Showing 105001 words to 108000 words out of 191594 words
zuba sosai daga bayansa.
Oga ya matsa bandeji a wurin yana cewa da ƙarfi:
“Ka ji ni? Ba ka da izinin mutuwa a nan!”
Jalaluddeen ya
ɗ
an motsa la
ɓɓ
ansa kamar yana son magana.
Oga ya matsa kunne kusa da bakinsa.
Da ƙyar aka ji kalmomi masu rauni ya ce .
“Ma’eesha…”
Sai jikinsa ya saki gaba
ɗ
aya.
Monitor
ɗ
in da aka kawo daga
motar gaggawa ya fara yin ƙara mai firgita yayin da jami’an suka yi shiru na wasu daƙiƙu.
Wani jami’i ya ce cikin murya mai rawa:
“Sir… muna rasa shi.”
Oga ya
ɗ
aga kai, idanunsa cike da tashin hankali.
“Ku motsa! Ku kai shi asibiti yanzu!”
Suka
ɗ
auke
shi da gudu zuwa motar asibiti, yayin da a wajen ma’ajiyar jami’an DSS ke kallon jinin da ya bari a ƙasa… kuma a karon farko cikin shekaru, aka fara jin tsoron cewa babban jami’in da ya tsallake hare-hare da dama… watakila wannan karon ba zai dawo ba.
*
Maman Ihsan ce*✍
🏻
[7/24, 4:17 PM] Antysalima Grp: *MAKAHO NE*
_Book 2_
Maman Ihsan ce ✍
🏻
JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
*LITTAFINA NA KUƊI NE KI BIYA NI HAKKINA KAFIN KI KARANTA MANI LITTAFI. NAIRA DUDU ƊAYA NE KACAL. ZA KI TURA MANI KUƊIN TA
WANNAN ACCOUNT NUMBER 2242538350 SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 09065327995*
Page1
️
⃣
3
️
⃣
3
️
⃣
Suka
ɗ
ake shi zuwa da gudu zuwa asibiti, yayin da a wajen ma'ajiyar jami'an DSS ke kallon jinin da ya bari a ƙasa... Kuma a karon farko cikin shekaru,
aka fara jin tsoron cewa babban jami'in da ya tsallake hare-hare da dama...watakila wanan karon ba zai dawo ba.
_Dady_
Yana zaune a falon mahaifinsa. Hajiya Turai ta saka shi gaba tana kallonsa, tana jin tausayinsa a ƙasar ranta. Ta rasa gane dalilin d
a ya da ta fita daga lamarin Ɗan nata guda
ɗ
aya da suka mallaka a duniya. Sanan ta mance da ƴarsa guda
ɗ
aya da ya mallaka a duniya . Goge hawaynta ta yi tana cewa .
"Allah ya bayyanar mana da ke Ma'eesha."
"Amin ya Allah."
Dady ya amsa da hawaye akan fu
skarsa.
"Na rasa gane dalilin da ya daka na waufantar da rayuwar ƴata
ɗ
aya tilo da nake da ita a wajan duniya. Bayan rasuwar mahaifinyarta kamata ya yi a ce ta samu kulawa daga wajana . Amma haka na dinga musguna mata ina kallon yadda amaryar da na aura t
ake wulakanta Mani yarinya a gidan inganta. Tana lalla
ɓ
a Jamil da Laila wa
ɗ
an da su agola ne ko uban su ban sani ba. Amma suka fi mai uban samun ƴanci a gidan ubanta. Ina ji ina gani ta kawo shawarar na aurar da ita ba Makaho nan, a lokacin fa Ma'eesha na
da samari da suke son ta. Amma matar nan ta hana na ba su aurenta. Akwai Abdul da wani police wanda su suna da kudi ƴaƴan manya ne. Amma Mamy ta hana ta ce dole sai wanan makohon mabaraci zan ba wa ƴata. Haka ba amince jikina na rawa na aurar da ita gare s
hi. Bayan
ɗ
aura auren na ce zan ba su gidan da za su zauna sanan na ba Ma'eesha jari ta yi sana'a amma Mamy ta hana. "
Hawaye ya goge tana tuna ranar da za makaho ya zo
ɗ
aurkarta Mamy ta saka ya ƙwace ATM card nata da gwala-gwalanta sabida ta sha wahala .
Ga shi yanzu an kasa gane inda suke.
"Allah tsare ki a duk inda kike."
"Amin ya Allah."
