Showing 30001 words to 33000 words out of 94381 words

Chapter 11 - Farar Wuta Complete

da har ƙasa suke kaiwa wajen ƙyaƙyata ta, daga baya ta zubo musu abinci a ƙaton faranti suka zagaye shi su bakwai suka cinye tas, a lokacin su Tanti duk sun tafi kuma har Amma ta yaba da atamfar da suka siyo bayan an nuna mata.

Maryam ma ta dawo it

a da ƙawayenta da suka tafi gidan wata mata tambayar Beads

ɗ

in da zasu yi amfani dasu a bikin, kuma ganin atamfar murnarta ta ƙaru don tace tayi kalar beads

ɗ

in da ta bayar ayi mata na atamfar da Baba yayi musu na fitar bikin. Kallonta kawai Amina take don

ta lura ita mantawa ma take da zancen cewar ba auren da suke so za'ayi ba, don gabadaya ma ta manta da zancen saukarsu da suke ta shiri, yanzu bikin ne a gabanta don ko jiya tana jinta tana takurawa Aminu cewa ya ƙara mata ku

ɗ

i zata siyo kayan da zata yiw

a ƙawayenta 'takeaway'.

"Tun safe Fatee, tun

ɗ

azu nake ta kallon hanya, baku dawo da wuri bane?"

Ta fa

ɗ

a lokacin da Fatima ta shigo gidan da daddare, don tun safe tace mata zasu je bikin ƴaruwarsu.

Sai dai maimakon Fatiman tayi dariya kamar yadda ta za

ta sai kawai tace.

"Go slow ne wallahi ya rike mu a wajen Gandu."

Da haka ta juya ta gaishe da Amma dake yankewa Hafsa farce anan tsakar gidan sannan a lokaci guda ta jawo hannun Aminan dake jikin durum tana kokarin

ɗ

i

ɓ

an ruwa a buta suka yi soro.

"Amin

a dama wanda zaki aura da kika ce min

ɗ

anuwanku ne shine wani Ma'aruf Bakori wanda gidansu yake a sharada?"

Sai da gaban Amina ya fa

ɗ

i duk da bata san me zata ce ba, ta gyada kai tana kallonta da fararen idanunta da ake gani tar a cikin rashin hasken soro

n.

"Eh, baki gani a jikin katin? Me ya faru?"

"Bikin da muka je a sharada ne Amina, kuma a layin gidansu, ƙanwar amaryar ce take gaya min cewa ta san duka ƴan gidan kuma da gaske bashi da hankali."

Sai ta girgiza kanta.

"Su Baba fa sun gama duk bincike

nsu Fatee, har ganin sa ma sunyi, sun ce ciwon ba mai yawa bane, sun ce har aiki yake yi a kamfanin babansa, ba wai bashi da hankali bane gaba

ɗ

aya."

Fatima ta girgiza kanta.

"Amina baki san me tace min bane..."

Da sauri ta sunkuyar da kanta sannan ta sh

iga girgiza shi itama tana fa

ɗ

in.

"Mutane sun iya ya

ɗ

a irin wannan jita-jitar Fatee, ba yau aka fara ba, musamman a sha'anin aure..."

"Yana da wa sunansa Jamal?"

Fatiman ta katse ta, ba shiri ta

ɗ

ago ta kalle ta yayin da muryar Baba ta kwanakin baya ke

haskawa a cikin kanta, lokacin da Amma ke tambayarsa idan Ma'aruf ƙani ne a wajen wanda suka je bikinsa a shekarun baya.

'A'a, shine dai wanda kuka je auren nasa, ai ya rabu da matar ne daga baya. Wa

ɗ

aya yake dashi sunansa Jamal kuma ya rasu shekaru goma

da suka wuce...'

"Ya rasu shekaru goma da suka wuce ko?" Muryar Fatiman ta tambaya tana karashewa da tunaninta.

"Me ta fa

ɗ

a miki?" Bata san lokacin da bakinta yayi tambayar ba yayin da zuciyarta da abinda take tunanin ƙasusuwanta ne suka shiga rawa ba t

are da kwakwaran dalili ba.

