Showing 3001 words to 6000 words out of 94381 words
kowa ne ya san cewa ba itace ta haife shi ba, Baba yasha gaya musu cewar ko gidan yaje baya iya banbance ƴaƴan ta dana uwargidan.
"Shinkafa da wake kuka yi? A zubo min dan Allah kafin yaron nan ya dawo."
Muryan Baban ta katse tunanin Amina daidai lokacin da Maryam a gefenta ta idar daga sallah, ta sake kallonsa ta cikin labulen sanda da yake cewa.
"Allah yasa Amina ta daka yajin nan nata mai da
ɗ
i."
A lokaci guda murmushi ya su
ɓ
uce a fuskarta, sai kawai
ta mike tana fa
ɗ
in.
"Akwai Baba, Bari in kawo maka."
***
Royal Brompton Hospital.
Sydney St, London SW3 6NP, United Kingdom.
...So I took your hand, back through lamp-lit streets,
I knew,
Everything led back to you
So can you see the stars over A
msterdam?
You're the song my heart is beating to...
Waƙar a hankali take fitowa daga cikin labtop
ɗ
in dake ajiye a wani
ɗ
an ƙaramin tebur da kujerarsa dake can jikin dogon windon
ɗ
akin,
ɗ
akin asibiti ne da banda gadon mara lafiyar da kuma tarin computers
ɗ
in gefe dake auna lafiyar wanda ke kwance, babu komai sai wata drawer daga can gefe wadda aka yi mata ado har da wasu ƴan fulawoyi,
ɗ
akin a gyare yake tas yana kuma ƙamshi mai da
ɗ
i, ga room heater dake fitar da wani
ɗ
umi mai da
ɗ
i sakamokon sanyin ƙanƙara
r snow
ɗ
in dake zuba daga waje.
A hankali idanun mara lafiyar dake kwance akan gadon suka bu
ɗ
e, kuma duk da lumshewar su girman su ya fito a lokaci guda, matashi ne mai siririyar fuska, yana da yalwar gashin kai da kuma na gira kamar yadda na idanunsa suk
e dogwaye ta yadda idan ka kalle shi zaka ga kamar baya iya bu
ɗ
e idanun nasa ne sosai.
Ya
ɗ
ago da hannunsa dake maƙale da allurar ruwan drip
ɗ
in gefe, ya kalli hannun tsawon wasu sakanni kafin yasa
ɗ
aya hannun nasa ya murza goshinsa alamun takaici, sannan
a lokaci guda ya fizge drip
ɗ
in daga jikinsa ya mike zaune,
jini ya shiga fitowa daga inda allurar ta fita amma bai ko bi ta kai ba ya kalli rigar dake jikinsa, rigar asibitin ce wadda ake bawa kowanne mara lafiya.
Ya shiga ƙarewa
ɗ
akin kallo a hankali h
ar zuwa kan drawer dake can gefe, a lokaci guda ƙwaƙwalwarsa ta tuna masa da jakar da Ishaq ya ajiye a ciki jiya don haka ya mike tsaye, jiri ya so
ɗ
aukarsa amma ya dage ya tsaya akan ƙafafunsa sannan ya isa ga drawer.
Ya bu
ɗ
e ciki ya fito da wata baƙar j
aka ya shiga fito da kayan ciki, ƙamshin turarensa na 'Dior Sauvage' shi ya tabbatar masa da cewar kayansa ne tun kafin ma ya gane su, kala biyu ne sai kuma wata ƙatuwar rigar sanyi wadda ke zuwa har gwiwa, bai yi tunanin komai ba ya shiga canjawa zuwa kay
an, sai da yazo
ɓ
alle ma
ɓ
allan rigar saman sannan ya kula da jinin dake fita daga hannunsa.
