Showing 48001 words to 51000 words out of 94381 words
saba da sabuwar rayuwar da zaki fuskanta don itace rayuwarki ta yanzu d
ama ta gaba.
A kowanne aure akwai sirri Amina, ki riƙe sirrin gidanki ki riƙe sirrin sa, ki zauna lafiya kamar mahaifiyarki, kina ganinta dai shekaru fiye da ashirin kenan da muka kai ta daki amma daidai da rana guda bamu taba jin bakinta ba. Kiyi wa miji
nki biyayya, ki girmama shi, idan kika yi haka kema kin girmama kanki.
Mace mai wayo ita ke gina gidanta Amina, sakarya kuma da hannunta take rusa shi."
Don haka a yanzu ma da Aunty Ma'u ta fara sai taji kukan da ta sha
ɗ
azu ya sake dawo mata sabo. Fatim
a ta taho ta rungume ta daga tsaye tana gaya mata abinda kowa ke fa
ɗ
a, cewa tayi haƙuri, kuma sai su Ummi ma suka karaso suna tayaa ta, tanajin yadda kukan bata ke jijijiga jikinsu kafin Aunty Safiyya tasa su suyi gaba.
"Wannan shine dakin da muka kawo mi
ki kaya, watakila zaki ga sauran biyun dake gefe sun fi shi kyau, amma kiyi zamanki a cikinsa Amina, don shine mutuncinki."
Aunty Safiyya ta ra
ɗ
a mata a kunne lokacin da kowa ke mata sallama, kuma tana ji tana gani dukkaninsu suka tafi, tayi niyyar tasowa
suje ko wajen kofa ne amma mamansu Ummi ta hana, tace tayi zamanta kawai.
Ta dade a zaune tana kallon hannyenta bayan tafiyar tasu, ji take yi kamar an saka ta a wani jikin ne da ba nata ba, an ce komai nisan jifa kasa zai fa
ɗ
o, ta yarda da auren nan kam
ar wasa, zuciyarta na hango mata shi a can nesa sai
gashi tun ba'a je koina ba har anyi an gama, kowa ya taka rawarsa ya matsa, an bar mata filin da tace zata iya yakin a cikinsa.
Kamar wani yana kallonta da kyar ta
ɗ
ago idanunta tana karewa dakin kallo,
kayan cikinsa dama ta riga ta sansu, har gadon a waya Aminu ta nuna mata don tare suka je shi da Baban wajen masu kayan katakon, labulen kuma duk a tsakar gidansu akayi ta dagawa ranar da su Aunty Safiyya suka siyo daga kasuwa, carpet din da aka shimfida a
kasan gadon ma, a
ɗ
akinsu aka jingine shi.
Don haka ginin gidan da shine baƙo a wajenta take kallo,
ɗ
akin kato ne yasha fenti da kuma tsarin fitulun da ba sai an gaya mata ba ta san masu tsada ne. Ta tuno yadda taji su Ummi nata yabon sauran bangaren gid
an, ba shiri taji wani abu ya wuce ta makogwaronta, kowa ya sani cewar akwai dalilan da suka kawo ta wannan gidan, ba'a banza kamar ita zata sami irin wannan wajen ba, kowa ya sani cewa akwai wani abu daban a tare da auren nan, kawai kowa yayi shirun ne ya
na jiran ganin abinda zai biyo baya.
Tafi minti goma tana tunane-tunanen abinda zai iya faruwa da kuma mafita kala-kala, amma duk abinda ta kamo sai ya su
ɓ
uce idan ta tuna cewar a yau zata yi ido biyu da mutumin da aka daura mata aure dashi, mutumin da ya
riga yayi mata gargadin cewa kar ta yarda ta aure shi, zuciyarta ta sake matsewa kamar zata fashe zuwa wasu dubunnan ƙananan atoms.
Da kyar ta cillar da komai a cikin kanta ta miƙe ta nufi toilet din dake manne a dakin, kuma sai da numfashinta ya tsaya s
anda idonta ya kalli ciki, toilet ne da yasha adon wasu baƙaƙen marbles masu kyalli da santsi, anyi wasu hadaddun drawers a ciki da wani bakin katako da ya dace da kalar marbles din, ta ja numfashi a hankali sannan tayi addu'a ta taka kafarta ciki a hankal
i tana jin sanyinsa na ratsa ta.
