Showing 141001 words to 144000 words out of 191594 words

Chapter 48 - MAKAHO NE COMPLETE

/>
"Majiyarmu ta tabbatar cewa wannan aiki ya samu nasara ne sakamakon wani dogon shiri na sirri da ya

ɗ

auki shekaru ana gudanarwa."

Sai ga hoton Jalaludd

een cikin kayan DSS.

Ya fito tsaye cikin cikakken kayan aiki.

Hannunsa riƙe da hular bulletproof.Idanunsa cike da nutsuwa. A ƙasa aka rubuta:

"Chief Superintendent Jalaluddeen..."

Mai gabatar da labarai ya yi murmushi.

"Shi ne jami'in da ya jagoranci wa

nnan aiki mai tarihi."

Fuskar Jalaluddeen ta bayyana.Mutane a gidaje dakasuwanni suka fara magana.

"Wannan ne?"

"Subhanallah!"

"Allah Sarki..."

"Wannan saurayin ne ya yi wannan aiki?"

"Wai shi ka

ɗ

ai ya shafe shekaru yana bibiyar Daula?"

A wani tasha

r...

An gayyato wani masani kan harkokin tsaro.

Ya gyara zamansa.

Ya ce,

"Wannan ba aikin mutum

ɗ

aya na yini guda ba ne."

"An shirya shi tsawon lokaci."

"Kuma wanda ya jagorance shi ya nuna irin ƙwarewar da ba kasafai ake samu ba.idan ba don wannan dabar

ar ba, da Daula ya sake ku

ɓ

uta."

A rediyo kuwa...

Masu sauraro suna ta kira.

"Wannan jami'in ya cancanci lambar yabo."

"Wannan jarumi ne."

"Allah ya kare shi."

"Wannan aiki ya ceci rayuka masu yawa."

Jaridun safiya ma ba su da wani babban labari sai

wannan. Babban kanun labarai.

"JARUMIN DA YA RUSHE DAULAR DAULA."

Wata jarida ta rubuta:

"Mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa domin ƙasa."

A shafukan sada zumunta kuwa...

Hoton Jalaluddeen ya mamaye ko'ina.

Ana rubuta:

"National Hero."

"Allah ya saka ma

sa."

"Nagartaccen jami'i."

"Najeriya ba za ta manta da shi ba."

A lokaci guda...

Babban asibitin da Mamy take kwance...

Ɗ

akin ya yi shiru.

Na'urar oxygen tana aiki cikin sannu.

Laila tana zaune a kusa da gadon.

Nurse ta shigo ta kunna talabijin domin Ma

my ta rage tunani.

Daidai lokacin aka sake fara labarin.

"...Jagoran wannan samame shi ne Chief Superintendent Jalaluddeen..."

Sai fuskar Jalaluddeen ta cika allon talabijin.

Mamy ta juya idanunta a hankali.

Da farko Ba ta gane ba.

Sai ta ƙara matsowa g

aba.

Idanunta suka zaro ƙwarai.

Numfashinta ya tsaya na

ɗ

an lokaci.

"A'a..."

Ta fa

ɗ

a a hankali sakamakon maganarta ba ta fita a hankali

"A'a..."

Ta ƙara matsowa.

Hoton ya sake bayyana.

Wannan karon yana sanye da kayan DSS.

A bayansa motocin runduna.

A

gabansa kuma Daula cikin ankwa.

Hannun Mamy ya fara rawa.

"Wannan..."

"Wannan ai..."

"Khalifa.. Makaho ne."

Ta fa

ɗ

a da ƙyar.

"Makaho..."

Hawaye suka fara cika idanunta.

Kai ta girgiza kai .

"A'a. Ba zai yiwu ba."

Sai mai gabatar da labarai ya ce,

"Maj

iyoyi sun bayyana cewa jami'in ya shafe shekaru yana gudanar da aikin sirri, inda ya sauya kamanni da rayuwarsa domin kutsawa cikin cibiyar masu laifi ba tare da sun gano shi ba."