Don haka ya saka rigar asibitin da ya cire ya goge sannan ya
ɗ
ora daya rigar, ya kuma jawo rigar sanyin ya dora akai, bai ko
ɗ
auke rigar asibitin dake kasa ba ya s
aita facing Cap
ɗ
in da ya
ɗ
auko a ciki daidai fuskarsa sannan ya nufi hanyar kofar
ɗ
akin, ya san duka wayoyinsa basa nan kuma Ishaq bai bar tasa a gefen labtop
ɗ
in ba don haka ya nufi ƙofar ya bu
ɗ
e, dogon korido ne a wajen mai dauke da kofofin
ɗ
akuna da ku
ma mutane dake ta wucewa ta cikinsa, ya tabbata babu ma'aikatan da suka san shi a cikin wa
ɗ
anda ke wucewa don haka kansa tsaye ya bi ta cikin mutanen dake tafiya ya saje, yana mai nufar hanyar waje.
Iskar dake ka
ɗ
awa a wajen mai tsananin sanyi ta ratsa fu
skarsa sanda ya fito daga asibitin gaba
ɗ
aya, dare ne lokacin, ga fitulu a koina, na kan titi dana motoci, ga mutane birjik musamman na ƙafa sai faman wucewa suke.
Haka ƙofar asibitin take a kullum, tun daga shekarun da ya fara zuwansa har yau. Sanyi ya s
higa ratsa kunnuwan sa dake bu
ɗ
e sannan a lokaci guda yaji wata irin yunwa ta mamaye shi, sai kawai ya saka tafin hannayensa duka biyu ya gefen fuskarsa lokacin da idonsa ya sauka akan sunan wani kanti daga can tsallake, kantin da yake yawan yin siyayya du
k lokacin da yazo kasar.
"24 dollors." (Dubu goma.)
Baturen dake kan kantar ya fa
ɗ
a a lokacin da ya gama lissafa abubuwan daya
ɗ
ebo.
Ya kai hannunsa bayan aljihu kamar zai fito da wallet sai kuma ya dawo dashi, ya matso daidai jikin kantar yana kallon m
utumin yace.
"You know me right?" (Ka san ni ko?)
Kallon da mutumin yake masa yasa ya cigaba da cewa.
"I used to come around, from that hospital...(Ina yawan zuwa, daga wancan asibitin..)"
Ya juya ya nuna asibitin sannan ya dawo ga fuskar mutumin da ba
ta canja ba, sai kawai ya daga hannayen sa sama alamun sallamawa sannan yace.
"What I mean is my brother is coming to pick me from here... So do you mind If I just wait for him while I eat these? Because honestly I dont have anything with me right now but
I assure you he's going to pay when he arrive...."
(Abinda nake nufi shine
ɗ
an uwana zai zo yanzu ya dauke ni anan... so ba zaka damu ba idan naci wadannan kafin yazo, don bani da komai a jiki na yanzu amma ina tabbatar maka shi zai biya ka idan yazo...)
Mutumin ya saka hannunsa ya danne kayan da yake shirin
ɗ
iba, sannan da sautin muryarsa da yafi kauri a yanzu ya sake maimaita masa adadin kudin.
"24 dollors." (Dubu goma.)
Har ya haƙura ya
ɗ
auke hannunsa yana shirin juyawa sai kawai mutumin dake tsaye
a bayansa yace.
"You're holding up the line, man! If you can't pay just leave."
(Malam kana riƙe mana layi, idan baza ka iya biya ba ba ka bar wajen mana.)
A sakannin da mutumin ya rufe bakinsa, a sakannin wani irin naushi ya ziyarci fuskarsa, naushin d
a ya kusan kaishi har kasa, ya
ɗ
ago jini na fara zuba ta hancinsa lokacin da wata mata a gefensu ta ƙwalla ƙara shi kuma ya furta kalmar zagi yana share jinin, kuma baiyi wata-wata ba ya nufo kansa da nasa naushin shima dsya haddasa fada a tsakaninsu ba sh
iri, kuma kowannensu yaji lokacin da mai kantin ya kwalla ƙara yana fa
ɗ
in.
"Someone should call the police!" (Wani ya kira ƴan sanda!)
****
British Transport Police Station
No. 2 Melton St, London NW1 2BW, United Kingdom.
"Kun tabbata dukkan wa
ɗ
annan
bayanan file
ɗ
in gaskiya ne?"
Ɗ
an sandan ya tambaya daga tsallaken teburin da Ishaq ke zaune tare da wani ma'aikacin asibiti a gefensa.
