Showing 36001 words to 39000 words out of 96447 words
/>
tunda dai yaga anyi zaman nan yasan abune mai muhimmanci yataso amma saboda shegantaka yazo ya fara danne dannen waya kuma shi iya gaskiyarshi kenan hakan kamar bawani laifi ban
e yake gani, dukansu kallonshi suke banda Janaan data kasa ko d'agowa dan karma su had'a ido dashi, gyaran murya Abbie yayi yace
"Ajiye wayar nan Modibbo magana zamuyi very important daku".
"Okay Abbie". Ya fad'a tareda d'ago kanshi ya kashe wayar
ya ajiyeta gefenshi ya maida hankalinshi kansu danjin abinda suke tafe dashi. Saidaya nemi Ayyah ta fara yin magana tace masa ta bashi dama yayi jawabi kawai.
Da bismillah Abbie ya fara ya d'ora da yiwa ANNABI MUHAMMAD sallallahu alaihi wa alihi wasa
llam salati sannan ya fara fad'in abinda ya tarasu a wajen.
"Kamar yadda kukaga munyi kiranku nan zamane da muke fatan ya zame mana alkhairi gaba d'aya mu daku muna fatan kuma zakuyi mana biyayya kamar yadda aka umarci y'ay'a suyiwa iyayensu".
Kai
kawai Abdallah ya jinjina yayin da Janaan tace
"Insha ALLAH". Cikin y'ar rawar murya har zuwa lokacin bata d'ago kaiba.
"Masha ALLAH. Abbie ya fad'a ya d'ora da fad'in
"Modibboo! Daga yau inaso ka fara yiwa Janaan kallo a matsayin matar da zaka
aura dan munaso mu had'aku aure kaida ita".
Duk yadda Janaan taso nuna jarumta da nuna abin bai dameta ba lokacin da maganar Abbie ta shiga cikin kunnenta hakan ya gagara dan da wani irin mugun sauri ta d'ago kanta tana kallon Ammi da itama d'in take
kallonta daga irin kallon datake mata tasan cewa alfarma take nema a wajenta na karta musawa maganar da Abbie yazo da ita duk da Ammin tasan mawuyacin abune Janaan d'in tayi hakan, saitaji kamar duk ta d'add'aure tane da jijiyoyin jikinta dan haka ta maid
a kanta k'asa idanunta cike fal da k'walla sai wani fat fat gabanta keyi da tsabar tsorata da maganar tanajin tamkar a mafarki hakan ke faruwa.
Shikam Madugu kallo d'aya idan kayi masa bazai sa mutum ya gano ainahin abinda ke fuskarshi ba sai b'ata fus
ka kawai yake ya had'e ran nan gabas da yamma kallonsu kawai yake d'aya bayan d'aya kafin yace
"Nifa Abbie ban gama fahimtar kuba ana nufin aure za'a had'ani da wannan yarinyar wadda ko cikakken energy bata dashi(Kai Madugu
🤦🙄
) ya k'are maganar yana
nuna k'irjinshi da hannunshi da Janaan d'in datake jin tamkar ta tashi taga mafarki ne take ba gaske bane.
"K'warai kuwa har mun riga da mun yanke hukunci akanku". Ayyah ta bashi amsa.
Kai ya shiga girgizawa yana fad'in
"Habaaa mana Ayyah nifa bana
son yarinyar nan saboda banason raini ya shiga tsakaninmu da ita impact ma ni ba yanzu zanyi aure bama dan ALLAH ku canza magana please".
"Dole kuwa haka zakayi hak'uri da wannan zab'in da mukayi maka bawai sonka ne bamayi ba a'a tsananin son naka da m
ukeyi ne yasa muka zab'a maka matar da muke ganin ba wadda ta dace dakai irinta saboda hak'urinta dan ba kowacce mace bace zata iya zama da rigimamme irinka ba dan haka kayi hak'uri kawai ka amsa da hannu bibbiyu insha ALLAHU alkhairi ne". Ayyah ce tayi ma
ganar tana kallon Abdallah.
