Showing 21001 words to 24000 words out of 96447 words

Chapter 8 - Wata Soyayya Complete

03 Sep 2026

22

bita bedroom tayi mata sallama ta fito bayan Ammi taja mata kunne kar takai dare, ALLAH ALLAH take tabar gidan dan haka komai cikin hanzari tayi shi ta shiga wata mota da Ammi tabata key d'in taja tabar gidan.

^√^√^√^√^

Daf da magreeb

ah tadawo gidan tana shigowa harabar gidan a motar shima Abdallah ya kunno hancin motar shi gidan, Ido ta runtse cikeda fad'uwar gaba tayi saurin yin parking ta fito daga motar ta d'auki bag d'inta ta nufi ciki da saurinta, shima parking din yayi ya fito y

ana kallon Jauhar datake ta uban sauri dan tsakanin parking lot d'in da k'ofar da mutum zai shiga general parlor d'in gidan akwai y'ar tazara, bai tsaya ya d'auki babbar jakar dake back seat ba wadda kayan daya karb'o daga wajen tailor ke ciki ba na biki y

abi bayanta yadda take sauri haka shima yake saurin kasancewar shi namiji kuma mai cikakkiyar lafiya yasa ya cimmata tana daf da isa k'ofar falon sai gani tayi yasha gabanta yayi mata tsaye aka ya rik'e k'ugunshi da hannayenshi duka yana kallonta, kana gan

inta kaga marar gaskiya saboda yadda take wuri wuri da zare ido.

"Wato danace kar kije saida kikaje ko? ke wai ba'a fad'a miki magana kiji ne?".

"Ahmm.... Yah Abdallah bafa Jauhar bace". tace cikin in ina da sanyin murya irin na Janan d'in tana k'ar

a yin k'asa da kanta.

Tsayuwar shi ya k'ara gyarawa yana shafa sajen fuskarshi yace

"Who?".

Gefen wuyanta ta shiga sosawa a hankali tace

"Uhmm.... Janan ce fa".

"Okeyyyy Janan ko?". yace yana murmushi yana wani jijjiga kanshi.

Kai kawai ta d'ag

a cikin ranta tana addu'ar ALLAH yasa yace ta wuce ta tafi gabanta sai fad'uwa yake.

Dariya kawai taga ya shiga yi cikin dariyar yake fad'in

"Bakida hankali yarinya wato a zatonki bana bambance tsakaninki da Janan ne? bari kiji to in fad'a miki abinda

baki saniba koda kikeji mutane na cewa basu ganeku to nibana cikinsu tun kuna jariranku nake ganeku bare yanzu da halayyarku tasha bambam keda y'ar uwarki tafiki hankali da nutsuwa da jin magana ko lokacin da kuke zanin goyo Mama saita duba shaidar jikink

u take ganewa amma ni kallo d'aya zanyi muku in tantanceku dan haka muje garden ki fad'amin dalilin dayasa na hanaki fita kika fita dan ubanki".

Kamar zatayi kuka tace

"Da gaske nefa Yah Abdal......."Zaki wuce muje ne kokuwa?". yace yana d'an d'age ri

garshi yafara k'ok'arin kwance belt d'in dake d'aure a k'ugunshi.

Da sauri tayi gaba yabi bayanta kamar makaho da d'an jagora data d'an waigo saitaga hannayenshi akan belt d'in da haka har suka k'arasa inda garden d'in yake suna shiga ya nemi kujera ya

zauna ya d'ora d'aya kan d'aya yace ta masa frog jump tsaye tayi tana kallonshi alamar abinda yace bai gamsheta ba.

"Bazakiyi bane?". ya fad'a yana k'ok'arin mik'ewa tsaye.

"Zanyi fa Yah Abdallah". tace da sauri tana ajiye bag da key d'in motar kan

grass carpet d'in dake ko ina a cikin garden d'in.

Haka tanaji tana gani ta tattare rigarta ta fara frog jump d'in kamar tafasa ihu haka take ji shikam yana kame kan kujera yafara latse latsen waya yana murmushi.

