Showing 108001 words to 111000 words out of 191594 words
/>
ita, ta
ɗ
auki nauyinsa ta siyar da wayarta ta kashe ma su kudin ta dauki dawainiyarsa tana masa kallon wanda bai da komai ba tare da ta san waye shi. Ba ta nuna masa ƙauna.
Ya tuna yadda ta rungume shi ta baya ranar da ya yi ma ta karya zai tafi garin me
duguri neman danginsa, kalamanta yake tunawa
"Kada ka tafi ka bar ni ba na son wani abu ya same ka ga shi ba ka gani ballantana ka kare kanka."
Hawayen da bai ta
ɓ
a zubowa a idonsa ba suka taru ƙarƙashin gashin idonsa.
La
ɓɓ
ansa suka motsa cikin rauni.
"Ma'eesha..."
Oga ya matsa kusa.
"Me yake cewa?"
Jami'ar lafiya ta girgiza kai tana cewa.
"Ba ya cikin cikakkiyar hayyacinsa."
Kwatsam...
Na'urar bugun zuciyar ta yi wani ƙara mai tsawo.
Beeeeeeep!
Jami'ar lafiya ta firgita ta ce .
"Ya shiga cardi
ac arrest!"
"CPR! Yanzu!"
Wani ya fa
ɗ
a a ru
ɗ
e.
Nan take aka kwantar da gadon.
Likitan gaggawa ya fara danna ƙirjinsa da ƙarfi.
"One!"
"Two!"
"Three!"
Wani ya ha
ɗ
a defibrillator.
"An shirya."
"Clear!"
Paaah!
Jikin Jalaluddeen ya
ɗ
aga sama sakama
kon lantarkin.
Na'urar ta sake dubawa.
Shiru.
"Har yanzu babu."
Likitan ya sake danna ƙirjinsa.
"Kar mu tsaya!"
Oga ya juya gefe, idanunsa suka cika da hawaye.
Ya da
ɗ
e yana aiki da Jalaluddeen.
Ya san shi a matsayin jajirtaccen jami'i mai biyayya.
Ba zai iya kallon yadda yake mutuwa ba.
Likitan ya sake
ɗ
aukar na'urar.
"200 joules!"
"Clear!"
Paaah!
Jikin Jalaluddeen ya sake girgiza.
Daƙiƙu biyu...
Uku...
Sai na'urar ta fara fitar da sauti.
Beep... Beep... Beep...
Jami'ar lafiya ta saki aji
yar zuciya.
"Mun dawo da pulse!"
Oga ya runtse idanunsa yana gode wa Allah.
"Alhamdulillah..."
Amma likitan bai yi farin ciki ba.
Ya dubi sakamakon na'urar.
"Har yanzu yana cikin ha
ɗ
ari."
"Mun yi asarar jini mai yawa."
"Cikin jikinsa ma akwai yiwuw
ar zubar jini."
A wannan lokacin motar ta tsaya da ƙarfi.
"Asibiti!"
Ƙ
ofofin motar suka bu
ɗ
e.
Tuni wasu likitoci da nas-nas suka fito da gadon
ɗ
aukar marasa lafiya.
"Ku yi sauri!"
A guje aka fito da Jalaluddeen.
Ana tura shi cikin doguwar hanyar Eme
rgency Department.
Ma'aikatan asibiti suna ba da hanya ana cewa
"Emergency!"
Wasu na cewa .
"Ku matsa!"
"Critical patient!"
Likitocin tiyata suna jiran isowarsa.
Da suka ga yadda jikinsa ya lalace,
ɗ
aya daga cikinsu ya girgiza kai.
"Wannan ya yi m
uni sosai."
"Harbi guda
ɗ
aya ba ne."
"Akwai mummunan rauni daga bugun ƙarfe."
"Da alama ƙasusuwansa ma sun sami matsala."
Suka shiga dakin gaggawa.
Nan take aka fara cire rigarsa da ta jika da jini.
