Showing 12001 words to 15000 words out of 191594 words
sa ita ma ta bu
ɗ
e murfin motar ta fita.
A
baya take binsa har zuwa cikin super market
ɗ
in.
Bangaren turarruka da kayan kwalliya ya nufa da ita. Ta zabi wadanda take so sannan kuma. Da ya ga ba ta diba da yawan ba ya sake
ɗ
ibar ma ta wasu. Sannan suka ke bangaren takalmin da jaka. Nan ma ta zabi
wadanda take so. Nan ma sai da ya sake kara ma ta wasu.
Sannan ya nufi bangaren kayan ƙwalama. Ta dauki su Ice cream da chocolate sannan suka nufi hanyar inda ake biyan kudi , bayan ya biya ne suka suka fito aka zuba ma su kayan a bayan motarsa.
Ya bude
murfin motar ya shiga, ita ma ta shigo.
"Kina da waya ne?"
"A'a ba na da waya."
"Okay Ina zuwa."
Yana fadar haka ne ya fita ya bar ta zaune a motar.
Bayan wani lokaci ya dawo hannunsa rike da wata ƙaramar leda.
Ya dora ma ta a saman cinyarta, bai yi
magana ba yayi wa motar key.
Ta duba jikin ledar ta gane kwallin waya ce.
"Na gode Allah ya saka da alkhairi ya kara nufi."
"Amin ya ALLAH."
Ya amsa yayin da yake hawa saman titin.
Ba wanda ya yi magana a cikin motar, sai sanyin ac da ƙamshin turare
nsa ke tashi. Dama shi ba mai yawan magana ba ne, ita kuma tana da baƙunta ba ta saurin sakewa da mutane.
Har suka iso gidan ba wanda ya yi magana, bai ce ma ta koma ba, sabanin Haidar dake yi ma ta hira lokaci zuwa lokaci.
Bayan sun yi parking motar ne
ya fito, ita ma ta fito. Wasu kayan ya rike ita kuma ta rike sauran suka shiga ciki
Suna shiga ciki suka fara jin ƙamshin girki tun daga falo. Safna ta zo da fara'a ta tarbe su.
"Oyoyo Sannu da zuwa Yaya."
"Sannu."
Ya amsa a takaice yayin da yake amsa
r kayan hannunsa.
Kallon Ma'eesha ta yi tana cewa
"Barka da zuwa Sis."
Murmushi ta yi tana cewa .
"Yauwa na gode."
Ɗ
akin Ma'eesha suka nufa da kayan. Duk da Ma'eesha ta so a nunawa Dada kayan. Safna ta ce ba sai an nuna ma ta na ta dai fada ma ta.
Ka
yan kwalliya da turarrukan suka jera a gaban dressing mirror.
"Bari na taya ki gyarawa duk da muna aiki kin san Gwaggon ku ta Abuja tana hanaya ita da yaranta. Sun ma kusa isowa a yadda muka yi wata da Saddiƙa take fa
ɗ
a mani."
"Ayya ko ita ce na ji ana c
ewa Dr za ta zo?"
"Eh ita ce, ranar firday babban Yaronta zai yi aure, kuma duka gidan nan za mu tafi ba wanda zai rage, a yadda Dada ke fada"
"Allah ya kai mu."
"Amin ya Allah."
"Bari na je na karasa aikin da nake taya su."
"Okay ba damuwa Allah ya
taimaka."
Tana ganin Safna ta fita sai dai ta zauna a bakin gadon. Take ta fara tunanin Jalaluddeen. Ta saka kuka tana jin zafi a zuciyarta.
Kusan Mintina talatin tana kuka, har idanunta sun kumbura. Sosai ta yi kakan da ke cike da takaicin abun da ya
yi ma ta tare da kishinsa da take ji a zuciyarta.
Dada ce ta shigo tana sallama.
Jin sautin kukan na jikarta ne ya sa hankalinta ya tashi .
