Showing 57001 words to 60000 words out of 191594 words
ko ta
ɓ
a ba.
Hannunsa ya rufe fuskarsa.
A wannan karon kuma, hawaye suka zubo ba tare da ya iya tsayar da su ba.
A karo na farko
cikin rayuwarsa, ya fahimci cewa wasu laifuka ba sa barin mutum ya zauna lafiya, ko da babu wanda ya sani. Mafi tsananin hukunci wani lokaci shi ne wanda lamiri yake yanke wa mutum a cikin zuciyarsa.
*Maman Ihsan ce*✍
️
09065327995
[7/13, 9:19 PM] Ant
ysalima Grp: *MAKAHO NE*
_BOOK 2_
*NA*
Maman Ihsan ce✍
️
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*
"LITTAFINA NA KUƊI NE KADA KI KARANTA MANI LITTAFI BA TARE DA KIN BIYA NI HAKKINA BA. NAIRA DUBU ƊAYA NE KACAL . A TURA NAIRA DUBU ƊAYA CIKIN WANAN ACCOUNT
2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank. Sai a tura shaidar biya ta wanan lambar waya. 09065327995.
Page1
️
⃣
1
️
⃣
2
️
⃣
A karon farko na rayuwarsa ya fahimci cewa Wasu laifuka basa barin mutun ya zauna lafiya .ko da babu wanda ya sani. Mafi tsananin hukunci wa
ni lokaci shi ne wanda lamari yake yanke wa mutum a cikin zuciyarsa.
_Yasmeen_
Ba abun da ake ji a cikin falon sai sautin kukanta. Dad ne ya kira sunan ta cikin wata murya mai sanyi.
"Yasmeen."
"Na'am Dad."
"Ki yi hakuri ki
ɗ
auki ƙaddara. Auren Jala
luddeen da Ma'eesha Allah ne ya ƙaddara shi a lokacin da babu wanda ya yi zaton sa. Mun yi magana da mahaifinki jiya akan makomar auren ki da Jalaluddeen. Mun so mu ce ya ha
ɗ
a ku duka biyu ya aura. Amma fahimtar cewa baya da ra'ayin ha
ɗ
a mata biyu ne sa ba
mu yi haka na. Domin mun fahimci zuciyarsa tafi karkata ga Ma'eesha akanki. Hakan ya da muka yanke shawarar ha
ɗ
a ki da ƙaninsa Doctor. Duk da mun yanke shawarar ba tare da neman amincewar ku ba. Fatan za ku yi mana biyayya ku amince da wanan hukunci da m
uka yanke."
Sadik dai bai motsa ba kuma bai
ɗ
aga kai ya kalli kowa a cikin su ba. Amma tabbas hukuncin da ake yanke a kan ha
ɗ
a shi aure da Yasmeen bai ma sa dadi ba, sai dai bai da ta cewa akai.
Dada ce ya gyara zama tana cewa.
"Alhamdulillah. Mun gode
wa Allah bisa ni'imomin da ya yi mana. Tun da dama auren Ma'eesha na rashin gata aka yi ma ta. To ina so ranar da za'ayi bikin Sadik da Yasmeen a hada ayi buki nasu suka su hudu. Biki na kece raini za'ayi ."
Ta karasa maganar tana ranga
ɗ
a gu
ɗ
a. Gabadaya a
ka saka dariya.
Kallon Dad ta yi tana cewa .
"Yaushe za'a
ɗ
aura auren?"
"Next week in sha Allah."
"To Allah ya kai mu, sai a fara shiri sosai da sosai, idan ta aka daura auren ranar sai kowacce akai ta gidan mijinta."
Yasmeen ta mike ta nufi
ɗ
akin Mo
m. Har lokacin kuka take yi.
Mom ta kalli Sadik da kansa yake a sunkuye ya kasa cewa komai .
"Ka je ka same ta ku yi magana, idan ba ta amince ba kada ka yi ma ta dole , sai s hakura Allah ya zama mana mafi alkhairi."
Cikin sanyin jiki ya tashi ya nuf
i
ɗ
akin Mom.
Da sallama a bakinsa ya tura ƙofar
ɗ
akin ya shiga ciki.
Tana tsaya ta kifa kanta da bango tana aikin kuka.
Ƙ
arasawa ya yi gabanta yana kallon ta.
Jin motsin mutum a bayanta ne ya saka ta juyo da sauri.
Idanu biyu suka yi da juna, kafin ta
ɗ
auke kai .
"Yasmeen."