Kowa da ya ga raunukan jikinsa sai da ya yi shiru.
A gefen ƙirjinsa akwai ramin harsashi.
Bayansa kuwa ya kumbura saboda bugun babban ƙarfen da ya fa
ɗ
o a kansa.
Likitan ya
ɗ
aga kansa ya ce .
"Ku kira shugaban sashen tiyata."
"Yanzu!"
"Wannan mara lafiya ba zai rayu ba idan ba a shiga da shi dakin tiy
ata cikin mintuna ka
ɗ
an ba."
A waje kuwa...
Oga ya tsaya gaban ƙofar dakin gaggawa, hannayensa cike da jinin Jalaluddeen.
Ya zura ido cikin jajayen tafin hannunsa.
A karon farko cikin shekarun aikinsa.
Ya ji tsoro.
Tsoron rasa jami'in da ya fi kowa ƙw
arewa.
Tsoron yadda zai sanar da iyalansa idan aka kasa ceton rayuwarsa.
Ya
ɗ
aga kansa zuwa sama ya furta cikin raunin murya,
"Ya Allah... kada ka
ɗ
auke shi yanzu."
"Kare mini Jalaluddeen..."
_Laila_
Laila ta da
ɗ
e tsaye a gefen titi tana kallon
hanyar da motar Taj ta bi har ta
ɓ
ace gaba
ɗ
aya. Sai da ta tabbata ba zai dawo ba sannan ta share hawayenta, ta shiga motarta ta kunna.
Hanyar komawarta gida ta kasance cike da shiru. Ko rediyon motar ba ta kunna ba. Zuciyarta cike take da fargaba da kuma
wani
ɗ
an ƙaramin fata cewa watakila Taj zai cika alƙawarinsa, ya dawo mata da dukiyar domin ta mayar wa Mamy.
"Ya Allah... kada ka bari na ƙara lalata komai..." ta furta cikin raunin murya.
Da ta isa gida, ta yi parking a hankali sannan ta fito. Gidan y
a yi tsit kamar ba a ciki. Ta shiga kai tsaye
ɗ
akinta, ta zauna bakin gado tana riƙe wayarta.
Mintuna suka ja zuwa rabin sa'a...
Rabin sa'a ya zama awa
ɗ
aya...
Har yanzu babu Taj.
Kowane motsin mota da take ji daga waje sai zuciyarta ta buga da sauri,
tana tsammanin shi ne ya dawo. Amma duk lokacin da ta leƙa ta taga, ba shi ba ne.
Ta sake duba wayarta.
Shiru.
Ta danna lambarsa.Wayar ta shiga.
Da sauri ta
ɗ
aga wayar kunne.
"Taj... ina kake? Don Allah ka zo mana. Ka kawo mini kayan nan. Ina so in ma
yar wa Mamy kafin komai ya lalace."
Sai ta ji wata irin dariya daga can
ɗ
ayan
ɓ
angaren.
Dariyar da ba ta ta
ɓ
a jin irinta daga bakinsa ba.
"Laila."
ya kira sunanta cikin sanyin murya. "Har yanzu kina tunanin zan dawo?"
Gabanta ya fa
ɗ
i.
"Me... me kake
nufi?"
Ya yi wata doguwar dariya.
"Gaskiya ban zata kina da sauƙin yaudaruwa haka ba."
Hannun Laila ya fara rawa.
"Taj... me kake fa
ɗ
a?"
"Abin da nake fa
ɗ
a kenan. Ni ban ta
ɓ
a son ki ba."
Wayar ta kusa zamewa daga hannunta.
"Ka... ka ce me?"
"Na ce
ban ta
ɓ
a son ki ba. Ballantana har in aure ki."
Idanunta suka cika da hawaye.
"A'a... ƙarya kake! Ka ce kana sona. Ka ce za mu yi aure. Ka ce za mu fara sabuwar rayuwa a ƙasar waje."
Ya yi murmushi mai cike da raini.
