Showing 27001 words to 30000 words out of 94381 words
daga lokacin da ya dawo daga karatu har zuwa ranar mutuwarsa, kuma a jikin kowacce takarda da hoto Ma'aruf ya zana tambarin × da jar marker alamun abinda yake nema bai
ɓ
ulle ga wannan hanyar ba, kusan hakan ne ma a jikin k
owacce takarda dake barbaje a
ɗ
akin har kuwa da wa
ɗ
anda aka yayyaga.
A wata durowa daga can ƙarshen
ɗ
akin ya shiga fito da duk takardun cikinta har hannunsa ya kai kan wani file daga can ƙasa.
A cikin file
ɗ
in tarin takardun Jamal ne wanda suka ha
ɗ
a da d
uk certificate dinsa na gama makaranta da kuma takardun
ɗ
aukarsa aiki a matsayin sabon ma'aikaci a kamfanin Baffa, takardun
ɗ
aukar aikin ya shiga bu
ɗ
awa
ɗ
aya bayan
ɗ
aya idanunsa na nazarin komai sai dai har yaje ƙarshensu bai ga komai
ɗ
in da yake nema ba,
ya zauna daga tsugunnen da yake, ya sake bin komai dalla-dalla, amma har a lokacin babu komai
ɗ
in.
Hannayensa duka biyu ya cusa cikin gashinsa yana fitar da iska ta hancinsa... Tunani da yawa ke tsere a cikin kansa, yana ji yadda yanayinsa ke ƙoƙarin canj
awa, ciwo na harbawa a cikin kansa yana gaya masa cewa zai koma halin da baidade da fitowa ba.
A lokacin ne kuma idanunsa suka hango masa wata ƴar mitsitsiyar takarda da alamun ta fa
ɗ
o daga cikin file
ɗ
in ne ba tare da ya kula ba, ya miƙa hannu da sauri y
a
ɗ
auko ta...
Rubutun Jamal ne, hanwriting
ɗ
in sa...
Mamaki ya kama shi tun kafin yafahimci me aka rubuta, don yasha bu
ɗ
e file
ɗ
in nan ya zazzage shi amma bai taba ganin takardar ba. Kuma mamakinsa bai karu ba sai da hankalinsa ya gane masa me Jamal
ɗ
in
ya rubuta a jiki.
Amina Sulaiman.
Gadon ƙaya.
***
Me kuke tunani ya ha
ɗ
a marigayi Jamal da Amina?
Me Hajiya Kilishi ke yi da magungunan Ma'aruf?
Me yasa Ma'aruf baya son hayaniyar yara?
Me Ma'aruf yake son cimma ne game da bincikensa?
Waye ya saka
kansa a takalmin Amina?
😅
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.
BABI NA SHIDA.
~~~~~~
Wani mai adaidaita sahu ya shigo layin har zuwa ƙofar wani gida mai baranda, kuma da tsayuwarsa Aminu ya fito daga ciki yana dariya alamun sun da
ɗ
e sun
a hira da saurayin dake jan adaidaita sahun wanda shima ya fito bayan ya kashe mashin
ɗ
in, kuma a tare suka kamo wani buhun shinkafa ƙato guda suka shiga kiciniyar shiga dashi cikin gidan, inda tin daga soro ƴar hayaniyar mutanen ciki zata shaida maka cewa
r an samu baki fiye da mutanen gidan.
A tsakar gidan Amma ce tare da ƴanuwanta su uku da suke uwa
ɗ
aya uba
ɗ
aya suke ta kiciniyar hada wasu kayayyaki a cikin kwalaye.
Yayarta mai suna Zahra'u da suke kira da Tanti wadda ke zaune a goron dutse ta kalli Am
man da ta fito daga kitchen riƙe da ƙaton tire
ɗ
in data yanko kankana tace.
"Ni kuwa Halima wai yarinyar nan kaya kala nawa ta
ɗ
inka a cikin lefen?"
Amma ta ajiye farantin hannunta a tsakiyarsu kafin tace.
"Ina ga kusan rabi ne, ai tun zuwan su Momi ƴar
gidan Kawu Mallam wancan satin suka
ɗ
iba suka kai mata wajen mai
ɗ
inkinsu, har da na fitar bikin."