"Nifa kawai a ruguje wannan maganar inba hakaba wllhy saina tada hankalin kowa a gidan nan kowa yasan halina b....tsawar da Abbie ya daka masa ce yasa shi yin shiru bai k'arasa abinda yayi niyyar fad'a ba kafin Abbie yayi ma
gana Ayyah ta rigashi da cewa
"Kayi hak'uri maigidana wannan abinda kag....."Nifa nace bazan aureta ba auren dole zakuyi min n..... kyakkyawan marin da aka sakar masa a kuncinsa ne yasa bai k'arasa maganar daya faro ba, gurin da aka mareshin ya dafe ta
reda d'aga kanshi ya kalli Abbie dake tsaye a kanshi yana huci wanda sam baisan lokacin daya taso daga inda yake zaune ba, cikin b'acin rai Abbie ke fad'in
"Ayyahn kake fad'awa haka saboda bakada mutunci? Ashe dama bakada kirki ban saniba? To bari kaji
abinda zan fad'a maka aure kaida Janaan babu fashi ba gudu baja da baya ban haifi d'an dazai dinga raina mahaifiyata ba, yana shirin d'orawa Ayyah ta katseshi da fad'in
"Ya isa haka koma ka zauna". K'wafa Abbie yayi ya koma inda ya taso ya zauna yana
kallon Abdallah daya k'ara had'e fuska har lokacin bai cire hannunshi daga inda Abbie ya mareshi ba, Janaan kuwa k'asa k'asa take kukanta cikeda d'imbin tararrabin wannan babban al'amarin dayake tunkarota aure itada Yah Abdallah? Bala'i kenan tarasa ta yad
da zata fassara lamarin nan mai kama da almara.
"A karo na farko zan baka umarni kuma dolenka kabi ko kanaso ko bakaso dole zaka auri Hassana kayi rayuwa da ita a matsayin matarka kum.....Bai k'arasa jin abinda zatace ba ya mik'e tsaye da sauri harda
buga k'afa ya nufi hanyar fita daga falon.
"Modibbo! Modibboo!! Ammi ta shiga kiranshi amma sam bai juyoba ya fice, tashi Abbie yayi yana shirin binshi Ayyah ta dakatar dashi komawa yayi ya zauna yana fad'in
"Ayyah ki k'yaleni inci uban yaron nan tun
da bashida mutunci".
Kai ta girgiza tace
"Rabu dashi ya gama haukan nashi dama aiya saba aure ne dai babu fashi ku zuba masa ido kawai". Kai kawai Abbie da Ammi suka jinjina mata, kallonta ta maida kan Janaan ta kira sunanta a hankali tace ta d'ago t
a kalleta da k'yar Janaan d'in ta d'ago kai ta zube idanunta da sukayi jawur kan Ayyah.
"Kiyi hak'uri kinji Hassana kar wannan buyagin nashi ya dameki muna rok'on alfarma dai a wajenki dan ALLAH kibamu had'in kai insha ALLAHU aurenku alkhairi ne kiyi ma
na wannan alfarmar karki gujewa wannan auren".
"Insha ALLAH Ayyah". Janaan ta fad'a cikin rawar murya ruwan hawaye na k'ara taruwa cikin idanunta batasan meyasa har su Abbie sukayi tunanin had'ata da Yah Abdallah ba to taya ma zasuyi zaman auren? Tambay
ar datake ta faman nanatawa cikin ranta kenan.
"Tashi kije ALLAH yayi miki albarka". Maganar Ayyah ta katse mata tunanin datake, cikin sanyin jiki ta tashi ta fita daga falon, saida suka k'ara d'an tattaunawa sannan Ayyah ta fita daga falon ta koma nat
a bedroom d'in.
2/17/22, 16:17 - Ummi Tandama
😇
: *WATA SOYAYYA*
💝
Oum Hanan
Page 20.