"Duk wasan kwaikwayo ne."
Laila t
a kasa numfashi yadda ya kamata.
"Wane wasa?"
"Aiki aka ba ni a kanki uban gidana Jalaluddeen ya bani akanki, amma ba ki san waye Jalaluddeen ba kasancewar ba da wanan sunan kika san shi ba.
Kamar an buga mata guduma a kai.
"A... aiki?"
"Eh. Aka ba ni
aikin in sa ki kwashe dukiyar gidan. Shi ke nan. Aikin ya ƙare."
Laila ta saki wani irin ihu.
"Kai maƙaryaci! Kai azzalumi! Ka yaudare ni!"
Ya yi wata ƙaramar dariya.
"Kin taimaka mana sosai. Gaskiya kin fi yadda muka zata."
"Taj! Ka dawo mini da duk
iyar nan! Don Allah!"
"Me zai sa?"
"Halin da Mamy take ciki zai kashe ta."
"Bai dame ni ba ai dama ta cancanci mutuwa ."
Laila ta durƙushe a ƙasa tana kuka.
"Don Allah... na roƙe ka..."
Ya katse ta ta hanyar cewa
"Ki koma rayuwarki ta baya. Rayuwar
talaucin da kika fito. Ni kuma zan ci gaba da rayuwata."
"Taj!"
"Sai an jima."
Ya kashe wayar.
"Lafiya lau..."
Laila ta sake kiran lambar.
An kashe waya.
Ta sake kira.
Har yanzu a kashe.
"A'a! A'a! Taj!"
Ta jefa wayar kan gado, ta kama kanta da
hannaye biyu tana ihu.
"Ka cuce ni! Ka lalata rayuwata! Ka yaudare ni!"
Kukanta ya mamaye
ɗ
akin.
"Na shiga uku! Na shiga uku!"
A wannan lokacin ne ƙofar
ɗ
akin ta bu
ɗ
e da sauri.
Mamy ta shigo da sauri, fuskarta cike da damuwa.
"Laila!"
Ta ƙaraso kusa
da ita.
"Me ya faru? Me yake faruwa?"
Laila ta
ɗ
ago kanta, idanunta sun kumbura saboda kuka.
"Mamy..."
Ta fa
ɗ
a tana jan numfashi sanan ta ce .
"Na shiga uku..."
Mamy ta riƙe kafa
ɗ
unta.
"Fa
ɗ
a mini me ya faru."
Laila ta fashe da wani sabon kuka.
"M
utumin da na ce zan gudu da shi..."
Mamy ta zuba mata ido.
"Me ya yi?"
"Ya yaudare ni."
Gabanta ya buga da sauri
"Wane irin yaudara?"
Laila ta share hawaye tana cewa.
"Shi bai ta
ɓ
a sona ba."
Mamy ta tsaya cak.
"Me kika ce?"
"Aiki aka ba shi a kai
na. Ya sa na kwashe dukiyar gidan... ya kar
ɓ
a... yanzu ya gudu da komai."
Idanun Mamy suka ƙara bu
ɗ
ewa.
"Ya gudu... da dukiyar?"
Laila ta girgiza kai tana kuka.
"Ya ce ban ta
ɓ
a zama masoyiyarsa ba. Ya ce aikin da aka ba shi ya ƙare. Ya ce in koma rayuw
ata ta talauci."
Mamy ta dafe ƙirjinta.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un..."
Numfashinta ya fara
ɗ
aukewa.
"Laila... kin ce... dukiyar ta tafi?"
Laila ta durƙusa gabanta.
"Ki yi haƙuri Mamy... ban san haka zai yi ba..."
Mamy ta ja da baya mataki
ɗ
aya.
Sai wani.
Hannunta ya ci gaba da riƙe ƙirjinta.
Fuskarta ta sauya kala.
"Laila..."
Ta kira sunanta da ƙyar.
"Kina nufin... babu komai ya rage?"
Laila ta girgiza kai cikin kuka.