Tanti ta gyada kanta tana fa
ɗ
in.
"Ko da naji, don na lura ita bata da wannan niyyar, a baki kawai Amina ta kar
ɓ
i zancen auren nan amma banda a al'amuranta
wallahi."
"Kinga ko jiya..." Ɗaya ƙanwar Amman mai suna Ma'u ta shigo zancen.
"... Abinda nake gaya mata kenan, nace tunda dai har ta amsa, ya kamata ta saki ranta tayi komai kamar kowacce amarya a haka ne zancen zai cigaba da rufuwa, komai ya tafi daid
ai."
Ɗ
ayar da take ƴar autarsu Safiya tace.
"Ai ce miki zata yi hankalinta a kwance yake, ba irin fa
ɗ
an da banyi mata ba wancan satin amma ƙiri-ƙiri ce min tayi ita ba abinda ke damunta."
"Allah ya kyauta, yaya kuka sake yi da ita Hajiya Kilishin? Yau
she za'a fara kai kayan ne? Ya kamata ma aje a ga wajen."
Aunty Zahra'u ta tambaya tana rufe ƙaton kwalin da ta gama tara ƴan ƙananun kayan kitchen a ciki.
Kuma tambayar ta dawowa da Amma tarin abubuwan da suka faru a cikin wucewar sati uku, yadda ka ran
ar da taje gidan Tantin a goron dutse, ta hau ta da fada bayan ta shaida mata komai, tace Uba yana da ikon za
ɓ
awa ƴarsa mijin aure don haka ita bata ga aibu a cikin zancen ba, tunda a yadda ta san Baba ta ba zai aurawa ƴarsa mara hankali ba kamar yadda Amm
an ta kira lamarin.
Don haka babu yadda ta iya dole ta ja bakinta tayi shiru, kuma kamar wasa al'amarin auren ya cigaba gudana bi da bi, a yanzu saura sati guda bikin, an kar
ɓ
i ku
ɗ
in aure hade da lefen da bai wani girgiza su ba kamar yadda take zato a gid
an Kawu mallam, sannan har sau biyu Hajiya Kilishi ta kira ta a waya tana shaida mata yadda wasu daga cikin al'amarin bikin zasu kasance a wajensu da kuma cewar gidan da za'a kai Aminan a cikin gidan da suke ne.
Sannan a jiya ta aiko da
ɗ
an aike ya kawo t
ulin wasu katinan
ɗ
an aure da ba su ko san yadda zasu yi dasu ba, don haka a dole ta kar
ɓ
i al'amarin itama suka fara shiri sosai, Baba yana ta fafutukar kayan katako da ƴan kudin hannunsa da kuma wanda yayyensa suka ha
ɗ
a masa, yayin da ita da ƴanuwanta mat
a ke iya nasu ƙoƙarin na kayan kitchen da kuma sauran na amfanin gida, wanda su Aunty Safiyan ke ta sintirin zuwa kasuwa tun wancan satin.
Sai da al'amarin ya kai duk da irin halin da zuciyoyinsu ke ciki, shirye-shirye a yanzu sun kama kamar dama sunyi ta
nadin lokacin. Don haka kafin ta bawa Tantin amsa su Aminu suka yi sallama a lokacin suna shigowa da buhun shinkafar nan.
"Yawwa master, nagode sosai..."
Cewar Aminun bayan sun jingine buhun shi da wani saurayi daya kamo masa, saurayin yayi waje yana fad
in babu komai yayin d shi kuma ya juyo ya kalli su Amma dake kallonsa suna jiran ba'asin abinda zai ce.
"Haba Amma ke ma fa kin san bana sata, Baba ne ya kira ni yanzu naje na kar
ɓ
o a wajensa."
Ya fa
ɗ
a cikin raha yana kallon Amman. Aunty Ma'u tace.
"Na
ga ranar da zaka yi al'amarin ka kai tsaye Aminu, in ma satar kake ai kowa ya san ba zaka kawo gida ba."
"Ameen wallahi..." Cewar Aunty Safiya.
"Amma da ƙyar ne canjawar Aminu, ai hali ZANEN DUTSE ne."
