Showing 90001 words to 93000 words out of 94381 words

Chapter 31 - Farar Wuta Complete

magana, kuma kayan jikinsa na T-shirt da gajeran wandon nan suka sake tuna mata da wanda ke jikinta itama, ba shiri ta hadiye wani yawu a maƙogwaronta tana jinjinawa kaddara, don in ba ƙaddarar ba ba zata tab

a hango kanta a irin wannan yanayin tare da wani namiji kuma dadin da

ɗ

awa a Hotel ba.

Ƙ

afafunta duka karasa a hankali har gabansa, ta tsaya daga gefensa sanda ya dago daga rubuta wani abu da yayi a jikin wata ƴar jotter yana kallonta, ya taimaka ya ture m

ata kayansa dake kan table din kafin ta ajiye plate din a hankali kusa da dayan sannan ta juya niyyar dauko ruwa wanda tun dazu ta ganshi a fridge din dake can gefe, amma sai kawai taji ya riƙo hannunta na hagu, dogwayen yatsunsa suka ratsa cikin nata yana

riko ta, a lokaci guda numfashinta ya katse a ƙirjinta yayin da yatsunta suka yi sanyi kalau!

Ya sake riƙo hannun nata sosai sannan ya jawo ta baya ta dawo gabansa, shi yana zaune ita kuma tana tsaye a gabansa da kafafunta duk a waje, ba shiri ta dunƙule

tafin kafarta akan sassanyan marbles din

ɗ

akin, sannan ta rufe idanunta a hankali tana jin yadda yake motsa yatsunsa a cikin nata.

Ta bu

ɗ

e su daidai sanda ya gama wayar, idonsa yana kan kafafunta ne da har yanzu ta rasa me yake gani a jikinsu, kuma kafin

ta gama tunanin hakan taji ya jawo ta zuwa kasa a hankali, ya durƙusar da ita a gabansa, dab dashi sosai wanda hakan yasa ta sunkuyar da idanunta ƙasa tana cije gefen lebbenta.

"Wata magana nake son muyi Please..."

Yadda muuryarsa a fito a hankali da ku

ma zurfi ya haddasa faduwa da saukar numfashinta.

"Zamu iya yi yanzu?"

Ya ƙara tambaya a lokacin da take kokarin tsayar da iska a kirjinta, da kyar ta daure ta daga kanta sau biyu babu kari. Shina ya gyada nasa kan a hankali yana cigaba da kallon fuskart

a.

"Na sani a yadda komai ya fara a tsakaninmu akwai tarin irin tunanin da kike yi akaina, na san an gaya miki tarin abubuwan da ba lallai ne na iya ƙaryata miki su ba, kinji wanene ni ta bangare da yawa na sani Amina, kuma har nima na bada gudunmawa waj

en saka miki wani tunanin akaina tun a wancan lokacin, wani

abu da nayi shi ne ba don komai ba sai don in hana faruwar auren a tsakanin mu."

Yayi shiru ya cigaba da kallon fuskarta, kuma ganin yanayinta bai canja ba yasa shi cigaba.

"I'm a mess Amina, ak

wai tarin abubuwan dake gabana kuma a tsakiyarsu ne na tsinci zancen aurenmu wanda ni tun bayan lokacin dana rabu da Ruƙayya ban kara tunanin cewa zan sake aure ba, abubuwa sunyi min yawan da bana son nauyin komai ya sake ƙaruwa akaina, saboda haka wannan

wasiƙar da na baki nayi ne don in tsorata ki ta hanyar da zai sa ki ƙi yarda sabida su Baffa baza su saurare ni ba a lokacin, abinda na manta a wannan lokacin shine ban isa in canja ƙaddarar da Allah ya hukunta ba tunda hakan babu abinda ya canja."

A wann

an lokacin numfashin dake ƙirjin Amina ya kasa tsayawa waje guda, sai kokari take dashi kamar kifin da ya fito daga rywa yana wutsil-wutsil, hasken fitukub dakin ya karu a idanunta yayin da wata iska ta shiga busuwa daga maka-makan windunan dskin kasancewa

r a sama suke.