Mamy ta zaro ido ta ce .

"Wai ba Makahon..."

"Ashe ba makaho ba ne?"

"Ashe

wasan kwaikwayo yake yi?"

Ta tuna...

Ranar da Jalaluddeen ya zo gidansu.

Yadda yake tafiya da sanda.

Yadda yake yin kamar bai gani ba.

Yadda ta raina shi.Yadda ta ce,

"Talaka ne..."

"Makaho ne..."

"Shi ya dace da Ma'eesha."

Ta tuna yadda ta matsa wa Dady

.

"Ka aura wa Ma'eesha wannan makahon."

Ta tuna ranar da aka daure auren ya ce bai da kudi dubu uku ya bayar kudin sadakin Ma'eesha, tana jin dadi za su sha wahala ashe wasan kwaikwayo yake yi ba ta sani ba ashe babban nutum da wanda yake da

ɗ

auka. Lallai



ɗ

an Hakim da ka raina.

Kalaman nata suka dawo suna dukan zuciyarta kamar guduma.

Ta rufe fuskarta da hannaye.

"Innalillahi. Me na aikata?"

Tana maganar zuci tana hawaye

Lailai ta zubawa TV idanun cike da mamaki kamar idanunta za su fito ta ce.

"Ya A

llah..."

Ta ce cikin mamaki.

"Wannan ai Khalifa ne."

"Makahon nan Mijin Ma'eesha? Dama jami'in DSS ne? Dama duk wannan wasan kwaikwayo yake yi?"

Ta ci gaba da kallon TV tana girgiza kai.

"Ashe shi ya ceci ƙasa baki

ɗ

aya?"

"Ashe shi ne jarumin da ake m

agana?"

Mamy ta fas She da kuka. Tana magana a zuciya .

'Na raina mutumin kirki. Naraina jarumi.Na raina wanda Allah ya

ɗ

aukaka.

Na kuma zalunci Ma'eesha.'

Ta rufe idanunta.

Kowace magana da ta ta

ɓ

a yi wa Ma'eesha tana dawowa cikin kunnuwanta.

Makaho ne

.Talaka ne Ba zai kai komai ba.

Ta tuna ranar da aka kira shi ya zo ya dauki matarsa. Ma'eesha ba ta fita da komai ba sai kayan sawar ta. Hatta ATM carda fa Gwala-gwalai ba abun da ta bar Ma'eeha ga fita da shi dai akwatin kayanta. Saboda ta sha wahala tu

n da mijin bai da komai ashe ba naka ba ne.

Yanzu kuwa...

Duk Najeriya ce take yabonsa.A wannan lokacin...

Ƙ

ofar

ɗ

akin aka bu

ɗ

e.

Jamil ya shigo.

Fuskarsa cike take da damuwa saboda halin Mamy.Da ya shigo...

Sai ya ga dukansu sunakallon talabijin.

Ya

ɗ

a

ga kansa.

Fuskarsa ta sauya.

Yana ganim Jalaluddeen a allon TV yana tsaye cikin kayan DSS, yana kar

ɓ

ar gaisuwar manyan jami'ai bayan nasarar aikin...

Sai murmushi ya bayyana a fuskarsa.

Murmushin farin ciki.Ya sauke numfashi ya ce.

"Alhamdulillah..."

Ya furta a hankali.

"Ko ba komai Ma'eesha tana hannun mutumin kirki ana tare da jarumi.Tana tare da mutumin da ya san darajar rayuwa."

Ya sake kallon talabijin.

A zuciyarsa ya ce,

'Allah na gode Maka... Ka ba Ma'eesha mijin da ya fi duk abin da muka ta

ɓ

a zato.

Sai ya juya ya kalli Mamy.

Ta rushe gaba

ɗ

aya.

Hawayenta ba sa tsayawa.

Ba ta ƙara kallon kowa ba.

