Showing 15001 words to 18000 words out of 94381 words
na zata iya daurewa ba don farin cikinsu.
"Baka ƙarasa zancen naka ba ai Mallam, baka gaya mata abinda yafi komai muhimmanci ba."
Kamar saukar ruwan sama a lokaci guda muryar Amman ta fa
ɗ
a, kuma a lokaci gudan Ami
na taji gabanta ya fa
ɗ
i, abu muhimmanci tace, kenan wani abu ne daban, wani abu da yafi girman abinda ya fa
ɗ
a, wani abu da wataƙila shine dalilin damuwar dake kan fuskar Amman da ma zuwansu gidan Kawu mallam a yau.
Taji Baba ya sake gyara zamansa sannan y
a kira sunanta.
"Amina..."
Ya kira kamar tayi nesa dashi, kuma ta san me hakan ke nufi saboda haka da sauri ta
ɗ
ago idanunta daga kan ƴan yatsunta ta kalle shi, ƙaguwar ya furta abinda zai fa
ɗ
a na haskawa tar a cikin idanunta.
"Kiyi hakuri Amina, amma s
un shaida min cewa yaron yana da matsalar ta
ɓ
in hankali!"
A daidai sanda ya rufe bakinsa, a daidai lokacin aka haska wata walƙiya har da tsawa a cikin
ɗ
akin!
***
A wannan daren....
Wajen ƙarfe tara saura a lokacin da wata mota ƙirar kamfanin 'Elantra'
ta shigo cikin layin, ƴan yara maza dake wasa akan hanya suka dinga darewa da gudu cikin wasansu suna bawa motar hanya kasancewar fa
ɗ
in layin ba zai yiwu ta wuce kuma suna wajen ba. Ko'ina yayi tar da wutar nepar da aka kawo don gaka ƙyallin sabubtar motar
haskawa kawai yake yi a idanun mutane kamar an shafe ta da maiƙo.
A cikin motar saurayin dake zaune a kujerar gefe mai suna Jamilu ya nuna ƙofar wani guda inda hasken jan kwai ke ci a samansa.
"Wancan ne gidan yalla
ɓ
ai, in dai gidan Alhaji Sulaiman
ɗ
in
daka kwatanta min ne to shine gidan."
Ma'aruf dake rike da sitiyarin motar a gefen sa ya gyada kai a hankali yana kallon ƙofar gidan shima.
"Nagode sosai kaji."
Saurayin ya washe baki.
"Ah haba yallabai ai ba wani abu wallahi. A sauka lafiya."
Ya fa
ɗ
i
hakan da tsantsar murna yana ƙara rike sababbin kudin da Ma'aruf
ɗ
in ya danka masa tun lokacin da ya shigo motar, a can farkon layin ya dauko shi, cikin dandazon wasu samari a inda ake sayar da rake. Kuma duk yadda ya kai ga kwatanta musu gidan Alhaji Sul
aiman
ɗ
in da yake nema, saurayin ne ka
ɗ
ai ya gane don haka ya roƙe shi yazo ya ƙarasa dashi.
Saurayin ya rufe ƙofar motar daidai lokacin da kira ya sake shigowa a wayarsa, tun dauko shi dama ake kiran wayar kuma daga nambobi biyu kawai Ishaq da Mami, yana
kallon yadda saurayin ma ke ta kallon wayar tun da ya shigo idanunsa na haskawa da mamakin cewa me yasa ba zai
ɗ
auki kiran ba.
Ya ƙyale wayar yayi gaba a hankali zuwa daidai kofar gidan da yake kallo ya tsayar da motar daga gefe sannan ya janyo ta.
"Ma'
aruf kana ina? Ina ka tafi?" Muryar ishaq ta fito a lokaci guda da ya amsa, sai ya koma da baya ya jingina kansa da kujerar motar sannan yayi murmushi.
"Kana magana kamar kana neman wani yaro
ɗ
an karami, sau dubu nawa a rayuwata na
ɗ
auki mota na fita da d
addare Ishaq?"
Yaji yadda Ishaq din ya fitar da numfashi cike da takaici.