Ya ƙaraso ciki da dariyarsa yana shirin bu
ɗ
e babin
shafin tsokanar Aunty Safiyan da yafi rainawa, amma tun kafin ya zauna Amma ta katse shi.
"Zaka koma ne?" Ta tambaya.
"Eh yace in
ɗ
ebi kati in kai masa."
Kai tsaye ya bada amsar da a lokaci guda ta shiga kunnen Amina wadda ta fito daga
ɗ
akinsu a lokaci
n riƙe da tsintsiyar laushin da abin kwashe sharar data
ɗ
ebi abinci fal a ciki kasancewar Aunty Safiya da Aunty Ma'un duk sun zo da ƙananun ƴaƴansu, suna ta dabdala a
ɗ
akin.
Riga ce ƴar kanti a jikinta kalar ruwan toka da wani tsohon zanin atamfa da babu
mitar da Amma bata yi ba amma ta kasa rabuwa dashi saboda da
ɗ
in
ɗ
aurawarsa, sai ta bayar da sabuwar atamfa ma amma shi yana nan, Gashinta mai laushi yana ta fitowa ta saman
ɗ
ankwalinta dake zamewa.
Tayi wajen sharar ta zubar lokacin da su Amma suka cigaba
da zancensu, Aminu kuma ya dage wai sai sun yi cinikin sabuwar motar Aunty Safiyan da mijinta ya siya mata kwanakin baya kasancewar sa mai hali.
Sai ta juya ta koma
ɗ
akin a lokacin da wata ƴar Aunty Ma'u mai suna Yusra ke janyo kaya daga cikin drawer ta.
"Me kike nema anan Yusrah?"
Yarinyar ta juyo ta kalle ta.
"Hijabi Aunty Amina, Sallah zanyi."
"To ya zaki yi da hijabina, duka sun fiki tsawo... Kije
ɗ
akin Amma ki
ɗ
auko na Hafsa, me yasa ma baki bi su Hafsa aiken ba?"
Ta fa
ɗ
a sanin cewar Hafsan da ƴ
ar gidan Tanti da kuma
ɗ
aya yayar Yusran basu da
ɗ
e da fita siyan kayan miya ba. Adam ma tunda ya samu sa'ansa
ɗ
an gidan Tanti mai suna Mubarak suka fita filin ball shikenan sai an gansu kuma.
Ta tsugunna tana ƙoƙarin kwashe kayanta bayan fitar Yusran, yay
in da hayaniyar ƴan ƙananan yaran da suka
ɗ
ane katifar Hafsa suna doki ke shiga kunnenta, tunda satin nan ya kama komai ƙara gaya mata yake yi cewar sauran wasu ƙaiyadaddun kwanaki rayuwarta ta fara daga ga
ɓ
ar da zata ƙare.
Musamman wannan ha
ɗ
uwar ta ƴanu
wan Amman a gidansu, wani abu ne daban da basu saba ba don Tanti itace babba a cikin su Amman, don haka mafi yawanci a gidanta ake yawan ha
ɗ
uwa, ko da Sallah kowa can yake tafiya su ha
ɗ
u har su, shi yasa ganin yadda gidan nasu ya zama wajen ha
ɗ
uwa yanzu ya
na ƙara tabbatar mata cewa da gaske komai ke shirin faruwa, gashi Baba ma har ya fara aiko da tanadin abincin biki duk da Amma ta da
ɗ
e da kafa layin cewa ba wani taro za'ayi mai yawa ba, ko ƴanuwansu a can Niger tace duk a waya za'a shaida musu kawai, sai
dai idan maza zasu zo
ɗ
aurin aure don ya zama shaida a wajensu.
Wani abu ya wuce ta maƙogwaronta lokacin da idonta ya kai kan tulin katinan
ɗ
aurin auren nan, sunayen mutane takwas ne a jiki banda sauran bayanai, amma idan ta kalle shi ba abinda idonta ke
gani sai nata sunan dake ƙasan rubutun Ma'aruf Mansur Bakori, sunan da ko sau nawa zata maimaita shi sai ta ji bugawar zuciyarta a cikin allon ƙirjinta.