"Da gaske muke ranka ya dade, mara lafiya ne ya fito ba tare da an sallame shi ba, kuma a yanzu haka ma ba'a hayyacins
a yake ba."
Ɗ
an sandan ya kalli ma'akacin asibitin da yayi magana, ya kara kallon ID Card
ɗ
insa da ya mika masa sannan ya gyada kansa yana sake kallon cikin file
ɗ
in.
"Naga dukkan wasu bayanai na cewar yana da matsalar kwakwalwa, amma banga wani bayani k
o sau daya na abinda ciwon ke saka shi ba..."
"Ai da yake yallabai, mu a asibiti cutar kawai muke bayani ba abinda zata haifar ba."
Jin haka yasa Ɗan sandan ya dawo da hankalinsa ga Ishaq dake zaune yana kallon can gefe inda aka ƙulle tarin mutane a cik
in wani budadden cell da aka zagaye da karafa kawai.
"Kai
ɗ
anuwansa ne ko? Zaka iya gaya mana abubuwan da yake yi, don mu san cewa ba da gangan yayi abinda muka kama shi yanzu ba?"
Ishaq ya gyara zamansa bayan ya dawo da hankalinsa nan, sannan cikin hars
hen turanci shima yace.
"Yayi abubuwa da yawa yalla
ɓ
ai, wa
ɗ
anda suka fi wannan ma, ba tun yanzu ba..."
"Misali..." Ɗan sandan ya katse shi. "Misali zaka bani ba wani bayani ba."
Jin haka yasa Ishaq ha
ɗ
iye yawu ba shiri, ya juya ya sake kallon idanun da
suke kallonsa daga cikin cell
ɗ
in sannan ya gyara zamansa ka
ɗ
an, muryarsa can kasa yace.
"Yallabai, a karo na ƙarshe da ciwonsa ya tashi saura ka
ɗ
an yayi kisan kai."
Idanun
ɗ
an sandan basu canja ba, ya cigaba da kallonsa na wasu sakanni kawai kafin ya gy
a
ɗ
a kai, sannan ya nuna file din dake hannunsa.
"Zan baku belinsa ne yanzu saboda wannan kawai, amma ku tabbatar bai sake barin asibitin nan ba sai da cikakkiyar lafiyarsa. Idan ba haka ba idan muka sake kama shi, mu zamu riƙe shi har sai ya warke."
Dukk
aninsu suka gyada kai alamun sun fahimta kafin ya juya ya kira wani
ɗ
an sanda dake ƙoƙarin wucewa.
"Stone! bring the Black one out." (Stone! Fito da baƙin cikinsu.)
Stone
ɗ
in baya bukatar wani karin bayani don wanda aka nuna masa shi ka
ɗ
ai ne baƙi a ciki
n tarin turawan cell din, don haka ya zaro muƙullai daga jikinsa ya nufi wajen.
Ɗ
an sandan ya sake kallon file
ɗ
in hannunsa a karo na ƙarshe, idanunsa suka sauka akan sunan dake rubuce a jiki.
Ma'aruf Mansour Bakori!
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#Fa
rarWuta.
BABI NA BIYU.
~~~~
"Kowanne
ɗ
an adam yana da tarin ƙalubale a rayuwarsa, amma ga wanda suke da cutar 'Bipola disoder' nasu ƙalubalen daban ne. Bipola disoder cutar ƙwaƙwalwa ce dake canja yanayin mutum a lokaci guda, ta canja ƙarfinsa, yanayin
tunaninsa har da
ɗ
abi'arsa. Cuta ce dake iya taba rayuwar mutum ta bangaren aikinsa, karatu, zamantakewa har ma ta iya dakushewa mutum hanyar cigaba a rayuwarsa, don tana yawan tashi ne akai-akai.
Cutar tana farawa ne daga lokacin ƙuruciya, kuma duk da c
ewar babu takamaimai maganinta ana samun saukinta ko kuma ƙaruwarta idan har ba'a bin ƙaidojin magani daidai. Tana da matakai hu
ɗ
u kuma na ƙarshen da ake kira da "Mania" shi yafi kowanne hatsari.