Lokacin da suke k'ok'arin shiga ga

rden d'in shikuma a lokacin Yah Ameen ya shigo compound d'in yana yin parking kuwa daya fito ya nufo garden d'in dan yasan bai wuce wata muguntar Abdallahn zaiyi ba shi duk zatonshi ma Janan ce, farin cikine ya kamata lokacin dataga Yah Ameen ya

shigo tasa

n zai k'waceta a hannun wannan mugun shi sam baima ga Yah Ameen d'in ba dayake ya juya masa baya ne sai maganar shi yaji yace

"Meye haka Abdallah? ya zakazo kasa yarinya tsallen kwad'o metayi maka?".

Waigowa yayi ya kalli Yah Ameen ta bayanshi yace

"K'yaleni kawai in casata Bros bakasan me tayi min ba".

Hararar shi Ameen yayi yace

"Kaji tsoron ALLAH wllhy Abdallah kowa yasan Janan batada hayaniya magana ma ba damunta tayi ba amma saboda zalunci saida kasan yadda kayi ka k'ak'aba mata wani laifi

n ko".

"Bros bafa Janan bace wllhy".

"Karka rainamin hankali mana Malam". Ameen ya fad'a yana d'an hararar Abdallah.

"Wllhy Bros ba Janan bace Jauhar cefa ka tab'a ganin nasa Janan haka?".

"Idan muguntarka ta motsa uban waye baka yiwa? yanzu ita

wannan daga zuwa biki kuma metayi maka?".

Juyawa yayi yana kallon Jauhar data daina tsallen kwad'on take kallonsu sun d'anyi nesa da ita bama ta jin abinda suke fad'a saida ya harareta sannan yace

"Ammi ce tace tazo ta tambayeni zata fita unguwa shi

ne nikuma na hanata ashe k'arya taje tayiwa Ammi tace na barta ta fita shinefa sai yanzu tadawo".

Jauhar Yah Ameen ya yafito da hannunshi alamun tazo yana fad'in

"To ayi hak'uri dai tsallen kwad'o saikace wasu maza, kekuma karki k'ara irin haka Jauhar

kinji ko". ya k'arasa maganar yana kallon Jauhar data k'araso wajen, kai ta d'aga masa murmushi yayi yace ta taho su shiga cikin gida inda ta baro ta koma ta d'auko jakarta da key d'in mota tazo suka nufo hanyar fitowa daga garden d'in basu bi takan Abdal

lah ba daya k'ara kishingid'a kan kujerar har lokacin da waya a hannunshi.

M&S

πŸ’

2/14/22, 08:58 - Ummi Tandama

πŸ˜‡

: 12.

^√^√^√^√^√^

∿

Anci gaba da gudanar da shirye shiryen biki tun daga ranar kuma Jauhar bata k'ara saka Abdallah a idanunta

ba dan bai cika zaman gidan bama.

Ana gobe kamu ranar laraba kenan duk suna zaune a falo harda Ammi maganar bikin ake tayi ana k'ara shirya yadda zai tafi Hassana ta kalli Ammi tace

"Ammi munyi waya da Mubarak d'azu yace ya kammala d'inkunan aje a k

arb'a".

"Toh ai saikuje ku karb'o d'in ko keda Jauhar ne, je d'akin Modibbo idan yana nan kice idan ya tashi fita yazo". Ammi tayi maganar tana kallon Jauhar dake kwance tana danne dannen waya.

Zaune ta tashi tana lalubar gyalen kanta daya zame kan

kujerar ta d'auka ta mik'e tsaye ta yafashi kan long skirt d'in dake jikinta black color da body hook mai dogayen hannu red colour ta zura plat shoe takalminta dake gaban kujerar black ta fita daga falon zuwa aiken Ammi.

A kulle tasamu k'ofar falon nas

hi saidata dad'e tana knocking ba'a amsa mata ba dan haka kawai ta murd'a handle d'in k'ofar ta shiga bakinta d'auke da sallama ta duba tagani ko yana nan dan duk zatonta baya nan turus tayi hangoshi datayi kan kujera yayi relaxing sosai akan kujerar

dayak

e ya d'ora k'afafunshi kan center table daya janyoshi kusa da k'afafun nashi k'aramar paper ce da pen a hannunshi batasan tsiyar dai dayake zanawa ba.