"Na shiga uku me ya samu jikata ne? Ba tare da Kabeer kuka fita ba? Ina yake mara Mutunci shi ne ya bata ma ki
rai ko? Na san shi da bakin hali."
Ta yi maganar tana fita daga
ɗ
akin.
Tana shirin zuwa part din sa ta hadu da shi a hanya ..
"To me yarinyar nan ta yi ma ka ne ? Ko bakin halin ne ya tashi . To bari ka ji wallahi ba zan dauki wani ya bata mata rai ba.
Irin musgunawar da kake yi su Safna ka ce za ka yi ma ta wallahi ran kowa sai ya
ɓ
aci a gidan nan har da ubanka ba zan bari ba.
Shi kam har ga Allah bai san akan wa take magana ba, kuma baya son hatsaniya, don haka ya yi ficewarsa baya tare da ya tanka ma
ta ba. Yana gab da fita ya ji tana cewa
"Yarinyar da ba ta dade sa zuwa ba har ka fara saka ta gaba don Masifa."
Sai a lokacin ya san akan wa take yin magana.
Komawa ta yi cikin daki. Ma'eesha.
Zama ta yi bakin gadon tare da dafa kafa
ɗ
ar ta ta ce .
"Me ya faru ? Ko za ki iya fada mani abun da ka yi ma ki?"
,Goge hawayenta t yi tana tashi zaune
"Ba komai Dada,."
"Me ya sa kike kuma ke da Kabeer ne ko?"
"Wallahi bai Mani komai ba Yaya Kabeer, sai ma abun arziki da ya siya mani, ya shi siyayya sosa
i ya kashe Mani kudi da ya yi, Allah ya saka ma sa da alkhairi."
Horn din mota suka ji tare da bude gate
ɗ
in gidan.
Su Safna suka fita da sauri har da Barrister Haidar don tarbar Dr Fatima.
Nam Dada ta dinga rarrashinta akan ta fada ma ta damuwarta sam
ta ƙi.
Suna nan har Dr Fatima ta a shigo dakin ita da Saddiƙa da su Safna. Sadik da Ahmad na falo suna zaune .
Dr Fatima ta janyo Ma'eeha ta rungume ta tana sakin ajiyar zuciya.
"Daughter me ya sa kike kuka?"
"Ba komai ."
"A'a akwai komai ."
"Kin
Sanni?"
"Na ji labarin ki wajan Sister Safna"
"To Daughter ki daina kuka na ji labarin komai , duk da ina da uzuri dale n bar shi na zo don na ganki."
"Na gode Mom."
"Ba damuwa."
"Ya shirin biki an ce za ku yi biki?"
"Eh Yayanki ne zai yi aure."
"Al
lah ya sanya alkhairi."
"Ameen, kowa na gidsn nan zai so biki har da ke ko?"
"Eh zan zo."
"To why not mu tafi tare gobe, ke da su Safna."
"Eh zan bi ku."
Ta yi maganar tana kin kaunar Mom har cikin ranta.
"Dada zs mu tafi tare da su gobe jibin sai ku
zo tare da Hajiya Saratu."
"Eh dams tare za mu zo Sulaiman ne ya bari sai ranar
ɗ
aurin aure ."
Daga nan Mom ta ja hannunta suka nufi falo, in da duk jama'ar gidan kowa ya taru.
Kowa ya yi ta tambaya abun da ya samu Ma'eesha amma ta ce ba komai .
Don
haka suka bar ta tun da ta ki fa
ɗ
a.
A tare suka nufi dinnig area suka fara cin abinci.
Ma'eesha ba ta wani ci abinci ba, ganin an matsa ma ta akan cin abinci ya sa ta ci don dole.
"Yarinyar nan akwai damuwa a tattare da ita, idan ba damuwa kuma Kun amin
ce ina son zan tafi da Ma'eesha."
Shiru Ma'eesha ta yi yayin da Dada ta ce .
"Ban ƙi ta taki ba, amma idan kika tafi da ita ba, na amince ku tafi da Ma'eesha amma da zaran an gama biki ƙafa ta ƙafarta ba zan yi nisa da ita.