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*
√^√^√^√^√^
∿
Da k'yar Janaan ta isa
bedroom d'insu saboda jirin dataji yana d'a
ukarta tana shiga ta zube kan gado ta saki kukan da tun d'azu take rik'eshi, Hassana dake gaban mirror tana shafa lotion dan fitowarta kenan daga wanka ta taso ta nufo inda Janaan take kwance wajen kanta ta zauna ta dafa bayanta tana tambayarta abinda yake
damunta, bata amsa mata ba ta cigaba da kukanta yayin da Hassana ta cigaba da tambayar ta, a haka har Hussaina itama data fito daga wankan ta samesu, itama wajen ta k'arasa ta zauna tana tambayar Hassana meye yasamu Janaan d'in?.
"Wllhy ban saniba sis
ter nima haka dai naga ta shigo ta kwanta tanata kuka kuma inata tambayarta meyake faruwa tak'i magana". Hassana ta fad'a tana kallon Hussaina. Ganin yadda duk suka damu da kukan datake sunata faman tambayarta kamar suma zasuyi kukan hakan yasa ta mik'e za
une suka sata a tsakiya suka zuba mata ido duk suna kallonta dan jin abinda zata fad'a, hannu Hussaina takai fuskar Janaan ta share mata hawayen dake gangarowa saman kumatunta tace
"Please sister dan ALLAH ya isa haka kiyi shiru ki fad'a mana meye damuw
arki kin tayar mana da hankali wllhy say something mana please".
Cikin rawar murya sf nida Yah Abdallah".
"Eyeee". Hassana ta fad'a da k'arfi tana zaro ido Hussaina ma k'irji ta dafe tana fad'in
"Bala'i aure da Yah Abdallah?". Kai Janaan ta jinj
ina musu tana share hawaye, shiru duk sukayi aka rasa mai magana kowa da sak'e sak'en dayake a cikin zuciyarshi, ajiyar zuciya Hussaina ta saki tace
"Dank'ari! Dole kiyi kuka sister zaman minti d'aya ma idan mutum yayi da Yah Abdallah ai saiya wahala ba
re zaman aure na din din din da ake saka ran sai mutuwa ce zata raba?.
"Hmmm ganemin hanya dai sister ni wllhy narasa abin fad'a ma ciwon kaine dai zakisha shi dan Yah Abdallah ma yafi headache wllhy ni bansan ma meyasa su Ammi sukayi wannan tunanin ba
wllhy kaiii Yaa ALLAH". Ta k'arasa maganar tana dafe goshinta. Anan dai suka cigaba da jajanta lamarin suna k'ara kwantar mata da hankali.
√^^√^^√^^
∿
Kai tsaye inda yayi parking motarshi bayan dawowar shi gidan ya nufa ya bud'e ya shiga
ya zauna ya tayar ya shiga danna uban horn mai azabar k'ara wanda ya gigita Baba maigadin harya rasa ta inda zai fara bud'ewar da k'yar dai ALLAH ya bashi sa'ar bud'ewa aikuwa da gudu ya fice daga gidan tamkar zai tashi sama, Baba maigadi yabishi da kallo
yana tunanin waye kuma ya tab'o wannan hargitsattsen mutumin?.
Da mugun gudu ya dinga jan motar zuciyarshi namasa zafi, meyasa za'ayi masa haka saboda me za'a had'ashi da wadda sam zuciyarshi bata tab'a jin sonta ba yana daf da fallasa sirrin zuc
iyarshi a gurin wadda yakeso yake k'auna kuma yake muradin tazama matar aurenshi? Dan me za'ayi masa kutse cikin al'amuranshi? Yasan tunda Ayyah ta shiga maganar shikenan zance ya b'aci dan yasan Abbie bazai tab'a juyawa umarninta baya ba saboda yadda yake
mata matuk'ar biyayya da kyautata mata.
"Oh My God". Ya fad'a da k'arfi yana cije baki gamida dukan sitarin motar so yayi fa cikin month d'in nan yaje yayi surprising d'inta ta yadda zai gigita tunaninta dan yasan zatayi mamaki matuk'ar mamaki.
Gefen titi ya gangara yayi parking ya had'a kanshi da sitarin ya shiga tunanin ta yadda zai b'ullowa lamarin kamata yayi yasamu Janaan d'in yaci uwarta tunda munafuka ce ita idan bata sonshi dan me bazata fito ta fad'a ba ita ga mai ladabi da biyayya ko za
ici ubanta kuwa, da sauri ya k'ara tada motar yayi reverse ya koma gidan.
