Showing 9001 words to 12000 words out of 96447 words

Chapter 4 - Wata Soyayya Complete

03 Sep 2026

25

/>
Fita yayi daga motar ya zagaya front seat inda Ja'afar yake shim

a lokacin ya fito shi ya shiga shima Ja'afar ya zagaya driver seat ya shiga ya zauna ya tada motar suka cigaba da tafiya.

Tunda suka tafi Abdallah bai k'ara magana ba duk da Ja'afar yana takalarshi da hira amma yai masa bakam kamar ba dashi yakeba gani

n haka yasa shima yaja bakinshi yayi shiru.

Suna shiga unguwar ana kiran sallahr magreebah dan haka Ja'afar yayi parking anan k'ofar gida sukayi alwalah suka shiga masallachin dan sauke farali.

Bayan an idar suka fito tare har lokacin Abdallah b

ai yiwa Ja'afar magana ba shima kuma bai kulashi ba dan yasan idan y'an tsiyar suna kanshi to duk surutun mutum bazai tanka masa ba.

Tare suka jera har k'ofar gidan Ja'afar yayi knocking k'ofa saboda yanasa ran zai k'ara fita shiyasa bai shiga da motar

ciki ba.

Babban falon gidan suka nufa Abdallah na gaba Ja'afar na biye dashi kamar makaho da d'an jagora, lokacin da suka shiga ba kowa a falon sai TV dake a kunne akan tashar sunnah TV inda suke haska wa'azin Dr Umar sani rijiyar lemo, dukansu waj

e suka samu suka zauna ba wanda yayi magana, daidai lokacin Mama ta fito falon ta gansu zama tayi tana fad'in

"A'ah yaushe kuka shigo gidan?".

Ja'afar ne kawai ya bata amsa da fad'in

"Yanzu muka shigo Mama".

Kallonta ta maida kan Abdallah da har l

okacin baice uffan ba yayi relaxing kan kujerar ya d'aga kanshi sama yana kallon Pop d'in falon da suka wadatu da fitilu masu haske, sai faman girgiza k'afa yake idanunshi a rufe.

"A'ah waya tab'o wannan d'an tutsun nawa Ja'afar?".

Dariya Ja'afar y

ayi yana kallon Abdallah daya d'ago kai yana hararar shi yaba Mama labarin abinda ya faru ya k'are da fad'in 'Nace masa maybe yanada wani uzurin ne na gaggawa shiyasa' murmushi kawai Maman tayi tace

"Abdallah ho, tunda dai ALLAH yasa ba abinda ya faru

daku ai sai a godewa ALLAH ko ta bakin na Ja'afar k'ila da wani uzurin dazaije ya gabatar".

"Amma kowane uzuri ne ai ya kamata ace ya tsaya yabamu hak'uri ko?".

"Gaskiya kam bai kyauta ba ayi dai hak'uri".

K'wafa yayi yana cije baki yace

"Wllhy

badan dattijon nan ba da sai naci........"Easy dai Alajiii". Ja'afar ya katseshi yana dariya dan yasan k'aramin aikinshi ne ya danna zagi yanzun nan.

Tashi Mama tayi ta bar falon tana dariyar Abdallah shifa duk abinda yazo bakinshi fad'a yake wani lok

acin saidai kai ya barka da jin kunya.

Shima Ja'afar tashi yayi yacewa Abdallah ya tashi su wuce side d'inshi yak'i kulashi sai waya daya zaro yafara dannawa, baki Ja'afar ya tab'e ya wuce ya barshi anan.

Ja'afar na barin falon na hango wata mata

shiyar budurwa mai kama da Janan sak ba abinda ya rabasu, sanye take cikin riga da siket na atamfa wad'anda suka d'an kamata kad'an kalar atamfar bak'i da orange ne sai touch d'in green kad'an tayi d'aurin nan na malha wanda ya k'awata zagayayyiyar fuskar

ta sai k'aramin vail datayi rolling dashi fuskarta fayau ba wata kwalliya powder ce kawai sai lipgloss data shafa wanda yasa y'an k'ananun lips d'in nata keta faman k'yalli da d'aukar ido, hill shoes ne sosai a k'afarta black color sai k'aramar jaka data s

ak'ala a hannunta, so simple kwalliyar tata amma ta bada ma'ana. Tunda ta doso wajen wani sassanyan k'amshi ya gauraye ko ina.