"Duk da hakan na gode ."
Dr
ta fada tana kallon Ma'eesha tana jin kaunar yarinyar.
"To sai ku tafi duk da sauran ƴan matan mu za mu zo daga baya ."
Cewar Dada kenan, sauran mutanen kowa ya amice.
Ma'eesha ta mike tsaye sakamakon yadda take ji kwana biyun nan.
Bin ta da kallo suka
yi ta nufi dakinta zuciyar ta na ma ta zafi .
Kafin ta shiga ne suka ji sautin '",Tim" cikin tashin hankali suka nufo ta inda ta fadi kwance.
*Maman Ihsan*✍
[7/4, 9:53 PM] Antysalima Grp: *MAKAHO NE*
_Book 2_
Na
Maman Ihsan ce✍
*JAJIRTATTU WRITE
RS ASSOCIATION*
*LITTAFINA NA KUƊI NE KADA KI KARANTA MANI LITTAFI BA TARE DA KIN BIYA NI KUƊINA BA. ZAKI TURA KUDIN KU NAIRA DUBU ƊAYA TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2242538358 ZAINAB ABDULLAHI UBA BANK. SANNAN A TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR.09065327995
Page9
️
⃣
2
️
⃣
Kafin ta shiga ne suka ji sautin "tim" cikin tashin hankali suka nufo ta i. Da ta fadi kwance.
Tana hankali. Kowa a tashe. Mom ce ta yi wa Saddiƙa alamar ta kama ta, ta taimaka ma ta sannan ya samu ko da suka samu suka kwantar da ita.
A ma
tsayin Mom na ƙwarsrriyar likita, ta duba Mai'eesha sannan
"Dan Allah ku yi hakuri kowa ya fita iuns bukatar kasancewa tare ke Daughter na."
Ba musu kowa ya bar
ɗ
akin aka bar ta tare da Ma'eesha.
_Nadra_
Suna zaune ita da Fahad a falon Aunty Rahama
.
Cikin takaici Anyy rmagana.
2
"Yanzu fisabil ta ta ya za'a ce ba su yi haka, a dauki zugegiyar budurwa a ce wai ta bi namiji har wata ƙasa? Wato yanzu na amince na bar shi kadai ko?"
"Eh haka ne, wai da su. so a ce mani mi ka
ɗ
ai ne za. Tafi sai ita Fa
risa kuma ta zuba ta a tare dai ita . Kuma na tabbatar da ceqqa wai ta suka 1 da ita dole ga sake yin wani photo."
Kallon Nadra ta yi sannan ta ce.
_
"Hakiks ban ji dadi. Tafiyar nan da zan'a yi yi tare da Farida. Na so a hana amma Mama ta de ba zai yiw
a a hana Farida zama a gidan Fahad ba, kamar yadda ba za'a hana Rumaisa ita ma zama a gidan nasa na ba. Saboda da Mama da Aunty Jima'i mahaifiyarmu ce. Yau ko bayan na ran Aunty Jumai Mama mai rike ma ta yara ne, yanzu ma abun da ya sa kiks ga na damu da i
ta akan tafiyar nan saboda na san cewa tana son Fahad har yanzu . Kuna ji in yafi da ihs ke ma
ɗ
an tayar da hankali. Sannan abu na biyu fa zan fada ma ki shi ne ki yi hakuri da Farida z ta yi wasu abubuwan amma kada ki sake ta wulakanta ki ko ta mutuncinki
domin ida.ln kika bar ta sai ta saka ki kuka. Sai kin shafa kwallin Rashin mutunci. Sannan kuma idan har kina ganin tana kokarin wuce iyakar ta a wajen mijin ki a duk lalokacin da ta yi yunkurin yin haka ta ku tabbatar ki nuna ma ta matsayinta. Duk da
na san ke ba za ki iya wannan fitsars da rashin kunyar nan ba sai dai ki yi shiru, to ta wanan bangaren ina son ki dauki halin Sidra ki yi amfani da shi akan Farida za ku fi zama daidai."