Domin a wannan lokacin ta fahimci gaskiya

ɗ

aya..Ita da ta ta

ɓ

a kallon Jalaluddeen a matsayin makaho talaka da bai isa komai ba, yau shi ne jarumin da

ƙasa baki

ɗ

aya ke

ɗ

aukaka, yayin da ita kuma take kwance a gadon asibiti cikin ƙunci, har ta kai ga rashin ikon biyan cikakken ku

ɗ

in maganinta.

Wannan rana ta zama rana mafi zafi a rayuwarta.

Ba don ciwon jikinta ka

ɗ

ai ba.bSai don azabar nadamar da ta far

a cin zuciyarta a hankali.

[8/3, 1:16 PM] Antysalima Grp: *MAKAHO NE*

_Book 2_

Maman Ihsan ce✍



JAJIRTSTTU WRITERS ASSOCIATION

*LITTAFINA NA KUƊI NE KI BIYA NI HAKKINA KAFIN KI KARANTA MANI LITTAFI.NAIRA DUBU ƊAYA NE KACAL. ZA KI TURO MANI KUƊ

INNTA WANAM ACCOUNT NUMBER 2242538358 SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA WANAN LAMBAR. 09065327995.*

Page1





5





0





Domin a wanan lokacin ta fahimci gaskiya

ɗ

aya... Ita ta ta

ɓ

a kallon Jalaluddeen matsayin makaho talaka da bai isa komai ba. Yau shi ne jarumim

da kasa baki daya ke daukaka. Yayin da ita kuma tane kwance a gadon asibiti cikin ƙunci.har ya kai ga rashin ikon biyan cikakken kudin maganinta. Wannan rana ta zama rana mafi zafi a rayuwarta . Ba don ciwon jikinta kadai ba sai don azabar nadamar da ta

fara cin zuciyarta a hankali.

_Sidara_

Tana zaune hannunta riƙe da wani littafi amma ko shafi

ɗ

aya ba ta karanta ba. Tunaninta yana wani waje dabam. Tun da sassafe ta lura gidan ya sauya. Ana ta kai da kawo kamar ana shirin wani babban biki.

Ƙ

amshin

miya da soyayyen nama na ratsawa har cikin

ɗ

akinta. Hayaniyar mata na tashi daga kitchen da falo. Ana dariya, ana hira, ana kiran sunaye.

Ta

ɗ

an tashi ta bu

ɗ

e ƙofar

ɗ

akin ka

ɗ

an.

Sai ta hangi Gwaggo Laraba tana shiga kitchen

ɗ

auke da babban tray, yayin da

Gwaggo Maimuna ke tsaye tana duba yadda ake shirya snacks.

Sidra ta daure fuska tana tambayar kanta

"Me yake faruwa ne?"

Ta tambayi kanta a hankali.

Amma ba ta fita ta tambayi kowa ba.

Ta rufe ƙofar

ɗ

akinta ta koma ta zauna.

A hankali ta jingina da ba

ngo tana sauraren hayaniyar da ke fita daga waje.

Zuwa can ta ji ana cewa

"A kawo fulawar nan!" Kar a manta spring roll

ɗ

in."

"Kai wannan meat pie

ɗ

in ya yi kyau."

"...A zuba lemun roba cikin fridge."

Ta ci gaba da jin komai, amma babu wanda ya shig

o ya gaya mata abin da ke faruwa.

Ta yi ƙoƙarin kawar da damuwa daga zuciyarta amma ta kasa.

"Ko wani biki ne kawai...

Ta fa

ɗ

a wa kanta.

Sai dai zuciyarta ta kasa yarda.

Lokaci na ci gaba da wucewa.

Ana ta girke-girke.

Ana ta

ɗ

ora tukwane.

Ana ta kawo

kayan abinci.

Har aka gama komai.

Ita kuwa tana cikin

ɗ

aki kamar baƙuwa a gidansu.

Babu wanda ya kira sunanta.

Babu wanda ya nemi taimakonta.