Ta rufe idanunta ta bu
ɗ
e tana jin yadda har yanzu zuciyarta ta kasa yarda cewa tana shirin bu
ɗ
e shafin
kaddarata ne da hannayenta. Ba lallai ne ya kashe ta kamar yadda ya rubuto a takardar nan ba ta sani, ya rubuta ne kawai don ya tsoratar da ita, amma hakan ba zai hana ta
ɗ
an
ɗ
ani gwargwadon azabar da ya tsara mata ba, tunda ta tankwabe garga
ɗ
in da yayi ma
ta.
Ta tuno shekaranjiya lokacin da Tanti ke tambayar Amma 'yaron kuwa yazo?' sai da ta ƙware da yawunta tsabar yadda tsoron hakan ya shige ta, ita har yanzu bata hango cewar in dai wannan Ma'aruf
ɗ
in da ta sani ne zata ganshi a kusa da ita ma balle ƙadda
ra ta ha
ɗ
a su. Gani take yi kamar za'ayi auren ne kawai a kaita wajen Hajiya Kilishin da sunanta ne ka
ɗ
ai ke yawo a gidansu game da auren. Shi yasa bata fatan kowa ma ya ambace shi, tafi son ayi dukkan abinda za'ayi a kaita
ɗ
in kawai, acan zata tsara matak
an da watakila zasu iya siyar mata lokaci kafin dukkan abinda zai faru ya faru har Amma tazo tace.
'Dama na gaya miki Amina'
Fatima ma tace.
'Me yasa kika yi tunanin zaki iya Amina?'
Maryam zata dinga da binta da kallo kawai, Aminu kuma zai iya cewa.
'Ko ba komai kin ƙoƙorta Amina.'
Baba ne kadai zai saka mata albarka ta sani, yayi mata addu'o'in da wataƙila zasu iya gyara rayuwarta a gaba, don ya san tayi komai ne don shi, don tallafar mutuncinsa.
Ta kai ƙarshen tunaninta lokacin da sallamar su Ummi
da Momi ta cika tsakar gidansu, taji su suna gaisawa dasu Amma har da muryoyin wasu daban don haka ta rufe wardrobe
ɗ
in ta juyo tana korar yaran zuwa waje. A lokacin Ummi ta
ɗ
age labulen
ɗ
akin ta shigo.
"To amaryar ƙulle, kina nan mu munje mun samawa ka
nmu mafita.."
Suka shigo suna ajiye ledojin hannayensu yayin da Momy ke cewa.
"Amina ruwa dan Allah, wallahi mun
ɗ
ebo rana."
Da murmushi ta fita zuwa kitchen ta
ɗ
auko jug
ɗ
insu na roba ha
ɗ
e da kofinansa ta
ɗ
ebo musu ruwa sannan ta dawo.
"Wai daga ina k
uke?" Muryarta a hankali ta tambaya tana ajiye musu ruwan.
Ummi ta miƙo mata ledar kusa da ita tace.
"Bu
ɗ
a ki ga."
Ta kar
ɓ
a kuwa ta shiga zaro wasu atamfofi masu kyau kalar ruwan hoda, (pink). Wani abu ya zarce ta maƙogwaronta, tun lokacin da aka kawo k
ayan lefen nan su Ummi suka san zancen auren, tunda suma sun san Hajiya Kilishin a matsayin ƴar uwarsu kawai dai tafi shiri da Baba ne duk a cikin si Kawu Mallam
ɗ
in, don haka sai rawar ƙafarsu ta ƙaru kamar me sanin cewar bikin irin wanda suke so ne.
"K
owacce dubu
ɗ
aya kenan da
ɗ
ari biyar, jikinsu mai kyau ne baza ki ta
ɓ
a cewa roba bace."
"Wai na meye?"
Momi tace.
"Har tambaya kike? To anko ne muka fito dashi tunda ke baki da niyya, kin san mu ƴan ayi sha'ani ne babu ta yadda za'ayi muyi biki lami ko
amaryar bata so."
Amina bata ce komai ba, Momi ta sake cewa.
"Ina Fatima? Ga guda
ɗ
aya nan ta Maryam mun siyo sai ta nunawa ƙawayenku ita, wanda yake da hali yayi tunda dai saura ƴan kwanaki, wa
ɗ
annan kuma ƙawayen mu ne su ma gashi sun siyo tasu."
