Showing 165001 words to 168000 words out of 191594 words

Chapter 56 - MAKAHO NE COMPLETE

wasu kuwa suka fara gyara mayafinta da

ɗ

aurin gyalenta.

A gefe guda kuma, ƙannen Abba, G

waggo Laraba da Gwaggo Maimuna, ba su bi sahun kawayen ba. Sun nufi part

ɗ

in Mimi cikin nutsuwa domin su isar da amanar da aka

ɗ

ora musu.

Da suka isa ƙofar falon, suka yi sallama.

"Assalamu alaikum."

Mimi ta amsa cikin fara'a.

"Wa alaikumus salam. A sh

igo mana."

Ta taso daga inda take zaune cikin mutunci, ta tarbe su da fara'a, ta nuna musu kujera.

"Barkan ku da zuwa."

"Barka dai."

Bayan sun zauna, aka kawo musu ruwa da lemo. Sun

ɗ

an sha ka

ɗ

an kafin Gwaggo Laraba ta gyara zamanta, ta kalli Mimi da m

urmushi.

"Alhamdulillah. Mun zo ne da amanar da iyayen Sidra suka

ɗ

ora mana."

Mimi ta gyara zamanta sosai, fuskarta ta nuna tsantsar kulawa.

"Ina jin ku."

Gwaggo Maimuna ta ce cikin taushin murya,

"Sidra tun tana ƙarama ta taso cikin kulawar iyayenta

da danginta. Yau Allah Ya kawo ranar da muka raka ta gidan aurenta. Mun zo ne mu miƙa miki amanarta. Daga yau ke ce uwa gare ta a wannan gida."

Gwaggo Laraba ta

ɗ

ora da cewa,

"Idan ta yi kuskure, muna roƙon ki ki

ɗ

auke ta tamkar 'yarki. Ki gyara ta da na

siha, ba da fushi ba. Ita ba cikakkiya ba ce, kamar yadda babu cikakken mutum."

Mimi ta saurare su cikin nutsuwa. Kafin su gama magana har idanunta sun cika da tausayin wannan amanar da aka damƙa mata.

Ta

ɗ

aga hannayenta ka

ɗ

an tana cewa,

"Wallahi na kar

ɓ

i wannan amana hannu biyu-biyu. Daga yau Sidra ba suruka kawai ba ce a wajena, 'yata ce. Zan kula da ita kamar yadda zan kula da

ɗ

iya da na haifa. Idan ta yi daidai zan yaba mata, idan kuma ta yi kuskure zan gyara ta cikin hikima da soyayya."

Ta

ɗ

an yi s

hiru sannan ta ci gaba.

"In sha Allah ba za ku ta

ɓ

a jin wani abu mara da

ɗ

i daga gare ta a gidana ba. Ina roƙon Allah Ya sanya albarka a wannan aure, Ya ha

ɗ

a zukatansu cikin soyayya da fahimtar juna."

Fuskar Gwaggo Laraba ta washe da murmushi.

"Alhamduli

llah. Wannan ita ce maganar da muka yi fatan ji. Yanzu za mu

ɗ

auke ta mu kai ta har can

ɓ

angaren ta sanan mu koma dare na yi.

Suka kama hannun Nadra do. Zuwa kai ta part din ta daga bayan na s7 M

Gwaggo Maimuna ta ce,

"Allah Ya saka da alheri. Allah Ya

sa ku ga zaman lafiya da zuri'a ta gari."

Mimi ta amsa da,

"Amin ya Rabbal Alamin. Allah Ya saka muku da alheri da kuka kawo mana amanarku cikin mutunci."

Suka ci gaba da hira na

ɗ

an lokaci cikin annashuwa. Ana ta yi wa juna addu'o'in fatan alheri, kow

a na nuna farin cikinsa da wannan ha

ɗ

in zumunci.

Daga bisani Gwaggo Laraba ta miƙe tsaye.

"To, yanzu za mu koma. Baƙi suna jiranmu can."

Mimi ita ma ta miƙe, ta raka su har ƙofar falon.

"Mun gode ƙwarai da zuwanku. Allah Ya kai ku gida lafiya."

"Amin.

"

Suka yi musabaha cikin girmamawa. Mimi ta tsaya bakin ƙofa tana kallonsu har suka shiga mota suka bar harabar gidan. Ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi, tana jin wani irin nauyin amana mai da

ɗ

i ya sauka a kafa

ɗ

unta, tana kuma roƙon Allah Ya sa ta sauk

e wannan amanar yadda ya dace.

