
"Hmm very nice wllhy
π
". Hassana tabata amsa lokacin datake k'
ok'arin zuba yankakkiyar hanta a cikin pot d'in dake kan gas cikin kayan miyan da akayi blending d'insu sama sama.
Y'ar dariya Hussaina tayi tace
"Zakije d'auko shine a airport?".
Ido Hassana ta d'an zaro tace
"Wllhy ba inda zanje tab! maybe Yah
Ameen ne kawai zaije fa".
"Nima dai zan masa addu'a daga nan ALLAH ya saukeshi lafiya". dariya suka saka gaba d'ayansu suka cigaba da aikinsu.
Maganar Yah Ameen sukaji daga falo yana yiwa Ammi sallama zaije airport ya d'auko Abdallah tayi masa fata
n dawowa lafiya.
KANO NIGERIA.
Mallam Aminu kano airport.
K'arfe 10@m jirginsu Abdallah yayi landing, bayan wani lokaci mutanen dake ciki suka fara saukowa. Mutum na shida dake cikin jerin masu saukowa idanuna suka kai kanshi 'Masha ALLAH' it
ace kalmar dana ambata lokacin dana ganshi, kyakkyawa saurayi fari tas mai had'e da sirkin jaa kwantaccen sajen daya k'awata fuskar shi ya k'ara fito da ainahin kyawun da ALLAH yayi masa, sai matse d'an k'aramin pink lips d'inshi yake wanda
yake tamkar ya
turasu da jambaki a tak'aice dai ya hadu ta ko ina komai yaji masha ALLAH.
Sanye yake cikin k'ananun kaya na kamfanin DKNY wandon da rigar duk blue black ne sai black jacket daya d'aureta a k'ugunshi k'afarshi sanye cikin bak'in boot hakama hannunshi
d'aure yake da bak'in agogon fata na kamfanin Gucci sai bak'ar P.cap dake kanshi wadda ya juya gaban hular baya ya toshe idanunshi da bak'in google hakan yasa ba'a ganin k'wayar idanunshi wata doguwar luggage ce goye a bayanshi ta gayu, cikin takunshi na m
ai cikakkiyar lafiya da kazar kazar yake saukowa daga step d'in jirgin harya k'arasa sauka gaba d'aya k'ugunshi ya dafe da hannu d'aya d'aya hannun kuma yakai kan P.cap d'in dake kanshi ya fara wuwwurga idon inda zaiga wani nashi saidai ba wani wanda yasan
i tsadaddiyar wayarshi dake hannunshi ya shiga dubawa da nufin kiran Yah Ameen yana shirin yin dialling number Yah Ameen d'in yaji daga bayanshi an dafa kafad'arshi hakan yasa ya juya dan ganin kowaye sukayi ido hud'u da Yah Ameen yana murmushi tareda mik'
o masa hannu alamun suyi musabaha shima hannun ya mik'a masa sannan sukayi hugging juna cikeda murnar ganin juna da sukayi. Bayan sun saki juna ne Abdallah yace
"Nifa ban ganeba bros yana ganka kai kad'ai, kana nufin kace kai kad'ai kazo taryana?".
"Dawa zaka ganni da? kaidai ba buk'atar ka akaika gidaba?". Yah Ameen ya amsa masa.
"Two months bana gida bros amma sai kai kad'ai ai kamata yayi ace an cika airport d'in nan da masu tarona ko".
Gaba Yah Ameen yayi yana fad'in
"Ai dayake ga d'an s
hugaban k'asa ko let's go malam inbaka zuwa inyi tafiya ta".
Bayanshi yabi yana fad'in
"Kaga Habeeb ma yace zaizo baizoba saina masa rashin mutunci wllhy".
Baki Yah Ameen ya tab'e yace
"Wannan kuma kunfi kusa".
Suna zuwa inda motar Yah Ameen ta
ke ya bud'e back seat ya jefa luggage d'in ciki yadawo ya bud'e front seat ya shiga Yah Ameen yayiwa motar key suka bar wajen, kujerar dayake kai ya kwantar yayi relaxing sosai akai tareda tallafe kanshi da duka hannayenshi idanunshi a rufe har lokacin bai
cire glasses d'in ba, juyowa Yah Ameen yayi ya kalleshi baidai ce komai ba ya juya ya cigaba da driving d'inshi, saida suka fara nisa sannan Yah Ameen ya shiga tambayar shi kan abinda ya kaishi Italy d'in yana a hakan yake bashi amsa daga nan kuma suka sh
iga hira ya shiga bashi labarin yadda ya gudanar da course d'in nashi a can. Da haka har suka k'arasa bakin wani k'aton gida yayi horn aka bud'e gate d'in ya danna hancin motar tashi ciki.