Abin ya ƙara saka ta cikin mamaki.

Can wajen la'asar...

Sai ta ji ƙarar motoci guda biyu suna shigowa harabar gid

an.

Ta

ɗ

an miƙe Ta matsa kusa da window.

Ta

ɗ

an yaye labulen a hankali.

Abin da ta gani ya sa idanunta suka zazzaro.

Mata ne masu shiga irin na manyan gida da an gan su an san Naira ta zauna a jikinsu.

suka fito daga cikin motocin.kowacce na sanye cik

in shiga mai kyau da tsada.

Wasu kuma maza ne suke bu

ɗ

e boot

ɗ

in motocin.

Nan take aka fara sauke manyan akwatuna guda biyu.

Seti biyu ne masu matuƙar kyau wato dozin guda. masu sheƙi.masu tsada.

An

ɗ

aure su da manyan ribbon masu launi.

Ana sauke su cikin

kulawa tamkar wani abu mai matuƙar daraja.

Sai kuma wasu manyan kwanduna.

Da cartons.

Da wasu jakunkuna na alfarma.

Sidra ta dafe labulen window da ƙarfi tana tambayar kanta.

"Mene ne wannan?"

Ta furta cikin raunin murya.

Ba ta san me ake kawowa ba.

Ba ta san wa aka kawo ba.

Ba ta san dalili ba.

Zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi.

Ta tana da kallon yadda ake shigar da komai cikin falo.

A wannan lokacin...

Sai ta fara jin ana taya murna.

"Waiii!"

"Masha Allah!"

"Allah Ya sanya alkhairi!"

"Allah Ya ba d

a zaman lafiya."

Nan take wata irin faduwar gaba ta sauko mata.

Numfashinta ya fara yin nauyi.

Hannayenta suka soma rawa.

Ta ci gaba da sauraro.

Sai muryar Gwaggo Laraba ta fito fili tana cike da mamaki.

"Kai Amma... Masha Allah!"

"Wannan fa Jabeer ya y

i ƙoƙari sosai."

"Wai wannan lefe haka? Wannan kayan duk na amarya ne?"

"Subhanallah... Allah Ya ƙara masa arziki."

Da jin sunan Jabeer...

Kamar an tsayar da zuciyar Sidra.

Kunnuwanta suka fara

ɗ

aukar ƙara.

Duk abin da ake fa

ɗ

a ya daina shiga kunnuwanta

.

Kalmar guda

ɗ

aya ce kawai 9take ta amsa kuwwa.

"Jabeer..."

"Jabeer..."

"Jabeer..."

Idanunta suka cika da ƙƙ8hawaye nan take.

Lips

ɗ

inta suka fara rawa.

Ta ja baya daga window kamar wacce aka doka.

A hankali...

Ta juya.

Amma ƙafafunta sun kasa

ɗ

aukarta.

Jikinta ya yi sanyi tamkar an watsa mata ruwan ƙanƙara.

Da ƙyar ta kai bakin gadonta.

Da zarar ta zauna...

Sai duk ƙarfinta ya ƙare.

8Ta fa

ɗ

a kan gadon da ƙarfi.

Ta rungume filo tana fashewa da wani irin kuka mai ciwo.

"Haba.Ya Allah...ml

Me yake faruwa

ne?"

Ta fa

ɗ

a cikin sheshsheƙar kuka.

Hawaye suka fara zuba ba tare da tsayawa ba.

Ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta.

Zuciyarta na bugawa dalsauri.

Tana jin kamar duniya gaba

ɗ

aya ta tsaya.

A waje kuwa...

Ana ci gaba da dariya.

Ana ta taya juna murna.

Ana ta yabon kayan lefen.

Ita kuwa tana cikin

ɗ

akinta, tana kuka cikin shiru, zuciyarta cike da tsoro da ru

ɗ

ani, domin har yanzu ba wanda ya gaya mata abin da yake faruwa, amma kalaman Gwaggo Laraba sun riga sun huda zuciyarta fiye da kowace irin ƙiba. Ta

kasa hana kanta tunanin cewa watakila wannan lefen da ake ta yabawa shi ne zai sauya rayuwarta gaba

ɗ

aya.