Ta juyo ta kalle shi sannan ta mayar da kai ta cigaba da rera kukan da take yi.
"Yasmeen."
Ya kira sunan ta cikin sanyin murya.
"Zan iya shigowa?"
"Ka riga ka shigo."
"Na san wannan ba lokaci ne mai sauƙi ba."
Goge hawayeta
ta yi kafin ta ce .
"Ba lokaci ne mai sauƙi ba ga kowa."
Jinjina kai ya yi kafin ya dora da cewa.
"Da ma ban zo ba... amma idan ban zo ba, zan ji kamar na gudu daga gaskiya."
"Na zo ne ba don in matsa miki ba.Na zo ne in ji ra'ayinki."
"Ra'ayi? Kana s
on a ji ra'ayina ne yanzu, bayan an gama magana a kaina?"
"Eh. Ko da kuwa abin da za ki fa
ɗ
a ba zai yi mini da
ɗ
i ba."
"Yaushe aka fara tambayar mata ra'ayinsu bayan an riga an yanke hukunci?"
"Idan kika ce a'a... zan fa
ɗ
a musu."
"Za ka fa
ɗ
a musu?"
"Eh
."
"Za su saurare ka?"
"Wannan ita ce tambayar da nake ta yi wa kaina tun da na fito."
"To kenan."
"Ko ka fa
ɗ
a, ko ba ka fa
ɗ
a ba... abin da Allah ya rubuta ne zai faru."
Ta yi maganar tana gobe tawayen tava karo na ba adadi.
"Idan aka ce kin aure ni.
.. me za ki yi?"
"Mutane suna rayuwa da abubuwan da ba sa so."
"Amma ke fa?"
"Ni ma mutum ce. Ina da zuciya, ina da tsoro, ina da abin da nake so da abin da bana so."
"Ban zo in dame ki ba."
"Sadik."
"Eh?"
"Idan zuciyar mutum ta karye... ana iya gya
ra ta ne?"
"Ban sani ba ko ana gyara ta kamar yadda take ba. Amma na san ana iya koya wa zuciya ta sake daina jin tsoro."
"Ba duk wanda ya karye ne zai iya sake tsayawa ba."
"Na sani."
"To me ya sa ka zo?"
"Saboda ban so ki ji kamar an yi miki shiru n
e kawai."
"Shiru ya fi magana ciwo wani lokaci."
"Na fahimta."
"Idan ka tafi yanzu, ka bar ni da wannan nauyin?"
"Idan na tsaya ma, ba zan iya
ɗ
auke miki shi ba."
"To ka yi mini alƙawari
ɗ
aya."
"Menene?"
"Idan ka ga ba zan iya ba... ka fa
ɗ
a musu gas
kiya. Kada ka bar ni in zama abin da wasu suka za
ɓ
a mini."
"Na yi alƙawari."
"Na gode."
"Ki kula da kanki."
"Ba kowa ke da damar yin hakan ba."
"Ki gwada."
"Zan gwada."
"Na tafi."
"Sadik..."
"Eh?"
"Na ji."
"Me kika ji?"
"Na ji cewa ba ka zo da
zuciyar da ta riga ta yanke hukunci ba."
"Ba zan ta
ɓ
a yanke hukunci a madadinki ba."
"To ka tafi kafin in sauya ra'ayi."
"Na tafi."
"Sadik?"
"Eh?"
"Ko da komai ya lalace... kada ka manta cewa na yi ƙoƙari."
"Ba zan manta ba."
"To je."
Ya juya a ha
nkali, zuciyarsa cike da nauyi. Ta tsaya a bakin ƙofa tana kallonsa har sai da ya
ɓ
ace daga gani. Sai ta jingina da bango, ta runtse ido, ta
ɗ
auki dogon numfashi kamar wadda ke ƙoƙarin tara ragowar ƙarfin da ya rage mata.
Dama tana da saukin kai Ummee ce
ke
ɗ
ora ta a hanyar da ba ta dace ba
A waje, iska ta busa a hankali. A cikin zuciyarsa kuwa, kalmomin da ta fa
ɗ
a suna ta maimaituwa kamar karar ƙararrawa: kada ka bar ni in zama abin da wasu suka za
ɓ
a mini.
Ya san yanzu ba magana ka
ɗ
ai ce ta rage ba. Akw
ai yanke shawara. Akwai gaskiya. Kuma akwai abin da zai iya canza komai.