Sai a
lokacin ta
ɗ
ago ta kalli ƙawayen nasu da murmushi a fuskarta tace.
"Allah ya saka da alkhairi, nagode." Ummi ta kalle ta tace.
"Su da ku
ɗ
insu kike musu godiya? Zo muje ni kiga wani abu."
Da haka ta ja ta suka fita daga
ɗ
akin, a tsakar gida su Amma duk
sun shige can
ɗ
akinta suna cigaba da ha
ɗ
a kayan dake ciki, sai Aminu kawai dake ta
ɗ
aga yaran nan sama suna dariya.
A ƙofar
ɗ
akin Baffa suka tsaya Ummin tace.
"Amina duk shiru-shirunki na san ba haka halaiyarki take ba, akwai wani abu game da auren nan d
a kike
ɓ
oye mana, kin sani ni da Momi ƴanuwanki ne kuma sa'aninki da zamu iya jin irin ciwonki, idan akwai matsala ki gaya mana, wallahi in zamu iya zamu taimake ki."
Amina ta ha
ɗ
iye wani abu, duk kau
ɗ
in su Ummi ta sani cewa suna da zuciya mai kyau a can
ƙ
asa, kuma ta sani cewa suna sonta fiye da yawanci daga cikin ƴan uwansu don haka zasu iya taimaka matan da komai, sai dai bata yi tunanin cewa Ummin zata iya ganin damuwarta sama da
ɗ
okin bikin da suke yi ba. Amma duk da haka ta san babu amfani sanin nasu
kamar yadda Baba ya shar'anta tun farko, musamman su biyun nan da ta san idan suka ji kamar ta saka lasifika ne a tsakar gidan Kawu mallam ta fa
ɗ
awa kowa. Don haka sai kawai ta girgiza kanta.
"Wallahi ba wani abu bane Ummi, kin san ban ta
ɓ
a kawowa kaina
aure a yanzu ba ne kawai, kuma sai komai yazo a lokaci guda shi yasa kawai nake jin wani iri."
Kamar Ummin bata yarda ba, amma bayan ta kalle ta na wasu sakanni sai ta gya
ɗ
a kanta tace.
"To ai shikenan, idan wannan ne da an kai ki sati
ɗ
aya na san zai ta
fi, don duk da ha
ɗ
a ku akayi ke bata wasa bace Amina, kuma duk yadda yake jin kansa na san zaki iya dashi....Wai yaushe zamu ganshi ne ma? Ya bamu ku
ɗ
in walima..."
Wai me yasa kowa yake son ganin sa? Me yasa kowa yake son jawo shi da baki? Basu san a lisa
fin tashin hankalinta wannan shi ne a sama ba? Jin bata ce komai ba yasa ta sake cewa.
"Ko da yake da alama kema ba wani ganinsa kike ba, masu kudin nan sai a hankali, amma dai na san zaku ha
ɗ
u kafin wani satin sai ki kar
ɓ
o a madadinmu, idan ba haka ba ku
ma ni zan kar
ɓ
i lambar wayarsa na tambaya da kaina."
Jin haka yasa tayi saurin girgiza kanta tace.
"Kar ki damu baza'a kai hakan ba ma."
Ina zata kai kanta idan har Ummi ta kira shi da wannan zancen? Ai ko a mummunan mafarki ta san wannan rashin sa'a ce
babba a rayuwarta. Ummin ta kalle ta sosai.
"Amina auren masu ku
ɗ
in nan fa dama ce da kuma rabo, ki saki jikinki ki ci ku
ɗ
in gayen nan son ranki, don baki san irinsa ba, ba lallai ne in kin shiga ma ya bu
ɗ
a miki ba."
A yanzu ta dawo Ummin data santa, ƙa
nwar ƴanmatan Kawu mallam me cike da buri, don haka sai kawai ta fa
ɗ
a
ɗ
a murmushin ta tana fadin.
"Toh shikenan."
Da haka suka koma wajen su Momi, inda suka dasa hira su da ƙawayensu, hirar da taso tafiya da yawan tunanin zuciyarta, don hira suke har da d
ariyar