Showing 36001 words to 39000 words out of 191594 words
kai.
"Shi ya fita da kansa... amma kalaman da aka ga
ya masa sun fi ƙarfin zuciyarsa."
Hajiya Amina ta dafe ƙirji.
"Wallahi tun ranar da na bar
ɗ
ana a hannunsu, ban ta
ɓ
a nadama ba. Na san sun ba shi tarbiyya da soyayya. Amma ban ta
ɓ
a tunanin wata rana zai fita daga gidan da zuciya a karye ba."
Dada ta dubi
Abbi.
"To yanzu kana tunanin yana nan ne?"
"Na fara zaton haka. Saboda ban san wani wurin da zai nufa ba."
Dada ta girgiza kai a hankali.
"A'a."
Abbi ya
ɗ
ago ya kalle ta.
"Jalal ba irin yaron nan ba ne da zai zo nan idan zuciyarsa ta ji ciwo. Ba zai so a
ga kamar ya gudu wajen iyayensa na asali ba."
Hajiya Fatima ina ta share hawayenta.
"Haka ne. Tun da ya san gaskiyar rayuwarsa, bai ta
ɓ
a sauya mana matsayinmu ba. Amma kuma bai ta
ɓ
a rage wa Maryam da kai girma ba."
Dada ta yi murmushin tausayi.
"Na san ji
kana. Idan ya ji ciwo, yakan ware kansa ne. Zai nemi wurin da babu hayaniya har sai zuciyarsa ta huce."
Nan take wayar Hajiya Fatima ta yi ƙara.
Gabansu ya fa
ɗ
i.
Da sauri ta
ɗ
aga.
"Assalamu alaikum."
Sai aka ji muryar Jalaluddeen a can ƙasan layi.
"Wa a
laikumus salam... Mom."
Da jin muryarsa hawaye suka zubo daga idanunta.
"Jalal... kana ina ne?"
"Ki yi haƙuri Mom. Na kira ne kawai domin kada ku damu. Ina lafiya."
"Ina kake yanzu?"
Ya yi shiru na wasu daƙiƙu.
"Ina gidan da na gama ginawa."
Abbi ya miƙa
hannu cikin sauri.
"A ba ni wayar."
Hajiya Amina ta miƙa masa.
"Jalal."
"Na'am Abbi."
"Ka tsaya a inda kake. Ina zuwa yanzu."
"Abbi..."
"Kada ka ce komai. Ni ne zan zo. Kuma ba zan bar ka ka kwana kai ka
ɗ
ai da wannan damuwar ba."
Jalaluddeen ya yi shiru,
kafin daga ƙarshe ya ce cikin sanyin murya,
"To Abbi... zan jira ku."
Wayar ta katse.
Dada ta
ɗ
aga hannu sama tana cewa,
"Alhamdulillah. Allah Ya daidaita zukatan iyali kafin wannan ƙaramar matsala ta zama babba."
Abbi ya miƙe tsaye yana kallon Hajiya a da
Dada.
"Mu je tare. Yau ba Jalal ka
ɗ
ai yake buƙatar iyalinsa ba... mu ma muna buƙatar mu nuna masa cewa har yanzu yana da gida a inda yake."
Motar Abbi ta fice daga gidan Kabir Arzika cikin nutsuwa. A ciki kuwa shiru ne ya mamaye. Hajiya Amina na riƙe
da carbi tana ta ambaton Allah a hankali, yayin da Dada ke kallon duhun da fitilun titi ke yanka lokaci-lokaci.
Abbi ne ya karya shirun.
"Dada... ina jin na gaza."
Ta juya ta kalle shi.
"Me ya sa ka fa
ɗ
i haka?"
"Na kasa kare shi. Ina nan a matsayin ubansa,
amma aka sa yaron ya fita daga gida cikin baƙin ciki."
Dada ta girgiza kai.
"A'a Musa. Kada ka
ɗ
ora wa kanka abin da ba naka ba ne. Wani lokaci fitina tana shiga gida ne domin ta gwada ƙarfin zumunci. Yanzu abin da ya rage shi ne ku gyara."
Ya sauke numfa
shi mai nauyi.
"In sha Allah."
...
A
ɗ
aya
ɓ
angaren kuma...
Jalaluddeen yana tsaye gaban tagar bedroom
ɗ
insa. Hannunsa na cikin aljihun pajamarsa, idanunsa suna kallon fitilun birnin da suke walƙiya daga nesa.
Wayarsa ta sake yin ƙara.
Ya
ɗ
auka ba tare da y
a duba sunan mai kiran ba."Na'am."