Wanda ta gani a zaune ne yasa gabanta yayi mugun bugawa, cak ta tsaya tana tunanin abinda ya kawo wannan Mr arrogant d'in gid

an nan kamar sunce suna gayyatar shi? yanzu zaizo ya fara takura mata dasa mata ido, k'aramin tsaki taja cikin ranta ta d'auke kai ta nufi wani dogon corridor dazai sadata da bedroom d'inta dan duk zatonta bai ganta ba saboda kanshi na k'asa yana latsa way

a batasan yana kallonta tun shigowarta ba ta k'asan idanunshi saboda tun dosowarta falon yaji bugun zuciyarshi ya

canza yasan kuma itace, d'agowa yayi lokacin da take daf da shigewa corridor'n murya ya d'aga sosai yace

"Ke zo nan". yayi maganar yana ma

ta alamun tazo da hannunshi.

Cak ta tsaya tareda turo baki gaba, tasan halin bala'i da masifarshi hakan yasa ta juyo ta nufo inda yake zaune, tsaye tayi a kanshi lokacin data k'araso tana faman zumb'urar baki.

Ajiye wayar yayi a kusa dashi ya d'aga kai

ya kalleta a fusace yace

"Ke bakida tarbiyya ko k'asa dan ubanki". ya k'arasa kamar zai tashi tsaye, cikin sauri ta durk'usa k'asa.

Cikin tsare gida yace

"Daga ina kike yanzu da magreebahr nan?".

Shiru tayi tak'i magana sai b'ata rai take tana

faman kumbura baki.

"Ba zakiyi magana ba". yace cikin tsawa

"Naje biki nefa na friend d'ina". kamar zatayi kuka take maganar tana hararar shi ta gefen ido.

Baki ya cije yace

"Biki kikaje? kuma sai yanzu kikaga damar dawowa ko saboda bakida mutun

ci, k'wafa yayi yana kad'a kai yace

"Zanyi maganinki ne very soon ware daga nan". kamar wadda ke jira kuwa ta tashi da sauri har tana gurd'ewa da takalminta mai uban tsini, dan tasan k'aramin aikinshi ne ya kai mata duka yanzun nan ba abin damuwa bane a

gurinshi.

Zama ya cigaba dayi a wajen har lokacin da Ja'afar ya dawo Mama ma ta dawo ta zauna suka cigaba da hira, Hajiya Yaya dai tana d'aki abinta bata fitoba tasan matuk'ar ta fito sai d'an banzan yaron nan yasata magana dan haka tai zamanta a d

'aki.

Suna nan zaune Alh Isma'eel yadawo gidan da sallama ya shigo falon suka amsa masa dukansu suna masa sannu da zuwa, sosai fuskarshi ta washe da fara'a lokacin dayaga Abdallah cikin fara'a yake fad'in

"A'ah my son saukar yaushe?".

"D'azu nazo

Daddy". Ya bashi amsa.

Ganin fuskarshi ba yadda ya saba ba yasa Alh Isma'eel yace

"Wai waya tab'o min mutumina ne haka?". yayi maganar yana kallon Mama daketa murmushi k'warai da gaske tanajin dad'in yadda mijin nata ke nunawa y'an uwanta kulawa mu

samman Abdallah da idan ba an fad'a maka ba zakayi zaton shine ya haifeshi saboda yadda suka shak'u da juna.

Cikin murmushi Mama tace

"To gashi nan dai wannan mutumin naka mai wuyar sha'ani wani ne ya tab'o shi daga waje".

Murmushi Alh Isma'eel ya

yi yana mik'ewa tsaye yace

"Tofa! zo nan ka fad'amin waye ya tab'aka".

Tashi Abdallah yayi Alh Isma'eel ya k'araso wajenshi ya sak'alo hannunshi a kafad'arshi suka fice waje yana k'ara tambayarshi.



Bayan sallahr esha'e aka had'u a dinning table

akayi dinner, sanin Abdallah na gidan yasa Jauhar tak'i fitowa yin dinner sai bayan da aka gama sannan ta fito ta d'iba nata a plate ta shige d'aki.