"Wai ka haukace ne gabadaya Ma'aruf? Yanzun nan fa muka dawo ƙasar nan, minti biyar kawai kayi a gida kayi wanka ka fito! Yanzu ƙarfe nawa? Tara fa ta wuce, ta yaya zaka
ɗ
auki mota
ka fita a halin da kake ciki?"
Ya sanya
ɗ
aya hannunsa ya cusa yatsuntsa cikin gashinsa yana tuno abinda ya faru bayan barinsu Office
ɗ
in Daddyn, tsaf ya zayyanewa Ishaq abinda Daddyn ya shaida masa tun a hanya kafin su ƙarasa gida, kuma zai iya rantsewa
kamar yadda maganar ta tsorata shi haka ta daki Ishaq
ɗ
in shima, amma duk da haka ya boye ta hanyar gaya masa cewa ya kwantar da hankalinsa kawai insha Allah zasu daidaita komai a hankali, wasu maganganu da jinsu kawai yayi a lokacin da yake furtawar.
Don
suna shiga gida wanka kawai yayi ya shirya cikin wasu riga da wando duka kalar baki sannan ya dauki wata rigar mai hula (hood) da dogon hannu ita kalar ruwan toka ya dora akai, ya rufe kansa da hular amma duk da haka ana ganin sumar kansa data taru itama
baƙa wuluk da ita kamar kayan.
Lokacin da ya fito falo Ishaq ya shiga wanka shima, don haka wayarsa kawai ya dauka da muƙullin motar Ishaq
ɗ
in yayi waje, don shi tasa motar tana can gida ba'a dawo da ita ba tun ranar da al'amarin ya faru (lokacin da ya
ɗ
a
uko mutumin da yayi wa duka daga Office ya kaishi wajen Daddyn.)
Ya tabbata Ishaq yaji lokacin da maigadi ya bu
ɗ
e masa gate ya fita, don bai ko bar kan layinsu ba kiransa na farko ya shigo, amma bai dauka ba, sai da ya katse sannan ya lalubo nambar Sameer
a a cikin wayarsa ya kira. Sameera itace kusan komai na gidan nasu don itake kula da kusan harkar komai a gidan, shi yasa duk wanda zaiyi wani abu sai ya neme ta, saboda haka ya sani duk wani information in dai ya ta
ɓ
a ratsawa da gidan ba lallai ne taƙi sa
munsa ba.
Daddy ya gaya masa cewa mahaifin yarinyar da suke zancen zata shigo rayuwarsa
ɗ
an'uwan Mami ne kuma sunansa Alhaji Sulaiman.
Don haka kai tsaye bayan Sameeran ta gama murnar dawowarsa da kuma shaida masa cewar ai direban Hajiya Madinan da yayi
clear dashi kafin ya fito titi zai kawo musu abinci yanzu, sai ya tambaye ta.
"Waye Alhaji Sulaiman a ƴanuwan Mami?"
Shirunta ya nuna alamun tambayar ta bata mamaki amma duk da haka mamakin nata baiyi tsawo ba tace.
"Ko wanda yazo jiya? Ɗan'uwansu Haji
yar Mami ne, yana
ɗ
an zuwa dai ba sosai ba."
Ya cije gefen lebbensa kafin ya sake tambayarta.
"Da yazo jiyan me yayi?"
"Bai wani da
ɗ
e ba Yaya, Mallam Sani ma aka saka ya tafi dashi office
ɗ
in Daddy wai zasu yi magana."
Da jin haka ya tabbata shine wand
a yake nema don haka kai tsaye ya sake tambayarta.
"Kin san gidansa?"
"A'a, amma Mami tace a Gadon ƙaya yake wai wajen layin transformer."
Ya gyada kansa.
"Kin san sunan ƴaƴan sa?"
"Eh, Babbar dai kawai na sani sunanta Amina."
Ya riga ya gama samun a
binda yake so don haka ya gyada kansa kawai yana gode mata sannan ya kashe wayar, kwatancen daya kawo shi har kofar gidan kenan a yanzu.
"Ina Gadon ƙaya."
Ya bawa Ishaq amsa ta cikin wayar.
"Gadon ƙaya? Wajen wa? Me zaka yi?"
"Ni da kai mun sani cewa a
binda Daddy ke shirin ba ƙaramin hadari bane Ishaq, don haka zuwa nayi na warware komai tun kafin lokaci yaja da abinda ba zai taba faruwa ba."