*America/New York City*

A cikin babban master bedroom na gidan Ambassador Fahad da ke America, Nadra ta kasa samun sukuni.

Tun da ta gama wayar

da Umma take sanar da ita auren Sidra zuciyarta take bugawa da wani irin farin ciki da ba ta ta

ɓ

a ji ba. Ta yi ta zagaye cikin

ɗ

akin kamar ƙaramar yarinya da aka yi wa albishir da kyauta.

Sai ta tsaya gaban mirror, ta kalli kanta.Murmushi.

Ta sake yin w

ani murmushin.

"Alhamdulillah..." ta furta a hankali.

Ta

ɗ

ora hannu a ƙirjinta tana jin zuciyarta kamar za ta fito saboda tsananin farin ciki.

A zuciyarta kuwa tunani guda

ɗ

aya ne yake yawo.

"A ƙarshe dai Aunty Sidra za ta yi aure... Allah na gode maka

..."

Ta ƙarasa bakin window ta

ɗ

an bu

ɗ

e labulen, tana kallon dusar hasken rana da ke haskaka harabar gidan.

Har yanzu murmushin bai bar fuskarta ba.

Ta kasa zama.Ta kasa tsayawa.Ta sake komawa bakin gado ta zauna.

Daƙiƙa ka

ɗ

an.Sai kuma ta miƙe. Ta yi da

riya ita ka

ɗ

ai.

"Wallahi ba zan iya jira ba."

A daidai wannan lokacin ne ƙarar motar Fahad ta shiga harabar gidan.

Da jin ƙarar motar, Nadra ta zabura kamar wadda aka tsikara.

"Ya dawo!"

Da sauri ta gyara hijabinta sannan ta fito daga bedroom da gudu.

A falo kuwa...

Farida tana zaune kan doguwar kujera tana karanta wani littafi.

Nadra ta fito ma ba ta lura da ita ba. Hankalinta gaba

ɗ

aya yana kan ƙofar shiga.

Fahad ya bu

ɗ

e ƙofar ya shigo cikin kayan aikinsa, briefcase a hannunsa, murmushi

ɗ

auke a

fuskarsa saboda ya saba ganin matarsa tana tararsa.Sai dai yaunBai gama rufe ƙofar ba.

Nadra ta ruga da gudu.

" Yaya Fahaaad!"

Kafin ya ankara...Ta fa

ɗ

a jikinsa ta rungume shi da ƙarfi.

Ya yi dariya.

"Lafiya kuwa, kada ki mana asarar babynmu.

Bai ji

ra amsa ba ya saki briefcase

ɗ

insa ƙasa sannan ya zagaye bayanta da hannayensa.

Da sauƙi ya

ɗ

aga ta cak daga ƙasa kamar ƙaramar yarinya.

Ta kwashe da dariya ta ce .

"Ka sauke ni..."

"Da farko ki gaya min me ya faru."

Ta girgiza kai tana ta dariya.

"W

allahi ba zan iya

ɓ

oyewa ba."

Ya

ɗ

an matse ta cikin kulawa.

"To fa

ɗ

a."

Ta kamo fuskarsa da hannayenta.

Idanunta na kyalli saboda farin ciki.

"Next week..."

Ta tsaya tana ƙoƙarin ƙara masa suspense.

Ya

ɗ

aga gira.

"Next week me?"

"Auren Aunty Sidra

ne!"

Idanunsa suka bu

ɗ

e.

"Da gaske?"

Ta gyada kai da sauri.

"Na rantse maka. Yanzu aka kira ni aka sanar da ni."

Fahad ya yi murmushi mai fa

ɗ

i ya ce .

"Alhamdulillah."

"Shi ya sa nake so..."