"To Aunty."
"Kai kuma na dawo gare ka."
Ta yi maganar tana kall
on Fahad.
"Ina jin ki Aunty."
Ka kiyaye abun da zai jawo ma ka matsala da matarka ta sanadiyar Farida. Ka san iya alƙar da za ka yi da ita. Don idan ka sakar ma ta fuska kai ma ka san sauran abun da zai iya biyo wa baya.
"In sha Allah."
Baby Zahrah ce
ta fito daga
ɗ
akinta tana wasa daTeddy
🧸
a hannunta. Nadra ta janyo yarinyar tana wasa da ita. Zaunar da ita ta yi bisa cinyarta ta miƙa mata chocolate daga cikin jakarta.
"Aunty ko za ki ba mu Baby Zahrah mu tafi da ita can. Ina son yara Aunty."
Nadra
ta yi maganar taba jiran jin me Aunty Rahama za ta ce.
Murmushi ta yi tana cewa .
"Ni, rufa ma ni asiri don Allah, Babansu ba zai yarda ba kar ki saka ya dawo garin nan ya ce sai na je na kar
ɓ
o ma sa ƴarsa. Allah ya ba ku naku.".
Marairaice fuska ta yi
kamar za ta yi kuks.
"Kin ha ba daga ni ba ne, Babansu ba zai yarda ba."
"Ba komai Allah ua ya raya ta."
"Amin ya kawo ma ki naki."
Da sauri Fahad ya ce .
"Amin Aunty kuma dozin za ta haifa ma ni."
Da sauri Nadra ta kalle shi kamar za ta yi kuka.
"
Tab wallahi ba na son haihuwa da yawa."
"Aiko ki shirya don ni ina son yara da yawa bibbiyu za ka haifa ma Ni."
"Hmmm Allah dai ya kawo ma su albarka."
"Amin ya Allah."
Ganin Aunty Rahama ta shiga kitchen ne ita ma ta bi bayanta don taya ta aiki.
A ta
re suka yi girkin, a falo suka zauna ba tare da sun je dinning table ba.
Da aka kira sallar azahar ne Fahad ya fita Masallaci ya ce Nadra ta yi sallah idan ya dawo za su tafi.
_Ma'eesha_
Tana kwance a gadonta kanta na saman cinyar Mom. Tana Mom tana
rarrashinta cikin hikima da dabara take yi ma ta wasu tambayoyi.
"Meke samun ƴata haka take shiga damuwa. Ba ki san ba na son damuwar Shaleleln Dada? Ga shi halin da kika shiga na damuwa da rashin cin abinci na neman zame ma ku ciwo. Yanzu ga shi jiri ne
ya
ɗ
ebe ki har kina yanke jiki kina fa
ɗ
uwa. Wanda ba don Allah ya taimaka ba da kin sami wani matsalar."
"Ba komai."
"A'a kar ki sake cewa ba komai, ki sanar dani a matsayin mahaifiyark ba matsayin yar ta ba. Ina son, ki dauke ni uwa ba Gwaggo ba."
"To
Mom."
"Kin san ba abun da ƴa za ta
ɓ
oue wa uwa ko?"
"Na sani."
"Fadi mani matsalar ki ina sauraron ki"
Shiru ta yi ba ta ce komai ba.
"Na san ba matsalar rabuwanki da gidan ba ne, don a yadda na ji labari ma ba dadin zama da su kika ji ba ballantana n
a ce kina so ki koma gidan ne. Sannan kuma na ji an ce mijin ki ya sake ki, ko kukan da samuwar na rabuwa da mijin ne, kina kuka don ya sake ki ne?"
"Ba komai Mom."
Dole ya hakura ta kyale ta don ba yadda za ta yi da ita .
"Yanzu yamma ya yi gobe da sa
fe za mu tashi, bari Safna ta zo ta taya ki zuba kayanki a trolly bag ko?"
"To Mom."