Suka ji mauryrsa daga baya wanda ya dade a tsaye yana sauraron duk maganganun da Ɗan su ke yi..
"Tashi mu je ba lokaci."
Dady ya mike cikin sanyin jiki. Hajiya Tu
rai ma ta saka hijabi .
"Mu je kam dole a yi a nemi maka taimaka da addu'ar warware shiri ko ka dawo hayyacinka."
Daga haka suke fita, Direban Alhaji Babba ya yi driving nasu suka bar gidan.
_Jalaluddeen_
Motar asibiti ta yi ƙarar siren tana yanka
duhun dare da gudu. A ciki, jami'an lafiya suna ta faman kokarin ceto rayuwar Jalaluddeen.
Ɗ
aya daga cikin Nurses din ya ce.
"BP yana sauka!"
Wani ya yace.
"A ƙara oxygen!"
"Ku shirya jini!"
Oga ya zauna a gefe, idanunsa sun ƙi kaucewa daga fuskar Ja
laluddeen da ta yi fari tamkar ba jini a jikinsa. Hannunsa ya matse cikin na Jalaluddeen yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa.
"Ka yi mini alkawari za ka dawo lafiya"
Ya furta a hankali.
_Deputy Detector_
A daidai wannan lokacin...
A babban ofish
in DSS.
Deputy Director ya zauna cikin kujerarsa ta alfarma yana kallon agogo. Fuskarsa ba ta nuna wata damuwa ba, sai dai wani siririn murmushi da ya
ɓ
oye da zarar aka buga ƙofar.
"Shigo."
Wani jami'i ya shigo ya yi sallama.
"Sir... mun samu rahoto."
Deputy Director ya
ɗ
aga kansa ya ce .
"Ya mutu ne?"
Jami'in ya yi shiru na
ɗ
an lokaci.
"A'a sir... amma yana cikin mawuyacin hali. An kai shi babban asibiti."
Wani
ɗ
an gajeren murmushi ya bayyana a fuskar Deputy Director.
"Da kyau."
Jami'in mai suna
Usman ya
ɗ
an daure fuska.
"Sir?"
Deputy Director ya miƙe tsaye ya nufi tagar ofishinsa yana cewa .
"Wani lokaci mutuwa ba ita ce hukunci mafi zafi ba. Wani lokaci ka bar mutum yana rayuwa tsakanin rai da mutuwa."
Jami'in mai suna Usman ya rasa abin c
ewa.
"Za ka iya tafiya."
Da Yana fita...
Deputy Director ya zaro wata ƙaramar waya daga aljihunsa. Wayar ba ta cikin tsarin aikin gwamnati, babu mai sanin yana amfani da ita.
Ya danna wata lamba.
Ba a jima ba aka
ɗ
aga.
Muryar mutum ta fito.
"An gam
a aikin?"
Deputy Director ya yi murmushi ya ce.
"Kusan haka ne ."
"DSS sun ceto shi."
"Na sani."
"To me ya sa ba ka hana su ba?"
Deputy Director ya
ɗ
an yi dariya tare da cewa
"Da na hana su, za su fara zargina. Yanzu suna ganin komai hatsari ne kaw
ai ba su san cewa shiryayyen al'amari ba ne.
Shiru ya biyo baya.
Sai muryar ta sake cewa,
"Daula ba ya son kuskure."
Deputy Director ya amsa cikin sanyi.
"Ku kwantar da hankalinku. Idan bai mutu yau ba... akwai gobe."
"Ka tabbata ba zai gano kai ba?"
Deputy Director ya juya yana kallon hoton Jalaluddeen da ke rataye a bangon ofishin ya ce .
"Shi ya fi kowa amincewa da ni. A wurinsa ni uba ne... shugaba ne... mai ba shi kariya ne."
Ya yi
ɗ
an murmushi.
"Kuma mutum ba ya zargin inuwar da yake hutawa
a ƙarƙashinta."
Muryar ta ciki waya ta ce,
"Madalla."
Wayar ta katse.
Deputy Director ya ci gaba da kallon hoton Jalaluddeen.
"Na ta
ɓ
a son ka, Jalaluddeen... saboda ƙwarewarka. Amma ka fara tona kabarin mutanen da bai kamata ka kusanta ba."
Ya bu
ɗ
e
wani sirrin drawer na teburinsa.
A ciki akwai wasu manyan fayiloli da aka rubuta DAULA a jiki.
Sai kuma wani hoto, Hoton Deputy Director tare da Khalid da wasu manyan mutane suna musabaha cikin farin ciki.