"What?" Ƙarara mamaki da kuma fargaba suka fito daga muryar Ishaq
ɗ
in, kuma Ma'aruf zai rantse ya shiga girgiza
kansa lokacin da yake fa
ɗ
in.
"Kar kayi haka Ma'aruf dan Allah, ka juyo ka dawo. Zuwa wajen mutumin nan ba shine zai kwance komai ba..."
"Ba wajensa nazo ba don dashi da Daddy duk abu
ɗ
aya ne. Ita nazo gani Ishaq, saboda a yanzu maganar ta koma ni da ita
kawai."
"Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un... Ma'aruf me zaka yi?"
Salatin ya saka shi sake yin murmushi yana cije lebbensa.
"Nuna mata zanyi irin ramin da ake shirin jefa ta, nuna mata zanyi da gaske bani da hankali."
"B, tsaya kaji..."
Dib. Ya kat
se kiran ya ma kashe wayar gaba
ɗ
aya. Idonsa ya sake kallon ƙofar gidan yayin da zuciyarsa ke zana masa dukkan hotunan abinda zai faru kafin ya kashe motar ya fito.
Ya sake janyo hular rigar yana ƙara rufe fuskarsa daidai lokacin da wasu yara biyu mace da
namiji suka zo shiga gidan idanunsu akan shi da kuma motarsa. Da sauri ya yafito namijin alamun yazo.
Ya kuwa taho yayin da macen ta tsaya tana kallon su hannunta rike da wani abu da take ta lasa.
"Bigboy ya sunanka?" Amon muryarsa mai zurfi da taushi ya
tambaya sanda yaron ya ƙaraso.
"Adam."
Ya gyada kansa yana murmushi lokacin da ya zaro wata sabuwar
ɗ
ari biyar daga aljihunsa yana miƙo nasa.
"Idan ka shiga gidan nan Adam kace wai Amina tazo."
"Toh."
Ya amsa da nasa murmushin shima sannan ya juya, i
danunsa ko ka
ɗ
an bama su ga ku
ɗ
in da yake bashi ba.
Da murmushin da bai san dalilinsa ba Ma'aruf ya maida kudinsa cikin aljihu yana kallon tafiyarsu zuwa ciki, ƴar yarinyar har sai da sake juyowa ta kalle shi lokacin da Adam
ɗ
in yaja hannunta zuwa ciki.
A hankali ya dawo da fuskarsa kan katangar gidan, idanunsa na hasko masa dukkan abinda zai faru nan da mintunan dake shirin tahowa!
***
Me zai faru??
Me zai faru??
.
.
.
Me Ma'aruf zaiyi??
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.
BABI NA HUDU.
~~~~~
"Kiyi hakuri Amina, amma sun shaida min cewa yaron yana da matsalar ta
ɓ
in hankali!"
A daidai sanda ya rufe bakinsa, a daidai lokacin aka haska wata walƙiya har da tsawa a cikin
ɗ
akin! Kuma bayan walƙiyar ta
ɗ
auke a idanun Amina, Baba ya cigaba da
maganarsa.
"Wannan maganar ita ta sanya a safiyar yau dana shaidawa Kawu mallam dukkan abinda ya faru ya tara meeting din da ya sanya yinin mu a gidan, don har su Kawu Ibrahim da Kawu Hamza sun zo a yau..."
Ba shiri tasirin sunayen ya sanya Amina ta sak
e
ɗ
ago da idanunta ta kalli mahaifin nata, yayyen Baba hudu ne kuma shine ƙaraminsu, Daga Kawu mallam sai Kawu Abubakar da suke kira da 'Baban kurna' sai kuma Kawu Ibrahim da Kawu Hamzan da dukkansu biyun suke zaune a garin Abuja tare da iyalansu, don haka
bata san adadin mamakin da zata iya kiyastawa ba na cewar saboda maganarta Kawu mallam ya taso su a yau tun daga can suka zo, ganin yadda Babn ke kallonta yana son fassara yanayinta yasa ta maida idanunta ƙasa a hankali yayin da hannunta na dama ya kamo k
arshen skirt dinta da ƙarfi.