"Babu..."
A take idanun Mamy suka juye.
Jikinta ya yi sanyi.
Ta
yanke jiki gaba
ɗ
aya ta fa
ɗ
i warwas a tsakiyar
ɗ
akin.
"Mamyyy!"
Laila ta saki wani irin ƙara mai firgita zuciya, ta ruga ta rungume ta.
"Mamy! Ki bu
ɗ
e ido! Don Allah ki bu
ɗ
e ido!"
Amma Mamy ba ta motsa ba.
*Maman Ihsan ce*✍
🏻
09065327995
[7/25, 7
:08 PM] Antysalima Grp: *MAKAHO NE*
_Book 2_
Maman Ihsan ce ✍
🏻
JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
*LITTAFINA NA KUƊI NE KI BIYA NI HAKKINA KAFIN KI KARANTA MANI LITTAFI. NAIRA DUDU ƊAYA NE KACAL. ZA KI TURA MANI KUƊIN TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 22425
38350 SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 09065327995*
Page1
️
⃣
3
️
⃣
5
️
⃣
Mamy! Ki bude ido! Don Allah ki bude ido.!"
Amma Mamy ba ta motsa ba.
_Daday_
Kamar yadda Alhaji Babba ya yanke shawarar cewa su je wajen wani malamin addini da aka sa
n yana yin ruƙyar shari'a da nasiha bisa Alƙur'ani da Sunnah.
Bayan tafiya mai nisa suka isa gidan Malamin.
Gidan yana cikin nutsuwa. Ana jin sautin karatun Alƙur'ani daga
ɗ
aki na ciki, abin da ya sa zukatansu suka fara samun kwanciyar hankali.
Suka yi s
allama.
"Assalamu alaikum."
"Wa alaikumus salam wa rahmatullah."
Wani almajiri ya tarbe su cikin mutunci, ya nuna musu inda za su zauna.
Ba da jimawa ba sai Mallamin ya fito. Dattijo ne mai annurin fuska, gemunsa ya yi furfura, hannunsa riƙe da tasbaha.
Ya zauna yana kallonsu ya ce.
"Bismillah. Me Allah Ya kawo ku?"
Alhaji Babba ya gyara zamansa.
"Mallam, na zo ne tare da
ɗ
ana da kuma mahaifiyarsa. Mun zo ne domin neman taimakon addu'a da ruƙyar shari'a. Mun ga abubuwa sun canza a rayuwarsu, kuma muna
son mu nemi taimako daga Allah."
Mallamin ya gyada kai ya ce .
"Madalla. Abu na farko, ku sani cewa komai yana hannun Allah. Mu ba ma tabbatar da cewa wani abu na musamman ne ya faru sai da hujja. Amma Musulunci ya koyar da mu yin ruƙya da addu'a domin
neman kariya da waraka."
Dukansu suka ce,
"Hakane, Mallam."
Ya dubi Dady.
"Ɗana, kana kiyaye sallolinka?"
Dady ya sunkuyar da kai sanan ya ce .
"Ina yi... amma wani lokaci ina samun sakaci."
"Karatun Alƙur'ani fa?"
Nan ma ya ce.
"Ba kullum ba."
M
allamin ya ce cikin taushin murya,
"To, daga yau ka fara kusantar Allah. Shi ne mafita ga kowace irin matsala."
Sannan ya dubi Hajiya Turai ya ce.
"Ke kuma Hajiya?"
Ta share hawaye tana cewa.
"Wallahi Mallam, abin da nake so shi ne Allah Ya gyara mana
al'amari."
"In shaa Allah."
Mallamin ya umurce su su zauna cikin natsuwa.
Ya fara karanta Ayatul Kursiyyu, Suratul Fatiha, Suratul Ikhlas, Suratul Falaq da Suratun Nas, tare da wasu ayoyi da addu'o'in ruƙyar da suka tabbata daga Sunnah. Muryarsa tana c
ike da nutsuwa, yayin da Dady da Hajiya Turai suka rufe idanu suna sauraro.