"Daga ranar da na fara ganinki Amina, nayi nadamar abinda nayi, na san cewa ban kyauta ba da har na saka wannan tsoron da na gani a cikin idanunki, wanda duk da hakan kuma bai hana ki kyautata min ba, bai hana ki nuna min kirkin ki da kuma

halayenki na gari ba, kuma yanzu wannan kirkin naki nake kwa

ɗ

ayin cigaba da samu Amina, ina son nutsuwar da nake samu a wajenki don itace babban abinda nake bukata wajen tafiyar da rayuwata a yanzu, shi yasa nake rokonki da ki manta duk wani hasashe da kik

e yi kaina Please, ki bani damar da zamu yi normal life kamar yadda kowa yake yi, wallahi nayi alkawarin ba zan ta

ɓ

a cutar dake ba insha Allah."

"....Kamar yadda na fa

ɗ

a miki mafitar ta riga tazo hannunki Amina, Kilishi ta bude miki kofar samun nasarar da

ita kanta bata sani ba, so nake ki dauki dukkan maganganunta kiyi wa taki zuciyar ado dasu Amina, don takunta zaki bi, dukkan abinda ta fada kema shi zaki yi, banbancin da za'a samu tsakanin ke da ita shine, ke ita zaki yiwa Amina, ita zaki lullu

ɓ

e da rig

ar amincinki ba kowa ba, ita zaki zamewa farar wutar da ba zata ta

ɓ

a sanin cewa ƙonata kike yi ba.

Kuma hanyar farko da hakan zata kasance shine idan kika sami soyayyar mijinki..."

Kalaman da Amma na

ɗ

azu su suka biyo bayan dukkanin bayanin Ma'aruf a cik

in kan Amina, ta tuna yadda take kallon Amman cike da ƙarin bayanin da bata furta ba Amman ta cigaba.

"Kilishi ta gaya miki cewa soyayyar mijinta ta fara samu a saman ta kowa, shi ya fara yarda da ita kafin ta bu

ɗ

e zuciyar kowa ta fara aiwatar da manufart

a, idan baki sani ba yau ki sani Amina cewar taƙamar kowacce mace a duniyar zuciyar mijinta ce, idan taci riba anan to wallahi duk girman wata matsala koda kuwa ta mahaifiyarsa ce ta tsallake ta.

Yaron nan ya riga ya zama mijinki a yanzu ko munso ko bamu

so ba, don haka kije ki ƙara dagewa, ki dage wajen kyautata masa har zuciyarsa ta ƙara yarda dake akan yanzu, sannan da zarar kun koma kije wajen Kilishi ki tsugunna ki gaya mata cewar kin yarda da shara

ɗ

inta bama sai lokacin da ta gindaya miki yayi ba, ki

ƙasƙantar da kanki a gabanta ta sigar da ba zata taba iya haska cikin zuciyarki har tayi wani hasashe ba, wa

ɗ

annan sune matakan farko Amina, kuma ina tabbatar miki idan kika tsallake su, dukkan sauran zasu zo ne bi da bi kuma a sauƙake..."

Wa

ɗ

annan sune

kalaman dake saka sa hannyenta rawa a

ɗ

azu, sune kalaman Amman dake rikita lissafinta suna gaya mata cewar ba zata iya dorar da wani

abu akan Ma'aruf ba tunda bata gama sanin tunaninsa akanta ba... Sai gashi tun ba'aje koina ba hanyar farko tazo mata da sa

uki.

Allah ya amsa addu'ar ta, Ma'aruf ya cire dukkan wani kokwanton dake zuciyarta da wa

ɗ

annan iya kalaman nasa, a yanzu ta yarda cewa shi da gaske zuciyarsa wankakkiya ce akansa, abinda take ta taraddadi daga bangaren Hajiya Kilishi yake dama.

Taji yad

da mamaki ke cinye zuciyarta tun daga ƙasa, ashe komai ba mai wuya bane kamar yadda Amman tace, kowacce mace tana da irin nata ikon a hannu, kawai burga da barazana ce ke saka wasu yin ƙasa su yarda cewa an fisu su baza su iya ba, gashi tun basu ko bar gar

in nan ba ta fara samun yardar Ma'aruf a hannunta, idan haka ne kuwa ta yarda da maganar Amma na cewar da gaske Kilishi ta kiyaye su, don ko ita a yanzu tana jin ƙarfin gwiwar cewa zata iya.