"Amina a jiya babu irin boren da mahaifiyarki bata yi min ba akan maganar nan, dukkan ku shaida ne cewa Halima mace ce mai biyayya gare ni, don tun daga ƙuruciyarku har yanzu babu ranar da
ɗ
ayanku zai ce kunji kanmu ni da ita
game da wani al'amari a gidan nan, duk abinda na fada ko nayi daidai ne a wajenta, amma a karo na farko jiya mahaifiyarki ta bijire min akan wannan hukuncin, tace bata yarda ba, tace ba ni kadai na haife ki ba itama tana da nata haƙƙin akanki don haka ba z
an siyar dake ga wasu mutane ba kamar yadda ta fassara al'amarin.
Kuma bayan zuwan su Kawu Ibrahim a yau sai suma duk suka goyi bayanta, da ni da Kawu mallam da Baban kurna Amina mune kadai muka hango wannan al'amarin ta fuskar alkhairi da kuma cigaban ki
wanda su basa gani. Don haka na
san a shekarunki da kuma hankalin yabzu zaki iya banbance daidai da akasinta, don haka muka yanke cewar matsayar tana gare ki yanzu, duk
ɓ
angaren da kika za
ɓ
a shi zai fi rinjaye kuma maganar ta zauna kenan har abada, kar ki
ga cewar na amsa musu acan, ki fa
ɗ
i ra'ayinki Amina babu wanda zai ta
ɓ
a ganin laifinki don rayuwar ki ce, mu duk ƴan kallo ne kawai.
Don haka kije kiyi tunani daga yau zuwa gobe, saboda idan har
ɓ
angaren mahaifiyarki kika
ɗ
auka, ina so ne muje mu sami mu
tanen tare da su Kawu Ibrahim kafin su koma kuma kafin wani abu ma daga
ɓ
angarensu yayi nisa. Kije kiyi tunani Amina."
Shikenan! Shikenan sai duk bayanin ya ƙare da wannan jimlar, lokaci kuma ya fara bugawa da adadin awannin da zasu tadda goben, goben da
Baba ta furta kamar tsawonta na shekara guda ne.
Taji lokacin da ya miƙe ya zo ya wuce ta, taji shi ya zura takalmansa daga waje sannan taji ƙarar takunsa na nufar hanyar soro, sai kawai ta rufe idanunta gaba
ɗ
aya tana hadiye wani abu da bata sanshi ba a m
aƙogwaron ta.
"Duk abinda mahaifinki ya fada haka ne ya faru Amina, kuma ba komai yasa nayi hakan ba sai don nemar miki ƴancinki..."
Da wani sassanyan amo muryar Amma ta maye gurbin ta Baban tun kafin ta bude idanunta
"... Ƴancinki nake nemar miki Amina
, don ni na hango abinda mahaifinki ya kasa ganowa, mutanen nan masu kudi ne da gaske, kuma duk tsananin kirkin mai ku
ɗ
i a zaune yake cewar baya taba son mu'amalar rayuwarsa da talaka kamar mu, zasu taimaka, zasu yi zumunci kamar yadda ita wannan Hajiya Ki
lishin ke yi amma aure Amina, aure babban abu ne da shine linzamin rayuwarka ta duniya har zuwa lahira, don haka kowa ya sani cewa hakan ba ƙaramin abu bane ga rayuwar mutum da zai ha
ɗ
a shi da kowa.
Da ke muka je auren wani
ɗ
ansu a shekarun baya da suka w
uce, kinga matar daya aura ai, kinga irin tarin dukiyar ubanta da danginsu, don ba a banza bahaushe ke cewa 'ƙwarya tabu ƙwarya ba... Kowa daidai dashi yake nema. Saboda haka Amina ko makaho yaji wannan zancen ya sani cewa mu ba daidai da mutanen nan muke
ba, sun nemi aurenki ne kawai don son zuciyarsu..."
Sai tayi shiru kamar tana kokarin ha
ɗ
ewa wani abu da ya taso mata ƙirji yayi sanadiyar canjawar muryarta.