Bayan ya gama karatun, ya yi musu doguwar addu'a ya ce.
"Ya Allah, Kai ne Mai warkarwa. Idan akwai wata cuta, Ka ba da lafiya. Idan akwai hassada ko wani sharri, Ka kare su. Ka s
hiryar da zukatansu, Ka ƙarfafa imaninsu, Ka sanya zaman lafiya da albarka a gidansu."
"Amin."
Dukansu suka amsa cikin sanyin murya.
Sai Mallamin ya kawo wasu kwalaben ruwa da aka yi wa ruƙyar shari'a da karatun Alƙur'ani.
Ya ce,
"Wannan ruwa ne da aka k
aranta masa Alƙur'ani. Ku riƙa sha da niyyar neman waraka daga Allah, domin Allah ne ka
ɗ
ai Mai warkarwa."
Sannan ya ba Alhaji Babba wani takarda.
"A nan akwai ayoyi da addu'o'in safe da yamma. Ku riƙa karantawa kullum. Ku kuma yawaita karanta Suratul Baq
arah a gida, saboda tana daga cikin abubuwan da Sunnah ta ƙarfafa."
Alhaji Babba ya kar
ɓ
a cikin girmamawa.
"Nagode ƙwarai, Mallam."
Mallamin ya ƙara da cewa,
"Kada ku dogara ga wani abu face Allah. Ku dage da sallah, istigfari, zikiri da addu'a. Idan k
uka yi haka, Allah zai sanya alheri."
Hajiya Turai ta share hawayenta tana cewa .
"Allah Ya saka da alheri."
Ya miƙawa Dady wani ruwan addu'a ya ce ya yi Bismillah ya sha .
Ya karba ya yi Bismillah ya sha.
Sai kuwa ya ji zuciyarsa ta yi wani irin sany
i. Karon farko cikin kwanaki da dama ya ji kamar an sauke masa wani nauyi daga ƙirjinsa.
Alhaji Babba ya miƙe tsaye.
"Mu tafi, in shaa Allah za mu yi aiki da duk abin da ka yi mana nasiha a kai."
Mallamin ya yi murmushi.
Yayin da Alhaji Babba ya
ɗ
auko k
udi ya ajiye a gaban Malam na sadaka.
Mallam ya ce .
"Allah Ya tsare ku a hanya, Ya gyara al'amuranku, Ya sanya albarka a cikin gidanku."
"Amin."
Suka fita daga gidan cikin kwanciyar hankali, kowannensu na
ɗ
auke da sabon fata cewa, da izinin Allah, al'
amuransu za su gyaru, kuma rahamar Allah za ta mamaye rayuwarsu.
_Laila_
Laila ta ci gaba da girgiza jikin Mamy, hannayenta na rawa, zuciyarta na bugawa kamar za ta fito.
“Mamy... Mamy ki bu
ɗ
e ido! Don Allah ki tashi!”
Amma babu amsa.
Fuskar Mamy t
a fara sauya launi. Numfashinta ya fara fita a hankali kamar mai wahala. Hannunta da ya dafe ƙirjinta ya saki ya fa
ɗ
i ƙasa babu ƙarfi.
Laila ta saki wani irin ihu da ya amsa kuwwa a cikin gidan tana kiran Yayanta.
“Jamil! Jamil!! Don Allah ka zo! Mamy za
ta mutu!”
Muryarta ta cika da firgici da nadama.
Ba a jima ba aka ji ƙarar takun gudu daga saman bene.
Jamil ya fito a guje, fuskarsa cike da damuwa.
“Laila! Me ya faru?”
Da isowarsa ya tarar da Mamy kwance a ƙasa babu motsi, Laila na rungume da ita t
ana kuka mai ban tausayi.
“Mamy! Ki yi magana mana!”
Jamil ya durƙusa cikin sauri, ya
ɗ
ora hannunsa kan wuyan Mamy yana duba numfashinta ya ce.