Kuma cikin wata irin sa'a, sai ya ƙyale ta bai nemi amsarta ba h

ar suka kammala cin abincin da komai.

Wajen ƙarfe goma sha

ɗ

aya saura Amina ta dunkunkune a karshe gadon

ɗ

akin har a lokacin tana ta faman sake-sake a ranar, don ko ka ka

ɗ

an ba bacci take ji ba, abubuwan da ta fuskanta a yau suna da yawan da har yanzu bas

u gama narkewa a cikin ranta ba. Ta juya bayanta ne tana kallon

ɗ

aya gefen

ɗ

akin yayin da hannunta ke wasa da ƙarshen bakin mayafin nan data yafa a akanta.

A yanzu fitulun

ɗ

akin duka a kashe suke, Ma'aruf ya kashe su kafin ya shiga toilet don ta riga shi

kwanciya, sai da ya gama aikinsa tana kwance tana sake-sakenta sannan ya tashi ya kashe fitulun duka ya shiga toilet din.

A yanzu babu wani haske sai na waje da yake shigowa cikin

ɗ

akin, kuma wucewar minti biyar kawai sai kofar toilet din ta bu

ɗ

e, hasken

fitilar ciki ya ratsa duhun

ɗ

akin kuma duk da ta juya bayanta sai da hasken ya shiga idonta kafin taji ya rufe ƙofar duhun na sake dawowa.

Taji gadon ya motsa yana shaida mata hawowarsa zuwa daya gefen da sanda yaje jan sauran bargon da ta rufe ƙafafunta

dashi zuwa nasa jikin.

Sakan

ɗ

aya, biyu, suka wuce tana cigaba da wasa da mayafinta kafin taji muryarsa, can ƙasa a hankali kamar duhun daren.

"Amina..."

Ya kira sunanta kamar wannan ne karo na farko daya fara fa

ɗ

a, yadda tunaninta ya tsaya cak haka ma

daren ya tsaya, kamar shima yana jiran amsar da zata bayar ne.

Tayi kokarin ha

ɗ

iye wata busashshiyar iska a makogwaronta sannan tayi dauriyar amsawa a hankali.

"Can I hold you.. ?" (Zan iya riƙe ki?)

Bata san me take tunanin a wannan lokacin ba, bata sa

n ma me taje yi va ko kuma abinda yake faruwa a cikin kanta, ta san dai kawai zuciyarta ta ƙirga wucewar wasu sakanni ne data san cewa jiranta yake yi kafin duk wata dauriyarta ta rinjaye ta wajen

ɗ

aga kanta a hankali.

Kuma bata san ya akayi yaji ta ba, d

on a lokaci guda yasa hannunsa daya ya janyo ta zuwa jikinsa, ya juyo ta tana fuskantar sa yayin da hannunsa

ɗ

aya ya zagaye waist

ɗ

inta, sannan

ɗ

an ka

ɗ

an ya ratsa ƙafafunsa a tsakanin nata.

Ya hade ta da jikinsa har tana jin kara bugawar zuciyarsa kamar k

a

ɗ

awar igiyar ruwa a bakin teku wanda sautinsa ya ha

ɗ

e da amon tata zuciyar, ya zama idanunta basa ganin duhun daren sai wanda ke tsakaninsu kawai, numfashinsu ya hade waje guda yayin da ƙamshin turare da kuma sabuntar kayansu ya cika hancinta.

Kuma bai i

sa Ma'aruf ya gama rikita zuciyarta ba sai da ya sunkuyo da fuskarsa daidai cikin wuyanta ba shiri kuwa jikinta ya shiga girgizawa gaba

ɗ

aya a cikin nasa, kuma ga mamakinta sai taji yayi wani abu kamar murmushi sannan a cikin kunnenta ya furta maganar data

rikito da duniyarta baki

ɗ

aya ta rugurguje.

"Kar ki damu, not now, not here." (Ba yanzu ba, ba anan ba.)

Shikenan! Ma'aruf ya gama da rayuwarta!

***

Kano.