"Yallabai."
Muryar direbansa ce.
"Na'am Usman."
"An sanar da ni cewa Alhaji Musa yana hanyarsa zuwa nan."
Jalaluddeen ya lumshe idanunsa.
"Na sani."
"Shin a bu
ɗ
e musu gate idan sun iso?"
"Eh. Kada a tsayar da su."
"To Yal
labai."
Ya ajiye wayar.
Ya sake kallon
ɗ
akin.
A yau ne ya fara jin cewa duk girman gidan nan ba ya da amfani idan babu mutanen da za su cika shi da rayuwa.
...
Bayan kusan mintuna talatin...
An ji ƙarar gate yana bu
ɗ
ewa.
Motar Abbi ta shiga cikin harabar g
idan.
Dada ta zaro ido tana kallon yadda aka tsara komai cikin tsari da ƙayatarwa.
"Subhanallah..."
Daa Gama ta kasa
ɓ
oye mamakinta.
"Wannan duk gidan Jalal ne?"
Abbi ya
ɗ
an yi murmushi.
"Eh. Shekaru yana ginawa a hankali. Yana so ya kammala komai kafin y
a tare."
"Kai..." Dada ta fa
ɗ
a cikin tausayawa. "Yaro ya gina irin wannan gida, amma ya rasa abin da ya fi muhimmanci... natsuwar zuciya."
Motar ta tsaya.
Kafin direba ya zagayo ya bu
ɗ
e ƙofa, Jalaluddeen ya fito daga cikin gidan.
Sanye yake cikin navy blue
pajamas, amma duk da haka kwarjininsa bai ragu ba. Sai dai fuskar nan tasa ta nuna gajiyar tunani fiye da yadda aka saba.
Da sauri ya ƙaraso.
"Assalamu alaikum."
"Wa alaikumus salam."
Bai tsaya komai ba, ya fara durƙusawa ya gaishe da Dada.
Ta dafa kans
a.
"Allah ya ƙara maka hankali da natsuwa."
Ya koma wajen Hajiya Fatima.
Ba ta bari ya gama gaisuwar ba, ta rungume shi tsam a ƙirjinta.
"Alhamdulillah... Alhamdulillah."
Jalaluddeen ya lumshe idanunsa.
Tun yana ƙarami bai ta
ɓ
a rasa wannan irin rungumar.
So ya sa a ce Mom ta je ta gani amma ranar tana asibiti. Washegari ya koma Kaduna
"Mom..."
"Kada ka sake tsorata ni haka."
"In sha Allah."
Sai ya matsa wajen Abbi.
Sun kalli juna na wasu daƙiƙu ba tare da magana ba.
Daga ƙarshe Abbi ya bu
ɗ
e hannay
ensa.
Jalaluddeen ya matsa ya rungume shi.
Rungumar da ba ta buƙatar kalmomi.
Abbi ya
ɗ
an buga bayansa.
"Ka yi kuskure da ka kashe wayarka."
"Cikin damuwa ne."
"Na sani."
Ya sake kallonsa cikin ido.
"Amma ka sani ko? Ko duniya za ta juya maka baya... ni b
a zan ta
ɓ
a juya maka baya ba."
Idanun Jalaluddeen suka cika da ruwa.
"Na sani Abbi."
Dada ta share hawayen da suka taru a gefen idanunta.
Ta yi addu'a a ranta.
"Ya Allah, ka ha
ɗ
a zukatan wannan iyali. Kada ka bari shai
ɗ
an ya samu gurbi a tsakaninsu."
Jalal
uddeen ya bu
ɗ
e ƙofar gidan cikin girmamawa.
"Bismillah... ku shigo gida."
Da suka taka cikin falon, kowa ya yi shiru na wasu daƙiƙu.
Ba wai saboda girman falon ka
ɗ
ai ba...
Sai saboda sun fahimci cewa duk wannan alatu ba ta iya
ɓ
oye ka
ɗ
aicin da mai gidan ya
ke ciki.
Dada ne da Mom suka zagaya suna duba ko ina na cikin gidan. Sai da suka duba ko ina sanan suka dawo suka same Abbi da Jalal a imds suka bar shi. Addu'a da fatan alkhairi suka yi ma sa.
"Yanzu ka zo mu koma gida ."
Jalal ya sunkuyar da kansa
ƙ
asa ya sosa kai.
"Abbi zan zo gobe idan Ummee ta sauko?"
Duk yadda Abbi ya so a Jalaluddeen ya bar gidan ya bar su zo su tafi Jalal bai bi shi ba.'