Ta

ɗ

an yi shiru.

"Gobe mu koma Najeriya."

Ya kalleta da

kulawa.

"Gobe?"

Jinjina kai ta yi tare da cewa

"Eh."

"Mu halarci bikin. Bayan an gama sai mu dawo America."

Ko daƙiƙa bai yi tunani ba ya yi murmushi tare da cewa.

"Shi ke nan."

Ta lumshe ido.

"Da gaske?"

"Duk yadda kika ce haka za mu yi."

Fari

n cikin Nadra ya ƙaru fiye da yadda yake.

Ta rungume shi sosai.

"Nagode mijina."

A gefe...

Farida ta daina karatun littafin da ke hannunta tun farko tana kallonsu cikin shiru.

Amma kalaman Fahad suka soka mata zuciya.

Ta ajiye littafin a hankali sann

an ta miƙe tsaye.

Fuskarta cike da

ɓ

acin rai.

"Haba Yaya Fahad."

Su biyun suka juya suka kalle ta.

Farida ta ci gaba da cewa

"Wannan ƙaramar yarinyar ce take juya rayuwarka kamar waina."

Nadra ta

ɗ

an ja baya cikin mamaki.

Farida kuwa ta cigaba da m

agana.

"Kai fa ka ce sai bayan watanni shida za ka je Najeriya."

Ta nuna Nadra da hannu.

"Amma da zarar wannan yarinyar ta fa

ɗ

i magana guda

ɗ

aya sai ka canja duk shirinka."

Falon ya yi tsit.

Murmushin Fahad ya

ɓ

ace.

Ya sauke Nadra a hankali ta tsaya

a gefensa.

Sai ya juya gaba

ɗ

aya yana kallon Farida idanunsa suka canja.

Murya a sanyaye amma cike da ƙarfi ya ce,

"Farida."

Ta ha

ɗ

iye yawu.

"Eh..."

"Ki saurare ni da kyau."

Ya

ɗ

an yi shiru sanan ya cigaba da magana a cikin gargadi

"Matar aure ba

ƙ

aramar yarinya ba ce."

Farida ta sunkuyar da kai.

Ya ci gaba.

"Ita ce matata."

"Abin da ya shafe ta yana shafe ni."

"Abin da zai faranta mata rai yana faranta mini rai."

Ya

ɗ

an matsa gabanta.

"Kuma daga yau..."

"Kada ki sake saka baki tsakanin ni

da matata."

Farida ta yi ƙoƙarin magana.

"Amma Yaya ni..."

Ya

ɗ

aga hannu ya dakatar da ita.

"A'a."

"Ki tsaya iya matsayin ki."

"Ba ruwanki da yadda nake tafiyar da gidana. Kada wannan ya sake faruwa."

Farida ta ji zuciyarta ta karyen ianunta suka ci

ka da hawaye Ta kasa cewa komai.

Nadra kuwa ta kasa

ɓ

oye murmushinta cikin tsantsar farin ciki ta sake zagaye wuyan Fahad da hannayenta.

Ta lamo a jikinsa kamar ƙaramar yarinya.

Ta

ɗ

ago tana kallonsa.

"Mijina..."

Ya amsa cikin taushi.

"Na'am."

"Ka k

ai ni

ɗ

aki."

Ya yi murmushi.

"Me ya sa?"

Ta yi dariya a hankali.

"Na gaji da wannan farin cikin."

Ta

ɗ

ora kanta a kafa

ɗ

arsa.

"Ka kwantar da ni... ka yi min tausa, na gaji."

Fahad ya yi murmushi yana girgiza kai.

"To Hajiya."

Ba tare da wata-wata b

a, ya kama hannunta cikin kulawa.

Su biyun suka nufi bedroom

ɗ

insu suna hira cikin annashuwa.Ƙofar

ɗ

akin ta rufe a bayansu.

A falon kuwa.Farida ta tsaya ita ka

ɗ

ai.

Hawayen da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login