A gaban katon mudubin ciki ta tsaya tana kallon yadda idanunta suka yi ja dama yadda fuskarta ta dan kumbura, sai kawai ta bude fanfon kasan sa tayi alwalarta, ta ha
ɗ
a da wanke wuyanta dama rabin bayanta, kuma dadin ruwan
yasa wata zuciyar tace mata taje ta
ɗ
auko sabulu a akwatin cosmetics
ɗ
in nan tayi wanka gaba
ɗ
aya amma ta girgiza kanta. Ba yau ba, ba yanzu ba.
A akwatin undies
ɗ
in nan da Maryam tace ta dauko hijabinta guda daya, ta dawo kan carpet din dakin tayi sallah
raka'a biyu, bayan ta idar ta dago da hannayenta da niyyar addu'a amma sai ta rasa ma me zata roƙa, saboda haka sai kawai ta dunƙule jikinta waje
ɗ
aya ta
ɗ
ora kanta daga gefen gadon tayi shiru.
Shirun da a cikinsa taji lokacin da aka bu
ɗ
e kofar dakin.
**
Karfe sha
ɗ
aya daidai ta iso da Ma'aruf ƙofar gidan, ginin ya tsaya a gabansa kamar wani tsauni, babu wanda zai ce ma a cikin gidansu aka fitar dashi, don gate dinsa yayi gefe da yawa ta daya bangaren. Ya lashe lebbensa na kasa daya bushe yana gayawa zuc
iyarsa cewa sun zo matakin da suke jira, sakon ya isa kuma maimakon ya dawo cike da kwarin gwiwa sai ya dawo da wani raunin da kalaman da Ishaq ya gaya masa a dazu suka yi sanadiyarsa.
"Ka sani cewa wannan ba labari bane Ma'aruf, ba labari ne da zaka rubu
ta a yadda kake so kuma har ka kai ƙarshe da son zuciyarka ba. Na fahimci dukkan abinda ka fa
ɗ
a da kuma dalilin da yasa ka dawo ka yarda da auren, amma hakan baya yana nufin cewa ka tsallakewa abinda zai iya faruwa ne.
Kar ka manta a baya ciwonka ko matak
in HypoMania bai kai ba abubuwan da suka faru suka faru, yanzu kana stage na karshe Ma'aruf, kai da kanka kana tsoron wannan matakin, ba sai ka gaya min ba, a idanunka kawai nake gane cewar kaima kana tsoron faruwar wani abu kamar yadda kayi tunani a farko
,
tunda ni da kai mun sani cewa ba lallai ne mu iya binne komai ba a wannan karon..."
Ya sake lashe le
ɓɓ
ensa yana jin yadda har a yanzu tasirin kalaman ke yawo a cikin kansa, gargadi Ishaq
ɗ
in yake yi masa ya sani, gargadin da shima ya riga yayi wa kansa
duk da cewa bai tsara komai game da auren ba bayan cewar yana son samun bayanansa daga yarinyar, zai tafi da abinda lokaci ya bashi ne kawai yana kuma ƙoƙarin kiyayewa dukkan abinda gaban zata haifar, haka ya gayawa Ishaq, ya kara gaya masa cewar shi yanzu
abubuwan dake gavansa ma Allah yayi yawa dasu, sai yaga komai ya lafa masa tukunna ma zai maida hankali kan yarinyar.
Ta cikin glass
ɗ
in motar ya hango ƙofar gate
ɗ
in shiga wajen su Mami dake can gefe, babu kowa a wajen alamun da gaske dare yayi don ya s
ani cewar an sha hidimar mutane tunda yau ne rana ta karshe a bikin.
Wayarsa ya jawo ya kira Mamin, bugu daya biyu, kuwa ta dauka tunda dama jiran isowar tasa take, har a hanya ta kira shi taji idan ya taho.
"Ma'aruf..." Muryarta dake shaida dimbin gajiy
a ta kira shi da sunansa.