“Laila, me ya same ta?”
Laila ta kasa magana saboda tsananin kuka.
“Ni... ni ce... laifina ne...”
“Ki fa
ɗ
a
mini me ya faru!”
Cikin rawar murya ta ce .
“Kawai... ta fa
ɗ
i...”
Jamil bai ƙara bata lokaci ba. Ya zura hannu ƙarƙashin bayan Mamy,
ɗ
aya hannun kuma ƙarƙashin ƙafafunta ya
ɗ
auke ta cikin gaggawa.
“Matsa hanya!”
Laila ta yi baya cikin kuka.
Jamil ya
nufi
ɗ
akin Mamy da sauri, ya kwantar da ita a kan gadonta cikin kulawa.
Da zarar ya aje ta sai ya lura da wani abu da ya sa gabansa ya fa
ɗ
i .
“Mamy...”
Ya kira cikin razana.
Gefen bakinta na hagu ya karkace ƙasa.
Wani farin yawu mai kauri yana ta fita da
ga gefen bakinta ba tare da ta sani ba.
Wuyanta ma ya karkace gefe
ɗ
aya.
Idonta
ɗ
aya a bu
ɗ
e yake ka
ɗ
an,
ɗ
ayan kuma kamar ya kasa motsi.
Jamil ya ji jikinsa ya yi sanyi.
“Laila...”
Ya kira da murya mai rawa.
“Zo ki duba nan.”
Laila ta matso tana share h
awaye.
Da ta ga yadda bakin Mamy ya karkace da yawan yawun da ke fita, sai ta saki ihu.
“Wayyo Allahna!”
Ta dafe baki da hannu.
“Mamy! Me ya same ki?”
Ta durƙusa gefen gadon tana share mata yawu da mayafi cikin rawar jiki.
“Mamy... ki yi magana mana...”
Amma Mamy na ƙoƙarin magana, harshenta ya yi nauyi.
“Lai...”
Kalmar ta tsaya a bakinta.
Ba ta iya ƙarasa ba.
Hannunta na dama ya yi wani irin karkarwa, amma hannun hagu ya yi laushi tamkar ba nata ba.
Jamil ya fahimci al'amarin ya fi ƙarfin zaman gida
.
Ya zaro wayarsa cikin sauri yana neman lambar motar asibiti, amma saboda tashin hankali yatsunsa na rawa.
“Laila! Ki kawo min mukullin mota yanzu!”
Laila ta miƙe a firgice ta je ta dauko ma sa ta dawo.
“Ga shi... ga shi...”
Ta miƙa masa mukullin tana
kuka.
“Mamy za ta mutu ne?”
“Kada ki fa
ɗ
i haka!”
Jamil ya katse ta da ƙarfi, duk da shi kansa zuciyarsa cike take da tsoro.
“Ki taimaka mini mu kai ta mota cikin gaggawa.”
Ya sake
ɗ
aukar Mamy a hannunsa.
Jikinta ya yi laushi gaba
ɗ
aya.
Yayin da yake f
ita da ita daga
ɗ
akin, yawan yawun da ke fita daga bakinta yana ƙara yawa, kanta kuma a karkace yake kan kafa
ɗ
arsa.
Laila ta bi bayansa tana kuka tana maimaita kalmomi cikin nadama.
“Ni na kashe Mamy... ni na jawo wannan...”
“Ya Allah ka ceci Mamy... don
Allah ka ceci Mamy...”
Gidan ya cika da tashin hankali. Babu wanda yake iya cewa komai.
A wannan lokaci kuwa, Jamil ya fito da Mamy zuwa harabar gidan cikin gaggawa, ya bu
ɗ
e ƙofar bayan mota ya kwantar da ita a hankali, yayin da Laila ta shiga gefe tana ri
ƙ
e da hannun Mamy tana kuka ba kakkautawa.
Motar ta yi ƙarar tashi da