"Shi ya kashe wan nasa Amina! Shi ya kashe Jamal

ɗ

in shekaru goma da suka wuce!"

****

"Kar ki

ɓ

ata min rai Saratu, don me Allah ya halicce ki a mace? Me zaki yi da ƙwaƙwalwar da ake cewa ko shai

ɗ

an na tsoron kaidin da zaki iy

a fitarwa ta cikinta?"

Muryar Hajiya Kilishi ta fa

ɗ

a cikin shirun

ɗ

akin yayin da wayarta ke kare a kunne. Ƙawarta da ta kira Saratun tayi ajiyar zuciya a cikin wayar kafin tace.

"Baza ki gane bane Kilishi, ba zaki gane yadda nake gaya miki cewa matar nan

ta addabe ni ba, shi yasa naje wajen malamin nan, amma gashi yanzun ma ku

ɗ

in da na zuba na neman tafiya a banza."

Wani murmushi ya su

ɓ

uce a fuskar Hajiya Kilishin yayin da fuskarta take fayau! Sai dai a cikin murmushin akwai wani

ɓ

ari na sirrin mafi yawa

n nasarorinta.

"Tsafi gaskiya ne Saratu, amma gaskiyar da bata

ɗ

orewa, kuma na sha gaya miki babu amfanin mallakar abinda ba zai

ɗ

ore ba, har wani ƙato a gefe ya isa ya magance miki matsalar da ke kike cikinta?

Sau nawa zan biya miki karatun nan ne? Shek

arata talatin a gidan nan kin sani amma babu rana

ɗ

aya da na taba takaws wajen wani malami da sunan taimako. Da yatsa

ɗ

aya nake juya kowa a gidan nan yadda nake so kuma kin san ko ƴanuwana da muke ciki

ɗ

aya su ma basu san wata fuskata bayan wadda Iyalan

g

idan nan suka sani ba. Shi yasa nake son ki gaya min meye amfanin bu

ɗ

e miki cikina da nake yi ke da Salamatu? Ba don mu taru akan bigire guda bane? To don me a yanzu zuciya zata ja ki ki kauce?"

Tambaya ce, amma Hajiya Saratun bata amsa ba, don ta san ha

lin Kilishin sarai, ranta ne ya

ɓ

aci amma har a cikin

ɓ

acin nata halayyar ta kan yi rinjaye a zuciyarta. Don haka tana jinta tayi ajiyar zuciya a cikin shirun sannan tace.

"Yanzu a ina kuka tsaya?"

"Yace ita zai mayar can Egypt

ɗ

in Kilishi, ni uwar garke

in zauna in kular masa da ƴaƴa."

Ta furta hakan tana furzar da wani irin huci da Hajiya Kilishin zata rantse tana jin zafinsa tun daga nan.

"Bi shi a hakan, kar ki sake ki nuna ranki ya

ɓ

aci, kiyi kwalliya ki tausasa muryarki, ki gaya masa za

ɓ

in da yayi

daidai ne, ya duba

ɗ

awainiyar yaranki ya taimake ki.

Sannan ki fa

ɗ

a

ɗ

a murmushin ki a gabanta itama, ki gaya mata ko da ke ya za

ɓ

a ba zaki bishi ba dama. Bayan haka kiyi mata

ɗ

awainiya a lokacin da zai gani, misali, samu yaji da irin su busashshen tattasa

i kice tunanin amfaninsu kika yi musu, don kwana biyu ne abincin can zai gundure su. Idan kin aikata hakan, ki kira ni sai mu

ɗ

ora."

"Kina ganin zan iya Kilishi? Ba kowa Allah ya halittawa irin zuciyarki ba fa?" Muryar Saratun ta tambaya

ɗ

auke da rauni d

a kuma wani irin tuƙuƙin dake cin ranta.

Sai ta sake wani guntun murmushin tana miƙewa tsaye kafin tace.

"Zuciyar da Allah ya halitta min nazo duniyar nan daban take da wadda nake da ita yanzu Saratu, ni da kaina na sami wannan zuciyar don haka kema ki t

ashi ki samarwa kanki abinda zai

ɗ

ore. Ki kira ni idan kin gama abinda na gada miki."