"Mami na iso amma ba zan shigo ciki ba."
Sai da ta
ɗ
anyi shiru kafin muryarta tace.
"Kai da mutane ne?"
Ya girgiza kansa.
"Ko Ishaq ma nace yayi zaman sa kawai. I'm alone."
"Tohm shikenan da safe na ganka, dama bana son kayi
dare sosai baka iso bane, don tun wajen Isha'i suka ƙawo ta, anyi muku addu'o'i masu tarin yawa, hatta ƴan uwan Hajiya Maimuna da basu so abin da farko ba sun yaba sosai da ita da kuma ƴanuwanta Ma'aruf, Ina fatan Allah ya sanya dukkan alkhairinsa a zaman
da zaku yi, Allah ya baka ikon sauke sabon nauyin da ya hau kanka."
Bai san lokacin da ya ha
ɗ
iye wani abu a makogwaron sa ba kafin ya amsa a hankali, don ji yayi kamar itama tana tuna masa da abinda Ishaq ya fa
ɗ
a ne.
"Insha Allah Mami. Nagode."
Yaji ka
mar ta gyada kanta kafin ta sake cewa.
"Na san da wuya idan kaci wani abun, ga abinci nan ma nasa Samira ta tanadar maka tun dazu, a miƙo maka ne?"
Ya girgiza kansa tun kafin ma ta ƙarasa, don baya tunanin a yanzu ko ruwa zai iya sha, tarin abubuwan da ƙ
waƙwalwar sa da kuma zuciyarsa ke rabawa basu da adadin da har zai sami nutsuwa ta cikinsu.
Saboda haka sai kawai ya canja zancen da cewar.
"Na zata ma kowa yayi bacci Mami."
"Baccin mai gaskiya? Yanzun nan fa suka dawo daga kai sauran amaren, ai gidan
nan yana nan kamar rana don baka shigo daga ciki bane, kuma naku
ɓ
angaren ai yasha dab-dalarsa, sai da kayi haƙuri da abinda zaka gani."
Wani guntun murmushi da bai san dalilin sa baya su
ɓ
uce a gefen fuskarsa, don shi a yanzu baya son ganin yarinyar baya
jin akwai abinda ya dame shi na harkar auren, sai kawai ya zaro hannunsa daga cikin gashin nasa yana bude kofar motar dashi sannan yace.
"Shikenan Allah ya bamu alkhairi, Allah ya huta gajiya, ta amsa kafin ya kashe wayar. Ya tsaya daga wajen yana kallon
ginin gidan kafin ya sake komawa kan wayarsa ya danna wata number, bugu
ɗ
aya biyu matar dake
ɗ
aya layin ta dauka, kuma bayan sun gaisa ta tabbatar masa da cewar Hamida tayi bacci sannan ya katse wayar.
Inda ya kira
ɗ
in, wani Creche ne kamar asibiti inda a
ke bawa yara kulawa ta musamman, na wasu ƴan Turkey ne musulmai, amma akwai hausawa a cikin ma'aikatan nasu, asibitin da aka kwantar da Hamidan ne da farko suka bashi shawarar ya kawo ta wajen, kuma sai hakan yazo daidai da cewar bai shirya kaita gida a lo
kacin da ake hidimar bikin nan ba.
Ranar farko da suka je, tayi rigimar cewa ba zata zauna, amma cikin ƙwarewar aikinsu da kuma tarin abubuwan wajen dake kama zuciyar yaro, sai rigimar tata bata je ko'ina ba.
A iya kwanakin nan yana zuwa kullum ya ganta
wanda hakan yasa yayi sabo da ita sosai don har ta fara sakewa dashi tana amsa duk ƴan ƙananan tambayoyin da yake mata, da farko ne duk maganar da zai yi mata sai dai ta kalle shi kawai, sai bayan barinsu asibitin ne da ya kawo ta nan sannan ta fara yi mas
a magana, kuma ya fahimci tana da maganar sosai, kawai bata gama sabawa dashi bane har yanzu, amma ya san aƙalla suna making progress din da za'a zo gabar da zata fahimci cewa shi mahaifinta ne.