^√^√^√^√^√^√^√^

Kwanan Abdallah biyu amma duk yabi ya gallabi Jauhar ya hanata sukuni, ko f

ita baya barinta yauma ta shirya zata fita tana fitowa ta ganshi zaune a farfajiyar gidan akan farar kujera ya fatattakota yace ba inda zata duk yadda ta dinga magiyar ya barta yak'i yace ba inda zata aikuwa taji haushi sosai haka dolenta takoma cikin gida

n kamar zatayi kuka harga ALLAH ta matsu yakoma garinsu ita bataga ubanda yazoyi nan bama wllhy aikuwa zaisan ya hanata fita wlhy.

Kome Jauhar zata yiwa Abdallah madugu

😅

.

Bayan tashin shi a nan ya shiga part d'in Ja'afar dan yin wanka, s

hirt d'in jikinshi ya cire da dogon wandon jeans d'in dake jikinshi ya rage dagashi sai boxer dama ba singlet a jikinshi ya shiga bathroom.

Bathtub ya cika da ruwa na sanyi dana zafi ya daidaita d'umin ya shiga ciki, yana kai hannu cikin ruwan da niyya

r d'ebowa yaji wani abu ya tsikareshi a hannu runtse Ido yayi lokaci d'aya yana saurin fito da hannun daga cikin ruwan tareda kai idonshi ciki dan ganin meye idanunshi suka nuna masa wata k'atuwar kunama bak'ikk'irin a tsorace ya mik'e tsaye yana zaro ido

cikin matuk'ar mamaki da al'ajabi tabbas lokacin daya shiga cikin ruwan ba komai a ciki to ta ina kunama ta shigo? Fita yayi daga ciki ya figo towel ya d'aura koda ya k'ara kai dubanshi cikin ruwan ba kunama ba alamarta, mamaki ne ya k'ara kamashi lallai a

kwai ayar tambaya akan wannan al'amarin anya ba Jauhar ce da wannan aikin ba? yess tabbas itace saboda ya hanata fita, lallai zaici ubanta kuwa muguwa.

Fitowa yayi daga bathroom d'in ya bud'e trolley d'inshi ya ciro bak'ar shirt da farin wando yasa du

k da halin dayake ciki saidaya d'auki farar P. cap data zame masa ta k'a'idah yasa

😂

dan zuwa lokacin hannun yafara masa rad'ad'i turare ya fesa ya fita ya rufo k'ofar d'akin ya fita harabar gidan sai faman cije baki yake yana tunanin irin hukuncin da zai

yiwa wannan muguwar yarinyar.

Yana fita compound d'in Ja'afar ya shigo gidan.

"Muje ka kaini hospital Ja'afar". ya fad'a lokacin da Ja'afar ya k'araso wajenshi, idanunshi sun kad'a sunyi jawur yana rik'e da hannunshi wanda yake masa uban zugi da za

fi.

"Meya faru ne Bros na ganka haka?". Ja'afar yace yana kallonshi da mamaki ganin yadda ya koma ga fuskarshi datayi jaa.

"Zaka wuce ne muje ko tambayata zaka tsaya yi?".

Baki kawai Ja'afar ya tab'e ya d'aga hannayenshi sama yana fad'in

"ALLAH

ya baka hak'uri".

Tsaki kawai Abdallah yaja yayi gaba inda motar Ja'afar take, yana zuwa ya bud'e front seat ya shiga yaja murfin ya rufe da k'arfi, Ja'afar shima daya k'araso ya shiga driver seat ya kunna motar kafin daga bisani yajata suka bar gidan.

Sai daya hau kan babban titi sannan Ja'afar ya k'ara waigowa ya kalli Abdallah dayake ta matse baki yana huci, dariya ce taso kamashi duk da baisan abinda ya sameshi ba mazewa yayi yace

"Wai dan ALLAH Bros meyake faruwa? meyasamu hannun naka?".



K'wafa Abdallah ya saki yana jijjiga kai yace

"Ni yarinyar nan zatayiwa haka? in hanata fita tayi min k'ofi? na rantse yau sai Jauhar ta gane kurenta".