09:30Am

No. 58 Mafara Street, NNDC Shara

ɗ

a Quaters.

"Wai har kun dawo?"

Surayya ta fa

ɗ

a a loka

cin da ta fito dafa daki tana kallon Amina daje zaune a tsakiyar falon nasu tare da Sameerah wadda ta cika gabanta da kayan breakfast.

"Tun wajen ƙarfe takwas fa suka dawo. Yayan har ya tafi aiki ma." Sameerah ta bata amsa lokacin da take hada nata tea di

n.

"Auren ma'aikacin kamfani na da wuya ko?"

Surayyan ta fada tana kallon Amina lokacin da tazo ta zauna a kusa da ita tana

ɗ

aukan pillow

ɗ

in kujerar zuwa cinyarta.

Da murmushi a fuskar Amina tace.

"Gashi nan dai, ni ban saba ba har yanzu."

"Gaya min

zaki yi idan da wuya tun wuri in kori Tahir."

Kafin ta amsa Sameerah tace.

"Ki kore shi ma, don Wallahi Baffa yace ba wanda zai sake yiwa aure a gidan nan sai man da shekara biyar. Su Salma sun karya tattalin arzikinsa."

Dariya kawai Amina tayi tana kal

lonsu lokacin da musun da suka saba a kullum ya kaure tsakaninsu, don ma wai Munaya na can

ɓ

angarensu ne.

Sai dai duk yadda dariyar tata ta kai akan lebbenta kawai take, don daga can kasan zuciyarta taraddadi ne fal da kuma tunanin abinda ke shirin faruwa

.

Don kamar yadda Samirah ta fadawa Surayya ne, tun wajen karfe takwas da ƴan mintuna na safe suka iso garin Kano, don Ma'aruf ya gaya mata cewar yana da tarin aikin dake jiransa a office, kuma ya sauke ta a gida ne ya tafi bayan ya rungume ta yayi kissin

g saman kanta lokacin da suka shigo ciki ya bu

ɗ

e mata gidan da muƙullin dake jikin na motarsa, sannan ya juya ya barta tana kokarin hada zuciyarta waje guda ya koma wajen motar tasa da ya bari a waje.

Kuma shigarta gidan ya sake tsayar da zuciyarta waje g

uda, yana tuna mata da kalaman Amma.

"...da zarar kun koma kije wajen Kilishi ki tsugunna ki gaya mata cewar kin yarda da shara

ɗ

inta bama sai lokacin da ta gindaya miki yayi ba, ki ƙasƙantar da kanki a gabanta ta sigar da ba zata taba iya haska cikin zuci

yarki har tayi wani hasashe ba, wa

ɗ

annan sune matakan farko Amina, kuma ina tabbatar miki idan kika tsallake su, dukkan sauran zasu zo ne bi da bi kuma a sauƙake..."

Zuciyarta ta gaya mata cewa wannan lokacin shine zaiyi daidai da zuwanta wajen Hajiya Kil

ishin, don a yanzu ne zata yarda cewa da gaske zuciyarta ta wanku wajen yarda da ita. Shi yasa ta tattaro dukkan dauriyarta ta taho cikin gidan inda Sameerah ta shaida mata cewa Mamin tana wanka.

"Kin gama? Mamin tace tana jiranki a ciki."

Muryar Sameera

h ta dawo da ita zahiri, ta

ɗ

ago tana kallonta daga can jikin hanyar koridon dakin Mamin, ta san lokacin da Surayya ta tashi ta shiga ciki amma ita bata san lokacin da ita ta tashi ba, taji zuciyarta ta buga a cikin ƙirjinta amma kuma sai fuskar Amma ta gi

fta a idanunta ta kore hakan, ta gyara yafen

mayafinta sannan ta mike a hankali tana zagaye table din da Sameerah ta cika da kayan breakfast din, kafafunta suka taja cikin korido din lokacin da Sameerah ke gaya mata cewa ta tafi ta shiga wanka, kanta kawai

ta gyada mata kafin ta rike handle din kofar dakin.

Da dukkan addu'o'in da zata iya karantowa a zuciyarta ta tura kofar dakin, kuma kamshin turaren wutar da taji tunda ta shigo dakin shi ya fara shiga hancinta, ta hango shi kuwa yana ci daga can kan beds

ide drawer dakin daga cikin wata ha

ɗ

addiyar burner irin wadda Sameerah ta taba kai mata.