_Ma'eesha_

Jalaluddeen ya ci gaba da shafa bayanta cikin tausayawa har sai da numfashinta ya fara daidaituwa ka

ɗ

an. Ya miƙa mata kofin ruwa.

"Ki kurkura baki a hankali."

Ma'eesha ta kar

ɓ

a da hannu mai rawa. Bayan ta

kurkura bakin, ta jingina da bango tana lumshe idanu, fuskarta ta yi fari tamkar wadda aka cire wa jini.

Jalaluddeen ya durƙusa gabanta, idanunsa cike da damuwa.

"Za ki iya tashi?"

Ta

ɗ

aga masa kai da ƙyar.

"Ina jin jikina ya yi rauni..."

Ba tare da

ɓ

ata lokaci ba, ya kama hannunta cikin kulawa ya taimaka mata ta miƙe. Tana

ɗ

an karkarwa, don haka ya sa hannu ya tallafe ta har suka fito daga ban

ɗ

akin.

Da suka dawo cikin

ɗ

akin kwana, ya zaunar da ita bakin gado.

"Ki zauna nan. Kar ki yi yunƙurin tashi.

"

Ya nufi closet ya bu

ɗ

e shi. Cikin sauri ya ciro wata rigar barci mai laushi, ya dawo gabanta.

"Kina buƙatar ki canza wannan kayan."

Ma'eesha ba ta da ƙarfin magana. Ta dai kalle shi da idanunta masu nuna kasala.

Jalaluddeen ya taimaka mata cikin gir

mamawa ta sauya rigar barcin zuwa wata mai sauƙi da za ta fi mata kwanciyar hankali. Da ya tabbatar ta gama, ya

ɗ

ora mata filo a bayanta.

"Ki

ɗ

an huta..."

Bai gama rufe wardrobe ba sai ya ga ta dafe baki da hannu.

Fuskarta ta sake canza launi.

"Yaya Ja

lal..."

Ba ta gama fa

ɗ

in sunansa ba, ta miƙe da sauri.

Ya miƙe tare da ita.

"Ma'eesha!"

Ta nufi ban

ɗ

aki da sauri tana dafe bakinta.

Da ta isa, ta durƙusa gaban washbasin.

Sai wani amai mai ƙarfi ya sake tasowa.

Jalaluddeen ya tsaya a bayanta yana ri

ƙ

e da ita kada ta fa

ɗ

i.

Bayan ta gama, ya

ɗ

ebo mata ruwa ta kurkura baki.

Ya yi tunanin abin ya ƙare.

Amma kafin ta miƙe.Sai cikinta ya sake juyawa.

Ta sake durƙusawa.

Wani amai na biyu ya sake zuwa.

Numfashinta ya yi nauyi, hawaye na zuba daga gefen

idanunta saboda tsananin wahala.

Jalaluddeen ya shiga ru

ɗ

ani.

"Ya Allah..."

Ya ci gaba da shafa mata baya.Da ƙyar ta samu ta zauna a ƙasa tana jingine da bango.

Ya ce cikin sanyin murya,

"Ki huta ka

ɗ

an."

Sai ta girgiza kai.

"Har yanzu..."

Kafin ya

tambaye ta me take nufi, wani tashin zuciya ya sake rufeta.

A karo na uku ta sake yin amai.

Yanzu kam gaba

ɗ

aya ta galabaita.Jikinta ya yi sanyi, hannayenta na rawa.

Jalaluddeen ya tsugunna gabanta, ya riƙe fuskarta cikin tafukan hannayensa.

"Ma'eesha

... ki kalle ni."

Ta bu

ɗ

e idanunta a hankali.

"Ina nan..."

Ya ga yadda idanunta suka yi jajir saboda gajiya.

Ba tare da bata lokaci ba, ya

ɗ

agata cak ya fito da ita daga ban

ɗ

akin. A hankali ya kwantar da ita kan gado, ya gyara mata filo sannan ya lullu

ɓ

e ta da bargo mai laushi.

Ya sake ta

ɓ

a goshinta.

Ba ya jin zafi sosai, amma damuwarsa ta ƙaru fiye da yadda zai iya

ɓ

oyewa.a yi ta kallonta na wasu daƙiƙu.

A zuciyarsa kuwa tunani iri-iri ne suke yawo.

"Me ya jawo haka? Shin gajiyar tafiya ce? Ko wata

rashin lafiya ce? Ko kuwa..."

Bai ƙarasa tunanin ba.

Abin da ya fi muhimmanci a gare shi yanzu shi ne lafiyarta.

Ya sake bu

ɗ

e wardrobe ya ciro mata wata doguwar hijabi ya ajiye kusa da ita.