"Wanann karon ma an dakatar dakatar da wanan auren sai mun tabbatar da gaskiyar lamari tsakanin ka da w
acce ka ce matarka ce , idan mun tabbatar da cewa ba matarka ba ce sai a daura aurenka da Yasmeen. Idan kuma matarka ce to sai ka zauna da matarka. Yasmeen ta hakura. Idan kuma kana ganin dukkan su za ka ha
ɗ
a ba damuwa , sai mu bi ka da addu'a."
Daga haka
suka yi ma sa sallama kasancewar ya nuna shi kadai yake son ya kwana a nan ba zau je gidan kowa ba.
Sai da suka tafi sannan ya dawo cikin gidan.
Suka hanya ne kiran Dad ya shigo wayar Mom.
Take sanar da shi suna hanya.
Bayan sun koma gida ne suka shi
ga ciki yayin da Abbi ya tsaya a mota ya ce wa Mom ta sanar da Dad yana jiransa a wajan .
Yana cikin mota Dad ya shigo ya same shi cikin motar. Nan Abbi ke sanar da shi komai daga kan abun da ya faru a wajen Dinner party har yadda sukanyibda Ummee Jalalu
ddeen ya tafi gidansa. Daga karshe ya nemi alfarmar Abbi kam kada a daura auren nan a jira gaskiyar alaƙar sa da Ma'eesha. A dakatar da daurin auren da za'ayi gobe."
Da farko Dad bai amice ba da kyar Abbi ya shawo kan Dad ya amince.
Sallama suka yi da j
una sanan ya shigo ciki.
*Washegari*
Suna zaune a falon suna hira cike da nisha
ɗ
i. Dada, Mom, Hajiya Safiyya da Hajiya Saratu.Kabeer, Haidar, Saddiƙa, Safiyya, da Safna, sai kuma Ma'eesha."
Hira suke yi cikin farin ciki da nisha
ɗ
i. Hira ne na na an da
de ba'a hadu haka ba. Ma'eesha ce kawai ta raku
ɓ
e gefe ba ta da walwala.
Horn ya danna maigadin ya wangale ma sa gate, bayan ya leka ya tabbatar waye.
Dada ke cewa .
"Ina Sulaiman ne?"
Mom ta amsa masa da cewa .
"Yana part
ɗ
in Alhali suna hira a can.
"
Murmushi ta yi tana cewa.
"Oho su suna can kenan suna masu daban."
"Ke Gwaggo kike wa ake kira ki?"
Ta yi maganar tana kware murya.
Da sauri Gwaggon mai aikin Mom ta shigo ta durƙusa a gaban Dada.
"Ga ni Hajiya."
"A kawo mana abun ta
ɓ
awa mana, kin
a ganin muna hira kin bar mu ba abun ta
ɓ
awa.?"
"To Hajiya ina zuwa ."
Ta yi maganar tana budar kitchen.
Nam ta fito da mayan farantai guda biyu da snacks a ciki .
Ta koma ta kawo masu abun sha .
_Jalaluddeen_
Tsawon mintina goma yana cikin motarsa
kafin ya fito ya shiga ciki .
Da sallama ya shiga cikin falon, suka amsa ma sa. Nan ya gaida Dada, Mom, Hajiya Safiyya da Hajiya Saratu. Sanan suka gaisa da Haidar da Kabeer. Saddiƙa da Safna da Jamila suka gaishe shi.
Ko kallon inda Ma'eesha take bai
yi ba.
Sai satar kallonsa take yi amma shi ko kallon ta bai yi ba. Hakan ya dame ta.
Karshe ya mike ya nufi part
ɗ
in Dad.
Bayan ya gaida Dad da Alhaji Sulaiman ya fito.
A falon ya zauna ya sa Saddiƙa ta kawo masa shayi ya sha.
Bayan ya sha shayin ya y
i ma su sallama ya sannan ya fita
"Ma'eeha na ganin ya fita sai ta nufi dakinta.
Jikin window ta tsaya ta janye labule tana kallon sa yana tafiya cikin takunsa na ƙasaita.
Har ya shiga motarsa ya fice daga gidan . Garin haka ya sa ga fashe da kuka .
*Maman Ihsan ce*✍
09065327995
[7/9, 6:02 PM] Antysalima Grp: *MAKAHO NE*
_Book 2_
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*
Page 1
️
⃣
0
️
⃣
4
️
⃣
Har ya shiga motarsa ya fice daga gidan. Ganin haka ya sa ta fashe da kuka.
Ma'eesha ta ci gaba da tsaye jikin
window, idanunta na bin motar Jalaluddeen har sai da ta
ɓ
ace daga gani.