"Lallai gayen nan yaci uwar rainin hankali wllhy shine dan wulak'anci yanaji tana knocking yayi bakam

dashi kamar bayaji dan tsabar wulak'anci? takawa ta shiga yi zuwa inda yake tana wani yatsina fuska jin alamun an shigo yasa ya tashi ya zauna sosai kan kujerar yana kallon Jauhar data tsaya kusa da wata kujera d'an nesa dashi ta dafa bayan kujerar, k'ara

min tsaki taja cikin zuciyarta ganin irin shigar dayayi milk wandone a jikinshi wanda da kad'an ya wuce cinyarshi gashi ya d'ameshi sai light ash color d'in riga mai k'aramin hannu shara shara baifi mab'allai biyu ne suke a b'alle ba daga k'asa sauran duk

bai b'alle suba hakan ya bayyana faffad'an k'irjinshi mai cike da yalwar kwantaccen gashi bak'i sid'ik sai P cap daya d'ora wadda ta zame masa kamar ibadah, dubeshi dan ALLAH sam ba tsari wannan shigar tashi duk ya wani bayyanar da surorin jiki, cikin zu

ciyarta tayi maganar tana k'ara jan wani tsakin gamida juyar da kanta gefe tana tab'e baki. Rai had'e yake kallonta yana k'ara tsare gida yace

"Meya kawoki nan?".

Tana daga tsayen tace

"Ammi ta aikoni tace idan katashi fita ka biya ta cikin gida".



Sai daya cije baki yana wani k'ank'ance ido kafin yace

"Ke bakida tarbiyya ko? dan uwarki haka akewa manya magana kinzo kin min tsaye akai tsabar bakida ladabi ko".

Wata shegiyar dariya tasaka ta rainin hankali harda d'an tafa hannayenta tace

"

Wai manya, suwaye manyan?. dariyar ta k'ara saki ta cigaba da fad'in

"Amma dai an cuci manya wllhy kabar manya irinsu Yah Ameen masu rik'e girmansu suyi magana amma ba kai....... yunk'urowar dayayi a fusace yana cije lips yasa ta dakata da abinda tayi n

iyyar fad'a ta juya ta fice da gudu tana dariya, k'wafa kawai yayi ya koma ya zauna yau bai cikin mood d'in hayaniya da har gaban Ammi saiya bita yaci ubanta mara kunyar yarinya kawai".

Tana komawa falon Ammi tace Jauhar da Hassana suje su shirya sa

i subi Modibbo ya saukesu shagon tailor d'in dake musu d'inkuna zasu karb'o d'inkunan su na biki saboda driver baya nan ta aikeshi kasuwa.

Tunda Hassana taji da wanda aka had'asu tafiya ta shiga bedroom ta fara shiryawa kafin yazo ya tashi hankalin kow

a na gidan itakam Jauhar koda ta shiga bedroom d'in saitayi zamanta tana cigaba da buga game d'inta da Janan ma tace mata bataji Ammi tace zasu fita da Yah Abdallah ba kuma ta zauna bata gyara ba banza tayi mata ta cigaba da abinda take yi.

Mayen k'

amshin turarenshi ne mai bala'in dad'in k'amshi da sanyaya zuciya ya fara yiwa falon sallama kafin mamallakin turaren ya biyo baya bakinshi d'auke da sallama, sanye yake cikin bak'in wando da red shirt mai dogon hannu sai black falmaran daya d'ora akai dag

a kan takalmin k'afarshi zuwa agogon hannunshi duk black color ne sai dark space daya toshe idanunshi dashi sumar kanshi tasha gyara sai k'yalli take simple dress ne amma sai fitinannen kyau dayayi mara misaltuwa.

Yana shigowa falon itakuma Ammi ta sauk

o downstairs d'in kusa da ita ya k'arasa yana fad'in

"My sweet Mommah ance kina nemana".

"Eh, zaka fita dasu Jauhar ne ka saukesu wajen Mubarak zasu amso mana d'inkunan mu na aiki driver ne kuma bai dawoba har yanzu".