_Ma'eesha_
Tana shiga cikin
ɗ
aki ta saki ajiyar zuciya, take ta ji wani farin ciki ya mamaye zuciyarta. Yanzu ta tabbatar da cewa Jalaluddeen nata ita kadai ba tare da Yasmeen ba.
Murmushi mai sauti ta ce yi tare da cewa .
"Alhamdulillah."
Daga bakin ƙofa ta ji mutuwarsa yana cewa .
"Ma sha Allah."
Da sauri ta juya ta kalle shi, yana tsaye ya sakar mata tsadadden murmushinsa.
"Farin ciki na maye kike yi Mrs J.?"
Ya yi maganar
yana karasawa in da take tsaye.
Ƙ
uginta ya riko ya mamna da da jikinsa,.
"Fa
ɗ
a mani wani abu."
"Wani abu.?"
"Wani abu zan fada maka."
"Ranar asabar ne za'a gudanar da bikin aure. Mu, Ina son zan yi wata ƴar tafiya na kwanaki uku , akwai aikin zan y
i Zan dawo ana saura kwana biyu bikin.zan dawo. Sannan kuma ina son ki za
ɓ
i ƙasashe guda uku da kike son mu je honey moon."
Murmushi mai sauti ta yi kafin ta ce .
"To ai ban san wasu ƙasashe sa da suke da dadi ba, ƙasashe biyu na ta
ɓ
a zuwa daga Saudiyy
a sai kasar egyp."
"Bari na nuna maki sunan wasu ƙasashen ki za
ɓ
a uku a ciki"
Ya kunna wayarsa, ya bu
ɗ
e wani shafi mai cike da hotunan wuraren bu
ɗ
e ido.
"Yau za ki za
ɓ
a. Duk inda kika ce, nan za mu tafi."
Ma'eesha ta matsa kusa da shi, idanuwanta
suka sauka kan allon wayar.
Jalaluddeen ya fara lissafawa.
"Na farko... Maldives."
Ya nuna mata hoton gidajen da aka gina a saman ruwa.
"Kalli wannan. Dakuna suna kan ruwa. Da safe idan kin bu
ɗ
e ƙofa, abin da za ki fara gani shi ne tekun shu
ɗ
i. Da dare
kuma ana cin abinci ƙarƙashin hasken taurari."
Ma'eesha ta saki ajiyar zuciya.
"Subhanallah... kamar ba a duniya ba."
Ya yi murmushi.
"Na biyu... Switzerland."
Sai ya nuna mata tsaunukan da dusar ƙanƙara ta rufe.
"Idan kina son sanyi, duwatsu masu k
yau, jiragen ƙasa masu ban mamaki da ƙauyuka kamar a cikin tatsuniya, wannan ya dace."
Ta yi dariya.
"Ni kam zan daskare."
"Duk da haka kina da kyau cikin manyan rigunan sanyi."
Ta harare shi da wasa.
"Ka dai iya fa
ɗ
in magana."
Ya ci gaba.
"Na uku..
. Paris, France."
"Birnin soyayya kenan?"
"Eh. Ana yawan cewa haka. Za mu zagaya cikin dare, mu ga fitilu, mu ci abinci a gidajen cin abinci masu kyau."
"Na hu
ɗ
u... Dubai."
Ya canja hoton.
"Ba sai na yi bayaninsa ba. Gine-gine masu tsayi, manyan shopp
ing mall, desert safari, jirgin ruwa..."
Ma'eesha ta ce,
"Wannan ma yana da kyau."
"Na biyar... Santorini, Greece."
Ya nuna mata gidaje farare masu rufin shu
ɗ
i.
"Mutane da yawa suna zuwa can domin honeymoon."
"Wai duk wa
ɗ
annan ka riga ka bincika?"
"
Na da
ɗ
e ina bincike tun kafin ki zama matata."
Ta dube shi cikin mamaki.
"Ashe dama kana da wannan shirin?"
"Na yi shi ne da fata. Ban san lokacin da Allah zai cika min burin ba."
Maganarsa ta ta
ɓ
a zuciyarta.
Ta kama hannunsa a hankali.
"Alhamdulilla
h."
Ya ci gaba da lissafi.
"Sai kuma Turkey, musamman Cappadocia, inda balloons masu launuka suke tashi da sassafe."
"Japan, musamman lokacin furen Sakura."
"Italy, Venice, inda ake yawo cikin kwale-kwale."
"Bali a Indonesia."
"Seychelles."
"Mauriti
us."
"Kuma Zanzibar."
Ma'eesha ta yi dariya.
"To, Alhaji, kana so mu yi wata shida muna yawon amarci ne?"