A matakin 'Mania' mara lafiya yana jin tsananin ƙarfi da ji
n cewa zai iya komai, da kuma tsananin fushi da yawan tunanin abubuwa barkatai, wanda ke jawo mutum ya harzuƙa ta yadda babu mai iyawa dashi, mara lafiyar yana samun ƙarancin bacci da kuma rashin nutsuwa sannan wasu ƙwaƙwalwar su tana bu
ɗ
ewa ta yadda za su
yi abinda idan a lafiyarsu ne baza su iya ba. Matakin dake bi wa wannan kuma shine 'HypoMania'...."
Duk wannan bayanin yana fitowa ne daga wata Tv dake kafe a saman harabar wajen, ƙaton wajen jira ne na asibiti inda tarin ma'aikata ke wucewa wajen wasu g
adaje daga can baya da aka kwantar da marasa lafiya, labulayen da aka sassaka a tsakanin kowanne gado sune kadai abinda ya raba gadajen.
Bayanin dake fitowa daga Tvn, na irin rashin lafiyar ƙwaƙwalwar da ake dubawa a wannan
ɓ
angaren asibitin ne, masu jira
n kuma na zaune suna saurarar bayanan da ake yi mai dauke da hotuna don sauƙin fahimta ga marasa lafiyar da kuma masu jinyar, Ishaq yana
ɗ
aya daga cikin masu jiran, yana zaune daga karshen kujerar kamar mai jiran ƙiris! Ya mike, kafarsa ta bangaren dama ya
ke faman bubbugawa yayin da gefen bakinsa yake a cije.
A bayyane yake ga duk wanda ya kalle shi cewa jira kawai yake likitocin dake tsaye a wajen gadon
ɗ
an'uwansa su fito daga bayan labulen da aka zagaye gadon dashi. Sun taru kusan su bakwai a ciki har da
Nurses don hankalinsu ya tashi jin cewar daga police station aka taho dashi bayan an neme shi an rasa.
Ya sani cewar dukkaninsu tsoro suke yi game da ciwonsa, don Ma'aruf ya riga ya kai mataki na karshe a ciwon ƙwaƙwalwar tasa, ya riga ya kƙure komai a B
ipolar Disoder, don idan har akwai wani mutum a duniya da baya taimakon kansa to Ma'aruf ne. A shekaru goma da cutar nan ta same shi babu irin fadi tashin da ba'ayi ba daga kowanne
ɓ
angare na iyaye da kuma ƴanuwansa amma rashin tasa tallafawar ya ha
ɓɓ
aka c
iwon har sai da ya ƙaraso matakin ƙarshe, 'Mania Stage'.
A baya bai fi ƴan awanni ko kwana
ɗ
aya zuwa biyu ba yake yi idan ciwon ya taso masa, amma a yanzu sati guda cur, har suka zo ƙasar nan Ma'aruf ba'a hankali sa yake ba, hakan yasa dole aka kwantar da
shi a asibitin da alluran bacci wanda suka taimaka, ya farka cikin hayyacinsa yanzu.
Don duk da cewar a police station suka je suka same shi, idanunsa kawai ya kalla ya san cewar ya dawo hayyacinsa tun kafin likitocin ma su gane, shi yasa ya matsu da fito
warsu a yanzu don yaje ya same shi, ya sauke maganganun dake
zuciyarsa tun daga ranar da Mami ta kira shi muryar ta na rawa taje ya taho gida Ma'aruf ya shigo musu da gawar wani.
Likitocin duka fito a daidai wannan lokacin, kuma bai tsaya jiran komai ba y
a zagaya ta
ɗ
aya hanyar da wandanda ba ma'aikata ba ke wucewa ya nufi wajen gadon.
"Minti biyar! minti biyar kawai na fita Ma'aruf amma kayi tsalle daga asibitin nan zuwa police station!"
Ya fa
ɗ
i hakan da harshen hausa daidai sanda ya banka
ɗ
a labulen da
aka zagaye gadon. Dama abinda Ma'aruf
ɗ
in yake jira kenan, ya riga ya sani cewar ya da
ɗ
e a waje yana ka
ɗ
a ƙafa yana jira likitocin su fita ya shigo da tarin ƙorafinsa, don haka hankalinsa a kwance ya
ɗ
ago da idanunsa ya kalle shi.