Da haka ta katse wayar tana mai taya kawar tata jin

ɗ

acin dake faruwa a rayuwarta, da ace tana da ikon juya zuciyar Saratu yadda taga dama, tayi rantsuwa a ciki wata day

a kacal zata gyara mata komai, ta samar mata fiye da ƴancin da take dashi a wajen mijin nata tun kafin sake aurensa.

Amma zuciya ce kowa da irin tasa duk yadda ka kai ga iyawa, wani a baki kawai zaka bashi labarin dukkan nasararka amma tasa zuciyarsa ba z

ata taba iya

ɗ

auka ba. Ƙawayenta biyu kenan a duniya Saratu da Salamatu, kuma bayan abotar tasu, tana zana su ne a cikin wasu mutane da suka taka muhimmiyar rawa a rayuwarta, suka yi mata amfanin da zata rantse ko uwar data kawo ta duniya bata yi mata ba a

wajenta, don haka su biyun ne kawai duk duniya kawai take iya bu

ɗ

ewa cikinta su ga ainihin kalolin da take

ɗ

auke dashi bayan farar fatar ta.

Matsalar guda

ɗ

aya ce a wajen kowannensu, zuciyar Saratu bata iya jajircewa abubuwa har tayi yaƙi da iyawarta kam

ar yadda ita kanta ta furta a yanzu, Salamatu kuma sun sha banban da abinda kowannensu ke wa kallon nasara, don ita yanzu ko aure bata dashi, tafi ganewa yawon kasuwanci ga manyan mutanen da zasu dinga bata ku

ɗ

in da suka fi ƙarfin kayan nata.

Ta ja tsaki

a hankali tana nufar ƙofar wardrobe

ɗ

in ta, yau ita ke da turakar Baffa, ta gama shiryawa tuntuni wayar Saratun ce ma ta tsaida ita, a cikin wardrobe din ta dauko wata baƙar ledar magani da kuma muƙullin

ɓ

angaren sannan ta nufi ƙofar

ɗ

akin ta bu

ɗ

e, ta bu

ɗ

e ta sanda hayaniya ta cika kunnenta, hayaniyar da a yanzu kullum cikinta suke saboda ƙaratowar bikin.

Mutane ne kawai ke zuwa musu Allah sanya alkhairi tun yanzu, musamman daga

ɓ

angaren ƴanuwan su Baffan na can ƙauye, masu kwana ma babu adadinsu don

wasu

tun wancan satin suka taho ma da zugarsu wai sun zo taya aiki, aikin da kullum sai anyi musu bayanin babu shi.

Don daga harkar jere har harkar abincin da za'aci lokacin bikin da duk wata hidima, ku

ɗ

i suka biya a dunƙule wa mutane daban-daban da zasu

ɗ

auk

i nauyin hakan.

Kamfanika biyu na interior decoration suka biya don su yi jeran gidajen amaren, kawai ƴanuwanta dana Hajiya Maimuna ne ke zuwa su sa ido akan aikin don a hada har da tunanin mata komai ya tafi daidai, don haka su

ɗ

in da suka zo, ba abinda

suke ma illa ƙara aikin, don in banda ci su da ƴaƴansu ba abinda suke yini suna yi, dadinta

ɗ

aya kawai basu barwa ma'aikatan gidan komai ba dasu ake girkin da duk wani aikin da ya taso, shi yasa ba wanda ya kai Inna Danejo murna a gidan yanzu ganin duk ind

a ta juya kawai ƴanuwanta take gani.

Surayya ta fara gani a falon tana danne-danne a wayarta kafin dandazon matan da ke ta fitar da kaya daga kitchen suna yin waje.

Ta wuce Surayyan da bata ko dago ba zuwa tsakiyar falon inda suka fara ganinta.

"Hajiya

sannu da fitowa."

Wajen mutum biyar dake rike da wasu manyan fanteku tun na aurenta suka fada.

"Yawwa, wa

ɗ

annan kayan fa? Ina za'a kai su?"

"Sameera ce tace a fita dasu waje Hajiya, na aikin cincin

ɗ

in da za'a fara ne."