Ya ha
ɗ
e fuska da wasa.
"Da ace aiki ba ya jira, da na yarda."
Ta girgiza kai tana dariya.
"Yanzu dai ka ce na za
ɓ
i uku."
"Eh. Uku kacal."
Ta
yi shiru tana sake kallon hotunan
ɗ
aya bayan
ɗ
aya.
Bayan wasu daƙiƙu ta
ɗ
aga ido.
"Na farko... Maldives."
Jalaluddeen ya yi alamar rubutawa.
"An rubuta."
"Na biyu... Switzerland."
"Shi ma an rubuta."
Ta
ɗ
an yi tunani.
"Na uku..."
Ta yi shiru har y
a fara kallonta.
"Kada ki ce Dubai."
"Me ya sa?"
"Saboda Dubai za mu iya zuwa ko bayan honeymoon."
Ta yi murmushi.
"To... sai Santorini."
Jalaluddeen ya tafa hannu cikin farin ciki.
"Excellent choice!"
Ya
ɗ
ago ya kalle ta.
"Maldives, Switzerland,
da Santorini."
Ta gyara masa.
"Amma da sharadi."
Ya
ɗ
an yamutsa fuska.
"Wane sharadi kuma?"
"Duk inda za mu je, ba yawon hotuna kawai za mu yi ba."
"To me kuma?"
"Ina so mu samu lokaci mu yi hira, mu yi yawo cikin natsuwa, mu tara abubuwan tunawa da
za mu riƙa ba wa 'ya'yanmu labari nan gaba."
Jalaluddeen ya yi shiru na
ɗ
an lokaci, kalamanta sun shiga zuciyarsa.
Daga bisani ya
ɗ
auki hannunta ya sumbaci bayan tafinta cikin girmamawa.
"Kin san abin da ya fi burge ni?"
Ta girgiza kai.
"Ba ƙasashen
da kika za
ɓ
a ba... abin da ya fi burge ni shi ne, duk inda zan je, muddin kina tare da ni, wajen zai zama mafi kyau a duniya."
Ma'eesha ta sauke kanta cikin kunya, murmushi mai cike da farin ciki ya bayyana a fuskarta.
"Allah ya sa mu je lafiya."
"Amin.
"
Ya ha
ɗ
a yatsunsa da nata.
"Ba kawai honey moon ba... ina addu'ar Allah Ya sa rayuwarmu gaba
ɗ
aya ta kasance tafiya mai cike da soyayya, fahimta da albarka."
"Amin ya Rabbal Alamin."
Sai suka zauna suna ci gaba da kallon hotunan wuraren, suna tattauna
abin da za su yi idan suka isa kowace ƙasa, yayin da dare ke ƙara yin shiru, zuciyoyinsu kuwa cike da fatan kyakkyawar rayuwar aurensu.
Wayarsa ta yi kara sunan da ya gani ne ya saka gabansa fadawa. Karo na farko a rayuwarsa da ta kira shi waya ya ji f
argaba.
*Maman Ihsan ce*✍
️
09065327995
[7/15, 9:15 AM] +234 806 751 7384: *MAKAHO NE*
_BOOK 2_
*NA*
Maman Ihsan ce✍
️
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*
"LITTAFINA NA KUƊI NE KADA KI KARANTA MANI LITTAFI BA TARE DA KIN BIYA NI HAKKINA BA. NAIRA
DUBU ƊAYA NE KACAL . A TURA NAIRA DUBU ƊAYA CIKIN WANAN ACCOUNT 2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank. Sai a tura shaidar biya ta wanan lambar waya. 09065327995.
IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA NA BAR KI DA ALLAH.
Page1
️
⃣
3
️
⃣
Wayarsa ta yi ƙara Sudan s
a ya gani yanda saka gabansa ya fa
ɗ
uwa. Karo na farko a rayuwarsa da ta kira tsaya ya ji fargaba.
Wayar ta ci gaba da ƙara a hannunsa.
Sunan da ke haske a jikin screen
ɗ
in ya sa murmushin da ke fuskarsa ya
ɗ
auke gaba
ɗ
aya.
Ummee Calling...
Numfashins
a ya
ɗ
an yi nauyi.
Ma'eesha ta lura da canjin fuskarsa, ta
ɗ
an matsa kusa da shi.
"Lafiya kuwa?"
Ya lumshe ido na
ɗ
an lokaci kafin ya ce a hankali,
"Ummee ce."