√^^√^^√^^
∿
. A kasalance ta fito falon dan d'aukar ruwa a kitchen fridge d'in bedroom d'insu kuma duk babu ruwa sai drinks hakan yasa ta fito d'auka a kitchen, gaba d'ay
anta yau batada walwala jinta take tamkar wadda tayi wata da watanni a kwance ba lafiya duk wani kuzarinta babu a hakan ma dan Ayyah ta sameta har bedroom ta k'ara kwantar mata da hankali da k'yar ma tasamu tayi wanka ta shirya cikin riga da siket na wani
plain material light blue ta saka k'aramin hijab kalar kayan.
Bata samu kowa a falon ba dan haka ta wuce kai tsaye k'ishirwa take ji sosai, tana daf da shiga kitchen d'in taji anyiwa hannunta wani irin fisga dayayi mugun tsorata ta tunda sam bataji m
otsi ko shigowar wanda ya kamata d'in ba,amma koda bata d'aga kai ta kalla ba tasan kowaye, idanunta ta d'an runtse saboda damk'ar dayayi wa hannun nata ba k'arama bace da iya k'arfinshi ya rik'eta.
Bata turje ba sam dan tasan duk turjewar datayi haka
n bashi zaisa ya saketa ba sai kawai ta cigaba da binshi da sauri dama kuma da saurin yake janta ko kallonta bayayi. Da k'afa ya tura k'ofar falon shi bayan isarsu part d'in suna shiga yayi wurgi da ita kan kujera bayanta ya bugi bayan kujerar, Ido kawai t
a runtse gam zuciyarta cikeda wani irin tsoro sai
harbawa take, k'aramin fridge d'inshi dake falon ya isa ya bud'e ya d'auko k'aramar robar ruwa na Eva ya b'alle murfin yakai bakinshi ya shiga sha.
A hankali ta bud'e idanunta ta zubesu a kan Abdallah d
aya d'aga bakin robar yana shan ruwa, da azama tayi saurin kauda idanun nata tayi k'asa dasu tareda sakin wata b'oyayyiyar ajiyar zuciya tanajin tamkar tayi fiffike tabar d'akin tsabar zullumin abinda zai mata.
Kad'an ya rage ruwan ya rufe ya cilla ro
bar kan kujera, wata k'aramar kujera ya turo da k'afarshi zuwa gaban Janaan ya tako inda take ya k'ara matsar da kujerar gabanta sosai yayi wani irin zama na rashin mutunci.
Tuni bugun zuciyarta ya k'ara tsananta taji tamkar ta saki fitsari saboda tsor
o kanta a k'asa batayi gigin d'agowa ba bare har su had'a ido dashi bak'ak'en maganganu ne dai tasan zata shasu da zagi idan ma tayi sa'a bai had'a mata da duka ba.
"Look at me". Ya fad'a cikin wata irin hargitsatstsiyar murya data k'ara tsoratata, k
asa d'agowa tayi saboda idanunta da suka ciko da k'walla.
"I said look at me". Ya fad'a cikin tsawa kamar zai daketa, a firgice ta d'ago ba tare data saniba ta kalleshi, sosai ya k'ara tsare gida ya wani k'ank'ance mata ido na tsabar masifa yace
"Tun
yaushe kika fara sona?". Wani iri taji tambayar yaushe tafara sonshi kuma? Lallai Yah Abdallahn nan shida a zatonshi sonshi take?.
"Zaki fad'amin ne kokuwa sainaci ubanki". Taji amon muryar shi cikin kanta.
A hankali cikin rawar murya tace
"Yah Ab
dallah ban fahimci abinda kake nufi bafa ni?".
"Okeyyyy kice mahaukaci ma kika maidani ko?". Yayi maganar yana kaiwa bakinta duka da sauri ta goce tana dafe bakinta bai sameta ba, k'wafa ya saki ya k'ara gyara zamanshi yace
"Janaaan ki fadamin dali
lin dayasa lokacin dasu Ayyah ke maganar had'amu aure baki fito kin nuna musu bakya sona ba?".