Ya sake kallon gidan, babu maigadi don haka shi ya shiga da
motar, sannan ya sake rufe gate din ya dawo, ƙafafunsa suka taka kan barandar gidan sannan ya tura ƙofar falon ya shiga a hankali.
Hasken fitulun
ɗ
akin ya shiga idanunsa tare da hotunan kayan da suke ciki, daga kujeru labulaye dama carpet
ɗ
in cikin komai
kalar Army green ne da kuma brown, babu wajen dining don haka kofofin korido biyu ne kawai da ya san
ɗ
aya ta kitchen ce
ɗ
aya kuma ta hanyar
ɗ
akuna, sai kawai ya juya a hankali ya rufe kofar falon.
Iskar da akeyi a waje mai zafi ce, yaji ta bayan ya fito d
aga Acn motarsa, amma a yanzu da ya shigo gidan yaga yadda labulayen falon ke dagawa sai yaji kamar ba irinsu
ɗ
aya da ta wajen ba. A hankali ya zame takalmansa daga kafarsa sannan yayi gaba, ya kuwa ji ƙurar da Mamin ke fada amma bai damu ba, ya shiga hany
ar koridon a lokacin da yake jin wani abu kamar bugun zuciyarsa na ƙoƙarin canjawa.
Ƙ
ofofi uku ne a ciki, kuma bai bu
ɗ
a kowacce ba don guda
ɗ
ayan dake gefe da kuma ta can karshe ta kasan kofofinsu ya kula duk fitulunsu a kashe suke, ta farko daga gefen d
aman sa ce kawai hasken cikinta ya saje da na cikin koridon.
Don haka kai tsaye ya ƙarasa gare ta ya
ɗ
ora hannunsa akan mariƙinta, sannan ya bu
ɗ
e ta a hankali ba tare da tayi wata ƙara ba, kuma babu wani hijabi idanunsa suka sauka akan matar da kowa ke ki
ra da tasa,
ɗ
an karamin frame
ɗ
in jikinta na na
ɗ
e a gefen gadon
ɗ
akin, ta jingina kanta da gefen gadon idanunta a rufe, rabin fuskarta na shigewa cikin gadon yayin da hasken fitilar
ɓ
angaren
ɗ
akin ya haske
ɗ
aya gefen fuskar tata.
Hijabin dake jikinta ne y
a shaida masa cewa sallah tayi, kuma kafin ya iya sake wani tunanin ta bu
ɗ
e idanuwanta duka biyun ta kalle shi.
Bai san me ya zata ba, bai san yadda yayi tunanin zai zo ya ganta ba, bai ta
ɓ
a ma hasko ta a cikin kansa ba balle ya kintaci yanayinta, amma a
lokaci guda yaji wani abu ya balle daga cikin zuciyarsa ganin ƙanƙantar ta, don duk a lissafinsa irin Ruƙayya zai gani, amma wannan ƙarama ce sosai, idanunta are so young haka ma jikinta ƙarami ne, yawun da ya sake ha
ɗ
iyewa yana kallonta yasa wannan karon
Adam's Apple dinsa motsawa sama da ƙasa. Kuma a lokaci guda kallon dake cikin idanunta ya canja zuwa wani abu kamar tsoro, yaga ta mike tsaye da sauri rike da hijabinta sannan ƙafafunta suka yi taku biyu baya, a yanzu ya tabbatar tsoratar tayi.
*
Lokacin
da ta mike tsaye tana kallonsa, zuciyarta ta shiga tseran kilomitoci a ƙirjinta, yayin da take jin ƙafafunta na rawa kamar ma zasu iya daukanta ba, don haka ba shiri zuciyar tata ta shiga ambaton kalaman Innalillahi har zuwa ƙarshe yayin da take cigaba ka
llonsa.
Bata yi tunanin kawai bude ido zata yi ta ganshi tsaye a gabanta ba, bata ma yi tunanin haka yake ba, yadda take hango shi a tunaninta ya zarta hakan, dogo ne sosai
ɗ
an siriri amma kuma mai cikar halitta, ba fari bane ko kadan haka nan ba baki ban
e, idanunsa na kallonta da wani yanayi da suke lumshewa, fuskarsa fayau yana tsaye yana kallonta daga bakin ƙofar, kayan jikinsa kalar ruwan toka ne mai irin sealed dinkin nan, babu ko hula akansa sai gashin kansa mai yawa da ya taru.