"Ki yi ƙoƙarin na sai maki wanan Za mu je asibiti yanzu."

Ta

yi masa kallon kasala kawai.

Ya taimaka mata ta shirya cikin kulawa, sannan ya tabbatar ta zauna lafiya a bakin gado.

Bayan ya ga komai ya yi, ya juya ya fita da sauri daga

ɗ

akin.

Matakansa suna amsa kuwwa a cikin falon saboda gaggawa.

Ya bu

ɗ

e ƙofar pa

rt

ɗ

insu ya nufi

ɓ

angaren baƙi inda Dady, Alhaji Babba, Hajiya Turai da sauran iyalan suke zaune suna hira.

Da suka ga shigowarsa, nan take suka fahimci wani abu ba daidai ba ne.

Dady ya miƙe tsaye.

"Jalaluddeen, lafiya kuwa?"

Alhaji Babba ya

ɗ

ora da c

ewa,

"Me ya faru?"

Fuskar Jalaluddeen cike take da tashin hankali.

Ya ce da murya mai nuna damuwa,

"Ma'eesha ba ta da lafiya. Ta yi amai sau da dama, yanzu ma ta galabaita sosai. Zan kai ta asibiti nan take."

Kafin ya rufe baki, Hajiya Turai ta miƙe d

a sauri tana dafe ƙirji.

"Innalillahi! Amai sau da dama?"

Dady ya

ɗ

auki mukullin motarsa ba tare da wata-wata ba.

"Mu tafi yanzu."

Alhaji Babba ya miƙe shima.

"Kar a

ɓ

ata ko da minti

ɗ

aya."

Matan gidan suka shiga tashin hankali.

Wasu suka fara addu'

a.

"Allah Ya ba ta lafiya."

"Ya Allah Ka sauƙaƙa."

Hajiya Turai ta riga ta nufi ƙofar.

"Ina son na ganta."

Dukansu suka bar part

ɗ

in cikin gaggawa suna bin bayan Jalaluddeen.

Da suka isa part

ɗ

insu, Jalaluddeen ya bu

ɗ

e ƙofar cikin sauri.

Kowa ya shi

ga da zuciya cike da fargaba, idanunsu na neman ganin halin da Ma'eesha take ciki, yayin da

ɗ

akin ya cika da yanayin damuwa da addu'o'in neman sauƙi daga Ubangiji.

*Maman Ihsan ce* ✍



[8/7, 9:09 PM] Antysalima Grp: 1





6





1





Kowa ya shiga da zuciya c

ike da fargaba, idanunsu na neman ganin halin da Ma'eesha ke ciki, yayin da

ɗ

akin ya cika da yanayin damuwa da addu'o'in neman sauƙi daga Ubangiji.



Alhaji babba da Daddy suka tsaya daga nan. Hajiya Turai ce ta haura sama ta bi bayan Jalaludden.

Ma'eesha

na kwance a bakin gadon ta galaibaita da amai da ta dinga kwarawa.

Hajiya Turai ta karasa gabanta tana cewa.

"Sannu Ma'eesha."

Idanunta da suka yi fari ta

ɗ

an bu

ɗ

e ta kalli Hajiya Turai da shi.

Hajiya Turai ta sunkuya kadan ta ta kai hannu kan fuskar

Ma'eesha tana bu

ɗ

e cikin idon Ma'eesha ta zuba ma ta idanu, sai kuma ta yi murmushi.

"Ma sha Allah, Alhamdulillah."

Cikin rashin fahimta Jalaludden ya cewa.

"Wani irin Alhamdulillah kuma bayan ga ta kwance cikin halin jinya."

Murmushi irin ta su ta m

anya ta yi, sannan ta ce.

"Ba za ka gane abun da nake nufi ba, amma mu je asibitin ka tabbatar da abun da nake zargi."

Hijabi ya dauko ya sakawa Ma'eesha, sanan ya

ɗ

auke ta a jikinsa suka nufi ƙofar fita,.duk yadda yake masa maganar akan ya sauke ta za t

a iya tafiya bai saurara mata ba, kai tsaye ya nufi downstairs da ita. Inda Daddy da Alhaji babba suke.

Ganin Jalaludden

ɗ

auke da Ma'eesha ya sa Daddy da Alhaji Babba hankalinsu ta tashi.

"Me ya same ta!?"

Kusan a tare suka yi tambayar.

"Amai take ta y

i za mu tafi asibiti ne."

Ya dan sunkuya kadan yana rike da ita ya

ɗ

auki key din motarsa a saman Centre table.