"Amina, ciwon yaron nan na 'Hauka' ne na tabbata suka yi masa ado da matsalar ƙwaƙwalwa kawai, k
uma kin san wannan ba ƙaramar magana bace, kowa ya sani, su ma sun sani shi yasa basu tunkari kowa da wannan zancen ba sai mu, mu talakawa da aka mayar kamar ba mutane ba, mahaifinki dasu Kawu mallam suna ta danganta al'amari da ƙaddara, alhalin basu ƙara
binciken komai akan yaron nan ba, amma ni nace idan har ƙaddarar ce me yasa basu kai ta ga irin ƴaƴan masu kudin da
ɗ
aya
ɗ
an nasu ya aura ba? me yasa sai a yanzu ne irinmu zasu yi musu amfani... Na sha gaya miki masu ku
ɗ
i basa kallon kowa sai kansu, suna g
anin talaka kamar shi ya za
ɓ
awa kansa rayuwar sa, kamar dama Allah ya halitto shi ne kawai don ya kawar musu da matsalolinsu.
Rayuwarki zaki sadaukar musu idan har kika za
ɓ
i tafiya Amina, don aure ba karamar gwagwarmaya bace ko da mutum mai hankali kuma w
anda kake so balle babu duk biyun a naki, rayuwarki zaki sadaukar musu a banza, dukkan wani mafarki da burinki sai ya mutu wajen yi musu bautar da baza su san kina yi ba, don wannan sigar auren a wajensu, bata da banbanci da cewar siyen ki suka yi..."
Ta
sake yin shiru sakamakon yadda Aminar ta runtse ido da tasirin maganar, amma duk da haka sai ta cigaba.
"...Annabi yayi gaskiya da yace kudi sune masifar ƙarshen duniya, a karo na ba adadi wallahi na sake yarda da hakan, don ban ta
ɓ
a tunanin cewa mutum ka
mar mahaifinki zai iya fa
ɗ
awa cikin tarkonsu ba..."
Wannan karon kalaman suka daki zuciyar Amina da tasirin da yasa a lokaci guda ta
ɗ
ago ta kalle mahaifiyar tata tana girgiza kai. Ta sani dukkan abinda ta fa
ɗ
a gaskiya ne, amma ba ta yarda da wannan hasas
hen nata na ƙarshe ba, ba zata ta
ɓ
a yarda cewa ku
ɗ
i zasu rufewa Baba ido har ya mika ta ga inda zata cutu ba, haba mana! ta manta ne? Ta manta duk wannan tarin ƙaunar tasu dake tare dashi? Ta mata tarin sadaukarwar da yayi a rayuwarsa saboda su kawai?
Sa
i dai kallon da Amman ke mata yasa ta sake sunkuyar da kanta a hakali tana rufe idanunta da ƙwalla ta taru a cikinsu, dukkan maganganun da Amma ta fada gaskiya ne ta sani amma har a lokacin ta kasa gasgata zancenta na karshe don ta sani cewa ko da numfashi
nta na ƙarshe a duniya ne zata yarda cewa ba zai ta
ɓ
a mika
ɗ
ayansu ga inda zasu cutu ba... A kullum shi mai son gyara rayuwarsu ne.
Ta kai hannu tana share idanunta lokacin da Amman itama tace.
"Kije kiyi tunani zuwa goben Amina, ki auna kowanne
ɓ
angare
ki ga wanda yafi rinjaye, ni dai a matsayina na mahaifiyarki kuma mace kamar ki na gaya miki abinda nake ganin shine daidai"
Ta rufe bakinta daidai lokacin sallamar su Adam daga makarantar dare ta kwararo a tsakar gidan. Shi da Hafsa ne suka karaso har ci
kin dakin bayan sun duba falon da babu kowa, da sauri Amina ta saka bayan hannunta ta share hawayenta kafin su ƙaraso da hayaniyarsu.
"Amma kaina ciwo yake yi." Muryar Hafsan ta ambata tun kafin ta shigo
ɗ
akin da kalar ƙorafinta na kullum yayin da Adam sh
ima ya shiga ƙaryata ta.
"Amma wallahi makaranta ce bata son zuwa gobe ƙarya take yi, yanzun nan fa har kusan fa
ɗ
a fa suka yi ita da wasu a wajen ƴar tsohuwa, ba don nazo da wuri ba da ko kafi-kazan data siya ma baza ta samu ba."
Babu wanda ya lura da ya
nayin dakin a cikinsu sai