Sai a lokacin Ja'afar ya fahimci inda akalar maganar take wato Jauhar ya hana fita unguwa itakuma t

ayi masa halin nasu na y'an biyu lallai ta tarowa kanta match.

Dariya ce taso kama Ja'afar ya wani maze ya shiga sosa kanshi da d'aya hannun da baya tuk'in dashi kafin kuma dariyar ta sub'uce masa ya shiga k'yak'yatawa harda dukan sitiyarin, haka ya has

ala Abdallah ya kaiwa Ja'afar naushi a baki yayi hanzarin gocewa yana dariya.

M



*TOP 10, TAKUN HASKE

💡

*

_INA MASOYA MA'ABOTA SON HASKAKA ZUKATANSU? KU MATSO KUSA GA DAMA TA SAMU DA ZAKU KWASHI GARAB'ASAR DA ZATA HASKAKA MAKU ZUKATA DAGA QUNGIYAR

HASKE WRITER'S, QAYATATTUN SHIRE_SHIRE HAR GUDA UKU DA KUMA HA'DA'DDUN LITTAFAI GUDA BAKWAI, DUK AKAN NAIRA 500 KACAL DOMIN FARANTA MAKU_

👇🏼



*IBTISAM:- AYUSHA MUH'D*



*WASU MAZAN:- BILLY S FARI*



*AZAAD JUNAID:- JEEDDAH ALIYU*



*ZO GARE NI:- HAJJ

A CE*



*KUKAN ZUCI:- SLIMZY*



*NIDA RAHEEMAH:- ASMY B ALIYU*



*WATA SOYAYYAH:- OUM HANAN*



*SHIRIN KOYAR DA GIRKE-GIRKE:- CHIEF DEEJARH BERVER*



*SHIRIN YANDA ZAKU GYARA JIKINKU, TSAFTA DA MATSALOLIN JINI:- UMM A'ISHA*



*SHIRIN HAD'A MAGUNGUNA:

- MAMAN KHADIJA*

_GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N500)TA WANNAN ACCOUNT

👇🏼

_

2083371244

ZENITH BANK AISHA M. SALIS

SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR

👇🏼

+447894142004

IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA WANNAN LAMBAR

👇🏼

07043079282

SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR

👇🏼

07065283730

_GA MUTANENMU NA QASAR NIGER

🇳🇪

ZAKU IYA TURA KUDINKU 550F TA NITA, AMANA, ALI'ZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR

👇🏼

_

+227 96 91 36 36 RAHINA daga niamey.

MUN GODE.

2/14/22, 08:41 - Um

mi Tandama

😇

: *WATA SOYAYYA*♥



🩸





*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

💡

(Home of expert & perfect writer)

*TOP TEN TAKUN HASKE BATCH {A} 2022*

Writer: Oum Hanan

From the writer of DR SAIF

🩸

Free page

Fiction story

06

^√^√^√

^√^√^

Wani private hospital Ja'afar yakai Abdallah inda wani abokinshi yake aiki, kai tsaye suka samu ganin Dr Naseer yayi mashi allura yabashi duk taimakon daya dace ayi masa, Ja'afar dai sai danne dariyar shi yake kar yaja abinda za'a zagi uwarshi da ub

anshi yanzun nan dan yadda yake a zuciyen nan kamata yayi mutum yayi baya baya dashi.

Har suka koma gida ba wanda yace uffan dan yasan yana magana maybe Abdallah ya huce a kanshi shiyasa yayi gum da bakinshi har suka k'arasa.

Yana yin parking Abda

llah ya b'alle murfin motar ya fice a fusace ya nufi main parlor na gidan a zuciye, Ja'afar ya bishi da kallo yana tunanin abinda yasa har Jauhar tayi masa haka kuma tasan halinshi sarai koma me yayi mata ita ta jawa kanta, fita yayi daga motar ya shige si

de d'inshi.

Ko sallama baiyiba ya afka falon inda Hajiya Yaya take zaune kan kujera tana kallo dayake Mama bata nan, bai kalleta ba kai tsaye ya nufi bedroom d'in Jauhar, da kallo Hajiya Yaya ta bishi tana fad'in

"Kai kai meye haka zaka shigo mana

waje ba sallama, bada Abdullahi nakeba wai". Sam baibi ta kanta ba ya shige corridor'n dazai kaishi bedroom d'in Jauhar.