A tare suka fita, ya nufi

ɗ

aya daga cikin motocinsa, Daddy ya yi saurin bu

ɗ

e masa bayan motar.

Ya saka ta ciki ya zaunar da ita Hajiya Turai d

a Daddy suka saka ta a tsakiya. Jalaluddeen ya shiga mazaunin direba yayin da Alhaji babba ya shiga gefen Jalaludden, kasancewar maigadin bai yi barci ba ya wangale ma su gate tare da fatan Allah ya ba ta lafiya.

Harabar babban asibitin ta kasance cikin

nutsuwa, kasancewar dare ne ƙafa sun fara

ɗ

aukewa. Jalaluddeen ya rage gudun motarsa a hankali kafin ya yi parking a inda aka tanada domin baƙi. Ya juya bayansa yana kallon fuskar Ma'eesha, Fuskar ta nuna

ɗ

an gajiya, amma murmushinta bai gushe ba.

Alhaji

Babba ya bu

ɗ

e ƙofa ya fito cikin nutsuwa. Duk da shekarunsa, tafiyarsa cike take da karsashi. Dady ya fito daga

ɗ

aya gefen motar, yana gyara hularsa, yayin da Hajiya Turai ta fito Kowa a cikinsu yana kallon Ma'eesha cike da kulawa da tausayi.

Jalaluddeen

ya zagayo gefen motar, ya bu

ɗ

e mata ƙofa.

"Sannu a hankali."

Ya

ɗ

auke ta sai ta

ɗ

an yi lumshe ido saboda jiri ka

ɗ

an da ya ratsata.

Nan take Jalaluddeen ya sa hannu ya tallafe ta.

Ta yi murmushi.

Alhaji Babba ya kalli Dady.

"Amin," suka amsa gaba

ɗ

a

ya.

Suka nufi cikin asibitin a tare. Bayan sun shiga, aka tarbe su cikin mutunci. Jalaluddeen ya yi magana da ma'aikaciyar kar

ɓ

ar baƙi, ta duba bayanansu sannan ta ce cikin girmamawa,

"Ku zauna ka

ɗ

an, likita zai kar

ɓ

e ku."

Ba su da

ɗ

e ba aka kira sunan M

a'eesha.

Jalaluddeen ya tashi tare da ita.

Dady ya ce,

"Mu ma za mu zo."

Likitar ta yi murmushi.

"Da farko bari mu kammala binciken, idan an gama sai mu kira ku."

Ma'eesha da Jalaluddeen suka shiga

ɗ

akin gwaji. Likitar ta fara yi mata tambayoyi game

da yadda take ji.

"Kina yawan jin gajiya?"

"Eh."

"Akwai tashin zuciya da safe?"

Ma'eesha ta

ɗ

an yi murmushi sanan ta ce.

"Kusan kullum."

Jalaludden ya kalle ta jin ta ce kusan kullum, amma ba ta ta

ɓ

a yi masa magana ba, ko kuma nuna wata alamar dake n

una cewa tana jin wadan nan abubuwan. Duk da yana lura da karsashin ta ya ragu. Wato tun a can ƙasashen da suka je honeymoon take fama da lalurar ba ta fa

ɗ

a masa ba. Ga shi sai da suka yi fiye da watanni uku sanan suka dawo Nigeria.

Likitar ta sake tambay

ar ta ta ce.

"Abinci fa?"

"Wani lokaci ina jin ƙamshinsa ya dame ni."

Likitar ta rubuta komai cikin fayil

ɗ

inta.

Bayan haka aka yi mata gwaje-gwajen da suka dace. An

ɗ

auki samfurin jini, sannan aka shirya mata gwajin ciki. Bayan

ɗ

an lokaci aka kuma yi

mata binciken da ya dace domin tabbatar da lafiyar cikinta.

Jalaluddeen yana zaune kusa da ita, amma duk da natsuwarsa, zuciyarsa cike take da fargaba da kuma fata.

Bayan wasu mintuna, likitar ta dawo

ɗ

auke da sakamakon gwaje-gwajen. Ta zauna tana kallon

su da fara'a tana fa

ɗ

in.

"Alhamdulillah."

Jalaluddeen ya

ɗ

ago kai.

"Lafiya kuwa, Doctor?"

Likitar ta yi murmushi mai fa

ɗ

i, sanan ta ce.

"Komai lafiya. Kuma ina taya ku murna."

Ma'eesha ta kalli Jalaluddeen cikin mamaki.

Likitar ta ci gaba da cewa,

"An tabbatar kina

ɗ

auke da ciki, kuma cikin yana da kimanin watanni biyu."

Na

ɗ

an lokaci

ɗ

akin ya yi shiru.