A hankali ta jingina goshinta da gilashin window.
Numfashinta ya fara nauyi.
"Ko kallona ma bai yi ba..."
Kalmar ta fito daga bakinta cikin ra
ɗ
a.
Tun ranar da suka ha
ɗ
u a dinner party
har zuwa yau, wannan ne karo na farko da Jalaluddeen ya zo gabanta ya fita ba tare da ya ko kalle ta ba.
Ba wai magana ba...
Ko
ɗ
aga ido ya yi ya ga inda take, bai yi ba.
Wannan shiru nasa ya fi mata kowace magana zafi.
Ta lumshe idanunta.
Hotunan abubuwa
n da suka faru suka fara dawo mata
ɗ
aya bayan
ɗ
aya.
Yadda Dad ya tambaye ta ko ta san Jalaluddeen...
Ita kuma cikin tsoro da ru
ɗ
ani ta girgiza kai.
"A'a... ban san shi ba."
Yanzu kalmar tana kara mata amsa kuwwa a cikin kunnuwanta.
Ta dafe ƙirji.
"Ya Allah
..."
Hawayen da take taƙurewa suka zubo.
"Ina na shiga ne?"
Ta zauna a gefen gadonta tana share hawaye.
Da ta ce ba ta san shi ba...
Ta yi tunanin hakan ne zai kawo ƙarshen komai.
Ashe ita ce ta ƙara dagula lamarin.
Yanzu idan Jalaluddeen ya yi shiru da it
a...
Da wace fuska za ta je ta ce masa ta yi ƙarya ne saboda tsoro?
Ta yi shiru tana kallon sararin
ɗ
akin.
Sai kuma wata magana ta fa
ɗ
o mata.
"An dakatar da auren..."
Sai zuciyarta ta buga.
Amma...
Wata zuciyar ta sake ce mata,
"Me zai hana ma an tabbatar
Ma'eesha ce matarsa... aka tafi aka daura musu aure yau?"
Nan take ta zabura.
"A'uzubillahi..."
Ta girgiza kai da sauri.
Amma tunanin ya ƙi barinta.
Ai tun da ya fita daga gidan nan...
Wataƙila yanzu yana tare da ita.
Wataƙila yanzu suna zaune suna hira.
K
o ma...
Ta kasa ƙarasa tunanin.
Wani irin zafi ya ratsa zuciyarta.
Ta dafe baki tana fashewa da kuka.
"Na rasa komai saboda ƙarya ta..."
Ta yi kuka sosai.
Ba wai saboda an yi mata wani abu ba...
Sai saboda yanzu ta fara fahimtar darajar mutumin da ta ƙarya
ta.
Jalaluddeen bai ta
ɓ
a tilasta mata komai ba.
Bai ta
ɓ
a tona mata asiri ba.
Bai ta
ɓ
a wulaƙanta ta a gaban kowa ba.
Ko bayan ta musanta saninsa...
Ya yi shiru.
Amma wannan shiru nasa...
Shi ne yake cinye zuciyarta.
Ta share hawayenta.
A karon farko ta furt
a da ƙarfi,
"Na yi kuskure..."
Ta sake rushewa da kuka.
A ƙasa-ƙasa tana maimaitawa,
"Ka yi haƙuri Jalal..."
"Wallahi ba don na tsane ka ba..."
"Tsoro ne ya sa na yi haka..."
Amma babu wanda yake jin ta.
A
ɗ
aya
ɓ
angaren kuma...
Motsi ta ji a bayanta, ta w
aiga a firgice.
_Ummee_
Falon ya yi tsitSai ƙarar agogon bango ka
ɗ
ai ke karya shirun falon.
Ummee tana zaune a inda Jalaluddeen ya bar ta. Idanunta sun kumbura saboda kuka, amma zuciyarta ta fi idanunta ciwo. Carbin da ke hannunta ya tsaya cik. Tun b
ayan fitar Jalaluddeen ba ta ƙara iya ambaton komai ba.
Sai aka ji ƙarar bu
ɗ
ewar ƙofar waje.
A hankali Abbi ya shigo.
Da sallamarsa ya tsaya yana kallonta.
"Assalamu alaikum."
Ba ta amsa nan take ba. Sai bayan wasu daƙiƙu.
"...Wa alaikumus salam."
Abbi ya
fahimci akwai abin da ya faru. Fuskar Ummee ta wadatar wajen bayyana irin tashin hankalin da take ciki.
Ya cire hularsa ya ajiye, sannan ya zauna a kujerar da ke fuskantarta.