"Toh Ammi ina jiransu suyi sau

ri dan ALLAH nima ina saurine".

"Gasu nan zuwa". Ammi ta amsa masa tana kallon Hussaina data kawo kai cikin falon tareda fad'in taje ta kirawo su Jauhar d'in yayin da shikuma ya juya ya fita daga falon.

Motar dazai fita da ita ya bud'e ya shiga ya

zauna yana jiransu, wucewar y'an mintuna basu fitoba hakan ya hasala shi ya tsani jira a rayuwar shi badan Ammi ce ta tsayar dashiba da zaiyi tafiyarshi ne kawai, wani uban horn yafara saki mai shegen k'ara wanda duk saidaya rud'a mutanen gidan da gudu Ha

ssana ta fito compound d'in jikinta sai rawa yake ta bud'e motar ta shiga a fusace yace

"Ina yarinyar nan kuma?". cikin rawar murya tace

"Gata nan yanzu zata fito".

"Dan ubanku da kunsan baku shiryaba kukasa aka tsayar dani".

Itadai Hassana shiru

tayi kanta a k'asa ita bataga abin tada jijiyar wuya ba anan ALLAH dai ya kyautawa halin Yah Abdallah.

Sai data gama shirinta tsaf cikin doguwar rigar atamfa kalar bak'i da milk ta yafa black vail k'arami tasa bak'in takalmi plat ta fita, takaici ne y

a kama Abdallah ganin yadda Jauhar ke tafiya hankalinta kwance tana wani taku d'ai d'ai wato shi ta tsaidashi k'wafa kawai yayi yana cije baki.

Tana zuwa ta bud'e back seat inda Hassana take ta shiga ta zauna, a fusace Abdallah ya juyo yace

"Uban wa

ye drivern ku anan?".

Baki Jauhar ta tab'e ta juyar dakai ba inda zata fita saidai yayi haukan nashi yagama saidai Hassana ta koma front seat d'in.

Hannu Hassana tasa ta zunguro Jauhar ta juyo tana kallonta da Ido Hassana tayi mata alamun takoma front

seat d'in tana marairaice fuska, kamar zata shareta saikuma ta bud'e ta fita ta koma gaban.

tsaki yasaki kafin ya tada motar suka bar gidan.

Tunda suka tafi ba wanda yayi magana shi ya maida hankalinshi kan driving Jauhar kam latse latsen waya take ta

faman yi, a haka dai har zuwa lokacin daya saukesu a shagon ya k'ara gaba.

Bayan sun karb'a suka shiga tricycle zuwa gidan Aunt Deejah dan kaimata nata d'inkunan dama wajen d'inkin su d'aya sai yamma suka bar gidan.

^√^√^√^√√^√^

Ranar alh

amis kamu bayan la'asar su Jauhar suka fito zasu tafi inda ake kamun y'an matan ne kawai su manyan sunyi gaba tana tsaye bakin motar itada Hussaina suna jiran Janan da Hassana su fito su wuce, doguwar rigar atamfa ce a jikinta orange color da fari sai bak'

i da aka d'an ratsa kad'an kanta ba d'ankwali sai rolling datayi da bak'in gyale k'arami takalmin k'afarta hill ne sosai mai igiya rigar ta d'ameta sosai daga sama k'asan kuma shima ya bud'e sosai tayi kyau sosai cikin shigar.

Kiran daya shigo wayarta

ne yasa ta maida kanta kan wayar dan ganin waye, baki ta tab'e ganin kowaye gefe d'aya na zuciyarta na tunanin abinda yasa ya kirata kamar bazatayi picking ba saikuma tayi ta kara wayar a kunnenta sarai tasan waye amma tayi kamar bata ganeba tana d'agawa t

ace

"Wake magana?".

"Ubanki ne, wannan dressing d'in naki baiyiba kije ki canza wani".

Ikon ALLAH wannan isa dayawa take, d'agowa tayi ta shiga wuwwurga idanu ko zata hango wannan sarkin y'an k'ok'arin saidai bashi ba alamun shi ko mai kama dashi

babu hasalima ba namiji ko d'aya cikin compound d'in daga maigadi sai mai bawa flowers ruwa ko daga ina yake hangota oho masa.