Ma'eesha ta kai hannu ta rufe bakinta, idanuwanta suka cika da hawaye na farin ciki.

"Alhamdulillahi..."

Jalaluddeen kuwa kamar ya kasa magana.

Ya zuba mata ido na wasu daƙiƙu kafin murmushi mai cike da godiya ya bayyana a fuskarsa.

Ya kamo hannunta ya matse cikin tausayi.

"Mar'atussaliha..."

Hawaye suka cika idanunsa.

"Allah Ya kar

ɓ

i addu'a ta.

Ma'eesha ta sunkuyar da kai ƙasa cike da jin ku

nya

"Alhamdulillahi... Alhamdulillah."

Likitar ta ci gaba da yi musu bayanin yadda za ta kula da kanta, irin abincin da ya kamata ta riƙa ci, muhimmancin hutawa, da kuma dawowa duba lafiyarta lokaci-lokaci.

Jalaludden ya fito da kudi masu yawa ya ba wa

Likitar tukuicin albishir da ta yi masa.

Bayan sun gama, suka fito daga

ɗ

akin.

Tun daga nesa Alhaji Babba, Dady da Hajiya Turai suka miƙe tsaye, suna jiran jin sakamakon.

Da zarar Jalaluddeen ya ƙaraso, murmushin da ke fuskarsa ka

ɗ

ai ya isa ya ba su am

sa.

Alhaji Babba ya ce cikin

ɗ

oki,

"Me likita ta ce?"

Jalaluddeen ya kalli Ma'eesha, sannan ya sake kallon iyayen.

Cikin muryar da ta cika da farin ciki ya ce,

"Alhamdulillah... Allah Ya yi mana babban alheri."

Ya

ɗ

an dakata.

"Ma'eesha na da ciki...

kuma cikin yana da watanni biyu."

"Innalhamda lillah!"

Hajiya Turai ta dafe ƙirji cikin farin ciki

"Ya Allah! Kai ne Mai bayarwa. Dubi yadda Ka faranta mana zukata."

Dady ya kasa

ɓ

oye farin cikinsa. Ya rungumi Jalaluddeen da ƙarfi.

"Allah Ya saka ma

ka da alheri,

ɗ

ana."

Alhaji Babba kuwa ya

ɗ

aga hannayensa sama.

"Ya Allah, muna gode Maka. Ka tabbatar mana da wannan ni'ima. Ka ba wannan cikin lafiya, Ka sa ya zo duniya lafiya, ya zama

ɗ

a nagari mai albarka."

"Amin!" suka amsa gaba

ɗ

aya.

Hajiya Tura

i ta rungume Ma'eesha tana shafa bayanta cikin tausayawa.

"Allah Ya kiyaye ki, 'yata. Wannan rana ce da ba zan ta

ɓ

a mantawa da ita ba."

Ma'eesha ta fashe da kuka, amma kukan farin ciki ne. Ta jingina kanta a kafa

ɗ

ar Hajiya Turai, tana ta maimaita,

"Alha

mdulillah... Alhamdulillah..."

Jalaluddeen ya tsaya yana kallon wa

ɗ

anda Allah Ya ha

ɗ

a masa a wannan lokaci mai cike da albarka. Zuciyarsa ta cika da godiya ga Ubangiji. A karon farko cikin dogon lokaci, ya ji tamkar duk wahalhalun da suka sha a baya sun z

ama tarihi, yayin da sabon babi na rayuwarsu ya bu

ɗ

e—babi mai cike da fata, farin ciki, da kuma jiran zuwan ƙaramin baƙon da Allah Ya yi musu bushara da shi.

Daga nan suka nufi hanyar komawa gidan zuciyar kowanne cike da farin ciki.

_Mimi_

Mimi ta

ɗ

an ja numfashi bayan ta yi sallama da baƙin da suka cika falon gidan. Hayaniyar biki na ci gaba da tashi a waje, ana ta shewa da bushe-bushe, amma zuciyarta tana can wajen sabuwar amaryarta. Ta gyara gyalenta cikin nutsuwa sannan ta nufi

ɗ

akinta da aka kil

lace wa amarya.

Da ta bu

ɗ

e ƙofar

ɗ

akin a hankali, sai ta hangi wasu daga cikin ƙawayenta da ta bari zaune a cikin

ɗ

akin.

Sidra na zaune ta raku

ɓ

e, mayafinta Ƙamshin turare ya cika

ɗ

akin, yayin da hasken fitilu ke ƙara fito da kyawun adon da aka yi ma

sa.

Can Mimi ta hango Sidra tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login