Babban parking lot d'in dake farfajiyar gidan ya shiga wadda
ke d'auke da manya manyan motoci da suka had'a dana Abbie na Yah Ameen d'in dana uban gayyar Abdallah saikuma ta Ammi guda biyu, yayi parking.
"Wow I'm very happy wllhy, gida na daban ne Bros". Abdallah ya fad'a yana tashi zaune, shidai Ameen bai kulas
hi ba ya bud'e motar ya fita shima bud'ewar yayi ya fita yana k'ara bin gidan da kallo kamar wanda yayi wasu shekaru baya ciki, Baba maigadi da isya mai bawa flowers ruwa suka k'araso suna masa barka da dawowa hannu yaba kowanne sukayi musabaha yana amsa m
usu sannan suka koma bakin gate inda suke zaune kan benci suna hira.
Tare suka jera da Yah Ameen zuwa general parlor d'in gidan suka shiga d'auke da sallama a bakinsu.
Ammi da fitowarta kenan daga kitchen suka shigo ta saki murmushi tana amsa sallam
ar.
"Oyoyo Amminaaaaa". ya fad'a da k'arfi yana dariya tareda bud'e hannayenshi ya nufeta da sassarfa ya rungume ta, kai kawai Ameen ya girgiza ya nemi waje ya zauna, cikin farin ciki Ammi ke fad'in
"Oyoyo my son welcome back andawo lafiya?". ta k
'are maganar tana d'agoshi daga jikinta.
"Lafiya Ammi saidai kewarku danayi I miss you so much wlhy". ya fad'a yana karyar dakai.
Murmushi Ammi tayi tace
"Toh koma dai meye ai gashi ka dawo sai fatan nasara kuma kan abinda akaje yi, yanzu ga dinni
ng can an shirya maka wanka zaka fara yine kokuwa?".
Glasses d'in daya cire tun shigowarshi ya mak'ala a gaban rigarshi yace
"Ammi zan fara yin wankan kawai saboda nagaji over wllhy".
"To shikenan oya aje ayi wankan". Ammi tace tana barin wajen
, juyawa yayi zai fita sai lokacin yaga Ameen ma ashe baya falon, har zai fita ya hangi su Hassana a tsaye sunyi tsamo tsamo kamar wad'anda sukayiwa sarki k'arya sai raba ido suke, tsaye yayi yana kallonsu kafin yace
"Tsayuwar me kuke a nan dan ubanku,
wato sannu da zuwan da zakuyi min shine ya gagara ko".
Da sauri suka had'a baki wajen yimasa sannu da zuwan suka d'ora da fad'in dama yanzu zasuyi masa.
K'wafa kawai yayi yana hararar su ya nuna Hussaina yace ta karb'o masa key d'in d'akinshi waje
n Ammi, cikin hanzari ta nufi upstairs itakuma Hassana ta lallab'a tabar wajen kafin ya lalubo wani abun yace tayi.
Key d'in ta karb'o takawo masa ya karb'a ya fita yana cillashi sama, k'irjinta ta dafe tana sakin ajiyar zuciya sannan ta nufi d'akinsu
.
Mrs Salees Mu'az
π
Maryam Ibraheem Aleeyu
HASKE WRITERS ASSOCIATION
π‘π‘π‘
TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A
ZAFAFAN LITTAFAI MASU SAKA SHAUK'I, FADAKARWA K'AYATARWA NISHADANTARWA HAR GUDA 7!!!
GA SHIRI NA MUSAMMAN
INA MASU SON KOYAN
GIRKUNA DA MASU SON KARA SANIN SIRRIN MALLAKE MAI GIDA
ππ»ππ»ππ»ππ»
KUDIN RAJISTA - 500 (NAIRA DARI BIYAR GABA DAYA)
*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*
GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA K
ARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair
Ι
ari biyal kacal.