Ya shafa hoton da yatsunsa.
"Shekaru goma sha
biyar muna gina wannan daula a
ɓ
oye."
"Ba zan bari jami'i guda ya rusa mana komai ba."
Ya
ɗ
auki lighter ya kunna wuta.
Takardun binciken da Jalaluddeen ya tattara kan Daula ya jefa cikin kwandon ƙarfe.
Wutar ta fara cin takardun
ɗ
aya bayan
ɗ
aya.
"Yanz
u babu wata shaida."
Sai dai bai san cewa. A cikin aljihun rigar Jalaluddeen da ke kwance a asibiti...
Akwai wata ƙaramar na'urar adana bayanai (encrypted flash drive) da Jalaluddeen ya
ɓ
oye tun kwanaki da suka wuce.
Na'urar tana
ɗ
auke da dukkan sirrin
Daula.
Har da sunan mutumin da ke jagorantar ta.
Da kuma sunan maci amanar da ke cikin DSS.
Wanda ba kowa ba ne.
Sai Deputy Director. A karo na farko cikin shekaru masu yawa...
Asirin da ya shafe lokaci yana
ɓ
oye yana dab da fitowa fili.
Amma har yan
zu bai san cewa ko Jalaluddeen zai tsira daga wannan mummunan rauni ba.Kuma idan ya tsira. Zai dawo ne ba domin kama Khalid ka
ɗ
ai ba. Sai domin rusa Daula baki
ɗ
aya, tare da fallasa macin amanar da ya da
ɗ
e yana fakewa da kujerar Deputy Director.
*Ameri
ca/ New York City*
_Fahad_
Motar Ambassador Fahad ta shiga harabar gidan cikin nutsuwa. Tun kafin motar ta tsaya, Fahad ya fito da sauri ya zagaya ya bu
ɗ
e wa Nadra ƙofa kamar yadda ya saba, amma wannan karon kulawar da yake nuna mata ta ninka ta da.
“Ki yi a hankali,”
Ya fa
ɗ
a cikin tausasawa yana miƙa mata hannu.
“Kada ki yi saurin sauka.”
Nadra ta yi murmushi cike da kunya.
“ Yaya Fahad, lafiya ƙalau nake fa. Likita ma ta ce cikin yana farkonsa ne kawai.”
Ya girgiza kaiya ce .
“Ban damu ba. D
aga yau babu wani abu da zan bari ya gajiyar da ke.”
Ya riƙe hannunta har suka nufi cikin gidan.
A dai-dai lokacin ne Farida ta fito daga falo tana sanye da kayan gida masu kyau. Da farko murmushi ne ya bayyana a fuskarta saboda ganin Fahad ya dawo, amma
murmushin ya dusashe nan take da ta ga yadda yake riƙe da hannun Nadra cikin kulawa da ƙauna.
“Welcome back,” ta fa
ɗ
a tana ƙoƙarin
ɓ
oye abin da ke cikin zuciyarta.
“Thank you, Farida,”
Fahad ya amsa cikin fara'a.
Nadra ta yi mata murmushi.
“Aunty Fa
rida.”
“Lafiya lau.”
Idanun Farida suka sauka kan hannun Fahad da ke riƙe da na Nadra. Wani irin zafi ya ratsa zuciyarta.
'Me ya sa yake kula da ita haka?'
Ta tambayi kanta.
Ba ta gama tunanin ba sai Fahad ya juya ya kalli Nadra ya ce .
“Kin gaji?”
“Ka
ɗ
an.”
“To ki zauna.”
Bai jira amsarta ba, ya jawo mata kujera a hankali. Da ta zauna sai ya cire mata jakarta ya ajiye gefe.
Farida ta tsaya tana kallonsu kamar mutum-mutumi.
A zuciyarta kuwa tana jin kamar ana ƙara zuba mata garwashin wuta.
Tun y
aushe Fahad yake irin wannan? A gabana yake yi mata wannan kulawar?
Fahad ya nufi kitchen yana cewa.
“Me kike so ki sha? Ruwan lemu ko madara?”
Nadra ta yi murmushi.
“Ko ruwa ma ya isa.”
“A'a. Dole ki sha abin da zai ƙara miki ƙarfi.”
Ya shiga kitche
n ya fito da ruwan lemu da wasu fruits da ya saya a hanya. Ya zauna kusa da ita yana bare mata apple da kansa.