Sai taji ta shaki wata busashshiyar iska a makogwaronta lokacin da ta hango Mamin, tayi wankan kamar yadda aka fada ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa da aka b

aza mata stones tana ta kyalli, kamar ƙyallin dake son nunawa duniya cewa ita kadai ce Kilishi irinta.

Ƙ

afafunta suka karaso ciki da sallama, sallamar da Mamin ta amsa da murmushi a fuskarta, murmushin nan nata mai nauyin da sai a yanzu Amina ke jinsa a s

aman kafadunta.

"Ashe ƴan jigawan har sun dawo, yaya kuka tarar dashi Amina?"

Takaicin da ya taho ya taru a kirjinta wani abu ne da ba zata iya misalta shi ba, amma haka ta daurewa masa ta amsa.

"Jikinsa da sauki Mami."

Kuma sai da ta jira ta nemi baki

n gadonta ta zauna sannan kai tsaye muryarta ta sake fitowa.

"Mami na yarda da dukkan zancenki, na yarda zanyi dukkan abinda zaki sani ba tare da wani ya san komai ba, dan Allah kar ki sa a sake ta

ɓ

a kowa a cikin ƴanuwana, raunin dake jikin Aminu yayi yaw

a, dukkan kafafunsa biyu sun karye... Zanyi dukkan abinda kika ce da yanzu Mami don ni kaina ina son rayuwata ta inganta, na miƙo miki hannayena kamar yadda kika umarta don ba zan ta

ɓ

a yin kato

ɓ

arar yin ganganci da rayuwar iyayena da ƴanuwana ba, darajarsu

tafi komai a wajena."

Muryarta tayi shiru na wani lokaci sannan ta sake ratsa shirun

ɗ

akin amonta na rawa.

"Na rantse da ubangijin daya halicce ni Mami, zan yi miki biyayya kamar yadda kika umarta, baza ki ta

ɓ

a dana sanin bayyana miki sirrina ba insha A

llah."

A cikin

ɗ

akin wani irin shiru ya sake giftawa, irin shirun nan mai tsantsar zurfi, zurfin da a cikinsa zukata ke saƙa abubuwa da yawa, kamar yadda zuciyar Kilishi ke saka mata dubunnan abubuwa a wannan lokacin yayin kallon Amina take da dukkan irin

nazarin da ƙwaƙwalwarta ke iyawa, tana jin yadda a bayan kanta wasu kofofi ke bu

ɗ

ewa kuma tunaninta na nutsewa cikinsu na son gano wani abu daban sa

ɓ

anin abinda bakinta ke furtawa.

Sai dai duk iya kokarinta, ta kasa gano abinda yake saman fuskar Aminan,

a wannan lokacin, don tsoro da kuma rudanin da take gani karara suna fitowa tare da kalamanta, kuma takaicin yadda ubangiji ya biye sirrin kowacce zuciya ya kamata, don baza ta ta

ɓ

a yarda kai tsaye cewa yarinyar nan ta karbi tayin ta kai tsaye haka ba, amm

a da yake ita Kilishi ce, sai tayi gyaran murya a hankali sannan ta fa

ɗ

a

ɗ

a murmushin dake kan fuskarta, a kusa zata gane komai ba sai anje da nisa ba ta yiwa kanta wannan alƙawarin.

"Shi yasa na barku kuyi tafiyar nan dama Amina, don so nake kije ki ga

ɗ

a

nuwanki ki san cewa babu wasa a al'amarina kamar yadda na jaddada miki komai, kuma Alhamdlilah naji dadi sosai da idonki ya bu

ɗ

e kika fahimci gaskiya tun a yanzu, tun kafin mu shigo da wasu cikin lissafin."

Muryarta ta fito ne da wani irin sanyi kamar ƙan

ƙ

arar dake narkewa a cikin ruwa, Kuma da fa

ɗ

in hakan bata jira komai ba sai ta taso, ta wuce ta ta nufi wardrobe

ɗ

in dake dakin. Wajen da ta bude na farko ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login