"Yau naga jaraba da rana tsaka, wannan yaron kanshi d'aya kuwa? tsaki kawai tasaki ta maida kanta kan TV'n datake kallo.

Tana

zaune a tsakiyar gadonta da books a barbaje a gabanta amma ba book d'in take karantawa ba wayace a hannunta tana dubawa, ta canza shigarta da wasu riga da wando plain ash color ba komai a kanta sai gashinta mai uban yawa da tsayi bak'ikk'irin dayake ta sh

ek'i, ba zato taji an turo k'ofa da k'arfi an shigo manyan idanunta ta zaro ganin wanda ya shigo d'in a tsorace ta mik'e tsaye tana kallon Abdallah saidaya murza key sannan ya k'araso bakin gadon tareda kai hannu kan k'ugunshi yana kwance belt d'in dake d'

aure lokaci d'aya yana fad'in

"Ni zakiwa k'ofi Jauhar? dan uwarki ni sa'anki ne da zakimin k'ofi". ya k'are maganar da kai mata duka da belt d'in tayi saurin gocewa ta shiga dire dire akan gadon tana yayyarfe hannu da fad'in

"Dan ALLAH Yah Abdallah

kayi hak'uri dan girman ALLAH wllhy bazan k'ara ba wayyo Mama wayyo Hajiya". tayi maganar cikin ihu.

Baki ya cije ya k'ara kai mata wani dukan yana fad'in

"Yau sai kinmin k'ofin maciji a gidan nan sannan zan yarda ke muguwace dan ubanki".

Hannu

tasa ta toshe bakinta d'ayan kuma sai yayyarfa shi take tana girgiza masa kai, haka sukai ta faman tsere shi a k'asa itakuma akan gadon har lokacin kuma baiyi nasarar dukanta ba, Hajiya Yaya dataji ihun Jauhar da saurinta ta taso ta taho bedroom d'in saida

i tana zuwa tajishi ansa key daga ciki.

"Kai dan ubanka ka bud'e d'akin nan, mugu kawai wato muguntar taka ce ta motsa kazo zaka sauketa akan yarinyar da bataji ba bata gani ba ko". magana take tana bubbuga d'akin saidai ba alamun za'a bud'e haka ta ga

ji ta juya tana ta faman bambamin fad'a tana zai fito ya sameta ne dan ubanshi yaro saikace mahaukaci.

Har zai bita kan gadon databi duk ta tumurmushe shi saikuma ya fasa ya juya, tana shirin sakin ajiyar zuciya dan duk zatonta fita zaiyi saitaga sa

b'anin hakan kan couch taga ya zube yayi wani irin zama, k'afa d'aya ya d'ora kan hannun kujerar d'ayar kuma ya ajiyeta a k'asa yana faman girgizata hannunshi rik'e da belt d'in, yana sauke numfashi idanunshi akan Jauhar data zauna kan pillow ta toshe baki

nta da hannu d'aya kanta a k'asa tana satar kallonshi ta k'asan ido.

"Jauhar". ya ambaci sunanta a hankali kamar wanda zai fad'a mata wata maganar arzik'i, d'agowa tayi ta kalleshi batare data amsa ba, cikin ranta banda ALLAH ya isa ba abinda take ja

masa ko wannan dire diren daya sata ai sai ALLAH ya saka mata mugu da wata R d'inshi dabata fita (Abdallah na daga cikin mutanen da basu iya harafin R ba).

"Zaki amsa ne kokuwa saina tashi kinga tsayina". yayi maganar yana shafa belt d'in hannunshi.

"Na'am". ta amsa da sauri.

"Kinaso inci uwarki a d'akin nan?".

Kai ta girgiza masa tana matso hawayen munafunci.

"Good, sonake kimin na maciji ya sareni in tabbatar dake d'in bak'ar muguwa ce, k'aryar mugunta kike yarinya kunama ai k'aramin alhaki

ce (Kunji mutumin naku fa

😂

).

Kanta ta cusa tsakanin cinyoyinta.

Yana shirin yin magana kamar ance ya juya ya hangi snake daga wajen wardrobe d'inta ba irin babban nan bane amma kuma da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login