Cikeda rainin hankali tace

"Wai waye ne nifa ban ganeba kayimin bayanin kanka".

"Bayanina bazai miki dad'i ba Jauhar idan

kuma so kike in fito zan fito d'in amma ki shirya zuwana kinsan halina sarai basai anbaki labari ba, kije ki canza tun kafin aji kanmu dake". tana shirin magana taji k'itt ya kashe wayar. Tsaki tasaki tana kallon Hussaina data tsura mata ido tana kallonta.

"Ya akayi ne sis?". Hussaina ta tambayeta.

"Hmm kibari kawai nida wannan isasshen mana kinji wai dress d'ina baiyiba inje in canza wani ko ina ruwanshi da shigata oho".

"To kije ki canza d'in mana Jauhar hanyar lafiya abita da shekara fa".

"Ba

inda zanje bazan canza kayan ba, Ina ruwanshi dani to tsabar neman bala'i irin nashi". cikin jin haushi tayi maganar harare harare kamar mai laifin yana wajen ne.

"Na had'aki da ALLAH kije ki canza d'in yadda yace Jauhar ALLAH har yanzu bakiyiwa Yah Ab

dallah cikakken sani ba muda muke zaune dashi mu mukasan halin bawan ALLAHn nan please".

Ta bud'e baki zatayi magana kenan wani kiran ya k'ara shigowa tana shirin yanke kiran Hussaina tayi mata alamu da ido ta d'aga k'aramin tsaki taja tayi picking tar

eda kai wayar kunnenta.

"Jauhar! kinaso in b'ata kwalliyar nan taki ko? bai bari tayi magana ba ya cigaba da fad'in karki kuskura inzo in sameki wajen bar ganin ina lallab'aki idan kika bari nafito uwarki zanci wllhy kibari kuma inzo in sameki anan, zak

ije ne kokuwa in fito?".

Kamar saki kuka dan haushi tace

"Zanje". saidaya saki wata dariya kafin yace

"Good girl kin taimakawa kanki". daga haka ya yanke kiran.

Tsabar takaici jitake tamkar ta had'iyi zuciya ta mutu, a fusace ta nufi k'ofar falon

taje zata shiga kenan Janan da Hassana sukuma sunzo fitowa suka had'u a bak'in k'ofar falon ba wanda ta kula tayi shigewarta ciki suka bita da kallo.

M&S

πŸ’

2/14/22, 08:58 - Ummi Tandama

πŸ˜‡

: 13.

Kallo suka bita dashi gaba d'ayansu Hassana ta

ce

"Ikon ALLAH ga wata y'ar uwar Yah Abdallah mai almatsutsai k'alau fa naga ta fito da fara'arta".

"Dama ai tafiyarsu d'aya dashi ai". Janan ta fad'a tana murmushi gamida kama hannun Hassana suka fice daga falon.

Saida sukaje wajen motar ne suk

e tambayar meya faru da Jauhar sunga ta shiga gida a fusace anan Hussaina ke sanar dasu wayar da Yah Abdallah yayi mata yace saita canza dressing d'inta na jikinta baiyiba, dukansu saida sukayi mamaki ko ina ruwanshi da shigar datayi koda yake ba abin mam

aki bane indai Yah Abdallah ne idan yaso neman rigimarshi ko mutum bai shiga sabgarshi ba toshi zaisan yadda yayi ya shiga ta mutum ALLAH dai ya shirya musu wannan yayan nasu.



Haka dole ta canza shigar tata tasa riga da siket na atamfa ruwan toka

da touch d'in bak'i da fari ta yane kanta da gyale mai d'an girma ruwan toka shima, tana faman zumb'ureΒ²n baki ta fito ta samesu har sun shisshiga motar Janan da Hussaina a back seat sai Hassana a front seat dama ita zatayi driving d'insu dan duk tafisu iy

awa saboda tafisu rawar kai har gara Hassana ma akan Janan da Hussaina, tana shirin shiga motar wayarta tayi k'ara batare data duba mai kiran ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login