*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*
*SAI YA TURA KUDINSA TA*
2083371244
Zenith Bank
Aisha
M.Salis
*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number
ππΌππΌ
*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA
BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*
*Ζ³AN NIGER
π³πͺ
, ZAKU IYA TURA KUΖINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
2/14/22, 08:40 - Ummi Tandama
π
: *WATA SOYAYYA* β₯
οΈ
π©Έ
β₯
οΈ
*HASKE WRITER
'S ASSOCIATION*
(Home of expert & perfect writer's)
*TOP TEN TAKUN HASKE BATCH [A]*
Writer: Oum Hanan
The writer of DR SAIF
π©Έ
Free page
Fiction story
03
Wani part d'in naga ya nufa ya bud'e k'ofar ya shiga wasu k'ofofi biyu suka
bayyana ta k'arshen ya bud'e ya shiga wani madaidaicin falo ya bayyana sam babu tarkace a cikinshi amma yayi kyau sosai ya tsaru, set d'in kujeru ne fari da purple sai curtains suma fari da purple saikuma plasma medium size dake jikin bango kusa da TV stan
d da akayi adon wasu k'ananun flowers akai, purple d'in grass carpet ne shimfid'e a tsakiyar kujerun sai k'aramin center table akai da kuma can tsakanin 3sitter da 2sitter kowace kusurwa ka kai idanunka a jikin bangon falon zaninnika ne kala kala a lik'e w
anda zai tabbatar maka da cewa mamallakin d'akin mai zane ne, tsaf komai yake a muhallinshi sai tashin k'amshi yake da alamu dai mai gyaran saida yayi taka tsantsan dan gudun h
ayagagar Abdallah
π
.
Wata k'ofa dake hannun damanshi ya nufa ya tura ya s
higa bedroom d'in, shima dai bawani babba bane irin sosai d'in nan madaidaicin gadone dayaji tattausan bedsheet da blanket da aka d'ora akai, sai clothes ta jikin bango saikuma mirror dake cike da kayan shafe shafe da uban turaruka tamkar wata mace sai k'a
ramin carpet dake shimfid'e a k'asan gadon, daga kan kayan gadon zuwa curtains da wallpaper dake jikin bangon duk fari da purple ne shima bedroom d'in da alamu fav color d'in mai d'akin ne tako ina an k'awata jikin bangon da drowing na tsuntsaye da fulawoy
i sai inda fuskar gadon take da aka lillik'a hotunanshi kala kala.
P. cap d'in ya cire kwantacciyar sumarshi ta asalin fulani ta bayyana wadda ta kwanto har bayan wuyanshi bak'a wuluk, ya wulla saman bed d'in ya kwance jacket d'in itama ya wullata ya
zauna bakin gadon ya sunkuya yana kwance igiyar takalmanshi kafin ya ciresu fara tas din k'afarshi ta bayyana mai d'auke da zara zaran y'an yatsu wadda tayi gumi kad'an, tashi yayi ya cire kayanshi ya shiga bathroom sharp sharp ya fito bayan yayi wankan fa
rar riga yasa mara nauyi mai yankakken hannu da farin wandon three quarter Arabian perfumes dake cike kan mirror d'in ya feffesa ya d'auki farar P. cap ya saka dan shi d'in ma'abocinta ne, wayarshi ya d'auka ya zura farin slipper mai taushi ya fita ya rufo
k'ofar ya nufi falon su Ammi hannunshi d'aya cikin aljihun wandonshi kanshi a k'asa yana duba number Habeeb abokinshi ne sosai tun a unguwar da suka fara zama tare sukayi primary school sukayi secondary har zuwa lokacin da kowa ya tafi k'asar da zaiyi kar
atu, sun shak'u sosai ta yadda har iyayensu ma suka k'ulla alak'a ta zumunchi a tsakaninsu, shikuma Habeeb d'an kasuwa ne gashi dai yayi karatun amma kuma kasuwanci yake abinshi zai d'an girmi Abdallah amma tsiran bamai yawa bane.
Lokacin daya shiga
falon a lokacin ne kuma Habeeb yayi picking d'in wayar yana fad'in
"Habeeb Umar Marafa ke magana who is the line?".
Saida ya d'an cije baki sannan yace
"Ubanka ne akan layi ni zakawa iskanci Habeeb?". Dariya Habeeb ya shek'e da ita, K'wafa Abdal
lah yasaki lokacin daya k'arasa dinning table d'in yaja kujera ya zauna yana fad'in
"Dan ubanka ya mukayi dakai jiya? yana maganar yana janyo plate gabanshi tareda tsiyayar coconut juice a glass cup yakai bakinshi ya fara sha
Cikin dariya Habeeb
yace
"Kasan ALLAH A.B seriously wani important issues ne ya tasomin wanda dole sainaje wajen naso inje airport in taroka amma karka damu zan shigo anjima ko zuwa dare ne insha ALLAH".
"Okay saika shigo d'in". Abdallah ya fad'a tareda yin hanging d'in
kiran, wayar ya ajiye ya bud'e wata warmer yaga tuwon shinkafa a ciki fari tas an sakashi a farar leda.