Kamar zatayi kuka tace
"Amma Yah Abdallah tayaya zan bijirewa maganar su Ammi koda ace ban......"Shut up munafuka ya katseta cikin hargagi shirun tayi ta su
nkuyar da kanta k'asa, cigaba yayi da fad'in
"Kega mai ladabi da biyayya ko? Tun wuri ki fito ki nuna musu bakya ra'ayin auren nan tunda ni ba za'aji magana taba idan ba hakaba kuma ko? Baki kawai ya cije yana jinjina kai, tsaye ya mik'e ya soke hannay
enshi cikin aljihun wandonshi yace
"Tashi kibar d'akin nan". Zumbur ta mik'e kuwa tamkar wadda ke jira kuwa dama kamar akan k'aya take, ta gefenshi ta rab'a ta wuce da sauri tun kafin ya canza shawara ya mata lilis dan kad'an daga cikin aikinshi.
Ruwan da bata shaba kenan duk da matsananciyar k'ishirwar datake ji kuwa ta koma bedroom, kai tsaye bathroom ta wuce bayan shigarta, gefen bathtub ta zauna ta shiga raira kuma mai tsuma zuciyar mai saurare, batajin duk wannan kurarin zaisa ta musantawa
su Abbie mutumin daya d'auketa tamkar d'iyar daya haifa da cikinshi, tako wane b'angare baya bambanta ta da y'ay'an daya haifa duk da dai bawani dad'ewa tayi a gidan sosai ba amma ya mata alkhairi masu tarin yawa da bazasu fad'u ba to danme ita zata watsa
masa k'asa a ido? Ta b'angaren Ayyah ma tanajin tamkar ta isa da itane tanajin sam bazata iya bata umarni ta k'etara shiba tsabar yadda take ganin girma da k'imarta, sannan uwa uba kuma Ammi wadda takejin tamkar ita ta tsuguna ta haifeta saboda k'aunar dat
ake nuna
mata idan ta bijirewa maganarsu kamar tayi musu butulci ne wanda bata fatan hakan ta kasance, zatayi biyayya kuma zata jure duk wasu halayen Yah Abdallah ko don jin dad'insu zatayi iya yinta taga ta kyautata musu ALLAH ya bata ikon yin biyayya kam
ar yadda ta k'udurce a ranta.
√^^√^^√^^√^^√^^
∿
Gaba d'aya yinin ranar Abdallah bai k'ara neman kowa ba a gidan kamar yadda ba wanda ya nemeshi dan haka Ayyah tace a k'yaleshi yagama fushin nashi ya sauko da kanshi dan haka ba wanda ya k'ar
a bi takanshi .
Sai k'arfe 12:10@m sannan yadawo gidan dama saidaya siyo take away d'inshi a wani restaurant, bayan dawowarshi yayi wanka yaci fried chicken and rice daya siyo kad'an yaci ma yaji duk ya ginsheshi gefe ya tureshi ya tashi ya nufi frid
ge ya d'auko exotic ya tsiyaya a tambulan d'in dake saman fridge d'in ya koma ya zauna yana sha, bayan ya gama ya d'aura alwalah yayi raka'ah biyu sannan ya kwanta bayan ya karanto addu'ar kwanciya barci anan fa barci ya k'auracewa idanunshi ya shiga tunan
in mafita na wannan al'amarin daya tunkaroshi, saidaya dad'e yana sak'a da warwara a zuciyarshi sannan ya yanke shawarar abinda zaiyi basai sun k'ara ganinshi bama har su aura masa itaba.
Ta b'angaren Janaan ma haka barci ya gagari idanunta du
k juyin da zatayi magana d'aya ce ke yawo cikin brain d'inta wai zata auri Yah Abdallah mutumin da suke mugun jin tsoronshi baya wasa dasu ko kad'an, tun tasowar su ta fahimci bashida dad'in zama wai kuma a haka shine zai zama mijinta? To takai tsoron nas
hi ina? ALLAH dai ya kawo