"Cincin kuma? Ina ita Samiran ta

ke?"

Tana tambayar kuwa ta fito ita da wata sa'arta mai suna Khadija da take ƴar ƙanwar Hajiya Kilishin, suka fito suna jan ragowar wani buhun sukari da ya kusan kai kwata.

"Cincin

ɗ

in me ake yi shirin yi a gidan nan Samirah?"

Ta tambaya tana katse dar

iyar da suke yi ta kasa

ɗ

aukar buhun.

"Mama yara ne ke jin yunwa kafin a sauke abinci musamman da safe, shine nace bari ayi cincin sai ya dinga rage musu hanya."

Girgiza kanta kawai tayi tana kallonta, kowa da irin ƙaddararsa a rayuwa, ita tata ta abinci

ce, don duk da science take yi a makaranta, amma course

ɗ

in da take son yi a University shima

ɓ

angaren girki ne, (Nutrition and dietetics.)

"Allah ya baku sa'a, kafin ku fara ki kawowa Baffa abincinsa yanzu, can zan je."

Ta fa

ɗ

a sanda ta juya, a cikin z

uciyarta tana lissafin layin da zata saka Samiran daya danganci ra'ayinta nan da shekara guda idan ƙwarya ta fashe!

Sahla ta fito daga

ɗ

akinta a lokacin riƙe da labtop

ɗ

in Munaya tana sake gyara gilasan idonta.

"Mami dan Allah ki bani 1000 muyi subscript

ion, datar da muke streaming ta ƙare kuma Aunty Munaya tace mu kai mata labtop

ɗ

in wallahi ba zata sake siya mana ba."

"Kije

ɗ

aki, na ajiye wasu canji akan mirror ku

ɗ

auka."

Ta san ita da Zahra ne don kullum suna manne da juna, shi yasa bata san me zai f

aru dasu ba nan da shekara

ɗ

ayan nan.

Ta fita daga

ɓ

angaren zuwa harabar gidan kamar wata sarauniya, don duk

ɗ

aukacin mutane kowa tsugunnawa yake yana mata sannu da fitowa yayin take binsu da murmushin da zuciyarta ta wanke shi tsaf, ta tace shi kafin fit

owarsa. Kuma

ɓ

angaren Inna Danejo ta fara biyawa ta kai mata maganin cikin ledar nan, na ciwon ƙafa ne wanda Innan tace tana jin da

ɗ

insa saboda haka take sawa ana kawo mata duk wata.

Kuma bayan sun yi ƴar hira da sauran tsofaffin dake wajen da kuma tarin

albarkar da Innar ke sanya mata, ta fito zuwa

ɓ

angaren Baffa, kafin ta shiga ta

hango Munaya daga gefen

ɓ

angaren tana waya, sai gyara glasses

ɗ

inta take alamun tana sauraren wani abu, kuma fuskarta ka

ɗ

ai ta kalla ta san a rikice take tunda dama ita ko dogu

war magana akayi yanzu zata rikice tace bata gane ba, duk kuwa irin mahaukacin ƙoƙarin da take dashi a

ɓ

angaren karatu, don tun suna yara Jamal ke cewa Ma'aruf da Munaya sune Geniuses (masu kokarin)

ɗ

in gidan.

Zuciyarta ta cunkushe a lokaci guda da ambata

r sunan, shekaru goma kenan da shafewarsa a doron ƙasa, amma har yanzu yaƙi barin zukata su huta, don ƙaryane a gidan nan ance an shafe sati guda na kowanne wata ba'a samu wani ya ambace shi ba, hatta ita kuwa tunaninsa na yawan wulga mata a zuciya, ta ta

bbata da ace Jamal na raye har yanzu to da itace a bayan ƙasa, don ta da

ɗ

e da lissafa cewa shi da ita mutane ne da baza su taba rayuwa a lokaci guda cikin duniyar nan ba.