"Tuwo kuma? yace yana b'ata fuska gamida ture warmer d'in gefe ya shiga k'walawa Hassana kira da uban k'arfi, lokacin suna zaune kowacce da handout
a hannunta suna dubawa sukaji kiran da sauri kowacce ta aje littafin hannunta tareda zaro ido suna kallon juna kowacce gabanta na bugawa, jin ya k'ara k'wala wani kiran yasa Hassana ta zabura ta fita cikin sauri har tana hard'ewa Hussaina ta bita da kallo
tana addu'ar ALLAH yasa dai bawani laifin sukayi ba saita kasa cigaba da duba littafin ta shiga tsumayen dawowar Hassana.
A tsorace ta isa gurin dinning d'in inda Abdallah ke zaune yana jefo mata harara, d'an nesa dashi ta tsaya jikinta na rawa kan
ta a k'asa cikin rawar murya tace
"Yah Abdallah gan......."Uban waye yace kuyi min tuwo? Indawo k'asar yau ku tareni da tuwo saboda bakuda mutunci dan ubanku". ya katseta cikin hargagi.
"Wllhy Yah Abdallah.... kallon dayayi mata yasa tayi shiru kama
r zatayi kuka, Ammi dataji hayaniyar Abdallah ta fito daga kan upstairs d'in ta tsaya tace
"Wai meyake faruwa ne anan Modibbo?".
"Ammi tuwo nefa sukayi min wai su rasa me zasu girkamin sai tuwo kuma sun san bana cinshi".
Kai Ammi ta dafe tana fad
'in
"Modibbooo meyasa kake hakane? shin ka bud'e sauran warmer's d'in kaga abinda ke ciki? wannan tuwon mafa na Abbienku ne yace yana sha'awa nayi masa kuma bansan wanda ya d'aukoshi ya kawo nan ba kake faman tada jijiyar wuya akai, dan ALLAH ka dinga sas
sautawa zuciyarka". daga haka ta juya ta koma bedroom d'inta.
Wata warmer ya janyo ya bud'e yafara zuba had'add'iyar fried rice dake ta tashin k'amshi kad'an ya zuba ya zuba cows low a gefe da cinyar kaza, ganin har lokacin Hassana na tsaye kanta a k'
asa tana tsoron tafiya yace tayi wani laifin.
"Zaki bar wajen nan ne kokuwa saina tashi kanki". yace yana k'ok'arin d'iban abincin a spoon batare daya kalleta ba, kamar wadda ke jira kuwa tabar wajen da sauri.
Tana shiga bedroom d'insu ta saki ajiy
ar zuciya tana zama kusa da Hussaina datake kallonta, Hussaina tace
"Wai kiran meyake miki ne haka?".
"Hmm waifa kawai dan yaga tuwo shine na wannan kiran wai ubanwa yace muyi masa tuwo".
Baki kawai Hussaina ta tab'e tace
"ALLAH ya kyautawa mutum
in nan wllhy, nifa maybe inyi tafiyata gidan Aunt Deejah wllhy wannan bala'i har ina".
"Idan ma kinje zaki dawone yarinya, kuma tunda ya dawo d'in nan kuma ai babu sauran sakewa, dad'ina da Yah Ameen kenan ba ruwanshi dakai indai ba gani yayi zaka kauc
e hanya ba".
Karatun da basu cigaba dashiba kenan suka shiga gulmar Yah Abdallah
π
.
^β^β^β^β^β^β^
βΏ
Yana gama cin abincin ya tashi ya fita part d'insu ya koma ya shiga d'akinshi ya kwanta, barci yakeso yayi saboda gajiyar dayake ji a
jikinshi bai dad'e da kwanciyar ba kuwa barcin yayi awon gaba dashi.
JANAN.
A gurguje tayi wanka bayan dawowar ta school yau tagaji sosai ga yunwa dan batayi breakfast ba ta fita kuma sam ita ba kasafai take cin abinci a makaranta ba, sama sa
ma ta shafa lotion da body spray ta zura doguwar rigar wani yadi mara nauyi ta yafa mayafi mai d'an girma akan rigar tasa slippers ta fita zuwa dinning table a falo.
Tana saka kai falon ta hangoshi akan kujera yayi wani zama shi ba'a kwance yakeba hak
a kuma ba'a zaune ba, hannunshi d'aya rik'e da juice yana sipping a hankali d'ayan kuma rik'e da waya yana danne danne, wani irin mugun bugawa gabanta yayi tayi saurin dafe k'irji tareda ja baya