Saddiƙa ce ta yi sallama ta shigo da waya a hannunta tana mikawa Mom wayar.
"Mom Yaya J. ne yake kiran wayarki."
Ta yi maganar tana mikawa Mom wayar .
"Hello Jalal y
a kake ?"
Daga can bangaren kuma ya amsa .
"Na'am Mom Barka da yamma."
"Barka dai ya kake ya mutanen gidan ?"
"Suna lafiya ."
"Ya shirye-shirye?"
"Mom ni bs wani shirin da nake yi fa, don yanzu na gama fada ma ta ba wani shagalin da zan halarta, idan
aka daura aure shi kenan , idan suna so su yi walima amma ni ba wani dinner party ko wani abu da zan halarta ."
"Amma na ga sun tsara abubuwa da za su yi, idan ka yi haka ba za su ji dadi ba."
"Umma ba na jin sha'awar duk wani abu da za'ayi wallahi ba n
a, so auren ma ki nake kamar a fasa shi kowa ya huta."
"Kul! Kada ka fara ma wallahi, wanan ne karo na uku da ake niyyar bikin nan, kuma shi ma kana so ka lalata shi kamar yadda ka lalata na baya ko? To bari ka ji wallahi wanan karon idan ka kawo wani uzu
rin da aka fasa suke nan sai ka hadu da
ɓ
acin raina. Zan yi ma ka abun da ban taba yi ma ka ba. Meye matsalarka ne na farko na lalata na biyu ka lalata sanan wanan ma kana neman lalata shi , to bari ka ji idan ka lalata auren a wannnn karon wallahi sai na
ba ka mamaki. Kuna ko da bakaje ka halarci sauran event ba dole ne ka je ka halarci
ɗ
aya daga cikin ukun da ake shirya. Ni ma gobe da safe za mu dawo in sha Allah. Idan na dawo ina buƙatar ganinka ka zo ka same ni."
Daga haka ta ka katse kiran wayar tana
takaici na abubun da yake tsiro da shi wa da su na son lalata auren.
Miƙawa Saddiƙa wayar ta yi daidai lokacin da Sadik ya shigo da salama.
Gaban Mai'eesha sai da ya fadi sakamakon jin muryarsa da ta yi, sai ya yi mata kama da muryar Khalifa makaho ke
nan.
Zuciyarta ta ji tana bugawa da karfi tana tsalle kamar za ta faso ƙirjinta ta fito.
Satar kallonsa ta yi daidai lokacin da ta ji muryarsa yana cewa .
"Mom ya jikinta?"
"Da sauki, har da damuwa da ta saka wa kanta ."
",To Allah ya yaye mata."
"A
min ya Allah."
"Ƙanwata ya jikin naki?"
"Na ji sauki."
"To ki yi hakuri ki cire damuwa a zuciyarki, komis zai wuce kamar ba'ayi ba."
"To na gode."
"Ba komai ."
Daga haka ya fita daga cikin dakin.
Safna ta shigo dakin , Mom ta ce ta jera wa Ma'eeha k
ayanta a trolly bag.
*Washegari*
Da misalin ƙarfe bakwai na safe sun gama shirinsu na tafiya. Har da Ma'eesha da Safna da Jamila za su tafi, su Dada da Hajiya Saratu da Hajiya safiya sai sanar Alhamis za su zo tare da Haidar da Kabeer. Alhaji Sulaima
n kuma sai ranar Juma'a zai je wanda ranar ne za'a daura auren.
Har harabar gidan wajan motarsu aka raka su, Sadik ke zaune mazaunin direba. Sai Mom ta zauna a gefensa. Baya kuma Ma'eesha ce da Saddiƙa, sai Safna da Jamila.
Har suka bar gidan sanan ma s
u gidan suka koma ciki suna ma su addu'ar Allah ya sauke su lafiya .
*Maman Ihsan ce*✍
*MAKAHO NE*
_Book 2_
Na
Maman Ihsan ce✍
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFINA NA KUƊI NE KADA