Ta zira muƙullin hannunta ta bu

ɗ

e bangaren ta shiga. Komai yana nan kamar yadda ta s

anshi, don dama

ɓ

angaren a suna yake na Baffan amma ita ke da iko da komai na cikinsa, me ta gayawa Saratu ne

ɗ

azu? Babu abinda ƙwaƙwalwar mace baza ta iya ba idan har ta saka kanta, ta tuno shekarun da ranta ke

ɓ

aci idan ta

ɗ

aga labulen

ɗ

akinta ta hango k

yakkyawar surar Hajiya Maimuna na shiga

ɓ

angaren Baffan, idan taci kwalliyar nan tata za'a shafe tsawon dare ana musu da wani cewa bata ajiye kamar Ma'aruf balle ma wanda yafi shi a duniya ba, kuma da tayi tunanin cewa bata don ganinta a wajen lokaci yayi

da zata bar mata bangaren ita ka

ɗ

ai, me ya faru yanzu?

Tayi wani guntun murmushi lokacin da take kunna turaren wuta a jikin burner, a lokacin kuma Samirah ta shigo riƙe da katon tray

ɗ

in dake shaƙe da kayan abincin da ita kadai ta san me ta dafa.

Ta ajiy

e su daga kasa kujerar da ta san nan ne wajen zaman Baffan sannan ta juya.

"Bana jin zan fito sai gobe kuma, kar ki da

ɗ

e a waje."

"To Mami." Cewar Samiran tana saurin fita, sai dai tana isa bakin kofar Hajiya Kilishin ta sake kiranta.

"Da gaske nake mik

i magana, kar ki wuce goma a wajen mutanen nan."

Kuma duk da ta amsa

ɗ

in sai da taga yadda ranta ya

ɗ

an

ɓ

aci kafin ta fita. Dole ne ma ta ƙara dagewa wajen kokarin fara

ɓ

anbare tarin abubuwa daga jikinsu, don komai ya kusa ƙarewa, wannan rayuwar ba dahir

ɗ

insu bace.

Fitar ta ke da wuya kuwa taji muryoyi daga wajen suna bin layin gaishe da Baffan da ta hango hasken fitilar motarsa da direba ya sauke shi ta labulen falon. Sai ta taho wajen kofar don ta bude, so take ya fara yin tozali da ita da kuma kwalliy

arta kafin wani abu ma na

ɗ

akin.

Sai dai kafin ta ƙarasa

ɗ

in wayar hannunta tayi ƙara, ya kalli lambar dake kiran ke shigowa kafin ta dauka, Kuma abin da muryar cikin wayar ta fa

ɗ

a tun kafin ta kai ga cewa komai, shi yayi sanadin da zuciyarta ta doka a ci

kin ƙirjinta sannan wayar ta zame daga cikin hannayenta ta fa

ɗ

i kasa ta tarwatse!

***

Hasken safiyar ya shigo ta tsakanin fararen labulen

ɗ

akin yana ratsowa har ciki zuwa kan gadon da shima komai a jikinsa fari ne, Rukayya ta motsa a cikin baccinta tana

ƙara binne kanta a cikin filon amma tasirin wasu dogwayen yatsu dake shiga cikin gashinta suka hana baccin nata cigaba.

"J dan Allah mana.."

Muryarta ta fito a can kasan numfashinta.

Jawad

ɗ

in dake tsugunne a gaban gadon sanye da singlet fara ƙal da ku

ma wandon gogaggiyar shaddar daya sanya bayan ya fito daga wanka ya sake motsa yatsun nasa cikin gashinta yana matso da fuskarsa kusa da ita.

"Na gaya miki ina da meeting by 10 a Abuja, ko so kike in tafi in barki anan?"

Bata bude idanunta ba tace.

"And

what time is it now? (Kuma yanzu karfe nawa?)

"Eight tana dab da ƙarasawa, kamar yadda zuciyata take dab da shirin fashewa akanki."

Bata san lokacin da tayi dariya ba sannan ta bude idonta akansa.

"Sai yaushe zaka dawo?"

"Sai nayi kwanakin da kika yi

Paris."

Ta juya idanunta tana jin yadda yatsun nasa ke ƙara shiga cikin gashinta.

"Ka san bani da matsala ko zaka ninka kwanakin ne."

Ya gyada kansa a hankali.

"Na sani Barbie, na san ni zan haukace..."

Sai kuma yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login