Da jin sunan, Ma'eesha ta yi shiru. Ta ji labarin Ummee a wajen Saddiƙa. Ta san irin burint
a na ganin Yasmeen ce ta zama matar Jalaluddeen.
Wayar ta sake ƙara.
Ta uku.
Ta hu
ɗ
u.
Ya
ɗ
an shafa fuskarsa da tafin hannu.
"Ka
ɗ
aga mana."
Ma'eesha ta fa
ɗ
a cikin tausasasshiyar murya.
"Kar ta ce kana gudunta."
Ya
ɗ
aga mata ido.
"Ban ta
ɓ
a jin tsor
on amsa kiran Ummee ba sai yau."
Ma'eesha ta kamo hannunsa.
"Ka yi mata magana cikin girmamawa. Duk abin da ta fa
ɗ
a, ka tuna tana cikin ciwo da ra
ɗ
a
ɗ
in abun da ya faru ne."
Ya gyada kai.
Sai ya latsa wayar.
"Assalamu alaikum Ummee."
Sai dai ba amsa
sallamarsa ya fara ji ba.
Muryarta ta fito a cike da kuka da takaici.
"Yanzu kai har kana da ƙarfin da za ka bar ni ina ta kira ka ba ka
ɗ
agawa?"
Ya runtse ido.
"Yi haƙuri Ummee..."
"Haƙuri?"
Ta katse shi.
"Jalaluddeen, wannan ita ce kalmar da ka zo
da ita?"
Ya yi shiru.
Ta cigaba.
"Na raini ka tun kana shekara
ɗ
aya a duniya. Allah Ya sani kamar
ɗ
ana na cikina na riƙe ka."
Muryarta ta fara rawa saboda kuka.
"Na share maka hawaye. Na kai ka makaranta. Na yi fama da rashin barci saboda kai. Duk lo
kacin da ka yi rashin lafiya, ni ce nake kwana a kanka."
Jalaluddeen ya sunkuyar da kai kansa.
Kowace kalma tana sauka a zuciyarsa kamar dutse.
A gidan Ummee kuwa...
Zaune take a saman kujera, idanuwanta sun kumbura saboda kuka.
Ta sake magana cikin
muryar da ke cike da ciwo.
"Ka san abin da ya fi mini zafi?"
Ya ha
ɗ
iye yawu.
"A'a... Ummee."
"Ba don ka auri Ma'eesha ba."
Ya
ɗ
ago kansa cikin mamaki.
"Abin da ya fi mini ciwo shi ne... ka bar ni ina gina buri shekaru da shekaru."
Ta share hawayenta
.
"Duk wanda ya tambaye ni matar Jalaluddeen, sai na ce Yasmeen.
"Wannan yarinyar tun tana ƙarama ake cewa matar Jalaluddeen ce haka ƙawayena ke cewa.
Muryarta ta ƙara karyewa.
"Ni na yarda. Kowa ya yarda. Kowa ya yarda."
Sai ta fashe da kuka.
"Amma
ashe kai ka da
ɗ
e da wata zuciyar."
Jalaluddeen ya dafe goshinsa.
"Wallahi Ummee..."
"Kada ka rantse."
Ta sake katse shi.
"Kada ka rantse mini."
Ya yi shiru.
Bayan wasu daƙiƙu ya ce cikin ladabi,
"Ummee... Wallahi ban ta
ɓ
a nufin na cuce ko na ƙunta
ta wa zuciyarki ba."
"To me ya sa ka yi mini haka?"
"Saboda..."
Ya kasa ƙarasa maganar.
"Ka yi magana."
Ya sauke numfashi.
"Saboda abin ya fi ƙarfina."
"Yaya ya fi ƙarfinka?"
"Da farko Dad da Abbi ba su san komai ba."
"Da suka sani fa?"
"Sai suk
a kira ni."
Ya
ɗ
an dakata.
"Suka tambaye ni gaskiya."
"Na fa
ɗ
a musu."
"Daga nan suka ce tunda an yi aure ba za a rusa abin da Allah Ya halatta ba."
Ya cigaba cikin sanyin murya.
"Su ne suka yanke hukuncin cewa Ma'eesha ita ce za ta ci gaba da zama ma
tata."
"Kuma Yasmeen?"
Ta tambaya da muryar da ta yi sanyi fiye da da.
"Su ne suka ce a ha
ɗ
a ta da ƙanina Sadik."
"Kai fa?"
"Ni..."
Ya lumshe ido.
"Ni
ɗ
ansu ne."
"Ba zan iya karya umarninsu ba, dole na yi ma su biyayya idan ina son ganin