"Kaima sani bana iya rik
e yunwa, na tafi in samu abinda zanci ne and you left me with nothing, ba dole su kaini police station ba."
Ishaq ya girgiza kansa.
"Ma'aruf ba a Nigeria muke ba, ko baka gane bane da ka farka? me kake tunani idan suka kama ka a ƙasar nan?"
Maimakon ya
bashi amsa kai tsaye, sai ya koma da baya a jikin gadon, ya zura hannayensa duka biyu cikin gashin kansa sannan yace.
"Na sha gaya maka kana damuwa da yawa Ishaq, kana damuwa akan abubuwan da suke faruwa dama wanda basu zo ba."
"Kuma matsalar kenan, kai
da baka damuwar, baka damuwa da kanka balle kuma na kusa da kai, shi yasa har muka zo wannan matakin Ma'aruf! Mania!"
Ya fa
ɗ
i sunan mataki na karshe a cutar da Ma'aruf
ɗ
in ke fuskanta, kuma ga mamakinsa, a lokaci guda Ma'aruf
ɗ
in ya juyo ya kalle shi, san
nan a cikin sakan biyu idanunsa suka haska da wani abu da Ishaq
ɗ
in zai rantse da ubangijin dake busa musu numfashi cewar bai taba gani a idanunsa ba. Tsoro da kuma fargaba! Sai kawai ya girgiza kansa sannan ya cigaba da fa
ɗ
in.
"Shekara biyu da suka wuce
a asibitin nan ko HypoMania test
ɗ
inka basu kai ba, baka da lafiya amma babu wanda ya sani babu mai ganewa, muna
ɓ
oye komai daki-daki don rayuwarka ta tafi daidai. Amma yanzu ka gaya min me kayi kafin mu taho nan Ma'aruf? Daniel ka yiwa dukan da har ya sum
a akan baiyi maka submitting takardu a office ba, ka dake shi har ya suma Ma'aruf sannan ka sako shi a mota ka kaishi gida, ka shiga dashi har falon Baffa kana gaya masa wai ka kawo shi ya kore shi daga aiki!" (Mahaifinsa.)
Yanzu ka gaya min a duk kamfani
n Bakori da
ɗ
aukacin jama'ar da suka sanka, waye bai san kana fama da ciwon ƙwaƙwalwa ba Ma'aruf?
Yanzu ka gaya min a duk kamfanin Bakori da duk
ɗ
aukacin kewayen da mutane suka sanka, waye a yanzu bai san cewa kana fama da matsala a ƙwaƙwalwa ba? Waye bai
san cewa kana da wannan nakasar ba Ma'aruf?"
Muryar Ishaq
ɗ
agawa take a lokacin da yake fadar hakan, sautin ta na fitowa cike da wani irin daci da takaicin duk abubuwan da yake fa
ɗ
a din, kuma har a lokacin yana ganin adadin kifta idanun da Ma'aruf ke yi
alamun cewa kowacce kalma tana bada ma'anar da yake son ya gane a ƙwaƙwalwar sa. Bai ce komai ba ya cigaba.
"Ka san me ya fitar dani
ɗ
azu? Ka san abinda yasa na bar
ɗ
akin har kaje ka aikata abinda kayi?..."
Ya tambaya kamar yana jiran ya bashi amsa.
"..
. Office din likitan ka naje, shi ya kira ni personally Ma'aruf! Yayi min dukkan bayanin halin da kake ciki, kuma albishirin ka abinda kake so zai faru, idan komai
ya cigaba da kasancewa yadda yake tafiya kana gab da rasa hankalinka gaba
ɗ
aya Ma'aruf! Kana
gab da rasa komai gaba
ɗ
aya..."
"And so what idan na rasa?!"
Yadda Ma'aruf
ɗ
in ya katse shi a lokaci guda da tasa sautin muryar ya bashi mamakin da har sai da ya haska a idanunsa. Kallonsa yake har a lokacin da nasa idanun da suka canja, yanayinsu na kara
lumshewa kamar kodayaushe idan yana cikin
ɓ
acin rai.
"Nace sai me idan na rasa komai? Idan dai har ragowar lokacin