Farida ta dafe kujerar da take tsaye kusa da ita saboda baƙin cikin da ya cika zuciyarta.
Babu wanda ya kula da yanayin fuskarta.
Fahad ya
ɗ
ag
a cokali ya miƙa wa Nadra.
“Ga shi, ki ci ka
ɗ
an kin ji Nadfah.”
Nadra ta yi dariya cikin kunya.
“Ni ba ƙarama ba ce.”
“A wajen wasu ba ƙarama ba ce. Amma a wajena yanzu kina buƙatar kulawa fiye da kowa.”
Farida ta ji kalaman suna shiga kunnuwanta kama
r allura.
Ta juya gefe don kada su ga yadda idanunta suka cika da hawaye.
A wannan lokacin Fahad ya
ɗ
auki wayarsa ya kira office
ɗ
insa.
“Hello, Michael.”
“Good afternoon, sir.”
“I won't be coming to the office for the next few days. Handle every urgen
t file and send me soft copies if necessary.”
Da mamaki yake kallonsa me zai sa ya fasa zuwa aikinsa na kwanaki.
“Is everything okay, sir?”
“Yes. My wife needs me at home.”
“Congratulations, sir.”
“Thank you.”
Ya kashe wayar.
Nadra ta kalle shi ciki
n mamaki.
“ Yaya Fahad, me ya sa ka ce ba za ka je office ba?”
Ya kalleta da murmushi.
“Saboda kina buƙatar kulawata.”
“Amma ba sai haka ba. Aikinka yana da muhimmanci.”
“Aiki zai jira ni.”
“ Yaya Fahad...”
Ya katse ta.
“Babu gardama. Daga yau zan
yi aiki daga gida idan zai yiwu. Idan kuma ba zai yiwu ba zan
ɗ
auki leave. Ba zan bar ki ke ka
ɗ
ai ba, musamman yanzu da akwai ƙaramin baƙonmu.”
Ya
ɗ
ora hannunsa a hankali kan cikinta.
“My baby deserves the best care.”
Nadra ta ji hawaye sun taru a idanu
nta.
“Allah ya saka da alheri.”
“Ameen. Wannan alhakin ne na.”
Farida ta kasa jurewa.
Ta yi saurin juyawa ta nufi
ɗ
akinta ba tare da ta ce komai ba.
Tana shiga, ta rufe ƙofar da ƙarfi.
Ta jingina bayanta da ƙofar.
Hawayen da ta da
ɗ
e tana dannewa suk
a zubo.
“Me ya sa?”
ta fa
ɗ
a cikin kuka. “Me ya sa Nadra take da komai?”
Ta zauna a bakin gado tana kuka mai tsanani.
“Da ni ce... da ni ce matarsa, ni ya kamata ya riƙa kula haka.”
Ta tuna yadda tun tana Najeriya take mafarkin zama matar Fahad, amma
ƙ
addara ta kawo Nadra ta kwace komai daga hannunta.
Ta share hawaye da sauri ta
ɗ
auki wayarta ta kira mahaifiyarta.
Bayan ring biyu aka
ɗ
aga.
“Farida, ya kike?”
ta ji muryar mahaifiyarta sai kukanta ya ƙaru.
“Mama...”
“Farida! Me ya faru? Me ya sa k
ike kuka?”
“Mama... ba zan iya ba. Wallahi ba zan iya ci gaba da zama ina kallonsu ba.”
“Mene ne ya faru?”
“Mama... Nadra tana da ciki.”
Shiru ya biyo baya.
Sai mahaifiyarta ta ce,
“Innalillahi...”
“Mama, da idanunki za ki ga yadda Fahad yake kula d
a ita. Kamar babu wata mace a duniya sai ita. Ya ce ma ba zai koma office ba, zai zauna a gida saboda ita da baby. Mama, zuciyata tana ƙonewa.”
Mahaifiyarta ta yi shiru na
ɗ
an lokaci kafin ta ce cikin murya mai sanyi,
“Farida ki kwantar da hankalinki.”
“Ta yaya zan kwantar da hankali? Kowace rana ƙaunarsa gare ta tana ƙaruwa. Yanzu kuma ga ciki. Wannan jaririn zai ƙara
ɗ
aure su fiye da da.”
Mahaifiyarta ta sauke numfashi.
“Ki saurare ni sosai. Kada ki yi gaggawa. Har yanzu kina cikin gidan. Ki yi amfan
i da hankalinki, ba da fushi ba. A irin wa
ɗ
annan lokutan ne ake samun damar raba ma'aurata idan mutum ya yi dabara.”