Zuciyarta ta cigaba
da fat, fat, tana kallonsa, so take yi ta tantance idan har shi
ɗ
in ne ma ko kuwa aljani, tunda bata ko ji sallamarsa ba, sai kuma wata zuciyar tace mata ta yaya mutumin dake shirin fara nuna mata wutar da ta kawo kanta zai fara da yi mata sallama?
Taji k
amar ta tafi ta shige toilet din dakin kawai ta kulle kanta, amma wani bangaren zuciyarta ya ture hakan, yana gaya mata cewa ya kamata ta jajirce ta fara ganin abinda zai yi tukunna, don ta gayawa zuciyarta zata iya yafi cikin carbi, kuma dukkan kalaman da
ta fa
ɗ
awa mahaifinta dama kowa suna nan a cikin kanta, don haka bai kamata ta fara karaya tun yanzu ba. Kuma ga mamakinta sai abinda take jira din ya faru.
"Assalamu alaikum." Muryarsa mai zurfi ce da a lokaci guda ta da
ɗ
a hargitsa tunaninta, tasa numfas
hinta katsewa a maƙogwaronta.
Ma'aruf ya sake lura cewa a tsorace take, don bayan yanayin fuskarta yana iya ganin yadda ta damke hijabin jikinta da duka hannayenta biyu tana cigaba da kallonsa, bata amsa sallamar ba, kamar ma bata ji yayi ba, kamar jira k
awai take yi yayi wani abu ta
ɓ
ace daga dakin.
Ya fitar da numfashin daga ƙofofin hancinsa, me ya zata dama ga yarinyar da yayi wa wannan barazanar, don haka ya sani cewar yanzu a farko dole ne yayi kokarin kore wannan tsoron nata game dashi, yasa ta fahi
mci cewa a yanzu ba abinda ke gabansa game da ita kenan ba.
"Ki kwantar da hankalinki, na shigo ne don kawai mu gaisa ki san cewar ba ke ka
ɗ
ai ce a gidan ba, idan akwai wani abu da kike bukata kuma zaki iya gaya min..."
Kalaman suka daki zuciyar Amina ta
yadda numfashinta ya tsaya cak! Wani abu a cikin kanta ya gaya mata cewar hatta lokaci sai da yayi shawara sau biyu kafin ya motsa. Kallonsa kawai take yi da tsananin mamakin da ta kasa auna shi a mizanin hankalinta.
Ya fahimci ba zata yi magana ba don h
aka ta ga ya sake riƙe hannun kofar sannan ya furta mata.
"Sai da safe."
Ya rufe ƙofar daidai lokacin da kafafunta suka kasa
ɗ
aukarta gaba
ɗ
aya.
**
Hasken safiyar dake shigowa ta liner labulen ne ya tada ita, ta kifta idanunta tana kallon yadda wajen ya
yi mata kyau a ido, yadda hasken ya ha
ɗ
e da kalar labulen dama liner yana ratsowa ta cikinsu, amma duk da kyan nasa sai taji kewar gida ta kamata, taji tana kewar
ɗ
akinsu har ma da katifarta don ba zata iya tuna rana ta ƙarshe da taje wani wajen ta kwana b
a tun bayan data gama makarantar Boarding fin da tayi.
Ta rufe idanunta ta bu
ɗ
e tana sake kallon windon wanda tsawon yadda take ganinsa yasa ta tuna cewa a ƙasa take, akan carpet din nan, don anan bacci ya dauke ta bayan zuciyarta ta cika da sake-saken al
'amarin da ta kasa ganewa.
Ba irin tunanin da bata yi ba da abinda bai zo kanta ba a jiyan nan, amma daga ƙarshe da ta tattara duk lissafinta da kuma abubuwan da aka gaya mata dama abinda ta shirya, sai taga cewar bata da wani za
ɓ
i illa