"Har yanzu kina nan?"
Ummee ta
ɗ
aga ido.
"Barci ya ƙi zuwa."
Abbi ya sauke numfa
shi.
"Ni ma."
Shiru ya sake mamaye falon.
Bayan
ɗ
an lokaci Abbi ya ce,
"Na gama magana da iyayen Ma'eesha."
Kalmar ta sa Ummee ta
ɗ
ago sosai.
"Me ka ce musu?"
Abbi ya ha
ɗ
e hannayensa.
"Na dakatar da batun auren."
Kamar an zabga mata mari.
Ta miƙe tsaye ba
tare da ta ankara ba.
"Me ka ce?"
"Na ce na dakatar da auren."
"Abdulrahman!"
Muryarta ta cika da firgici.
"Ka san abin da kake fa
ɗ
a kuwa?"
Abbi ya kalle ta cikin nutsuwa.
"Sosai ma."
"A'a!"
Ta girgiza kai da ƙarfi.
"Wannan aure ba zai tsaya ba."
Abbi ya
yi shiru.
Ummee ta ci gaba.
"An riga an
ɗ
aura aure. Mutane sun san komai. Dangi sun taru. Yanzu saboda rikicin yaro za ka ce an dakatar?"
Abbi ya ce cikin sanyin murya,
"Ba rikicin yaro ba ne."
Sai ya
ɗ
an dakata.
"Maganar aure ce."
Ya jingina bayansa.
"Kum
a aure ba wasa ba ne."
Ummee ta yi dariyar takaici.
"Saboda wata yarinya?"
Abbi ya
ɗ
aga gira.
"Ba saboda ita ka
ɗ
ai ba."
"To saboda me?"
Saboda Jalaluddeen da kansa."
Ummee ta yi shiru.
Abbi ya ce,
"Kin ji abin da yake fa
ɗ
a."
Ta
ɗ
an kau da kai.
"Ya ce Ma'ee
sha matarsa ce."
Kalmar ta rataye a tsakanin su.
Abbi ya ci gaba.
"Ko gaskiya yake fa
ɗ
a ko ƙarya, ba zan bari na tura Yasmeen cikin gidan da ba mu san hakikanin matsayinta ba."
Ummee ta ce cikin fushi,
"Na san Jalaluddeen. Zuciyarsa ce kawai ta rikice."
"K
o da haka ne."
Abbi ya amsa.
"Shari'a ba ta tafiya da rikicewar zuciya."
Ummee ta yi saurin cewa,
"Wannan yarinyar ce ta ru
ɗ
e shi."
Abbi ya girgiza kai.
"Kada mu
ɗ
ora komai a kanta."
"Sai wa?"
"Jalaluddeen."
Kalmar ta fito da ƙarfi.
"Shi ya yi abin."
"Shi
ya bar amaryarsa."
"Shi ya bi wata."
"Shi ya jefa iyalinsa cikin wannan hali."
Ummee ta runtse ido.
Duk da tana fushi da Jalaluddeen, jin wani yana
ɗ
ora masa laifi gaba
ɗ
aya yana ƙara mata ciwo.
Ta ce,
"Amma Yasmeen fa?"
Abbi ya amsa,
"Shi ya sa na dakatar
."
Ta kalle shi cikin rashin fahimta.
Ya ce,
"Ina son kare Yasmeen."
"Kare ta ta wace hanya?"
"Ta hanyar tabbatar da cewa ba za mu miƙa ta ga mutumin da zuciyarsa take wani wuri ba."
Ummee ta
ɗ
aga murya.
"Amma tana sonsa!"
"Na sani."
"Shi ma yana sonta."
A
bbi ya yi murmushi mara da
ɗ
i.
"Da yana sonta yadda ya kamata, da bai bar ta a ranar aurenta ba."
Kalmar ta yi wa Ummee zafi.
Ta juya gefe.
Abbi ya ci gaba cikin natsuwa.
"Na gaya wa iyayenta cewa sai an bincika wannan batu."
"Idan Ma'eesha matarsa ce da ga
ske..."
Sai ya yi shiru.
"...to sai mu san yadda za a warware abin."
Ummee ta yi saurin cewa,
"Ba za a warware komai ba."
Abbi ya
ɗ
aga kai.
"Me kike nufi?"
Ta kalli idanunsa.
"Ko da Ma'eesha matarsa ce..."
Sai ta ha
ɗ
iye yawu.
"...dole ne Jalaluddeen ya zau
na da Yasmeen."
Abbi ya zura mata ido.
"Me kika ce?"