Farida ta share hawayenta.
“Mama... kina nufin har yanzu akwai fata?”
“Matuƙar suna raye, komai yana iya faruwa. Amma ki yi hankali. Kad
a Fahad ya fahimci abin da ke zuciyarki. Ki ci gaba da nuna kamar kina son Nadra, amma ki riƙa sa ido kan komai.”
Farida ta matse wayar a hannunta.
“To Mama... zan yi yadda kika ce.”
Ta kashe wayar, ta kalli madubin
ɗ
akin.
Fuskarta ta kumbura saboda ku
ka, amma a cikin idanunta akwai wani sabon haske ba hasken farin ciki ba, sai dai hasken kishi, ƙiyayya da kuma wata niyya da ta fara bayyana a hankali.
A lokaci guda kuwa, a falo, Fahad yana zaune kusa da Nadra yana murmushi yana shafa cikinta cikin taus
asawa, ba tare da ko ka
ɗ
an ya san irin guguwar da farin cikin da ya samu ya tayar a zuciyar Farida ba.
*Maman Ihsan ce*✍
🏻
[7/25, 7:13 AM] Antysalima Grp: *MAKAHO NE*
_Book 2_
Maman Ihsan ce ✍
🏻
JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
*LITTAFINA NA KU
Ɗ
I NE KI BIYA NI HAKKINA KAFIN KI KARANTA MANI LITTAFI. NAIRA DUDU ƊAYA NE KACAL. ZA KI TURA MANI KUƊIN TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2242538350 SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 09065327995*
Page1
️
⃣
3
️
⃣
4
️
⃣
A lokacin guda kuwa a falo, Fahad yana zaune
kusa da Nadra yana murmushi yana shafa cikinta cikin tausayawa, ba tare da ko ka
ɗ
an ba ya san irin guguwar da farin cikin da ya samu ya tayar da zuciyar Farida ba.
_Jalaluddeen_
Ƙ
arar siren motar asibiti ce ka
ɗ
ai ke ratsa daren birnin yayin da take y
anke hanya cikin matsanancin gudu. Fitilunta masu walƙiya suna haskaka tituna
ɗ
aya bayan
ɗ
aya, direban na yin iya ƙoƙarinsa domin isa asibiti cikin gaggawa.
A cikin motar kuwa, yanayin ya fi na filin yaƙi tsanani.
Jalaluddeen yana kwance a kan gadon gagg
awa, jikinsa ya yi sharkaf da jini. Riga da wandon da ya sa sun tsage a wurare da dama sakamakon fa
ɗ
uwar da ya yi da kuma tarkacen ƙarfe da suka danne shi.
Numfashinsa yana fita a hankali kamar zai tsaya ko wane lokaci.
Na'urar auna bugun zuciya tana ta
fitar da sauti.
Beep... Beep... Beep...
Amma sautin yana ƙara raguwa.
Wata jami'ar lafiya ta matsa bandeji mai kauri kan gefen ƙirjinsa inda jini ke ci gaba da malalowa.
"Jinin bai tsaya ba!"
Wani ya amsa da sauri.
"BP ya sauka zuwa sittin bisa arba'
in!"
Cikin tashin hankali aka ce .
"Ka ha
ɗ
a oxygen!"
Nan take aka
ɗ
ora masa abin taimakon numfashi a hanci da baki.
Sai dai duk da haka, ƙirjinsa na
ɗ
agawa yana komawa ƙasa da wahala.
Oga yana zaune kusa da shi, fuskarsa cike da damuwa. Wannan shi ne
karon farko da ya ga Jalaluddeen cikin irin wannan hali.
Domin ya san ce cewa Jami'i Jalaluddeen bai ta
ɓ
a tsoro ba...
Jami'in da ya saba ceton rayuwar wasu...
Yanzu shi ne ke kwance tsakanin rai da mutuwa.
Oga ya riƙe hannunsa.
"Officer... ka ji ni?
"
Babu amsa.
"Jalaluddeen!"
Yatsun Jalaluddeen suka
ɗ
an motsa ka
ɗ
an.
Ya yi ƙoƙarin bu
ɗ
e idanunsa, amma nauyin ciwo ya hana shi.
Hotuna suka fara yawo cikin kwakwalwarsa.
Ya ga Ma'eesha tana murmushi.
Ya tuna ranar da ya
ɗ
aura aka
ɗ
aura masa aure da